Showing 96001 words to 99000 words out of 295116 words
dubu ko wanne rapper uku uku 5k kawai ta Ciro daga cikin 'yan 1k din ta mayar ta rufe tana tunanin Kiran magaji yazo ya Ciro Mata kudin saboda irin haka Bata bukatar komai tunda ba abinda ba'a aje Mata ba wani abu
n ma Sai a shekara Bata nema ba.
Bayan ta kawo musu sukayi gdy suka fita, gurin Aunty zilan Zahra ta shige.
***********
Karfe biyar na yamma jirginsu Ammi ya sauka a sokoto, lokacin data fito Harabar da masu jiran saukar 'yan uwansu suke,Habu direban H
ajiya Inna ne ya nufo Ammi da sauri Yana fadar "barka da sauka Hajiya, nine Hajiya Inna ta turo nazo na tare ki".
Ya fada Yana karbar karamar luggage din dake hannunta .
"To sannu da kokari nagode kwarai".
Direct gidan Hajiy innar ya nufa da ita da yake u
nguwar mabera, duk yanda Abban su Mahmud yaso ta zauna part dinta daya Gina Mata Amman ta nuna tafi son daga nesa dai.
Har kofar falon Hajiya Malam Habun ya kawo ta bisa umarnin Hajiya, lokacin da ze tafi dauko ta fada masa ya kawo Mata ita har kofar parl
our.
Kafin ta fito Yara qananu guda biyu suka fito da gudu daga parlour wanda yayi dai dai da fitowar Ammi daga mota da gudu suka karaso, suna fadin ga Ammi! Ga Ammi" suka fada jikinta a tare suna fadin "Ina kikaje Ammi Baki tafi damu ba mukayi ta kuka".
K
ansu ta shafa tana fadin "sorry My babies ba gashi na dawo ba, ai kuka Kuma ya Kare"
Hannunsu ta rike ta nufi kofar da suka fito, sun riketa ram kamar zata gara guduwa ta barsu.
A zaune Ammi ta samu Hajiya inna tana lazumi, gurinta ta nufa cikin takunta na
nutsuwa tana fadin "Hajiya barkanmu da yamma".
.
Ajiye tasbahar dake hannunta tayi tana kallon Ammi wadda tayi wani tas da ita, bazaka taba cewa ta aje kamar' Mahmud ba, idan aka jera su mafi yawan mutane zasu ce yayarsa ce. Gefen Hajiyar ta zauna daga ka
sa wannan d'abi'ar ta ce Bata taba Zama a kujera matukar Hajiya na Kan kujera, cikin ladabi irin na D'a da uwa Ammi ta gaishe da Hajiyar Tana fadin "Masha Allah zainabu kin cika Alkawarin da Kikayi min Koda kuwa ba a lokacin bane nagode kwarai da gaske Al
lah ya Albarkaci zuciyar ki ya Baki rinjaye akan duk masu son su tagayyara Miki zuri'a, ki Kara hakuri akan Wanda kike yi lallai duk Wanda akace yayi hakuri an Bata masa ne, Allah yayi Albarka yanda kike min biyayya kema Allah ya Baki surukar da zatayi Mik
i fiye da yanda like min, Wai kin samu yin magana da mutumina kuwa bayan munyi wayar nan?".
"A'a har yanzu be nemi kowa ba ina ganin ko ba lafiya ba dai shirun tayi yawa ya Kamata ace zuwa yanzu yayi hakuri ya huce ya dawo gida".
Ammin ta fada cikin damuwa
.
"Ba komai in Sha Allah lfy na fada Miki yanda mukayi da mustapha kema kince kina bibiyarsa ayi ta addu'a Allah ya sassauto da fushinsa ya waiwayo gida wallahi ko cikin dare yaron Nan ya Fadi min a Rai to barcina ya Kare Kullum ta Allah sai anyi mini sauk
ar Alqur'ani akan Allah ya bashi kariya a duk inda yake wallahi nayi Dana sanin fada masa maganar da nayi danasan maganar tawa ze dauketa da zafi wlh da bazan fada masa ba yana cikin zafi".
Hawaye ne ya balle Mata kamar lalataccen famfo har da shashhsheka
r ta.
"Dan Allah Hajiya kiyi hakuri wlh ba maganar ki bace tasa yabar gida nakin dai yazo Kan gab'a ne kawai".
"A'a keda Baki Nan mukayi yazo Nan Yana ta huci Dan motar dazo a ciki ma ko kashe ta baiyi ba ya fado min Kamar an jefo shi, Yana huci Yana Fadi
wlh duk duniya ba Wanda ya Isa yasa ya auri safna Koda Matap sun kare shi Daman koya aureta biyayya ne zeyi Yana da wadda yake da muradin aure, ni kuma a lokacin bani da cikakken masaniyar abinda yake faruwa kinja layin kada a fada min gaskiyar maganar,In
a bude Baki sai ce Masa nayi idan ya ciki shi d'ane na halali ya shiga duniya ya Nemo min yarinyar da yake maganar a kanta Wanda take ganin darajarta tafi ta zuwairiyyar, wlh shiru yayi a inda yake tsaye kasa cemin komai yayi Kusan tsawon minti biyar, kafi
n ya kalli idona yace min wlh zakiga cikakken Dana halak, ki rubuta ki aje idan kin qara ganina a sokoto ba tare da ita ba to kuwa shege ne ni,idan Kuma ban sameta nida sokoto har abada ya juya ya wuce ko motar Bai kalla ba Kuma tun daga Ranar har Rana Mai
kamar ta yau ban Kara saka mahmudu a idona ba, sai dai Babban yaronsa Yana zuwa ganina Yana kawo min duk abinda Mahmudun yake kawo min ciki kuwa harda magungunan da nake sha na hawan jini".
Ammi tayi mamakin Jin Sameer na zuwa gurin Hajiyar koda Wasa Bata
taba Jin haka ba, Kenan wato kafa ya bawa mutane Yana cikin Nigeria din kenan bawai inda ake zaton zashi ba.
"Allah kyau Hajiya ki daina damun kanki, jikina Yana bani Yana cikin kasar Nan Kuma Yana da labarin komai tunda kikace min Sameer na zuwa, duk ind
a yake ya sani ya hana shi ya fada ne kinsan halin kayanki dai".
Mardiyya da Urat Hajiyar ta kalla Tana fadin "yan nema kunki iyayenku sai uwar wasu tun barinki garin Nan yaran Nan suka tare a Nan Wai saina kaisu Yamai gurinki tunda aka fada musu naje suka
tada hankalin iyayen sai su dawo Nan idan Zan koma na tafi dasu, Kinga mardiyya jiya da Iyayen sukazo daki ta gudu ta rufe Dan ma kada su tafi da ita, ko makaranta sai dai direban ya biyo ya dauke su anan ya dawo min dasu Nan".
Kansu Ammi ta shafa tana f
adin rigima ta kare tunda ga Ammin ku ta dawo ko?".
Kai suka gyada Mata a tare.
Masu aikin Hajiya ne suka shigo ta kofar baya daga kitchen suna fadin "lale marhabin da Ammi barka da zuwa".
Gaisawa sukayi a mutunce tana tambayar su iyalansu.
Abinci na mus
amman masu aikin suka gabatarwa da Ammi Wanda Hajiya ta hanasu sakat tun safe ake saukewa da dorawa da gaske Babu Mai shafewa Ammi Zane a gurin Hajiya tana sonta kamar me.
Sai bayan insha'i Ammi ta kwashi su Urat ta nufi gida cikin motar data Bari a gidan
Hajiyar. So take ta bada mamaki yanda ta fice batare da sanin kowa ba a wayi gari a ganta batare da kowa yasan sanda ta dawo ba, duk gidan amintacciyar Mai aikinta kawai ta Kira ta fada Mata tana Nan Zuwa garin yay ko su Abeeda ba Wanda ta fadawa tasan zum
udin su ze saka kowa ya sani.
************
Safa da marwa take tun bayan gama wayarta da Aunty Ladi ranta idan yayi dubi a bace yake Wai shi wannan yaron wane iri ne aiki akeyi a kansa Amma Kamar ana zubawa a teku wannan guri na uku ne da Aunt
y Ladi taje Mata a Jos Amma amsar daya ce wannan yaron yafi karfinta, Mata ne guda biyu a teaye a kansa da addu'a sannan yana da tsarin jiki na ban mamaki Nan kusa ba abinda zeyi tasiri a kansa sai ikon Allah.
Wayarta ta dauko Asabe ta Kira cikin k"an k'an
in lokaci ta daga Kiran "kizo ina jiranki yanzu". Ta kashe wayar tayi wurgi da ita Kan gado.
Cikin abinda bai wuce minti Sha biyar ba Asabe ta shigo gidan ko part din Ammah Bata shiga ba kamar yanda ta Saba direct ta wuce gurin Mama.
Parlourn ba kowa ganin
haka yasa ta wuce bedroom dinta a tsaye ta sameta tana kaiwa da kawowa Ido yayi Mata jawur kamar na tsohon mashayi.
Ko sallamar ta Mama Bata ba ta amsa ba ta, fara fadin "Ina ne garin da kikace min 'yar dago kawarki ta fada Miki da wani shahararren mutum
Mai aiki kamar yankan wuka?".
Shigowa tayi ta zauna tana kallon mamar "Wai lafiya na ganki haka?"
"Ina fa lafiya! Aunty Ladi ce ta tasheni daga barci take fada min taje har guri uku ba sa'a, Wai yanda suka fada Mata yanzu ne ma Zahra ta gamu da Wanda ake
ta fada Mana a baya bawai wadanda mukayi ta aiki a kansu ba, Kuma Shi wannan din duk ya fisu Shirin jiki Dan da alama yanda sihiri baya tasiri a jikin ita yarinyar shima baya yi a jikinsa, Wai wasu Mata ne guda uku a da maza biyu tsaye a kansa duk juyi si
hirin baya kaiwa inda yake, yanzu Kiran da nayi miki ina son Jin tabbacin kin koma kin tabbatar da Mai gadin ya saka wannan abubuwan da Kika bashi?".
Dan murmushi tayi irin na kwararrun 'yan duniya din Nan kafin tace "Haba Hajiya shekara nawa muna tare ban
taba ha'intarki ba sai yau an aiwatar da komai sai jiran sakamako kawai ai wannan yaron bama Azare ba Kasar Bauchin ma gaba daya shi da ita har abada, Kuma malamin da 'yar dagon ta fada min a wani gari yake cikin kasar katsina ana ce Masa Bakiyawa tace i
dan na shirya zata rakani garin iyayen mijinta ne daya rasu". Hake sukayi ta kullawa da kwancewa,Asabe nata Kara zugata akan ko nawa zata kashe kada ta Bari Ammah da 'yar zumunta su fisu komai, tunda ta Nan take samun nata rabon a jikinta idan Bata encoura
ging dinta itama zata rasa income nata.
**
Tun bayan ganawa da Bakinsa Mahmud ya shige bedroom ya Haye gado yaso ya Kira Zahra suci gaba da Hira Amma saiya fasa Dan yasan yanzu gari ya waye sosai a 9ja Bari ya kyaleta sai dare hirar zatafi tafiya yand
a yake so. Bai tashi ba sai lokaci sallah, wanka yayo ya saka kananu Kaya yayi sallah yana cikin addu'a yaji ana knocking din kofa umarnin shigowa ya bayar Sameer ne ya shigo Bakinsa yaki rifuwa.
"Barka da Rana". Sameer ya fada Yana mikawa Mahmud wayar han
nunsa.
Hannu yasa ya karba yaga menene yasa shi irin wannan murmushin.
Wani fine Baby ya gani nade cikin farin towel na jarirai fari sol.
Kallon shi Mahmud yayi Yana neman Karin bayani.
"Takwaranka ne madam ta haihu jiya cikin dare".
Cikin madaukaikin mama
ki Mahmud ya kalli Sameer "are you serious?"
Kai ya gyada Masa Yana Fadin " yes sir".
Mahmud sai juya wayar yake Yana Kara kallon babyn.
"Masha Allah, my friend Allah ya Raya mana, amma me yasa ka taho ka baro yarinyar mutane a watan haihuwarta ai sai iyay
enta suga rashin kyautatawar ka ga 'yarsu".
Shafa Kai yayi Yana Dan murmushi "ba wani Abu,idan na zauna me zanyi musu duk abinda ake bukata nabar musu".
Wani kallon baka da lfy Mahmud yayi Masa "an fada maka Bata bukatar kulawar ka ne a irin wannan lokaci
n?" wlh Dana San lokacin haihuwata yayi ba inda zakazo Kuma yanzu ka nemi visa ka koma gida daman Nan anyi clearing din komai U A.E din naji da komai kawai, naji kace takwara na nayi zaton sunan Abban koko za'a saka masa?".
"Ai umarninsa ne yace nayi masa
huduba da sunan ka".
"To Masha Allah! Godiya ta har gida zanje na yiwa Abban tafi karfin ta waya Allah ya Raya Mana Mahmud yayi Masa Albarka, kaje ka Fara shiri tun yanzu ka shiga kasuwa kayi musu abinda ya Dace".
"In Sha Allah".
Godiya Sameer yayi ya nuf
i kofa Yana fita alarm na shigo Masa Wanda Saida ya girgiza shi baya yayo yana Murda kofar ze dawo ya jira yayi locking dinta, dariya yayi Yana Fadin "manya gatan Wasa, Allah ya biya maka bukatunka na Alkhairi".
A Ranar cikin dare suka bar Kasar su duka Sa
meer yayi Nigeria shi Kuma Mahmud ya nufi U.A.E .
✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH.
Page 34
AssalamuAlaikum warahamatullahita'ala wabarakatuhu.
'yan uwa muna barar addu'oin ku bisa rashin abokiyar aiki da mukayi ECCD co-ordinator ta KIRIKA
SAMMA LOCAL GOVERNMENT JIGAWA STATE muna rokon Allah s.w.a ya jikaanta yayi Mata Rahama yasa Aljanna makomarta tare da Iyayen mu da sauran Al'ummar musulmi Baki daya ya Raya abinda ta Bari ya Albarkaci bayanta.
______ Misalin karfe uku da rabi jirgin su
n Mahmud ya sauka a DUBAI INTERNATIONAL AIRPORT (DXB) cikin amincin Allah, yana cikin kusan rukunin mutanen karshe a fitowa, yana sanye da suit ash colour na kamfanin Armani hannunsa sanye da ogogo Rolex, baya tare da komai sai jakar laptop dinsa a hankal
i yake gangarowa cikin takunsa na cikakken namiji me ji da lafiya da karfi, direct gurin da taxin airport suke ya nufa, baya bukatar asan yazo garin so yake ya tantance wata jimurda da aka hada, taxin ya shiga saida sukayi balance a titi sannan ya fadawa d
ireban ya kaishi JW moritte marquis hotel cikin harshen larabci,sunyi tafiya mai tsayi kafin su karaso hotel din, bashi da matsalar kama daki dan tun yana china yayi booking din dakin ta online, katin dakin kawai ya karba ya koma waje yin 'yan uzurirrika
daga baya ya nufi ciki, wanka ya fara kafin yayi order abinci, sai da ya gama komai sannan ya kwanta dan yayi matukar gajiya, yaso kwarai ya kira 'yar gidansa amma yana son su tattauna sosai, sai yanzu yake jin haushin wani ra'ayin nasa badan haka da sun
a tare da ita suna hutawarsu, yanzu kadaicin rashinta da be dameshi ba, wlh da beyi alkawari ba da visa zesa ayi mata ta sameshi a nan saboda hotel din yayi masa, yana daga cikin lattest hotels na duniya be taba sauka a wani hotel ba a dubai sai BURJ AL AR
AB JUMAEIRAH dakinsa parmanent ne duk mai hulda dashi a dubai nan suka sani, duk da yana da gidaje a kasar shi be fiye son yakai abokanin bussiness dinsa gida ba. Wannan shigar ta sirri ce shi yasa ya canza sheka baya son asan ya shigo kasar mamaya sake so
n yakai wasu gurare, yanda har ya gama abinda yake yabar kasar wani be sani ba duk da abune mawuyaci hakan ta faru.
Barcinsa yasha sosai dan har akayi sallar magariba be sani ba, lokacin daya tashi ana gab da kiran sallar insha'i, a gurguje yayi wanka ya z
ura sabuwar jallabiyar daya saya cikin kayansa a kasar, a cikin dakin yayi sallar magariba ya fito yabi lifter zuwa masallaci,koda suka idar da sallah be dawo daki ba a nan harabar hotel din ya Zauna da gaske yanayin gurin ya burge shi sosai, coffee yayi
order ba'a jima ba wata matashiyar balarabiyar yarinya ta kawo masa coffeen sai yaga kamar 'yar gidansa, nan da nan yaji duk rintsi ita yake muradin gani number dinta ya lalubo ya kira duk ba baya son kira direct yafi son ta Whatsapp.
Suna zaune a parlour
ita da zilai tana Shan mutuniyar tata farm fresh, Kira ya shigo a wayarta dake kusa da ita, tayi mamakin ganin code din Dubai har sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka, batayi magana ba Shima baice komai ba, ganin shirun yayi yawa yasa zilan Fadin "naji
kinyi shiru koba Kira bane".
Karamin tsaki Zahra tayi "wlh na daga amma naji shiru inaga ko wrong number ne dan code din na Dubai ne ni kuwa waye ze kirani daga Dubai da dai Aunty Nawwara Bata saudiyya da saina dauka ko sunje ne da mijinta tunda business
man ne, Bari na kashe wata kilama ba'asan an Kira ba"..
Kafin ta dauke wayar daga kunnen ta taji yayi magana cikin husky voice kada ki kashe min waya, ki bude data zamuyi magana". kit ya kashe Kiran wayar tabi da kallo a zuciyar ta tana Fadin "ikon Allah
shine Kuma a Dubai ya illahiy, to Wai wannan Dan talikin waye shi lamarin fa Yana neman Zama abin tsoro fa, yace Yana yiwa kungiyoyin waje aiki ita Kuma a gefe guda wani Abu yake yi irin na Mai bada umarni Kuma bataga yanayi gaban kowa ba sai ita, kamar R
anar da taji yana Kiran zayyan da umarnin daya Bashi akan lallai ya sameshi da safe Kuma Bai karya Umarnin ba"
Wayar ta kalla tana mikiwa zuwa bedroom dinta Saida ta shiga ta duba data idan Babu ta saka tunda Sam Bata taba saka data ba tunda ta Fara amfani
da wayar datar data gani tayi bala'in Bata mamaki 4.5 BT ta gani sub din shekara daya ne.
Cikin sofa ta zauna Tana juya wayar Bata bude datar ba, wani Kiran ne ya sake shigowa still dai nashi ne, dagawa tayi tana fadin Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'
ala wabarakatuhu".
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, meya hanaki bude datar danace a bude?"
Shiru tayi ta kasa magana,.
"Wai ko sai nayi ramuwar sayen bakin da banyi bane ake min jan aji irin haka. Dan Allah kimin magana kona samu nutsu
wa wlh ji nakeyi Kamar na gudo tun ba'a gama ba duk kin mamaye ko Ina na kasa komai sai tunanin ki, Ni danasanin zuwan ma nakeyi gashi sun rarraba mu wasu suna London mu kuma suka kawo mu hadaddiyar daular larabawa, shine nace Bari na kira na fada Miki Kod
a abinda kike bukata na taho Miki dashi tunda da kudinki a gurina"
"Kudina kuma? Name nene kuma yaushe na baka".
"Bake Kika bani ba ke aka bawa na manta na Baki Sai a Nan na tuna danaga Kaya irin naku na 'yan Mata".
Ya fada Yana dariya.
"Wai 'yan Mata".
T
a fada tana Dan turo Baki irin bataji dadin Nan ba.
"Au ashefa an wuce wannan stage din ko?"
Ya fada da alamun zolaya.
"Wato kinki bude data sai kin cinye min 'yan