Showing 9001 words to 12000 words out of 295116 words

Chapter 4 - AUREN HUCE HAUSHI COMPLETE

gadon ne yace "ai ta farfado ba wata matsala ana so ne dai ta samu hutu sos

ai jininta ne yaso Hawa Amma cikin ikon Allah anyi controlling dinsa".

"Oh no 'yasu Allah ka dubi lamarin wannan 'yar maraiya duk da Bata tashi da rashin gata ba sai yanzu ka kawo Mata Tata jarabawar Allah ka shiga cikin lamarinta".

Aunty Hasana ta fad'a i

tama tana goge hawaye.

Baba Tabawa dasu Sajida suka amsa da "ameen ya Rabbi"

Dakin 'yan da'i da'a aka kaita tunda tana bukatar isolation.

Saida komai ya Zama dai dai an saka Mata drip sannansu Sameer sukaje gurin likitan. Fad'a yayi so sai akan yanda aka

yi har karamar yarinya kamar wannan damuwa tayi Mata yawa har har take barazana ga lafiyar ta.

A can gidan biki Kuma Amma ta rasa inda su Hasana da Inna suka tafi Dan hankalinta Bai kawo Mata Hajiya kaltume ma Bata Nan ba sai da abokiyar zamanta tazo san

nna ta fuskanci itama Bata Nan din wayarta ta dauko ta Kira Hasana, lokacin tana zaune gaban gadon da aka kwantar da Zahrar.

Sunan Ammah ta gani sai lokacin ta tuna Ashe Bata fad'a Mata ba.

" Assalamu Alaikum Ammah".

"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala

wabarakatuhu, wai Ina Kika tafi ne babu ke Inna maimuna ma Bata Nan Hajiya kaltume ma banganta ba".

Dan Jim tayi har Saida Ammah tace "kina jina?"

"Eh inaji Ammah duk muna tare dasu, muna Nan gurin Zahra Bata Jin dadi ne Amman da sauki yan haka barci tak

e".

"Wane irin zance ne wannan kamar Bata Jin dadi Kinga Hasana fadi min gaskiya yanzu kina Ina?".

" Muna F.M.C wlh jikin da sauki sosai kawai sunce ana dai San ta huta ne, kada ki tada hankalin Dan Allah".

"To Allah ya kyau Amma Ina hankali ze kwanta".

W

aje Aunty Hasanar ta fito gurin su Baba tabawa da sajida tace

"Baba tabawa Dan Allah kuje gida da sajida tasan inda aka aje abubuwan da zasu bawa kawayensu tunda yau zasu wuce sai ki fad'a musu tana gida gurin Abba, ta kalli Sajida ke Kuma duk tmbayar da

saying Miki kice Baki Sani ba mu barsu a haka".

Kudi ta mikawa Baba tabawan sannan ta karasa gurinsu Inna maimuna da Hajiya kaltume, Suma bayi tayi musu na Kiran Ammah tace suje gidan Dan hankalinta ya kwanta.

*********

Da kyar Amma ta Bari akayi sallar m

agariba ta shiga bangaren Alhaji Jafar ta same shi da Hassan da Abdul Hakeem suna magana akan Zahra Hassan Yana ta mitar meyasa Abban yayi haka ai da hakuri kawai akayi har lokacin da Allah ze kawo Mata wani.

Dan murmushinsu na manya yayi Yana "fadin wanna

n ma in Sha Allah Babu Dana Sani a cikinsa ni nasan nagartar Dana gani tare da yaron yasa na bashi, Kuma ko bayan Raina zakuce na fad'a muku".

Jiki ba kwari Amma ta gaishe da Alhajin tana Masa ban gajiya tare da godiya.

Sannan ta Dora da fadin "Dan Allah

ko zaka Bari naje Naga jikin nata?"

Tsai yayi Yana kallon ta "da kinyi hakurin zuwa Suma da anjima zasu taho gida yanzu ma daga cen muke ko zuwan mu Bai isar ba?"

Cikin Jin nauyinsa tace "A'a ya badatar"

Ta tashi ta nufi kofa da kallo Abban ya bita ita kan

ta tausayi take sashi da gani zuciyar ta ba Dadi.

Da sallama suka shiga dakin lokacin Aunty Hasana tana sallar insha'i ita Kuma zahra farkawarta kenan tana kokarin tantance Wai inane ma Nan din inda ta gani idan dai ba gizo idanunta ke Mata ba kamar asibi

ti.

Sallamar ce ta katse Mata tunani ta Dan dago kanta kadan sukayi arba dashi Ido cikin Ido da sauri ta runtse idanunta zuciyar ta na wata irin bugawa tana ambaton Allah a zuciyar ta, meya kawo wannan dodon nata gurinta, Kara rufe idanun tayi it fa wallah

i zata iya rantsewa Allah duk duniya ba idanun da suke figitata kamar nasa.

💋





AUREN HUCE HAUSHI

💋





Strory

&

Written

By

MAMAN FATIMAH



Page five



📖🖋



_______ Shiru dakin ya dauka har zawan lokacin da Aunty Hasan

a ta idar da sallar.

Dan juyowa tayi kadan tana fadin "wa'alaikumus Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, sannunku da zuwa Bismillah ga kujeru nan ku zauna".

"To mun gode Aunty" Sameer ya fada.

Cikin ladabi da mutuntawa suka gaishe ta ta

re da tambayar Mai jikin, ta amsa musu da sauki, sai kuma dakin ya Kara daukar shuru Zahra dai tunda ta rufe ido Bata Kara gigin budewa ba, ita ji take duk ya cika dakin ita tun ganinta na farko dashi a duniya ya birkita Mata lissafi, Kuma saboda Allah mey

a kawo shi gurinta asibiti duk da tasan mutumin Ya Abdul Hakeem ne Amma sai taga kamar ba sai yayi Masa Kara ba, ko Kuma yazo wata sagbar ne asibitni ya Sami labarin shine ya shigo ya dubata.

Magaji ne ya shigo dakin da sallama sai Kuma ya Dan tsaya baiyi

tunanin ganinsa ba Sam da fara'a ya karaso Yana fadin "Ashe Kuna Nan ai tare muke da Ya Abdul Hakeem ma".

"Ok" abinda Mahmud ya fad'a kenan

Shi Kuma Magajin ya karasa gurin Auntyn Yana gaishe ta.

Abdul Hakeem ne ya shigo Yana rike da wayarsa a hannu da

sauri ya karasa gurinsu Mahmud din Yana fadin "A'a angon ne da kansa" Yana Mika masa hannu.

Saroro Aunty Hasana tayi ita wace iri ce kawai dai taga sun shigo sun gaisa wallahi Sam Bata kawo ba ita da akace Mata Alamajirin Baba malam ne ai ta dauka irin w

annan gaddawan ne, yo ta Ina wadannan sukayi wani Kama da kolaye ai ita zallar ilimi ta gano da wayewa a tattare dasu.

Hanyar wajen ta nufa tana janye da hannun magaji duk sai taji kunya ta kamata Ashe sukanta ne.

Ita kuwa Mai gayya Mai aikin ai tana jin

an ambaci ango ta bude idonta girjinta Yana wata irin dokawa "ango a nan to waye a tsakaninsu da suka shigo tare?

Abdul Hakeem ne ya kalli gurin gadon Yana fadi.

"Masha Allah! Ashe kin tashi, ya jikin?"

Ya fad'a Yana karasawa jikin garon Sameer ma Dan mats

awa yayi Yana dubata Kai kawai ta gyada musu, tana kallon Ya Abdul Hakeem din, kallo irin na neman Karin bayani.

Yi yayi kamar Bai Gane ba ya juya yana yiwa Sameer magana suka fita.

Har suka fice Bai dago ba Yana ta faman tab'a waya sai da ya Mula Dan kan

shi sannan ya tashi ya tunkari gadon.

"Ya jikin?"

Ya fad'a Kai tsaye, Bai Kuma jira ta amsa ba Dan ko kwakwkwaran motsi ta kasa sai tunanin da yake Mata Kai komo.

"Badai wannan bane ake nufin an daura min auren dashi Amman da Naga ta kaina".

Shine ya kats

e tunaninta.

"Ki kwantar da hankalinki ki daina saka damuwa a ranki da kannan shekarunki, ki kuma dagawa Ammah

í

nata hankalin, idan nine bakya so ba damuwa Nima kusan hakan take. Amma kada mu watsawa iyayen mu kasa a ido Mana tun yanzu gara ki nutsu ki k

wantar da hankalinki daga baya sai a duba Mai yuwuwa tunda nasan bazaki so Zama da almajiri marar karatun boko mai zurfi, ga karqncin wayewa ga rashin madafa ta yau da kullum, Nima kasada ce tasa na yarda da tayin da akayi min tunda Naga nema ake a tozart

a min da iyayen a kunyata su a idon duniya aci mutuncin su".

Ita da'i ko motsin kirki ta kasa da gaske gani take duk ya cika dakin, ga wani fitinan kamshinsa duk ya cika Mata hanci.

A bazato taji ya Dan shafi gefen fuskarta idan ba kunnenta ne suka jiy

o Mata ba da'i dai ba sai taji kamar yace "my previous" a hankali sannan ya Mike Yana fadin "Bari a kawo maganin ki saimu wuce gida tunda doctor yace zamu iya wucewa, Amman yace ki rage yawan tunani Yana haddasa cututtuka".

Har dakin Amma Abdul Hakeem ya

raka Zahra lokacin duk yawancin bakin sun tafi sai 'yan uwan Amma na Mubi Dana Jimeta sai Kuma Aunty Hasana da take dakon dawowar su, ai tunda magaji ya Kara Kora Mata bayani akan Mahmud ta tafi daga asibitin tunda Mai dungurungum din yazo ita bataga ta Za

ma ba.

Saida ta matsawa Zahrar tayi wanka Tasha tea da magungunan ta kwanta sannan tayi haramar wucewa gida.

Sai wurin karfe Tara sannan Hajiya mama ta shigo dakin tana fadin "wallahi daga idar da sallar ta barci ya dakeni sai Dana tashi zilai Mai wanke

wanke take fad'a min an dawo da Zahra har sun shigo sun duba ta".

"Wallahi kuwa ai jiki da sauki yanzu Tasha magani ta kwanta"

"To Allah ya Kara lfy, Wai Hajiya wanene mijin yarinyar Nan ne naji ana fadar Wai cikin Almajiran baba Malam ne, shine nace haba

yaushe Alhaji zeyi wannan danyen aikin ya rasa bazai bawa aure Sai a cikin Almajirai".

Inna maimuna ce tace "ai mu Hajiya ko waye Alhaji Jafar ya aurawa Fatima wallahi mun karba da hannu biyu mun gode tunda mun San har abada Babu cutarwa a tsakanin Asama'u

da dashi da ita Fatiman da abinda ya Haifa bamu taba ganin banbanci ba, Dan haka mun karba da kyakykyawan niyyarsa Allah ta tabbatar Mana da Alkhairi".

Gaba daya suka amas "Amin"

Hajiya mamar ta Dan jima a dakin kafin ta koma dakinta.

Bayan Zahra tayi sal

lar Asuba ta gama Azkar dinta komawa tayi ta kwanta har lokacin kanta Yana Mata ciwo kadan kadan, sai gurin takwas da rabi Inna maimuna ta tasheta tana fad'a Mata tayi maza ta kimtsa Abbansu Yana nemanta.

A gurguje tayi wankan ta fito lokacin an kawo Mata

kunun gyada da fanke, kunun gyadar kawai tadan Sha kadan ta shafa lotion dinta ta saka doguwar rigar atamfa ko dankwalin Bata daura ba ta fito cikin takunta na nutsuwa Wanda da yawa mutane ke gani a matsayin yanga da jiji da Kai.

A tsakar gidan suka rinka

gaisawa da tsirarun yan uwansu na Mubi da sauran ma'aikatan gidan Mata.

Da sallama a bakinta ta shiga falon Abban nasu, tayi mamakin ganin kusan duk 'ya'yan Abban suna Nan sai su Ammah da Inna maimuna da kanwar Abban Maman lafia.



"Zo nan kusa dani Uwata"

.

Abban ya fad'a Yana murmushi, itama murmushin tayi ta karasa kusa dashi ta zauna nata fadar "Abbana Ina kwana?".

"Lafiya kalau Alhamdulillahi Uwata".

Sannan ta juya tana gaishe da jama'ar gurin.

Said Kuma dakin yayi shiru.

Abban ne yacewa Imam "Mai sunan

Malam ayi Mana addu'a".

Ya jima Yana addu'a sanan aka shafa. Sannan Abban ya Dora da cewa.

"Alhamdulillahi ala kulli halin, dole ne mu godewa Allah s.w.a a cikin kowane Hali mutum ya Samu kansa, kowa yasan yanda lamarin Auren Uwata ya ringa kasancewa a ba

ya abune ba Mai dadin maimaitawa ba, to wannan karon ma tarihine yaso maimaita kansa Amma na yanzu sai yafi sauran tada hankali ni Kuma Naga a wannan gab'ar bazan Kara bada wata kafa ba wadda za'a dunga walagigi da rayuwar yarinya karama ba kamar Uwata. Su

nanta Ya kira Fatima dago ki kalleni, cikin girmamawa ta dago kanta kamar yanda yayi Mata umarni. Hannunsa yasa ya nuna kansa yace kina ganin zan iya zaluntar k?" Da sauri ta girgiza Kai hawaye na zubo mata.

Yace "To Fatima na daura Miki aure da bakon yaro

n Nan Mahmud na wajen Aminina Malam Bukar". Duk da taji haka daga bakinsa a jiya Amma Bai hanata kara shiga rudu ba saboda wannan taji daga bakin da bazeyi Mata karya ba, Nan da Nan ialahirin jikinta ya shiga rawa wallahi ita a jiyan jinsa kawai take gani

take kamar almara ce kawai.

Muryar Abbansu ce ta Kara katse Mata tunani "kiyi hakuri Uwata kowa da irin jarabawar da ubangji yake Masa ki dauka taki jarabawar kenan, ki yadda da kaddararki sai Ubangiji ya jibinci lamarinki wannan ba hadin kowa bane hadin A

llah ne, kiyiwan mininmi biyayya in Sha Allah zakici ribar rayuwa, ki cire yaron Nan Musbahu daga zuciyarki ki rungumi abinda Allah ya baki. Allah yayi Miki albarka yanda Kika yi min biyayya Allah ya Baki 'ya'ya Wanda zasuyi Miki biyayya kema, Allah ya alb

arkaci aurenku ya tsone idon makiya da mahassada".

Hajiya mama ce ta fasa Kuka tana fadin "Haba Alhaji wannan wane irin danyan hukunci ne? ya zaka dauki 'yar marainyar Allah ka baiwa Wanda ba'asan asalinsa ba, ai duniya saita zage ka Dan Allah ka janye ma

ganar Nan da wannan ba gara kaba salmaun gidan Hajiya Dago ba tunda ya jima Yana son yarinyar Nan Amma ka Hana shi"

Kowa a falon kallonta yake ba Wanda ya tofa sai danta Hamza yace "haba mama menene haka kikeyi Dan Allah kiyi shiru da wannan maganar salman

un me Allah ya sauwake me za'a da wannan zuri'ar".

Hannu Abban ya dagawa Hamza Yana fadin "ya Isa haka tunda ka Bata amsa basai nace komai ba, Amman ki rubuta ki aje in Sha Allah sai wannan auren ya Zama abin kwatance Kuma abin alfahari duk Wanda ze za

geni ya Dade Bai zageni ba, Kuma duk Mai ganin zalunci ne yasa na aurawa Fatima Mahmud na barshi da Allah wallahil Azeem ban taba kallon Uwata a matsayin 'yar wani ba kullum Ina Mata kallon 'yata malak malak a makaranta ne kawai ban saka Mata sunana ba shi

ma nayi haka ne Dan tasan nata mahaifin ta rinka Yi musu addu'a".

Addu'a Abban yasa Imama yayi yaba kowa izinin tafiya Amma yace Ammah ta tsaya ita da Hajiya mamar da Inna maimuna da Maman lafia.

Aunty Hasana ce ta kamo hannun Zahra zuwa dakin Ammah tan

a kuka, yarinyar tausayi take Bata kamar yanda Abban ya fad'a ana walagigi da rayuwar ta.

Cikin bed room din Ammah suka wuce, bayan sun zauna ne Auntyn ta riko hannun Zahrar "kiyi hakuri kinji Allah Yana sane da halin da kike ciki, Dan Allah kad'a ki watsa

wa Abba kasa a Ido ki bijirewa auren nan wallahi irin wanna auren Yana albarka fiye da tunanin".

Wasu sabbin hawayen ta goge. Cikin shashhshekar kuka tace "wallahi Aunty nifa tsironsa nakeji idan muka hada Ido wani Abu nake gani a idonsa".

Sororo Auntyn ta

yi kafin tace "ban Gane ba tsoronss kamar Yaya, Daman kinsansa ne runtuni?.

Kai ta gyada Mata alamar Eh.

"Allah ya kyauta" kawai Auntyn tace.

"Ko meme ma dai wannan tsakaninku ne kin gyarota can".

Ta Mike tana fadin "Bari na koma gida sai zuwa an jima za

mu shigo da Sajida da Amatu itama Bata tafi ba jiyan.

********Tun bayan suka dawo daga sallar Asuba Mahmud yake ta faman aiki a cikin laptop dinsa, Yana kallon Sameer Yana kwasar barcin gajiya. Bai gama aikin ba sai kusan karfe takwas na safe, kai tsaye t

oilet ya nufa ya jima a ciki kafin ya fito daure da towel a kugunsa karami Kuma a hannunsa ya goge sumar kansa me baka sidik Mai laushi Saida ya shirts cikin wani farin yadi filtex marara nauyi ya feda turarensa Alburaq sannan yaje gefen bedside ya dauki w

ayarsa ya kunna.

Abinci ya bukata a kawo musu, yana Gama wayar Kira ya shigo sunan Habib ya gani, ya daga da sallama daga cen Habib Fara fadar.

"Habe Dan Allah dukka tadawa Baba malam hankali baka kwana a gida ba abinda baka Saba ba Koda wasa duk dare zaka

dawo Amma jiya daga Bari kaje ka dawo shi kenan kayi layar zana Kuma ka Kama ka kulle waya".

Dariya yayi Yana cewa "kana tunanin Kona bi dare nayi Gudun auren dole ko?"

Shima Habib din dariyar yayi.

"Ka Gudun Mana idan ka Isa mai wannan tsaleliyar Ina z

aya ya barta koka gudu ka dawo da kafarka, kawai da malam ne ya matsa yaji kana ina".

"Ok shi kenan Bari na kira shi Dan hankalinsa ya kwanta Ina Nan tare da Oga Sameer shine ya rikeni nayi Masa wani aiki".

Yana kashe wayar ya nufi sofa ya zauna yana jany

o stool din da aka Dora abincin.

"Oh ni Sameer yaushe na rikeka? ka rikeni dai ka Hanani tafiya ka barni da kame kame ga madam can tana fama da kanta ba mataimaki gaskiya yau in Sha Allah sai kano".

Ya fad'a yana nufar toilet shima.

Can hayin bankin suka F

ara zuwa gurin masu aikin gidan Masha Allah aikin yayi nisa kamar ba jiya aka Fara ba Sam an canzawa gidan fasali kamar bashi ba, duk abinda ake bukata Sameer ya danka shi a hannun Binya.

Sannan suka nufi cikin gari.

Wani mall suka shiga Mahmud ya jido k

ayan fruits dasu kayan tea sai chocolates dasu farm fresh yogurt da fresh milk. Leda uku aka cika manya Saida suka dauki hanya Sameer ya kalli Mahmud yana fadin "wadannan kayan fa yallabai na waye".

"Dubiya zamu saika Bata tunda ni dai kowa yasan bani da k

udin sayansu.

💋





AUREN HUCE HAUSHI

💋





🔷

Page six

🔷

P

📖🖋



________Sun jima a gurin Baba Malam Yana yiwa Sameer godiyar dawainiyar da yasha akan wannan lamarin, sannan yayiwa Baba Malam din sallama akan zai wuce sai hutu ya Kare zasuzo da mutanen s

u suna son su kawo wasu ayyukan da za'ayi.

Har gurin mota Malam dasu Habib sukayi Masa rakiya, Baba malam Yana fadin "Bari muyi addu'a".

Nan yaja doguwar addu'a akan Allah ya tsare hanya, har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login