Showing 285001 words to 288000 words out of 295116 words
tana barcin Allura batasan yaje ba,yau ga dan 'yar uwarta Mai ingizata tayi komai Dan Hana Allah ikonsa itace Dan cikinta ya yiwa yarinyar ta cikin shege.
Da kukanta share-share ta ringa fadawa
Sameer ya nemar Mata yafiyar Zahra akan abubuwan data yi Mata.
Kusa da Salis sameer ya zauna ya gaishe da Mahmud sannan suka gaisa dasu Salis din, sannan ya dauko musu tickets dinsu na jirgin Sha biyu da rabi na Rana, godiyar dai suka Kara yi musu har Mah
mud na fadin "wallahi idan ya Kara Jin godiyar na zasu bata.
**
Ranar da suka cika kwana goma sha biyu Mahmud tun dare ya fadawa Zahra ta shirya da safe ze kaita gidan Ammi shi kuma zeje Lagos wani aiki, Bai barta tayi barcin kirki ba a Daren,dan daga ba
ya ma cewa yayi ta shirya ta raka shi suje su wuni su dawo, da kyar ta samu ta lallabashi da kalamai sannan ya hakura Amma Saida ya Kara rage tafi.
Tun asuba zahra ta Kira Aunty zilai suka Fara aikin dabun kaji dasu cake sai da sauran tarkacen snacks Tunda
su duka gwanayene kafin takwas da rabi sun Gama hada har breakfast, sama Zahra ta koma lokacin Mahmud ma ya farka Dan nine thirty flight dinsu ze tashi daga sokoto zuwa Lagos. Tare suka fito sukayi break sannan yace ta dauko gyalenta su tafi ya ajeta ya w
uce, fada Masa tayi tare zasu tafi dasu Aunty zilai, waya ya yiwa zayyan ya saka wani ya kaisu Aunty zilai can family house nasu, lokacin da akace su fito sai gani yayi ana ta fitowa da manyan warmers ana sakawa a boot din mota, Bai nemi Jin abasin menene
ba itama Bata fada masa ba.
Su suka Fara yin gaba sannan suma suka fice daga gidan, sunzo wucewa ta kofar gidansu Dr Haseenah ya Dan shafo cinyarta, tsuke fuska tayi tasan abinda yake nufi.
"Komu shiga ku gaisa tana garin har yanzu Tunda Nima Ina garin kin
san lokacin da Ina Nan ai a Nan take aiki Saida nabar garin ta koma Kano da aiki Tunda daman a kanon aka riketa kuma masu fada aji ne, jiya da har zatazo ku gaisa sai tace sauri takeyi gurina kawai tazo wani lokacin ida ta dawo ta shigo ku gaisa".
Hade Rai
tayi ta hade gabas da yamma tayi kicin-kicin duk yanda yaso ta kulashi tayi banza dashi har sukaje gidan.
Abbie baya k'asar yaje Benin republic akan wasu Kaya nasa da aka rike a can.
Direct part din Ammi suka nufa duk yanda yaso ta saki ranta abun ya fask
ara Dan da gaske ya Bata Mata rai ita fa ta tsani matar Nan ba kadan ba shi Kuma ya kasa ganewa.
Yana tsayawa tayi wuf ta fice Bata tsaya ya fito ba ta wuce Abinta tana ayyana itama ai Amminta ce bazata tsaya shi ba,Amma kafin takai ga kofar parlourn ya ci
mmata.
"Ke meya faru Wai kike ta hade min Rai haka?".kauda Kai tayi tana jin zuciyar na Mata zafi.
Janyota yayi ya rungumeta a Nan da sauri ta dago tana rarraba idanu.
"Dan Allah ka sakeni kada wani yazo ya ganmu a haka wallahi ba komai,Dan Allah ka Bari k
ada ace bamu da kunya plssss...."
"Baki San anyi min tambarinta ba a gidan Nan wannan ai ba wani Abu bane,nida kace nayi abun a gidan Nan ko kin manta?".
"Ai sharri ne wancen, wannan Kuma gamu in reality ne".
"To shine me? Ai ba haram bane ko.....,"
Bai ka
rasa ba yaji alamun za'a bude kofar da sauri ya saketa Dan bazeso kannensa ko Ammi su gansu a haka ba,ko maid din Ammin sai girma ya Fadi.
Sahalatu ce 'yar Babban yayansu Abdallah da Afnan da hannunta suka fito, ai yarinyar na ganin Zahra ta Fara zillo tan
a dariya, itama zahrar dariya tayi Mata ta nufesu da sauri ta karbeta daga hannun sahalatun tayi wuf ta shige tana amsa gaisawar yarinyar.
Ammi ce dasu Aunty Aishat a parlourn farkon sai Aunty zilai daga gefe a zaune bintar dai Bata gurin Zahra batayi mam
aki ba Tunda ita 'yar gida ce, gaba Daya suka amsa sallamarta cikin nutsuwa Zahra ta karasa kusa da Ammin ta tsuguna har kasa tace "Ammy Ina kwana?".
Ammi wadda bakinta yaki rufuwa saboda farin ciki ta amsa Mata "Lafiya kalau Zahra ya gidan naku?".
A kunya
ce ta amsa "lafiya kalau Ammy".
Ammin sai hamdala take yiwa Allah Daya azurta danta da irin wannan matar, a Nan Kan carpet ta zauna duk yanda Ammi tayi akan ta tashi ta zauna kiyawa tayi sai hakuri Ammin tayi.
Zahra tayi mamakin Ina Kuma ya tsaya Bai shigo
ba? Saida ta Jima da Zama sannan ya shigo ta baya Yana amsa waya taji Yana fadin "ka sayi ticket din online yanzu" Tunda ya shigo Ammin taga ya wani Kara girma da haske ga cikar Kamala da taga yayi da gani ya samu kwanciyar hankali.
Kusa da Ammin ya zaun
a Yana gaisheta suka gaisa da Aishat wannan su batool suka gaishe shi, tashi su batool sukayi suka koma wani falon Aunty zilai ma kitchen ta nufa Tunda ta Saba tana Taya masu aikin aiki a Dan zaman da tayi kafin ta koma gidan Zahra.
Parlourn ya rage daga A
mmi da Yan biyunta sai Zahra da Afnan hira suka Fara a junan su Zahra na Zaune tana yiwa Afnan wasa, hira Mahmud yakeyi Amma 100% hankalinsa na Kan Zahra har dai Aishat ta gaji ta jefa masa tambayar data bashi mamaki.
"Waini bros ko dai laifi kayiwa madam
ne Naga ka kasa nutsuwa sai kafeta da Ido kakeyi irin na neman sulhu din Nan".
Dan murmushi yayi Yana Dan shafa gefen sajen fuskarsa.
"Ko Daya kawai burguni sukayi ita da Afnan yanda suke kaunar juna tamkar sun shekara da sanin juna, ki karbeta ma tafiya
zamuyi".
A tare Zahra da Aunty Aishat suka kalleshi Bai kalli zahrar ba Aishat ya bawa attention dinsa ..
"Zuwa Ina kuma mobile?".
"Lagos zamu".
Ai Zahra Bata San lokacin da bakinta ya subuce ba tace.
"Kaiiii..meu amor bafa haka mukayi da kaiba, kace fa wu
ni zamuyi a Nan Kuma yanzu zaka ce wai tare zamu Dan Allah ka barni na zauna a Nan din plssss...."
Saida ta Kai Aya ta Farga da inda suke sauri tayi ya rufe fuska da gyalen dake jikinta.
Yau taga ta kanta ita wace iriya ce.
Dan murmushi Ammi tayi kawai tas
an da wata a kasa saita basar Aishat ce ta shiga maganar "a'a kuyi tafiyarku kawai ba wani wunin da zakiyi Tunda kukazo kafa ya kafa ai nasan tafiyarku Daya idan yayi niyyar ki wunin ai ke kadai zakizo amma fa su binta suka Fara zuwa".
Sai lokacin Ammi ta
tuna an kawo musu abubuwa ganinsu ya shagaltar da ita.
"Zahra munga sako fa. Allah ya saka da Alkhairi mun gode kwarai da gaske".
"Meta kawo ne haka Ammi?".
"Ina ruwanka ku tashi ku tafi kada kuyi missing flight".
Narai narai Zahra tayi da fuska kamar zat
ayi kuka.
"Tashi kuje kinji Tunda haka yakeso Allah ya tsare gobe ma Rana ce sai kizo ki wunar min din kinji".
A kunya ce ta tashi tana fadin " To Ammy nagode mun tafi sai mun dawo".
Har gurin mota Aishat ta takasu tana mitar Bai Bari zahrar ta shiga saur
an parts din gidan ba.
"Bari kawai da anan zata wuni sai Kuma ta nemi ta hanani sakat idan na tafi ma babu nutsuwa Dan yanzu ta birkice min a hanya ai gara muje tayi min bayanin abunda nayi Mata, idan tana Nan ai wallahi aiki baze yuwu ba zuwan banza zanyi
, nifa Naga alama sai yanda Hali yayi Dan yarinyar Nan..., Ki bari kawai sai mun zauna".
Hannu Zahra tasa ta dafe kirjinta, tana mamakin furucinsa.
"Wallahi Aunty fada kawai yake ni babu Abinda nayi masa kawai dai bana son Yana min maganar wannan doctor di
n shi Kuma Koda yaushe sai ya yi ta yi min maganarta ni Kuma banaso".
"A'a gaskiya tayi ma hakuri idan nice saina maka yaji wallahi kawai ka tasani gaba kana min zancen wata ai baka taki gaskiya ba" ."Hummm kinsan abinda yarinyar nan tace Mata Ranar dana n
una Mata sabon gidansu?"..
Girgiza Kai tayi alamar a'a.
"Cewa fa tayi Wai mace ba gaba ba baya"
Aishat Bata San lokacin data fashe da dariya ba.
"Well done, wallahi ba karya tayi ba to Kai karya ta fada?".Kiran wayar da akayi masa ya katse maganar da suk
eyi.
Abinda aka fada masa yasa yayi saurin duba agogon dake daure a hannunsa.
"Bari mu wuce lokaci yaja kada muyi late".
Karfe Sha daya har sun karasa gidansa na Lagos Tunda tsakanin gidan da airport din babu nisa sosai nan ma Aljannar duniya ce dan Sai ta
ga kamar yafi kowane gida kyau ma, dan daya wuce wurin meeting kasa Zama tayi a kowane parlour, bedroom ta koma ta rufe kanta dan abin yafi karfin tunaninta, to Dan Allah shi wace irin dukiya ya mallaka haka da kananun shekaru irin nasa? ita fa tana Jin ts
oron irin wannan dukiyar a gurin matashi kamarsa gaskiya.
AUREN HUCE HAUSHI.
Maman Fateemah
09062432330
08055362975
Page 96
________Karfe shida da kwata su Mahmud suka shigo gidan shida Sameer da zayyan dake driving dinsu, Basu tab'a tunanin zasu K
ai wannan lokacin ba a gurin meeting din, suna cikin meeting ne kiran gaggawa ya shigowa sameer injinan sabon kamfanin hada Madarar gari da 'yar Amana condensed milk suka karaso Wanda za'a bude a Azare,tunda tuni an Gama ginin gurin, to dole suka nufi dep
ort can tincan island, Saida sukayi clearing din komai suka baro gurin, sai Kuma goslow ya rikesu.
Mahmud na sauka Shima Sameer ya sauko zayyan ya wuce da motar ma'adanar aje motoci, ciki suka shiga shi Kuma zayyan ya wuce nasa masaukin dake wani bangare
na gidan.
Shiru parlours din duka babu alamar dake nuna da mace a gidan Dan da alama ko abincin dake saman table ba'a tab'a ba, jakar laptop dinsa Sameer ya aje Yana fadin."Bari naje ba watsa ruwa naji Kiran da madam ke jera min lokacin muna meeting kasant
a Bata da hakuri yanzu haka danta ne yake Zazzabi Dan dazu da safe take fada min wai taji jikinsa da dumi ga Kuma mura".
Kallo daya Mahmud yayi Masa Mai nuna alamar baka da hankali.
"Meya faru kuma?".
Coat dinsa ya cire ya nufi ciki ba tare Daya tanka Masa
ba, Dan murmushi Sameer yayi yasan halinsa na son Yara da tattalin mace wato yayi laifa kenan.
Shima juyawa yayi ya fice Yana ayyana idan oga yayi nasa yaran ko Yaya, yasan dole ya Basu kulawa fiye da tunaninsu dan Sam baya Wasa da Lamarin Yara Allah ya
jarabce shi da son Yara matuk'a.
A kalla Saida ya shige parlours biyar sannan ya haura steps ya shiga corridor Wanda aka kawata shi da wani irin mirror Mai shegen kyau irin Wanda ake ajewa din Nan a corridor,bedrooms hudu ne biyu na facing din biyu, Wanda
ya barta a ciki ya nufa, ya gaji iya gajiya, Kati ya saka ya bude kofar, can karshen gado ya ganta a takure kamar Mai barci, da sauri ya karasa Yana fadin.
"Menene precious?".
Shiru tayi Masa Dan yau dai tayi dana sanin biyo shi Lagos yafi sau shurin mas
aki, Dan wuni tayi da yunwa ga fridge din dakin ruwa roba biyu ne kawai a ciki sai tarin lemukan gwangwani irinsu Pepsi da Coke ita Kuma ba kukanta Nan ba.
Zama yayi kusa da ita Yana dago da fuskarta, ba zato yaga ruwan hawaye suna bin Kumatunta.
"Subhanal
lahi! Previous meya faru?pls fada mini, baki da lafiya? Me yasa Ina ta kiranki Baki daga ba?".
Babu amsa Daya data iya bashi sai kwantar da kanta tayi a jikin gwiwuyinta.
"Ya subhanallah! Wai fushin ne har yanzu ba'a huce ba? Kiyi min magana Dan Allah kada
ki sakani a damuwa mana, to Bari na Kira Miki Ammi ko Ammah wata qila su ki fada musu Abinda yake damunki".
Ya fada Yana kokarin Kiran wayar.
Da sauri ta karbe wayar tana fad'in.
"Ni wallahi tsoron gidan nakeyi tunda ka tafi ko kofar dakin Nan kasa fita n
ayi Ni dai ka mayar Dani sokoton gara can da nan, kace wuni Daya zamuyi gashi har dare ya kawo jiki muna garin babu alamar tafiya, Kuma nifa gaskiya hankalina ya kasa kwanciya da abubuwan da nake gani a tare da Kai,Wai kana nufin wannan mahaukacin gidan ma
naka ne, idan haka ne to sai dai idan kana da wata sana'ar a boye wadda ba kowa ne ya sani ba" .
Mahmud tsayawa kawai yayi Yana kallonta, bil haqqi da iya gaskiyarta take maganar, tsura Mata idunusa yayi Yana Kara nazarinta, yama rasa Abinda ze ce mata.
S
aida ya hadiye wani busashshen yawu Daya kalato daga bakinsa ya hadiye sannan ya Sami zarafin yi Mata magana.
"Kice ko abinci Baki fita kinci ba kenan? To me kike tsoro a gidan Nan Dan Allah? Gida da jama'a a kalla sun Mutum talatin Amma Kika takure kanki?
Na fada Miki yanzu ma Zan Kara fada wallahi babu Abinda ze sameki sai ikon Allah Amma Dan mutumci dai Kam kafin ya cimmiki ya Kai kasa da karfin Allah,wayarawa an zo a duba min ke ance bakya Nan a duk parlours din gidan, sera tace Sam throughout Bataga k
o gilmawarki ba,na shigo Mai makon special we'll come sai bacin Rai harda hawaye ga zirgina da kika Bari shedan ya sauwala Miki a zuciya, kina zargin ko Ina kauce hanyar Allah a gurin nema na ko? To Bari nayi sallah na dawo nayi Miki Abinda Ina ganin kamar
ze gamsar dake".
Ya tashi tsam ya wuce toilet ya barta tana shefe hawaye.
A gurguje yayi wanka ya fito baibi ta kanta ba ya Dan shafa lotion ya zura jallabiya ya baza turarensa ya wuce masallaci.
Itama shiga tayi tayo Alwalarta Bata bukatar wanka Dan wuri
n biyar da rabi tayi nata da taji wani Abu Yana fita daga jikinta, ita abun harya Fara damunta ita kadai sai tayi ta mutsu mutsu.
Bai shigo ba sai kusan takwas da kwata Dan harta kwanta suna chart da sajida da Amatu a group da suka hada mujiba ce Bata onli
ne sai Dan biki suke mata data fada musu suna Lagos, Dan caaa sukayi Mata suna fad'in lallai a samu musu Dan Legos ladar meeting.
Kusa da ita ya zauna Yana Dan leken wayar boyewa tayi.
"Inyeh kice na zage dantse kenan, da Ina Shirin mubi flight din seven t
hirty,kice na fasa booking din mu kwankwaje a nan tunda bestie ta zabar Mana nan'.
Shiru tayi masa kamar kurma.
"Ke! Wai Dan Allah me nayi da zafi haka ne? Ki rufa min asiri kada na kasa gane komai, wallahi kinji na rantse Miki duk abinda Kika gani da Wand
a Baki gani ba duk halaliyata ne idan Ina wata sana'ar da take haramtacciya ko Ina wani Abu daya sabawa shari'a Ubangiji ya....... Da wani irin hanzari ta toshe bakinsa da tattaussan tafin hannunta tana girgiza Masa Kai, idanunta sun cicciko da hawaye.
"Wa
llahi ba Ina zargin kana sabawa Ubangiji bane kawai abun ne Yana bani tsoro, naganka yaro da Kai Amma ka mallaki Abinda yafi karfin tunanin mai karamar brain irin tawa, amma kayi hakuri bazan sake maka tambaya irin wannan ba Naga kana niyyar debo rantsuwa
kawai Dan kaga Ina fushi,na fa maganar Dr din Nan ce banaso, Allah da gaske bana sonta har zuciyatw wallahi".
"Sorry my previous na daina har abada kada ayi min tawaye a gudu Jordan kamar yanda akayi niyya a can baya saboda ita, da yake Allah ya tarfawa ga
rina nono yasa a ranar naji kamar ana ingizoni na taho da yake Allah Alhakimu ne Saida aka nemo min ke da tsohon dare danma a lokacin ba wani caring kawai dai gani Nan ana kallona Ina ragaita ba'a nunawa kurciya baka ba, tashi muje ki Samar min Abinda Zan
saka a bakin salatina kafin nayi aikin bada hakuri kada ayi min nak'i".
Ya fada yana dariyar Nan tasa Mai sakata shagala da kallonsa.
Itama dariyar tayi tana kokarin tashi tana fad'in "yau dai anyi abun kirki babu 'yan.."
Bata karasa tunanin ba taji sauka
r hannunsa a jikinta, Batasan lokacin Daya furta "Ashe ba'a yabon dan kuturu Saiya shekara da yatsu".
"Gaskiya Kam ai kena gani kamar kina bukata ta a kusa dake ko ba haka bane?".
Shiru tayi Masa idan ta biye Masa zeta Bata kunys ne kawai, ta rasa ta Ina m
a ya ganota.
Basar da maganarsa tayi.
"Tashi muje kaci abincin kaji meu Amor,.nasan kana Jin yunwa ko?.
"A'a muci dai kema ai bakici ba, tun break din safe". Tare suka fito Yana manne da ita.
"Wai me kike tsoro a gidan nifa tsoron Nan naki Yana damuna king
a duk gidajen ki haka suke sai dai idan abokiyar Zama kikeso to wannan fa sai ta ringa debe Miki kewa yanda zakuna Jin motsin juna ai hakan yayi Miki ko?".
Da sauri ya raba jikinta da bass kamar wadda huta ta yiwa shocking.
"Kishiya Kuma? Har ka gaji Dani
Nan da Nan haka? Daman abunda kake fada min ba gaske bane harka Gama Dani Kuma sai wata? Na shiga Tara, Dan Allah Dame na kasa maka ko ba irin type din da kakeso nake ba"..
Sai hawaye sharrrr.....
"Ya salam.! Previous meya hau kanki ne Wai tsakanin jiya da
yau? Wace iriyar magana ce wannan marar dadin saurare, kece na gaji dake? koko ba irin type din da nakeso ba? Wallahil Azim ban tab'a son wata mace ba kamarki tunda Allah ya halicceni idan Kika cire uwata to ba'ayi ba Kuma Ina ganin har abada babu wata ma
ce da zata samu matsayi irin naki