Showing 99001 words to 102000 words out of 295116 words

Chapter 34 - AUREN HUCE HAUSHI COMPLETE

canjin da aka saka Mana kinsan dai ni ba iya saka Kati zanyi a kasar Nan ba, pls Dan Allah k

i bude datar na ganki kona samu nutsuwa nayi aikin daya kawoni, naso ace kina gefena a wannan gurin Kinga dakina kuwa? da Hali gareni anan zamuyi honey moon irin Wanda naji su Habib suna fada idan ana hira ko Zaki biya ki taho ki sameni?"

Ido ta ware kamar

Yana kallonta.

"Na biyoka nayi maka menene?"

"Kiyi min abinda mace take yiwa mijinta ai kin gane?".

"Ya Salam haba Ya Mahmud menene haka kaifa yayana ne".

Wata dariya ce ta kubce Masa "A yaushe na zama Yayanki? Ki gyara zancen niba Yayanki bane, haka kawa

i ki haramta min abinda Allah ya halasta min idan Zaki Ware ki Dan ina dawowa labarin ze canza salo gara mu fuskanci juna ki tausaya min Kinga Sameer fa ya Zama Daddy madam dinsa ta haihu sunyi min takwara,ai gara muma mu zage dantse ko?"

Dokin haihuwar da

aka fada Mata ita ta Hana ta gane inda nasa zancen ya dosa, cikin nuna farin ciki tace "Dan Allah da gaske yaushe Fateehar ta haihu? Masha Allah! Allah ya Raya kace mu sai Kano ko Yaya?".

"Allah bakinki ya kiyayi fada min yayan Nan tsabar kinibibi kawai y

au Kika tashi dashi Wai wani Yaya kamar a kauye, kibar 'yan garinmu su Fadi Amma Banda ke wato Ni da yake ba Dan bokon kirki bane ba baza'ace min sweetie ba ko irin su my love ko Dear, saboda almajirin soro ne ni ko?"

"A'a wlh ni ban fada ba, kawai dai Nag

a abokin Ya Abdul Hakeem ne kai ai kaima yayan ne".

"To anki wayon, Kuma da kike cewa Zaki Kano ganin yaro keda wa zakuje kuma waye ze kaiki Kuma kice Mata wacece ke".

"Address zata turo min Mana, Kuma maganar kaiwa sai Malam Bala direba kaimu nida mujiba

wuni daya dai, Kuma nace Mata matar yaron mijinta ce ko ba haka ba?

"Yayi Kam Amma saina dawo ki rakani muje tare anfi saurin ganeki ga kafarki ga tawa, kice na sawo Miki kayan baby na zuwa barka kenan? ko kema a hado Miki kayan naki babyn? tunda da karfi

na Zan dawo wata kilan ni double shoot ma zanyi tunda Nima Dan biyu ne Ina da twins sister Aishat".

"Twins sister da gaske?"

"Kin taba ganin nayi Miki karya? wlh mu biyu Ammin mu ta haifa first born dinta, mun B'ata ne da ita shiyasa bakisanta ba. Amma na

n gaba zaki santa ne Amma fa Zaki Sha surutu Dan sister Aishat parrot ce".

"Amman laifin me tayi maka da zafi haka? Mu namu twins din basa doguwar batawa gaskiya gashi kaima Ammin irin na Ammah tayi mace da namiji".

"Ki Bari kawai labarin da tsawo sai na d

awo ai nace Zaki San duk labarina kaf ba abinda Zan boye Miki tunda kin sarkafo min zuciya tun kina free matured dinki Kika Hana duniyata zaman lfy,da farko na dauki irin mutum ya burge ka ne Ashe diban Karan mahaukaciya Kikayi da gudan tsokar kirjina".

Da

riya maganarsa ta bata.

"Au dariya ma kike min ko? bayani zakiyi da yarenki, yanda nayi ta fama da garari saina fanshe kayana tas idan Zaki shirya ki shirya".

Cuno Baki tayi kamar tana gabansa ta Fara turza kafa tana fadin "Ni yaushe kaga Ina maka dariya k

awai dai... ni banyi maka dariya ba kaifa yayana ne koka manta my big bro....." Ta wani ja cikin salon da ita kanta Bata San tayi ba.

"Ya salam" ya fada a hankali Dan yanda tayi magana har cikin bargonsa.

"Kinaso ki karya min budget ko?"

Ya jefa Mata tamba

yar.

"Wane irin budget Zan karya maka kana Nan Ina Nan".

"Idan kina min irin haka ai sai kisa na saki layin Dana hau na tattaro ya nawa ya nawa ko komo gida ko ba'a gama ba".

"To me nayi daga magana tom shike Nan sai anjima".

"Wlh Kika kashe min Kira sai

kinzo Dubai ko a kafa ne kuma saina yi Miki abinda bazaki manta ba Dan tarihi me kyau Zan kafa Miki ki kashe ki gani, muna hira kina bani nutsuwa Zaki gudu nida ake yashewa Yan canjina Baki tausaya min ba shine Zaki tsere ki barni da Mata masu farauta ta k

o? Yanzu haka guda uku tun dazu suke shawagi a gabana suna tunanin irin nasu ne Dan hannu".

Gyara Zama Zahra tayi kirjinta ba dukan tara tara bama uku uku ba.

"Mata kace ko me?"

"Eh Mata Mana bake kina min rowar ganin halalina ba to gashi Nan free sai Wand

a yayi maka ka zabi son ranka, ba nace ki bude data na kalli kayana ba Amma kika Kiya Kinga kuwa yanzu saina duba na darje na zaba ta rage min dare, koya kikace my previous?"

Ya Dana Mata kiss ta cikin wayar ya kashe abarsa.

Yana fadin gobe ma idan bace ki

bude datar ki qiya, saina kowa Miki kishina ba gaske kafin na kaiki Ina zakiyi da hujja Amma ki shiga yanzu ai Africa ce da sauran gyara.

AUREN HUCE HAUSHI

MAMAN FATEEMAH



PAGE 35.





________Yana katse Kiran ya tashi tsam ya nu

fi masaukinsa laptop dinsa ya janyo ya shiga aiki sai kusan karfe daya ya kwanta lokaci bayan lokaci sai yayi murmushi idan ya tuno yanda suka rabu da 'yar gidansa yayi zance mata tana neman tikitawa kanta lissafi Wai ita me miji, kamar ta wani san dadin m

ijin,Saida yayi wanka yayi nafila sannan ya kwanta.

*

Zahra kasake tayi da waya a hannu kamar itace Mahmud din "me yake nufi da zasu rage Masa dare kenan neman Mata yajeyi?"

Take wata zuciyar tace Masa A'a Yana zolayarki ne da manemin matan ne

koda karfin tuwo saiya nemi wani Abu a jikinki, kauda wannan tunanin tayi daga zuciyar ta tasan zato zunubi ne, parlour ta koma gurin zilai sukaci gaba da hirarsu sai kusan Sha daya suka shiga ciki.

Washe gari Zahra Bata tashi da wuri ba sai kusan Sha

daya, tun cikin dare bata Jin Dadi wata irin murdawa mararta ke Mata, tana samun irin wannan pain din duk karshen wata idan zatayi period Amma wannan yanda yake mata yayi tsanani sosai tun wurin karfe ukun dare ciwon ya tashe ta farka a gigice, inda Allah

ya taimaketa Bata sakaci ta rasa maganinta duk rintsi Yana tare da ita, a lokacin ta sha cikin ikon Allah lokaci kalilan ciwon ya lafa ta koma barci da Asuba ma data tashi sallah da sauki sosai sai Kuma yanzu data farka taji Yana neman dawo Mata, da kyar

tayi wanka ta sake inner wears ta zura rigar matarial marar nauyi ta koma ta kwanta idan tana wannan yanayin ko turare Bata so sai guda daya kawai body mist ne na strawberry shi ta fesa ta koma ta kwanta Dan abinci dai baya ciyuwa a irin wannan yanayin.



Ganin Sha biyu tayi Zahra Bata fito ba yasa zilai nufar bedroom din nata ta gani anya lafiya kuwa?

Knocking tayi taji Shiru ta qara you taji Shiru Bata kara ba uku ba ta tura kofar a can tsakiyar gadon ta ganota a kudundune, da sauri ta karasa gaban

gadon tana ambatar sunan ta "Zahra kafiyarki kuwa har Sha biyu ta gota Baki tashi ba abin Karin ki har ya Fara sanyi?"

Da kyar ta dago ta kalli zilan cikin miryar marar lafiya tace Mata "bana Jin dadi tun cikin dare marata take ciwo".

"Subahaballa

hi Kuma Kikayi Shiru Baki fada ba idan haka ne bani da amfani Kenan ace tun cikin dare kina fama da ciwo ki kasa fada mini, ina maganin da kike Sha yake na dauko Miki Ni wlh cewa nake tunda ance idan Kikayi aure ze dena, to na dauka kin rabu dashi yanzu, a

i haka wannan likitar ta fada Miki zuwan mu na karshen ko?".

Kai Zahra ta gyada Mata kawai alamar Eh Dan ita kadai tasan azabar da takeji.

"Fada min Ina maganin yake na dauko Miki"

A hankali tace mata "Na sha".

"Kin sha Kuma marar Bata Dena

ciwon ba?"

"Eh" ta fada tana runtse ido saboda azabar ciwo.

Fita zilai tayi da sauri ta koma dakin da aka sauketa ta lakubo keyboard dinta ta lalubo number Ammah, lokacin tana tare da Abba suna maganar komawa makarantar Imam Kiran zilan ya shigo.

"Abba Bari na daga Kiran Nan Zilai ce naji ko lafiya".

"In Sha Allahu ma lfy".

Abban ya fada.

"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu"

Ammah ta fada bayan ta daga wayar daga can zilan ta gaishe da Ammah sannan ta Dora da f

adin "wlh Ammah jikin Zahra ne ba Dadi tun cikin dare ciwon mararta ya tashi Tasha maganin Kuma a banza shine nace Bari na Kira na fada Miki Koda abinda zakiyi mata tunda kema Aikinki ne ko Kuma a turo Mana malam Bala ya kaimu Asibiti taga likitar ta" .

"I

kon Allah! Yanzu ina zahrar?".

"Tana daki tana faman mukususu kamar me nakuda wlh abin gwanin ban tausayinsa".

"To shike Nan ki dubata za'a San yanda za'a yi ki jira".

Ta kashe wayar ta dubi Abba Wanda Shima itan yake kallo, kafin tayi magana ya rigata.

"M

eya samu Uwata naji Kuna magana Bata da lfy ne?"

Ajiyar zuciya Ammah ta sauke "wlh ciwon mararta ne Wai ta tashi tun cikin dare Tasha maganin da take Sha Amma ba wani cigaba shine zilan tace ko Asibiti zasu koma suga likitar da take gani Dan munyi expectin

g idan tayi aure zasu rabu to Kuma a yanda zilai ta fada min kamarma yafi na baya zafi".

"Ikon Allah! Allah ya saukake Bari a tura musu magaji ya kaisu Asibitin tunda duk sauran basa Nan sai mu bisu daga baya mu kuma, ai hakan yayi ko?".

Kai ta gyada Masa

tana kokarin tashi da nufin tafiya, riko hannunta yayi ya mayar da ita inda ta tashi dayan Kuma Yana Kiran wayar magaji.

"Ka dauki mota kaje can hayin banki zaka Kai uwata Asibiti".

Ya kashe Kiran yana kallon Ammar.

"Ina zaki Kuma Kika tashi? Ki kwantar d

a hankalinki in Sha Allah ba wata damuwa Kika sani ko jika zamuyi kwanan nan"

Ya fada Yana dariya irin tasu ta manya.

Itama Dan murmushi tayi tana fadin Allah yasa".

"Amin yauwa kokefa dauko gyakenki mu bisu wata Kila muje tare tunda gani a gida araha sai

nayi aikin bariki tilas ne".

Zilan Ammah ta Kira ta fada mata su shirya ga magaji Nan ze kaisu Asibitin, Suma zasu samesu a can..

Dakin Zahra zilan ta koma yanda ta barta haka ta sameta, kusa da ita zilan ta matsa tana fadin na hado Miki ko ruwan shayi ne

kisha Asibiti zamu".

Kai ta girgaiza Mata alamar bazata Sha ba.

"Ki daure ko kadan ne Dan Allah Kinga wata Kila ayi Miki allura gara kici ko kadan ne".

"Cornflakes".

Abinda ta iya fada Kenan ta koma ta kwanta.

Ba laifi tasha cornflakes din da Dan dama, ro

lling kawai tayi suka nufi parlour zilai na rike da ita. Basu jima ba sukaji dirin mota alamar magajin ya karaso Kenan, zilaice ta bude kofar tun Bai karaso ba direct inda zahrar ke kwance ya nufa akan two seater.

"Sannu Adda ya jikin naki?"

Da kyar ta cir

a Kai ta dubeshi tana fadin "da sauki".



"Allah ya Kara sauki, kamota muje kada Rana ta karayi yanzu twenty five minutes to one fa".

Zalai ta riketa tana tafiya da kyar suka fito compound din Zayyan yana zaune Yana game a waya tunda bashi da

aikinyi a Nan sai zama,ba zato yaga an fito da Zahra haka, da sauri yayi wurgi da wayar Allah ya taimake kan jacket dinsa ta fada da sai dai wata ba ita ba, ya nufo gurinsu Yana tambayar "Lafiya meya faru? Oga kuwa ya sani? sannu" duk a lokaci daya yake

jero wadannan tambayoyin da gani a rude yake.

Magaji ne ya nufi inda yake suka Kara gaisawa Yana farin.

"Ba wani abun damuwa bane Bata Jin Dadi ne zamuje Asibiti kada ka damu".



Zilai magajin ya duba "kun fadawa mujinta kada mu tafi babu san

in sa".

"A'a bamu fada Masa ba ai ko daga bayane an fada Masa yanzu dai muje Asibitin wannan ma wani Bata lokacin ne".

Da sauri Zayyan ya bude musu gate suka fita yayin da Zayyan din ya dauko wayarsa Yana Kiran Mahmud.

Ya kirawo shi Amma Sam taqi shiga sa

i text kawai Zayyan ya tura Masa ya koma ya zauna yana mamakin ogan nasa na neman gurin Zama a wannan Dan gurin shi ko takura ma yaga alama bayayi wata sabuwar rayuwa yake shimfidawa cikin kwanciyar hankali.

Direct A&E magaji ya nufa zilai ce ta taimawa Z

ahra ta fito daga mota suka shiga ciki shi Kuma magaji ya nufi inda ze karbo file.

Ba jimawa yazo ya kawo file din, bayan duguwar tambayar da wata likita da take on call tayi Mata ta rubuta Mata magunguna da allurai da drip ana cikin saka Mata ruwa su Amma

h suka shigo dakin, ma'aikatan da masu jiyyar suna ta gaishe da Abba, gaban gadon Abban yaje ya tsaya sunan ta Abban ya Kira ta bude Ido ta kalli Abba tana kokarin tashi zaune "A'a uwata koma ki kwanta ya jikin naki?"

"Da sauri Abbana, Ina kwana?"

"Lafiya

kalau".

Ammah ce ta matso tana fadin "sannu Ashe ciwon cikin ne ya tashi?"

"Eh Ammah wlh har yafi Wanda nakeyi kamar Zan mutu".

Ta fada tana goge hawayen daya zubo Mata.

"A'a uwata Banda kuka ai kin girma".

Abba ya fada Yana dariya. Itama Zahra dan murmush

i tayi ta juya Kai kunya ta kamata ta.

Abba Bai bar Asibitin ba Saida aka Maida Zahra Aminity ward.

Tun bayan tafiyar su Zahra Zayyan ya kasa tsaye ya kasa zaune, ya nemi number Mahmud tafi cikin carbi amsa daya balarabiyar da akayi linking da computer k

e bashi wadda ba fashimta yake ba, sai dai hasashe kawai number Bata tafiya take fada Masa.

A gida Abba yayi sallar Azzahar bayan an fito ne ya fadawa Baba malam Zahra tana Asibiti Bata Jin Dadi.

Cikin nuna jimami Malam yace "tun yaushe take Asibitin ba'a

fada min ba, kuma menene yake damun diyar tawa?".

"Wlh ciwon cikin ne take fama dashi tun cikin dare shine dazu Mai Taya ta Zama ta kita Asma'u ta fada mata, sai nasa magaji ya Kai su Asibitin sai suka Bata gado Wai zasuyi Mata hoton cikin da sauran gwaje

-gwaje don su fadada bincike akan ciwon tunda ta jima tana fama da lalurar".

"Ikon Allah! Allah ya Bata lfy yasa kaffara ne, ai da anyi magana tun a bayan da an Nemo Mata taimakon ciwon Amma yanzu ma Bata baci ba, idan anyi binciken an gano wane irin ciwo

ne a fada mini akwai magungunan ciwon cikin Mata da yawa a gurina in sha Allah koda tsiron mahaifa ne da sauransu in Sha Allah zasu narke Koda na aikine zebi jinin al'ada ya narke ya zube".

"To in Sha Allah Zan fadawa Asma'u kome Kenan Zan fada maka".

Sun

jima a harabar gidan Abban kafin suyi sallama.

Bayan sallar la'asar malam yasa Habib ya tukashi zuwa Asibitin lokacin da sukaje Zahra tana barci sun gaisa da Ammah Malam ya jajanta Mata Habib ma ya jajanta Mata jikin Zahrar Basu dade ba suka tafi.

****

Tun safe da Mahmud ya fita tare da daya daga cikin amuntattun hadimansa na kasar suka fice sun Kai ziyarorin bazata Dan tono wasu laifuka da ake son binnewa, ya dakatar da mutum hudu ya sallami mutane biyu wadanda sukayi sama da fadin maqudan kudade tun b

ayan rashin sanin inda Mahmud din yake ganin tafiya tayi nisa Kuma baya bibiyar su Sam sai kawai suka tsunduma cikin dukiyar sukayi dumu dumu a ciki, zuwan Sameer ne ya bankado badaqalar wadda tafi karfin shi wadda tasa dole Saida Mai takanas din ya taso,

China Kuma issue ne na rufe musu kamfanin laces da materials da akayi Wanda suke zargin ba'a biya kudin harajin kasa ba a tun farkon bude kamfanin, Mahmud yayi kokarin tura duk evidence dinsa ta wibeside nasu Amma sunqi yarda Wanda dole tasa Saida yazo da

kansa sannan lamarin ya gyaru.

Sai dare sosai ya dawo masaukinsa yaso ya fita ya dan shaqata beach Amma yayi matukar gajiya sosai Koda yayi wanka coffee kawai yayi order da snacks, tunda garin Allah ya waye Bai samu kanshi ba sai yanzu wayarsa ya dauko ya

kunna Dan rabon da ya kunna ta tun jiya, sakonni ne suketa shigowa rututu, amma na Zayyan da Habib su sukafi daukar hankalinsa lfy? Ya tambayi kansa.

Sakon Zayyan ya fara budewa ai baisan lokacin daya Mike tsaye ba duk gajiyar dake tare dashi Nan take tay

i nata guri, cikin tashin hankali ya Fara lalubar number din Zayyan cikin kankanin lokaci Kiran ya shiga, Bai saurari gaisuwar da yake Masa ba ya Fara fad'in "wace irin magana kake min haka? Ashe ajiyekan da nayi bashi da anfani,tun safe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login