Showing 81001 words to 84000 words out of 295116 words
fada Yana tsareta da idanunsa masu razana ta.
"A
'a ni bana wani good term da Mama ko kadan Dan da sam ita da Aunty salma basa yina Daman Hameeda ce tawa idan tana gurin ba Wanda ya Isa ya Fadi marar Dadi a kaina, to ita dinma bansan meya canzata ba lokaci daya tayi min cin fuska ba ko Kara gani a tsaye,
ita Kuma wannan Asabe ce aminiyar Mama ce komai tare sukeyi".
"Ok ba damuwa".
Wayarsa ce ta dauki wani slow music alamar shine ringtone din wayar, dauka yayi tare da sallama.
Magana ya Fara Bai jira Wanda yayiwa sallamar ya amsa ba.
"Kazo Azare katagum lo
cal government a cikin local government ne na Bauchi state ne a duba map zakaga inda location din yake amma kada ka biyo ta jos Nissan yayi yawa ka shigo ta Kano kawai karfe bakwan safe tayi maka a garin".
Abinda ya fada kenan ya katse Kiran.
Wani Kiran
ya Karayi ringing daya aka dauka.
"Bilya a canzawa Mai gadin gidana gurin aiki ya Koma Sharar compound din makarantar yaran Nan kawai" kit ya kashe Kiran duk tana binsa da ido.
Agogon jikin wayarsa ta kalla Sha biyu da Rabi.
A marairaice ta dube shi "yau
she zamu tafi nifa Ina Jin tsoron dare fa".
Kansa ya kwantar a cinyarta Yana facing din face dinta.
"A Nan zamu kwana bakiga harda jakar matafiya ba? jiranki nake ki bani labarin naki kinyi shiru kin shareni".
Dan turo Baki tayi "Toni me zance maka ai kasa
n komai"
"Kamar Yaya nasan komai, harda labarin da aka turo min ta msm na duk Wanda kikayi tare dashi Saida ya sanki 'ya mace yaji test din Bai Masa ba tunda kyawun iya jiki da fuska kawai ya tsaya" shima Hakan ne tunda anfada min?"
"Cikin razana ta nun
a kanta da hannu.
"Ni Kuma Zina? Waye yayi min irin wannan tozarcin? Me nayi musu haka da zafi da har za'a yi min bita da kulli irin wannan?" Sai hawaye.
"Ya Ilahiy!! Ken wace iri ce daga tambaya sai kuka kewai kuka baya da wahala a gurinki Kamar wata 'yar
film, tab kice na iya bakina, idan na karanto Miki sauran yau ma a Asibiti zamu waye kinga the chapter is closed labarin ma a bar shi Gama Shan apple din ki kwanta Naga alamun barci a idonki Ni aiki Zan karasa".
Cikin shashhsheka tace "basai nayi komai b
a tunda banzo da kaya ba haka ma zan iya kwantawa".
Luggage din ya nuna Mata da Hannun. "Ki bude akwai komai a ciki ya janyo laptop dinsa ya Fara aiki bai Kara bi ta Kanta ba, yayi biris da ita Kamar besan Allah yayi ruwan tsirarta a dakin ba.
Nuku nukunta
ta Gama sannan taje ta bude jakar kamar yanda ya fada kayansu ne ita harda sleeping dress Kusan uku Saida ta duba sosai sannan ta samu wata doguwar Riga Mai Dan dama dama ta dauka ta nufi toilet duk abinda take Yana kallonta ta gefen ido har ta shige.
Ruwan zafi ta hada ta zuba turarikan wankan data gani a gurin ajiye, shigewa tayi ciki tayi kwance ruwan Yana ratsata kamar zatayi barci ta jima sosai sannan tayi wankan ta fito, sai da ta goge jikinta ta zura rigar barcin cotton ce mai laushi ta sauko Mat
a har Kusan gwiwa sai da matsalar ta dayi zif akayi Mata har kasa ga saman rigar wani net aka saka transparent komai a waje yake ba wani sirri Kai kawo da dinga yi a toilet din daga karshe towel na wanka babba ta rufo a jikinta ta fito.
Dago ido yayi yana
kallon ta sai Kuma ya janyesu yaci gaba da aikinsa cikin kware, idan yaci gaba da kallonta wlh wata dariya zata kubce Masa, shi dai yasan duk wayon Amarya sai an Sha manta.
A darare tazo ta zauna a nesa dashi.
" Ki tashi ki kwanta ya nuna Mata tsakiyar gad
on. Jinjina Masa Kai tayi ta Haye tana Jan blanket din tana rufe jikinta. Kusan Rabin hankalinsa Yana Kanta Yana kallonta tayi Addu'ointa shafa a jiki, tun Tana Dan Jin dar a jikinta har barci yayi awon gaba da ita.
Sai gurin daya ya kammala duk abinda ya
kamata ace ya gama.
Wanka yayo tare da alwala pyjamas ya saka masu kalar off-white sannan ya tada nafila raka'a hudu yayi ya sallame ya jima Yana addu'a kafin ya nufi gado dariya ta bashi blanket din daban ita daban sai barcinta takeyi cikin nutsuwa face d
inta ya kurawa ido "yes she's beautiful" ya fada a hankali kamar Mai tsoron kada taji.
Kusa da ita ya kwanta kamshi turarensa Dana turaren wanka sai suka bada wani kamshin Mai dadin shaka, madaurin jikin rigarsa ya since ya zare rigar daga jikinsa ya kwant
a a jikinta Bata ko motsa ba a hankali ya saka hannunsa ya zuge zif din jikin rigarta yayi mamakin nauyin barcinta blanket din ya janyo ya lullubesu da shi sannan a hankali ya mannata da jikinsa yana sakin ajiyar zuciya, a cikin barci taji Kamar hannu na y
awo a jikinta a Dan tsorace ta bude idonta ga dakin ba haske so sai, Sam saita kasa gane takamaiamai a Ina take ga ta Kuma a jikin mutum ko Riga Babu.
"Wayyo Allah na!!!" ta fada jikinta ya dauki rawa..
"Shittt, cool down nine kiyi barcinki Nima barcin nak
eji..
.
✨✨
✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
Page 28
____Hankalin Zahra be kwanta ba sai da taji Yana maida numfashi a hankali alamun barcin ya dauke shi ajiyar zuciya ta sauke da farko Bata yarda ba da yace barci zasuyi
Saida ta gani da gasken yayi barcin.
Kokarin zame kanta da yayi Mata pillow da gefen kafadarsa tayi, a cikin barcin ya kara janyo ta jikinsa yana gyara Mata kwanciyar amman idonsa dai a rufe, shiru tayi lif a jikinsa Dan Bata son ya farka su hada ido a
i da kunya amma taga alama shi bashi da ita misqalazarratin idan wani ne ai zuwa yanzu Basu wani sababa yanda abun yazo musu a hagunce, ko dan shifa yana ikirarin ya santa batun yanzu ba to a Ina?Kuma waye shi?daga Ina yake? Waye sameer a zahiri shi yaron
sameer ne ita Kuma a bad'ini shi yake bashi directive abin da daure Kai Kuma yace ya manta garinsu da komai nasa Amma a gurinta yana fada Mata ya tuno kakarsa har da 'yar tsamar da sukeyi.
Tunani barkatai ta dunga yi har barci yayi awon gaba da ita, ka
rfe hudu da rabi na Asuba alarm din daya saita ya tashe su kusan lokaci daya suka farka har lokacin tana jikin shi, shiru tayi Bata nuna ta tashi ba, so take ya wuce toilet.
Addu'ar tashi daga barci yayi a hankali ya zare ta daga jikinsa kura Mata Ido
yayi a cikin dimligh din dakin face dinta sai glowing takeyi ko Ina a jikin fresh sai wani sansanyan kanshi ke fita daga jikinta wanda har ya zauna a jikinta Dan duk jikinsa kamshin yakeyi, light kiss ya Bata a kumatu ya gyara Mata rufar saboda sanyin AC g
a sanyin Asuba. Duk abinda yake tana jinsa bakam tayi Dan ji tayi wani irin nauyinsa ya rufeta Wai wane irin barci ne tayi har yayi sabgar rabata da rigarta amman Wai Bata sani ba, Jin karar ruwa yasa tayi saurin tashi ta janyo rigarta tana cuno Baki.
"Haka kawai duk a kalleka waya sani ma ko Abu ya saka a cikin Apple din Dana Sha shike Nan na Kama barcin asara sai yanda yayi Dani" da sauri ta ida janye blanket din tana duba jikinta Jin ba wani bakon Abu yasa taji sanyi a cikin ranta, sai Kuma abun ya
Bata dariya, Jin ze fito yasa ta koma ta kwanta jallabiya ya zura ya saka tashi ka fiye naci, ya dauki tasbasha (counter( ya matso kusa da ita Dan guntun ruwan alwala na fuskarsa ya yarfa Mata kadan a fuskar ta.
"Ki tashi kiyi alwala an kusa tada sall
ah nasan idonki biyu tun lokacin Dana tashi".
Ya fada Yana nufar kofa zuwa masallacin cikin hotel din.
Tashi tayi ta nufi toilet din a gurguje tayi wanka ta daro alwala lokacin data fito har an idar da sallar, lotion din data gani ta shafa ta bude
jakar duk wani abun da zata bukata ya sako a ciki ita mamaki take to a Ina ya Sami kayan ita dai ba nata ya dauka ba, hatta bra ma size dinta ce doguwar Riga ta cire daga leda ta saka baka Mai aikin stone, hijab ta saka ta tada sallah.
Har ta gama azkar Ba
i shigo ba sai gurin shida da rabi ya shigo directly inda take ya nufa.
"Barka da Asuba".
Zahra ta fada tana sadda Kai kasa, shiru yayi kamar Bai jita ba sake maiamaitawa tayi.
"Taso kiga yanda ake gaida Dear ba irin wannan local gaisuwar ba"
Sunne Kai ta
yi tana Dan murmushi, tsugunawa yayin daf da ita yana kallon 'yan yatsun Hannunta sumul sumul dasu kamar Bata aikin komai da Hannun, dagota yayi gaba dayan ta ya mannata a jikinsa "ji nakeyi kamar kada nayi tafiyar nan ko Kuma na daukeki mu tafi, idan na t
una zanyi nesa dake wlh wani irin rauni ne yake kamani naji kamar idan bana Nan wani Abu ze faru".
Ya fada cikin muryar karaya da gaske a 'yan kwanakin Nan Yana Jin wani Abu daya fi na da a tare dashi.
Cikin 'yar siririyar muryarta tace "ba komai kaje k
awai Allah Yana tare damu ba abun da ze faru sai abinda ya hukunta a kaina, Allah ya bada nasara yasa a Dace, kawai dai Dan Allah kayi min wata alfarma kafin ka tafi".
Hijabin ya zare a hankali daga kanta ya Dora a Kan bed side kafin ya zaunar da ita a jik
insa as usual.
"Fadi wace bukata gareki".
Dan shiru tayi kamar bazatayi magana ba.
Oya fell free with me, kiyi magana Mana kinsan eight thirty nake so na wuce".
"Daman so nake na ringa zuwa Dr.sulaimanu Adamu college of Hygiene inda nayi service na ringa
yin lectures ko sau biyu ne a sati".
Wani kallo yayi Mata na Amma Baki da lissafi.
"Ni matata da yawon aiki? Gaskiya A'a! Wannan bukatar Bata karbu ba, me kikeci na baka na Zuba indai aiki ne wlh sai kin gaji da yinsa, tashi daga jikina kin wani samu cinya
kin dane,kada na makara nayi missing flight mu tsuguna duk dan burin bawa ya rushe".
"Yanzu Allah bazaka Bari na rinka Zuwa ba".
Ta fada a marairaice.
"Kinsan Allah wlh Zan hadaki da zayyan Dan nasan Yana daf da shigowa garin Nan ya juya min dake can kauy
e gurin Hajiya Inna ko banza kin tuka mata tuwon dawa kin mata shara, kinga ita gaba ta kaita balarabiya na mata aikatau ita kuwa bakar fata Kinga sai mu Dora a media muma 9ja munci gaba ana zuwa daga middle East ana Mana aikatau".
Ya karasa fada Yana Jan
Dan tsinin Karan hancinta.
Tana kokarin magana wayarsa dake Kan bedside ta dauki wani kidan larabawa Mai dadi.
"Dauko min wayata Dan tsabar na Zama mijin ......, Gashi Nan ringtone din ma kidan kune na saka". Wayar ta dauko, Zayyan ta gani kwalalo idanu ta
yi Ashe da gaske yake da yace Shi wannan din zezo yanzu ko waye shi kuma "oho" ta fada a zuciyarta.
Wayar ta Mika masa.
"Ka karaso?" Abinda taji ya fada kenan Bata San me yace Masa ba taji yace "ok, ka shigo ciki akwai securities a kofa zasu zasu rakoka gu
rin da Zan ganka".
Ya kashe Kiran Yana nufar kofa, ki shirya kafin na dawo yanzu zamu wuce".
Yayi Gaga abinsa ya barta da Baki a sake "ikon Allah shi Kuma ko waye yake bada umarni cikin dare ya wayi gari da abinda ya bukata tasan ko waye daga nesa yake Da
n jiya tanaji Yana fadin kada a biyo ta jos a biyo ta kano, ita duk ya Gama Dame Mata lissafi wlh.
******
A hankali yake tafiyar cikin nutsuwa Amma da gani kasan tafiyar ta ingarman namiji ce, tunda ya doso gurin Zayyan ya kafe shi da ido, take ya shiga j
injina lamarin ogan nasa wato ana zaton wuta a maqera said gata a masaqa, waze tab'a tunanin sa a irin nan yayi masifar bada kafa.
Bai Farga ya kureshi da ido ba Saida yazo daf dashi, "sorry sir" ya fada Yana sadda kai, baiyi magana ba ya mika Masa hannu w
annan d'abi'ar sa ce baka Masa irin gaisawar Nan sai dai kuyi musabihwa. "Barka da Asuba ya Hanya?".
"Alhamdulillahi."
Ya fada sai da Mahmud ya zauna kafin Zayyan Shima ya koma ya zauna.
Kamar bazece komai ba gurin ya dauki shiru.
Saida yaja fasali sannan
yace. "I hope ba Wanda ka fadawa munyi waya ga Kuma inda zaka sameni?"
Kai ya girgaiza "ko daya oga ba Wanda yasan inda na tafi kawai nace musu zanje gida ne na samu Kiran gaggawa".
"Good, na kiraka ne zaka zauna gidan da wife Dina take zanyi tafiya, Wand
a na saka gadin Naga alamar gaskiya Bata isheshi ba, ko Kuma ze iya komai saboda kudi, zan turo maka pictures na wasu Mata koda Wasa kada kabar kafarsu ta shigar min gida shi yasa na taso ka da tsohon dare ".
Zayyan jin magwnar yayi wani banbarakwai "wif
e Kuma? To ta ina Hakan ta faru? mutumin da ake tunanin baya kasa sai Kuma ya ganshi a nan Yana wata irin rayuwa hankalinsa kwance, ga abubuwan tambaya Amma ba Halin yinta.
"To in Sha Allah baza'a samu matsala ba".
"Yanzu zaka shiga cikin Ibrahim ze nuna m
aka dakin da zaka huta daga Nan zuwa sha daya Binyaminu ze shigo kuje gidan".
Ya fada Yana mikewa.
Da kallo zayyan ya bishi har ya b'acewa ganinsa, ajiyar zuciya ya sauke Yana jinjina Lamarin ogan nasu wato duk yanda kasan Shi idan yayi wata bada Qafar sai
ka rasa gane wace alkiblar ya kalla. "Wife Dina". Yanda yayi maganar kasan ba wasa cikin Yana wannan tunanin Ibrahim ya karaso Bai sani ba.
Da azama ya shiga falon a zaune ya sameta da luggage dinsa a kusa da ita tayi rolling da Veil din rigar sai tayi ma
sa wani irin kyau, a slow ya karasa inda take zaune ya saka hannu ya dagota tsaye ya sumbaci saman goshinta.
"Nayi Miki irin gaisawar ku, Ina key din lokaci Yana ja kada da gaske nayi sakaci kija Mana, muna lallabawa, kin hakura da Zuwa makarantar naji Bak
i ce komai ba?"
"Bani da say, sai yanda kace haka za'ayi".
"Nace A'a! in dai Ina raye da lafiya ta bazaki nemi komai ki rasa ba Koda kuwa faskare zanyi to zanyi na samu abinda zankula dake".ya fada Yana daukar luggage din ita Kuma ta nufi kan fridge inda
ya ajiye key din jiya.
A jere suke tafiya sunyi wani irin dacewa wadda dole idan ka kallesu ka qara suna kokarin fita daga reception su Zayyan suna kokarin shiga, Mahmud ya kalla da jakar matafiya a hannu Yana rike da Hannun Zahra,.
"Kam bala'i"
Yaji Baki
nsa ya subuce ya fada Yana matsawa baya Kamar yanda Ibrahim yayi.
"A sauka lfy" Ibrahim din ya fada shi kuwa Zayyan kamar an saka makulli an datse Masa baki.
"Ka bashi key din dakin ka biyoni mota Zan baka sako".
Ya fada Yana duban Ibrahim, mota Zahra ta s
hige ta barsu suna tattaunawa kafin ya shigo ya tada motar ya nufi get din fita har yabar harabar hotel din, Zayyan na lekensa ta window sai dai yasan idan yayi magqnar Nan da wani kwabarsa ce zatayi ruwa daya fesa labari, oga da rije jikar mace uwa uba ya
na tukata da kansa Kai wannan abin surprised da yawa yake"Ga bikin zuwa ne babu zani.
Tafiya yake da hanzari Dan ma safiya ce sosai titin ba yawan jama'a cikin Kan kanin lokaci suka shigo unguwar, Horn ya danna da karfi da gudu Mai gadin yazo ya bude yan
a fadin "barka da zuwa!"
Da gudu ya Koma ya dauko sakon dasu mama suka kawo jiya Yana fadin "barka da Asuba yallabai gashi jiya bayan futarku su Hajiya Babba sukazo suka bada a ajewa Hajiya".
Ya fad'a Yana risinawa Yana mikawa Mahmud ledar.
Saida ya karew
a shi da ledar kallo, sannan ya hade gabas da yamma yace ka rika idan kana so, Kuma
Ka hade kayanka in anjima kadan binyaminu ze zo da Wanda ze canjeka aikin Nan adalci daya nayi maka ban koreka ba zaka koma share-sharen makarantar Yara kawai".
Jiki na tsu
ma Mai gadi ya durgusa Yana fadin "Yallabai me nayi haka da zafi Dan Allah kayi hakuri wlh baza'a qara ba ka rufa min asiri".
"Iya Alfarmar kenan bana korar ma'aikaci sai lefinsa ya Kai uku to Kai daya kayi ba tare da kasan laifi bane shi yasa nayi maka uz
uri bazan rabaka da rufin asirinka ba dauki kaje yanzu Zan fito". Jiki ba kwari ya dauki ledar ya juya Yana ta faman tunanin ta ina ya kuskuro yallabai jiya lafiya kalau suka rabu yau Kuma ya tashi da canjin gurin aiki da Allah ma ya dube shi da Rahama dab
a Kora bace days shiga uku.
Suna shiga Mahmud yayi bed room dinsa ita Kuma