Showing 291001 words to 294000 words out of 295116 words
fada Yana Masa murmushi, Shima Habib murmushin yayi kaf
in yace.
"Ai Ubaidat an kasani ta samu Mai kudi a Itas gadau Amma mazaunin Abuja har anyi biki wata Daya Daya wuce tayo min text Wai nayi hakuri a gidansu ne aka takura Mata, to nima lokacin lna cikin tawa damuwar ta lalurar Baba malam wallahil Azim ban ji
komai ba fatan Alkhairi nayi Mata kawai Kuma Daman a yanda take bijiro min da bukatu na kudi banga alamar zamu dai daita ba da farko ba haka take ba sai daga baya na fuskanci ta fiye rokon kudi Kuma duk mace Mai wannan d'abi'ar sai wadda Allah ya tsare Da
n an Bata da yawan 'ya'ya Mata masu irin d'abi'ar".
Jinjina Kai Mahmud yake kafi ya nisa yace.
"Allah ya kyauta, wato tsakanin hakuri da rashinsa tak'in kadan ne da tayi hakuri babu Abinda zata nema ta rasa da izinin Allah, ka tuna wata magana daka tab'a f
ada a dakinta mu na Azare? Lokacin da kace min muma ai ba haka Allah ze barmu ba".
Dariya Habib yayi ya tuna lokacin da aka bawa Mahmud Auren Zahra ne ya Fadi haka.
"Kada ka damu kaje ka nemi suhailat kanwata ce na kori Mai zuwa gurinta sauran masu neman i
zini ma na fadawa uncle Mustapha ya fada musu anyi Mata miji Daya nemi sanin waye mijin na nuna masa hotonka da irin karamcin da kayi min, take ya nuna goyon baya Shima na saka ya kirata ya fada Mata ya nuna Mata hotonka yace taje tayi tunani idan kayi Mat
a tana sonka ze kirata bayan kwana biyu, to Alhamdulillahi tayi shiru ta sadda Kai lokacin daya Kara tambayar ta, hakan ya nuna ta amince, to Daman da da maganar Ubaidat din biyu zan maka Rana Daya kaima ga hoton suhailat Nan idan tayi maka idan Kuma batay
i ba Dan Allah kada kayi min Kara ka fada min gaskiya idan ka rufe min saimun tsaya gaban Allah da kai".
Ya fada Yana mikewa tsaye Yana Danna wayarsa yayi gaba Saida ya danyi nisa ya juyo ya kalli Habib Daya rasa bakin magana.
"Ka duba WhatsApp Dinka na tu
ro maka pictures dinta". Ya wuce ciki..
Habib jikinsa har tsuma yake ya bude Whatsapp din ai Bai San lokacin daya Mike tsaye ba Yana tsarkake sunan Ubangiyi buwayi gagara misali, yarinya ya gani danya sharab Mai wani irin kwantaccen kyau da gani gayu yaci
gidansu a gurin tayi wani smile Daya kusa ya saka shi zaucewa, shi kadai Fadi yake.
"Yessss... Yessss... Tayi"..
Take a Nan yayi sujudush shukur Dan yasa Rahamar Allah ta bashi wannan yarinya ba Wai iyawasa ba, ya Kara jinjina girman Qudurar Allah wato ida
n aka hada wani connection din sai dai bawa ya zuba Ido yayi kallo, a watannin baya da za'a ce Masa za'a baka aure a Family din DANGE dake sokoto ze rantse harda girman Allah hakan bazata tab'a faruwa ba Dan ba'a hada kankana da guna.
Komawa yayi ya zauna
Yana Kara duba hotunan sai yaga ai Wanda ya Fara dubawa ma Bai Kai sauran kyau ba sai lokacin yaga number wayar ta daga kasa da Dan bayani a kasan number.
"Ga number ta Nan ka kirata sauran aikin Kuma naka ne tunda Nima Ni nayi nawa aikin. Ina Maka fatan d
acewa kamar yanda Nima AUREN HUCE HAUSHI da akayi Mana ya huce Mana namu haushin Dana iyayen mu.
Dariya Habib yayi ya Dan kwantar da kansa jikin kujerar da yake a Kai ya zubawa fuskarta Idanu Yana tasbihi ga sarkin da yake amsa Addu'oin bayinsa, yayi Addu'
a iya Addu'a akan neman zabin Allah akan mace ta gari.
****Washe gari su Baba malam dasu Abubakar suka wuce Nigeria, su Mahmud Kuma suka nufi Dubai, a hotel dinsa na gudun hijira suka sauka tunda Shima permanent room ya kama, a MJ.moritte Marquis hotel di
n, Zahra ta Kara tabbatar da Mahmud bana Wasa bane ganin irin wannan hotel din Daya Kama permanent daki a cikinsa zamansa yake Kuma ana biyan kudin daki duk wata tunda booking din monthly akayi shi.
Sun huta iya hutawa sunyi honey moon yanda ya kamata zahr
a taga gata iya gata taga soyyaya kamar ya hadiyeta sunyi wani irin mahaukacin kyau bare Zahra tamkar ka taba ta jini ya fito tayi Shar da ita ko uhum tace Saiya ce menene a Nan watan Ramadan Mai Albarka ya samesu, dole ya rage Zama har hakan ya tayarwa da
zahra hankali Dan baya dawowa sai gaf da Kiran sallar magariba har dai ta gaji tayi masa magana yace Mata aiki ne yayi yawa yanzu, ranar da suka Kai Azumi na bakwai Yana Zaune a office Yana karatun Alqur'ani Kiran Sister twins dinsa ya shigo, bayan sun ga
isa ne take tambayarsa " Waime yasa baka son Zama a gurin Zahra ne? kullum idan na kirata sai tace min baka Nan".
Dan murmushi yayi yasan juya abin Aishat tayi Amma ba haka abun yake ba kararsa kawai ta Kai gurinta, ita Kuma sai tayi Masa Education.
Ba wan
i rufa-rufa ya bude Mata aiki tunda ba kunyarta yakeji ba.
"Kina jina idan na zauna a gurinta wallahi matsala za'a samu dan azumi dai karya shi za'ayi bako tantama saboda wata irin fitina takeji da ita kwanan Nan wallahi wani lokacin sai munyi wanka muke s
allar insha'i da asham to gane min idan Ina zama gurinta sai mun shekara muna kaffara wallahi".
Tunda ya Fara Kora Mata bayani Aishat ke kunshe dariyarta.
"Ok na gane Zan Mata bayani, Amma Anya Bata da ciki kuwa? Kuje a bincika ana samun irin haka ga wasu
matan idan suna da shigar sabon ciki".
"Kai Anya bana tunanin hakan ba kune kuka dunga zabga Mata hade hadenku ba gashi Nan ya mayar da ita fitinanniya, ga azumi Kuma".
Dariyar ce ta kwace Mata Saida tayi Mai isarta sannan tace "nidai ba ruwana gyaran jiki
kawai nasa akayi Mata"
"Kuka sani dai babu Mai sakani kaffara Ina zaman zamana" dif ya katse kiran, Yana Jin dariyar Aishat din.
A ranar Bai shiga ba Saida yayi har asham sannan ya shiga ya sameta a kwance a parlour a kasan Kan carpet sai juyi take da sa
uri ya karasa Yana tambayar ta menene?
Mararta ta nuna masa. "Bari muje Asibiti".
Kai ta girgiza masa alamar a'a yanda yaga eyes dinta yasan da magana cak ya dauketa yayi bedroom da ita.
Karfe Tara na dare suna gaban doctor Mahmud ne ya fada Masa bukatars
u ta binciken madam saboda tayi fama da matsalar fibroid, Bai fito yace Yana zargin ko ciki ne.
Tashin farko ana Dora abun scanning saiga ciki kwance a mahaifarta, kusan wata biyu kuma lafiyayyan cikin da babu tantama, tun a gadon scanning din ya rungumeta
Yana godiya ga Allah da yayi musu wannan kyautar da kudi ko mulki basa badawa. Aishat ya Kira yayi Mata Albishir din cikin, yana fadar Ashe da gaske ne Abinda ta fada, kenan ba kowa ke kwanciya ciwo ba yayin laukayin ciki? Dariya kawai tayi masa, duk murn
a ta cikata tana son ta fesawa Ammi labari.
A ranar zahra taga kulawa ta musamman Dan biye Mata yayi ganin da gaske baby dinsa ne ya canzata.
Zahra taga soyyaya gurin Ammi Dan cewa tayi ya dawo Mata da ita Nigeria tunda Daman tayi fama da lalura a mahaif
a kada cikin ta samu wata matsala tunda lokacin da zahra ta fadawa Mahmud baya zamqn gida mummy Bada'a Aishat ta Kira ta fadawa itace tace ta tambaye Shi dalilin hakan tasa bazeqi fada Mata ba, to bayan ta Kira ta fada Mata yanda sukayi da Kuma Abinda resu
lt din scanning ya bayar shine mummy din tace ko gida ze dawo da ita tunda ga yanda abin yake kada su birke cikin, da kyar ya shawo Kan Ammin ta hakura suje umarar daga can suje Jordan din.
Sunyi umara sun karasa azuminsu a saudia ranar idi suka koma Madin
a duk da can suka sauka sukayi ziyarar qabarin Manzon Allah s a.w.w
A bin mamaki a can suka samu Ummee da Abie Suma sun zo sunyi umarar sunso Zahra ta kwana a gurinsu Amma kememe ta k'iya tace unguwa zasuje jidda gobe sun dawo,haka tabi Mahmud suka wuce a
i Bata son Abinda ze raba su dashi Nan kusa saboda yanzu ne komai ze tafiyar Mata daidai an Gama Azumi
Sun Riga su Ummee zuwa Jordan a gidan daya saya kusa opposite dasu Ummee suka zauna gidan da yake tafiya da imaninta ga shi ansa masa gidan Zahra Ashe na
ta ne.
Ranar dasu Ummee suka dawo a can take wuni har dare da yake ba 'yan fitinar bane a kanta,tun a saudia Ummee ke ganin zahra da wata Kama Amma fata furta Mata ba ta dai San da magana.
Watansu Daya a Jordan suka wuce Oman 'yar karamar k'asar larabawa c
e Mai dadin Zama ga wadatar arzikin man fetur.
Nan ma sunyi kwanan wata Daya a cikinta lokacin cikin watansa hudu dai dai lokacin ne Ammi ta hurawa Abbie wutar nacin ya yiwa Hussein magana ya dawo da yarinyar nan gida tunda cikin ya Fara mik'awa dole tasa
yayi maganar, badan Mahmud yaso ba suka tarkato suka nufo Nigeria, suna dawowa da sati daya suka nufi Azaren katagum, murna gurin Zahra kamar ta zuba ruwa kasa Tasha zayyan ne ya daukosu daga Bauchi inda suka sauka, Saida suka Fara shiga Azaren sai Kuma wa
ta irin kunya ta rufe zahra a hankali ta Kara shigewa jikinsa saboda da Abinda yayi musu shamaki da zayyan din da Daya daga cikin yaransa dake gaba.
"Nifa kunyar Ammah nakeji wallahi tunda magaji ya kirani yace min wai yagi su Ammah suna magana da Ammy Wai
Ina da ciki bakaga ko Ammyn na kasa hada Ido da ita ba? Kowa fa yasan Abinda akayi kenan fa".
Baisan lokacin daya Fara dariya ba, dan bilhaqqi da gaske kunyar takeji, ya gani a kwayar idonta.
"Gyara Mata Zama yayi sannan ya lakuce Mata cheeks dinta.
"Ki s
hare kawai kowa yayi aure Abinda ake fatan ganin an samu kenan shine Albarkar Auren ai bakiga idan babu haihuwa ana shiga damuwa ba har ya Zama matsala wani karshen Auren Kennan?".
Kai ta gyada Masa badan zata iya murje idanun ba.
Sai kusan shida na yamma
suka shiga unguwar Famfon shanu direct gidan Malam suka nufa Wanda aka rushe akayi ginin zamani,Sam zahra batayi mamaki ba indai shine to zeyi Abinda yafi haka. Suna tsayawa mutane sukayo chaccc saboda zuwa lokacin an San waye Mahmud din malam, suna Dubai
ya turowa da Habib kudi aka sayi shinkafa dasu filawa da suga,mai, gero da masara aka raba a unguwar a wadace harda kakocin unguwar unguwar.
Ciki Zahra ta wuce bayan sun gaisa da Baba malam ta samu iya Abu da wasu Mata biyu da alamar bak'i tayi, da farko b
ata gane zahra ba Saida ta karaso sannan ta waye da ita.
Sun gaisa tana ta kakabin yanda zahrar ta koma.
Bata Jima ba ta fito har lokaci Mahmud Yana tare da jama'a Amma tun fitiwarta hankalinsa ke kanta harta shige gida, da Auta ta Fara cin karo da gudu ya
juya yana fadin "Ammah! Ammah!! Ki fito ga Adda zahra".
Magaji ne ya dakatar dashi.
"Dallah ka cikawa mutane kunne a gidanwa kaga zahrar bayan dazu mukayi waya nasan kuwa da zasuzo zata fada min".
Sallamar Zahra ta kashe Masa fadan da yake yiwa Auta, Amma
h ce ta fito tana bin ba'asin fadan da ake yiwa danta sai ganin Zahra tayi tana shigowa cikin parlourn.
Ai tuni Zahra ta manta da wata kunya ta fada jikin Ammah.
"Kibi a hankali Mana keda bake kadai bace".
Sinne kanta tayi jikin kafadar Ammahn.
"Kai gaskiy
a gara dai ki haihu mu huta da halin yaran Nan da kike Mana a gidan Nan".
Magaji ya fada Yana nufo inda suke.
Bayan magariba Ammah da zahra suna Zaune suna hirar yaushe gamo irin ta da da mahaifi Ammahr ke fada Mata bikinsu Abdul Hakeem fa an saka shekaran
jiya duk gaba Daya za'ayi harda kanwar mijinki da aka bawa Habibun malam.
Sai lokacin ta tuna sakon sajeeda ta gani tana fada Mata an saka Rana ta basar ta dauka tana zolayarta ne.
Baywn insha'i Mahmud ya shigo suka gaisa da Ammah tayi Masa godiya abin Al
khairin da yayi Mata duk da tayi Masa ta waya, gurin Mama yace Zahra ta raka shi ya Kara dubata, sai lokacin zahra ta tuna da ita a gidan Dan tunda ta shigo ko duriyarta bataji ba.
Tare suka fita suka nufi dakin a hanya zahra ke tambayarsa.
"Amma dai ba ra
shin kirkin zaka Kara Yi Mata ba dai ko?".
"Kai! Nine marar kirkin?".
"To ai Lamarin naka ne ba'a ganewa a fuska sai ka aiwatar ake gani".
'yar dariya yayi.
"Kinci bashi".
Sau biyu zahra tayi knocking sannan aka bude, Saratu ce Autar su Mama ta bude ita ga
skiya tana da kirki ba kamar su Mamar ba, da fara'a ta Fara fadin "Masha Allah Ashe Amarya ce, sannunku da zuwa". Ya fada tana Basu hanya, Saida suka shigo ta rufe kofar ta biyo bayansu tana Kare musu kallo ta tashihi ga ubangjiin dake tsara halittar bayin
sa.
Mamar tana Zaune da casbaha a hannunta tana lazimi, saura kadan dariya ta kubcewa Zahra ita dai iya saninta da Mama Bata tab'a ganinta a Zaune Wai tana zikitillahi ba, tayi collapse tayi wata irin Rama ga bakinta ya karu sai idanu a waje, tana ganin Ma
hmud ta sadda kanta kasa tana jiran taji yau Kuma Dame yazo.
Har kusa da it's suka karasa zuka zauna a kujerar kusa da ita, saratu ta gaishe da Mahmud duk da ta girmesa nesa ba kusa ba,ya jajanta Mata Mai jiki, sannan Zahra ta gaisheta suka gaishe da Mamar
da jiki, Zahra dai tayi shiru taji yau Kuma meze baro Amma sai taji yayi shiru daga karshe ya Bata cheque na kudi Wanda suka girgiza zahrar yace a Bata gudunmawar bikin Yara da akayi ta tashi tsam ya nufi kofa Saida ya kusa Kaiwa kofa ya jiyo muryar Mamar
tana fadin Dan Allah ka karbi kudinka wallahi Abinda kayi min ma nagode.
Baibi ta kanta ba ya fice Zahra ma ta tashi tana fadin "Allah ya Kara sauki".
"Amin ya Hayyu ya Qyyum".
Saratu ta fada tana faman godiya, Mama na shafe hawaye ta Fara fadin "Zahra Da
n Allah ki yafe min Kona samu salama wallahi sharrin.shedan ne da Shawarar Aunty ladi Amma in Sha Allah bazan Kara yiwa kowa mugun Abu ba, Dan Allah ki bawa Abbqn ku hakuri yasa Baki 'yar uwarki ta koma ta karasa karatunta tinda ita shafi ce ta shafeta, to
mijin yace sai yaji daga bakin Abban naku ze barta ta koma shi Kuma nayi Masa magana har Ammah ma tayi yace duk Wanda ya Kara masa magana zega bacin ransa".
Sai hawaye, itama zahra zuciyar imani sai taji nata idon ya ciko da hawayen da sauri ta nufi kofa
ta fice itama, Dan da gaske tausayin Mamar ya kamata babu nuna isa ba izza ba nuna kin jini saima nadama karara a idanunta.
Data fito bayanan ya fice sai wurin goma ya kirata yace ta fito su wuce.
Satinsu Daya a Azare suka koma sokoto, cikinta nada wata bi
yar da 'yan satittika aka Fara bikinsu Habib da suhailat, Ya Abdul Hakeem da sajida, sai Aunty Rukayya da zakariyya Ya Abban sajida, ita Zahra abun ya hade Mata amma Kano ta nufa tunda an sassab'a kwanakin programs din da za'ayi.sun hade daurin Auren a Kan
o tunda na Ya Abdul Hakeem a kanon na suhailat a kanon Dan Alhaji sa'ad mahaifin su Sameer ne ze daura gana Rukayya Shima dai a kanon A masallacin Jama'a na round din Dangi aka daura Auren.
Sai dinner ce suka hade ta a Nan Azaren tunda Nan za'a kawo Amaren
sajida da suhailat, Aunty Rukayya Kuma sukayi tasu a ShopRite, ranar Azare taga bak'in 'yan gayu na gani kashe ni, anci an Sha a walimar Dan ko yaran makarantar malam Saida aka sabunta musu abinci Dan sun Sha gara a ranar lemon roba da ruwa kuwa tamkar a
kamfaninsu, lokacin da ake bikin Ubaidat tazo wani bikin itama a garin Nan take Jin labarin Habib yayi Aure a sokoto a family dinner su wani Mahmud Daya zauna a gidan malam Ashe shine young Rich guy din Nan MM DANGE Wanda yayi fice a kasar Nan harma da kas
ashen duniya, to shine fa ya bashi kanwarsa Kuma ya bashi aiki a Dubai.
Hankalin Ubaidat ba Karamin tashi yayi ba Dan kuwa hangen hadarin nesa tayi Ashe mugun matsolone ta aura bajintar a waje take sai dai da gida Mai kyau Amma wani lokacin taliya da manja
ake dafawa tayi data sani tafi sau dari.
Zahra Bata raka kowace amarya ba Mahmud ya dauketa suka wuce gidan Dan ta gaji iya gajiya.
Da asuba ma da kyar ta tshi tayi sallah, har Mahmud ya fice Zahra na barci Karan wayarta be ya tasheta wurin Sha daya, su
nan sajida ta gani yana yawo akan screen din.
Dauka tayi tare da sallama, Mai makon taji yanda ta Saba jinta sai ta jiya lukui kamar garin masarar daya sha nikan laushi.
",Ke Wai meye haka Zaki kirani kiyi shiru, ai ba zato taji shashshekar kukanta.
Wani m
urmushi Zahra tayi ta ayyana "anzo gurin".
"Bestie menene Wai kike kuka keda ba halinki ba".
Daga can taji dif an kashe wayar ta yukura ta tashi tana fadin "ku karata a ke soyayya ba ai gata Nan sai anji jiki kafin a Fara fuskarta komai 'yan Mata anzo han
nu".
Kwanansu hudu suka juya fir ya hanata zuwa gidan Amaren yace sai sun zama 'yan gari taje shifa yayi hating din wannan d'abi'ar ta malam bahaushe.
Sajida tayi mita harta bawa uku Lada ita dai Zahra bada