Showing 153001 words to 156000 words out of 295116 words
Dade ba sukayi sallama, Saida ta Gama sannan take fadawa Zahra yayanta Abba yace a gaisheta.
"Yar dariya tayi tana tuna farkon haduwar su wadda itace sila.
"Wato
Aunty Rukayya Ina Kara girmama.girman ubangiji idan naga wani connection din, gaki dai garinku Daya amma da yake haduwar taku nice connecter Saida ciwo ya kamani kamar baze kyakeni da Rai ba, har ya Zama sanadin Zuwana garin Nan ganin likita aka Bata min r
ai naji gara kawai na tafi inda Zan Dan Sha iska Kota awa goma ne, ashe akwai dalilin da yasa zuciyata ta azalzala nabar gidan da Alherin da Zan qullla a can, to wallahi Aunty haihuwar farko idan mace ce Fatima ce gaskiya shine tukuici ne".
Ta fara dariya
ganin Aunty Rukayya ta ware Mata idanu.
"Ki Fara kokarin aje Mana namu babyn kafin kiyi tsallen Albarka ki Fara lissafin dokin Rano Mai Rai da matacce".
"Kai Aunty nifa da saura tukuna bakiga bani da auki ba". Ta fada tana wata dariyar.
"Zakiga rashin auki
iya ganinki, Ina tausaya Miki yarinya wallahi Ya Mahmud ba irin ragwagen mazan Nan bane, ni bansan abinda mommy ta ankare dashi ba ta wani rikice a karawa 'yarta gyara har yanzu budurwa ce".
Kunya maganar ta Kara Bata,daman ana ganewa idan anyi wani Abu
da mace kenan? ko duniyanci mace keyi da akawi masu ganewa.
"Dan Allah Aunty ki Bari Allah kunyarki nakeji".
Ta rufe fuskarta da tafin hannuwansa farare sol dasu.
"Ni ba wata kunyata da kikeji, da kina Jin kunyata da Baki Fara dauko zancen ba. Gaskiya gobe
Zan dawo da Mai kunshi da gyaran jiki tayi miki duk da ba wani Abu da jikin yayi Amma wanka dadin kyau inji Yan magana, ai gara a Fara amarcin nan ko Yaya na ya Kara samun nutsuwa".
Kafin Zahra tayi magana kamshin turarensa yayi musu sallama da sauri Zah
ra ta Fara waige waige Dan yanda taji kamshin Yana Daf dasu ne, Ido huhu sukayi dashi Yana tsaye ya harde hannuwansa a kirjinsa as usual yana kallonta Basu San ta inda ya shigo ba.
Rukayya ce ta Fara fadin "Lah! Ya Mahmud sannu da zuwa tana mik'ewa tsaye,
a hankali ya tako Yana fadin.
"Yauwa Ruky sannu da kokari".
Ya fada Yana kallon zahra kasa-kasa.
"Sannu da zuwa"
Zahra ta fada Yana kokarin Hawa stairs, sai Mai lura ze kula da Dan kallon da yayi Mata a fusge baice komai ba yayi hayewar.
"Auntyn mu haka k
ike tarbarsa idan ya dawo? Maimakon ki tafi ki shige jikinsa ki ringume kayanki ki bashi happiness, saiki zauna kina fadin wasu local words ai masu fadar haka sai irin mu kanne da saura hadimai".
Baki ta turo.
"Kuma a gabanki Zan Masa hakan? Wlh bazan iya
ba".
Wayar Rukayya ce ta dauki qara alamar Kira ya shigo tana cirowa taga sunan ya Sameer.
Tana dagawa tace "gani Nan".
Ta wurga wayar jaka ta nufi kofar fita,da sauri zahra tabi bayanta da babbar ledar da karama tana fadin.
Aunty Rukayya Baki dauki kayank
i ba".
Da sauri ta dawo tana Fadi Babu abinda zan karba kije kiji da Yayana Yana bukatarki kusa dashi" .
"Allah sai kin karba ko naje na fada masa ya Baki da Kansa".
"To kawo ki koma ki tarairayi kayanki Kinga an kusa Kiran magriba, na gode kwarai da gaske
"
"Ki gaishe min da mommy kiyi Mata godiya kafin nazo".
"In Sha Allah Zan fada Mata".
Ta fada tana ficewa daga parlourn.
Cikin takunta na halitta Wanda wasu ke ganin tsabar yanga ne Dan tasan yes tayi ta ko Ina, ta nufi stairs din itama ta haura kenan ta
shiga hadaddan falon saman kawai taji an yi sama da ita ana juyawa.
"Wayyo Allah na!"
Ta fada a shagwabe Saida yayi juyi biyu ya sauketa a Kan sofa da take gefe ya shige jikinta Yana shinshinar kamshin da yake fita ta bayan kunnenta,da gaske yayi missing d
inta na wuni gudan nan ba kadan ba. Yana ganin nan gaba kadan dole ta Zama brief case dinsa ko Kuma credit card tunda yanzu an samu modern technology.
"Precious".
Ya fada deeply.
Da kyar ta samu zarafin amsa Masa.
"Na'am".
"Wai bakiyi kewata ba? Na dawo
ba irin welcome din Nan Mue Amor dinki ya dawo, ki taho kiyi hugging dina kina bani hot kisses left and right".
Ya fada yana sakar mata hot kiss a wuyanta, hannuwansa suna Kai kawo a jikinta, cikin rawar murya ta Fara fadin "Pls Amor meu (my love) Dan Al
lah".
"Dan Allah me? Eu amo voc
è
(I love you).
Ya fada cikin kunnenta.
Kankameshi tayi Dan ba karya sakon Yana zuwa inda aka aike shi, cikin muryar data jiku da desire ya fara Mata magana cikin kunnenta "Wai Baki San Ina tare da kishirwarki ba? ki barni in
rage zafi Mana babu abinda zan Miki ai har yanzu bamu shiga master bedroom ba Wanda akayi shi is for you only,kin gane ki barni nayi Wanda nakeso a Fara rage wannan kunyar da zata cutar Dani,sabuwa Kar zan kaiwa Ammina ke ta ganki a yarinyar ki ban taba
komai ba".
Runtse Ido tayi kalamansa sun mata nauyi, ita fa wani lokacin mamaki yake Bata yanda yake treating nata kamar ya shiga zuciyar ta yaga yanda take son tsara future dinta.
Sabgarsa yaci gaba dayi karshe ma daukarta yayi ya nufi bedroom din Daya kw
ana ciki yayi musu masauki a tsakiyar gadon,da gaske dai fitinar yakeji ta gasken gaske.Dan ba Karamar yamutsa Masa lissafi ganinta yayi ba, abubuwan Daya saka tayi Masa sun girmewa saninta duk tsumar da jikinta keyi Bai saurara Mata ba Saida ya samu nuts
uwa sannan ya kwanta a Kanta Yana sauke numfashi.
Shiru sukayi Kamar Allah Bai hallici mutane a dakin ba, a hankali ya rada Mata.
"Precious fada min me kike tsoro ne naji har yanzu jikinki Yana rawa?"
Juya masa Kai tayi gefe, ita ya kyaleta da abinda yayi
Mata ma Mana sai Kuma ya Kama tambayarta salon ya hanata sakat kenan, batayi magana ba saima rife ido da tayi.
"Za kiyi bayani ne, Ina nan zakizo kina nemana Ina Miki yanga ki Bari ki Zama 'yar hannu ina ganin saina ringa guduwa dan Naga alama bazaki saur
ara min ba irin wannan styles tab, rufe idon gulma ne kawai kike min tun yanzu kina bani irin wannan inaga labari ya Sha banban, gaskiya Allah ya sakawa su Abba da Baba malam da Alkhairi da suka gwangwajeni da irin wannan gwanar, Allah ya biya Ammah da Alk
hairi data Baki cikakkiyar tarbiyya, ya jikan su Ummee da Abie yasa Aljanna makomarsu".
Shashshekar kukanta yaji "ya Salam menene kuma?"
Ya juyo da ita suna facing juna, Kai ta girgiza alamar ba komai.
"Ki fada min meye?.
"Ba komai kawai ka tuno min da mah
aifana ne Wanda ban taba sanin ya dadin iyaye yake ba,duk da ban taso cikin kukan maraici ba Ammah ta tsaya tsayin daka ta hanani wannan kukan".
"In Sha Allah Nima har abada bazaki kukan marairaicin ba a zamantakewar mu, Zan Baki farin ciki Zan zamar Miki
komai na rayuwarki, daina kuka kinji my precious, idan da abinda bana son na gani a rayuwata to kukanki ne, yana taba min zuciya".
Lallashinta ya shiga yi da kalamai masu kwantar da zuciya a haka har ya shagalar da ita ganin Yana neman komawa ruwa yasa ta
kwace Kanta ta matsa gefe tana maida numfashi tare da fadar.
"Ana Kiran sallah".
Mirginowa yayi Yana fadin "Naji ba wani Abu zakiyi min ba, ki Bari na Kara Jin duminki Dan Allah".
Tanaji tana gani ya Kara kanainayeta a jikinsa, da gaske fitina yakeji Kuma
so yake ya bude Mata Idanu dole.nan ya lalace ba zato ya tsinkayo ana tada kabbarar sallah mirginawa yayi gefe ya Mike yasa hannu ya daukota ya nufi toilet.
Ruwa ya hada suka shiga tare Nan ma ba karamin kauda Kai yayi ba da saiya sake yamutsa ta shifa ga
skiya dole yayi abinda ya kamata a kwana kusa din nan, ya rigata fitowa a gaggauce ya wuce masallacin duk da an Gama sallar.
Bata Dade ba itama ta fito tayi ta tattarra abinda ya kamata ta wuce dakin tada bawa kanta.
Bayan ta Idar da sallah ta tashi ta kom
a ta gyara dakin ta cire bedsheet din yaje ya saka a injin wanki, ta canza wani bedsheet din ta Kara karfin A/C ta fesa freshner ta Kara Zuba wani a burner ta kunna ta janyo dakin, ta koma ta gyara wancan ma ta saka wasu fitinannun kananun Kaya riga da wan
do ta karasa busar da gashinta ta shafa man gashi da hair spray ta matse gashin da pink din band kalar rigar, lokacin da aka Kira insha'i after dress ta Dora tayi sallah tana azkar din yamma da Bata Sami damar yiba ya shigo dakin, ganin tana Addu'oin yasa
ya juya ya fita.
AUREN HUCE HAUSHI.
Maman Fateema.
Page 53.
_________Zahra na gama azkar ta cire after dress din ta fito, bude dayan bedroom din tayi baya ciki, batayi attempting din shiga dayan bama tunda bataga an bude shi ba. Ita fa
jiya ya barta da tarin damuwa da tunani Wai kaurace mata yayi kenan? Wato ita matar shige ce ko? Da wadda ya gurzu da zafin soyayyar ta ne dole ya ringa ririta ta duk tsiyar da zata shuka Masa, amma ita Bata jiba Bata gani ba ya mayar da ita sakarai, shiy
a Kaita gurin da suka hadu da musbahun amma yazo Yana Mata zafin Kai haka kawai badan Allah yayi Mata gyadar dogo ba sama 'ya'ya kasa 'ya'ya da yanzu labarin yasha banban wata qila da Tasha dinkin likita Dan a yanda yake din nan kanin fyade ze mata, yarfe
santala santalan hannuwanta tayi farare sol tana jinjina Kai.
A hankali Cikin takunta na nutsuwa da rausaya kamar bishiyar da iska ke kadawa, ta sauko kasa, parkour na biyu shiru baka jin komai sai sanyin A/C da sansanyan kamshi, kamshinsa ne ya doki hanc
inta duk inda ya gitta saiya bar wannan mayen kamshin nasa ita tun ranar da sukayi wannan arangamar a soron gidan Baba malam dashi ta San shi, Kuma har yanzu Bata Gama tantance wane turarene ke da tashin kamshin nan ba.
Main parlour ma baya nan kitchen ta
nufa ta Dora cus-cus Daman tayi vegetables soup tun yamma ita da Aunty Rukayya.
Sauran kazarta ta dauko daga freezer ta Dora a wuta.
Fridge din dake gefe Wanda drinks ke ciki ta bude ta dauko masa Shani ita Kuma ta dauki Madara hollandia da ruwa Nestle.
M
inti goma ta Gama dafa cus-cus din, sauran kazarta ma a bowl ta juye ta fita dasu dining ta jera, ta koma hadu fruit salad ne ya gangaro daga sama cikin kananun Kaya Yana daura agogo Rolex a hannunsa, tsayawa yayi cak daga tafiyar da yake ya Zuba mata idan
u ganinta yayi tamkar an canza Masa ita, hankalinta be Kai Kansa ba Amma kamshinsa shi ya fallasa shi, Dan tsai tayi tana duba cikin parlourn, a tsaye ta ganshi ya Zuba Mata ido.
Limshe Ido tayi, gani tayi yayi Mata wani irin fitinannan kyau, sauda yawa ta
na Jin wani irin Abu a cikin zuciyar ta game dashi, Amma ita Kanta Bata San ko asalin menene ba. Jin kamshin nasa a daf da ita yasa tayi bude sexy eyes dinta a hankali ta sauke shi a Kansa, matsota yayi sosai har suna musayar numfashi.
Hannu yasa ya karbi
bowl din data zubo fruit salad din, Bata Hana shi ba ya rik'e bowl din da hannu Daya. Daya hannun ya riko nata suka nufi dining din.
Bowl din ya aje sannan ya gyara Mata kujera ta zauna, abincin ya shiga budewa.
"Wow! Irin wannan delicious, Dan Allah a Ina
Kika koyi girkin Nan ne? Gaki Nan a ido kamar raguwa Mai son jiki, amman a zahiri Kuma ba hakan bane, Allah yasa a ko Ina ma haka kike".
Shiru tayi masa ta yunkura zata tashi ya mayar da ita da sauri Yana fadin.
"Ai kin gama naki aikin yanzu duty na ne, d
aga yanzu Kullum in dai Ina gida aiki nane nayi serving din mu, Ina ga girkin ma Zaki koya mun duk da na dan iya a gurin Hajiya Inna da Aunty Badi'a, Amma naki yafi nasu Dadi nesa ba kusa, ai zaki kowa mun ko? Tunda ni dai bana son abincin masu aiki Kinga
ko Ammina ita take min abincina da kanta".
Hannu yasa ya rufe bakinsa da alama ya saki layin da Bai shirya Masa ba, sai ya b'arar da zancen da fadin.
"Wai Kinga yanda kika canza kuwa?duk Wanda ya ganki zeyi zaton nayi ajiya fa, ko Azare muka koma zasu dauk
a mun samo Dan Kano ko 'yar kano"..
Sarai ta gane bada kafa yayi, sai itama ta share Bata nuna ta fuskanci abinda ya sharewar ba.
Dagowa tayi tana fadin.
"Ka cire shiga kitchen a Cikin abubuwan da zaka koya a gurina babu wannan meye amfanina in dai zaka s
higa kitchen da sunan girki ai umarni ne kawai naka" .
Gefen fuskar ta ya shafa.
"Ko?"
"Gaskiya Kam".
"To idan Kika samu ciki Mai laulayi fa Yaya zamuyi kenan?".
Rufe ido tayi da hannunta.
"Gaskiya a bar maganar shike nan the chapter is closed, muci abinc
in nasan ba lallai kaci wani abu ba fa?".
Saida ya matso da komai sannan ya zauna Yana fadin..
"Ai kin kosar Dani, kawai fruit salad din Zan Sha bana son Abu Mai nauyi da dare".
Dan shagwab'e fuska tayi tana bude flask din data Zuba cus-cus din tana fadin.
.
"Bafa Mai nauyi na dafa mata ba ka gani".
Ta dauko Masa ta nuna Masa.
"Ok, to bari na Zuba Mana kadan da gaske bana Jin yunwa fa".
Abincin ya Zuba musu sukaci tare ba laifi yaci sosai Dan Saida yayi mamakin abincin da yaci.
Bowl din sauran pepper soup di
n da mommy ta aiko Mata ta janyo ta tura masa gabansa.
"Menene wannan din Naga wasu itace a ciki?"
"Kaci kaji Mana mommy ce ta bada aka kawo min dazu da Aunty Rukayya tazo".
Wani killer smile yayi.
"A'a na koshi ki cinye abinki kawai kizo muje ki rakani wa
ni guri".
Ture Naman tayi tana fadin.
"Nifa kaina ragewa naci nawa na koshi".
"A'a ki aje a fridge ki cinye abinki da safe ai sakon babu ni a lissafin"
Ya fada Yana Zuba Mata madara a cup, lemonsa ya bude Yana Sha. Saida ya Taya ta suka kwashe kayan wurin
suka Kai kitchen, Yana tsaye Yana Mata Hira ta wanke kayan da suka b'ata.
Taso ta sake wanka ya Hana yace ze tafi ya barta Yana son yayi abu Mai mashimmanci ne, after dress din ta Dora ta gyara rolling din suka nufo kasa sai kallonsa take kasa kasa Dan ba
karya yayi wata irin haduwa sak matashi Dan hutu ajin farko, duk Wanda ya kalleshi Saiya kara, Sumar Nan Tasha gyara tayi kwance sai walkiya takeyi.
Motarta ta gani a kofar parlourn, da alama da ita zasu fita duk da taga bakin motoci a gidan, da kansa ya b
ude Mata ta shiga ta zauna.
Gurin malam Musa yaje sukayi maganar sannan ya dawo ya shiga motar ya tuqa suka fice daga gidan, malam musa na fadin A dawo lafiya yallabai.
Direct hadejia road ya nufa suna tafe yana Mata bayanin abubuwa da guraren da Bata san
i ba.
Be tsaya a ko Ina ba sai welcare, tare suka shiga bangaren magunguna suka nufa wani magani ya dauko.
A bangaren kayan kwalam da makwalashe lodarsau yasa tayi kamar ba gobe, yaje ya Basu Kati suka cire kudinsu.
Aka Kai musu mota, ta dauka gida zasu k
oma sai taga sun Kara gaba, Ring road suka shiga basuyi nisa ba Sosai taga sun shiga wata kwana bata tantance Ina sukazo ba Saida taga sign board din Asibiti M.D.S.
Abin ya Bata mamaki to me zasuyi a Asibiti?. A mota ya barta ya shiga Cikin be Dade ba ya d
awo Yana fada Mata ta fito tazo, ba musu ta fito suka jera wasu majiyyata sai kwllonsu suke, ofis din Dr. Suka shiga.
Mutum me fara'a ya karbesu hannu bibiyu suka gaisa da Mahmud sosai, da alamar ba wannan ne haduwar su ta farko ba, da sanayya.
Zahra ma ta
gaishe da likintan. Sannan suka zauna, Mahmud bayanin Dan abinda ya sani yayi masa.
Tambayoyi Dr din ya Fara jerawa zahra daga karshe shima yace Bari ayi hoto da wasu test a Nan ze tabbatar da abinda yeke tunani.
A Nan ya sake Mata scanning da tests na j
ini.
Zahra tayi mamaki kwarai da sukazo Nan din itafa ta dauka be damu da matsalarta ba tunda taga be Kara Mata maganar ciwon ba tun bayan Wanda suka tattauna.
Suna zaune wata nurse ta shigo da result din da sakamakon test din jinin ta bawa likitan tayi ga
ba abinta, ya dauki lokaci Yana nazarin abin Wanda har Mahmud din ya tamabaye shi ko matsalar tayi zafi ne?
Kai ya girgiza masa kafin ya aje takardar dake hannunsa ya kalli Mahmud din Yana fadin.
"Tabbas da matsalar fibroid a mahaifarta, sai dai wani abun
mamaki Dana gani ya Fara narkewa sakamakon wani Abu da take Sha harma jinin jikinta yake wankewa, Dan haka ba maganar aiki a yanzu dai gaskiya mu jira zuwa next month idan lokacin period din yayi a Nan zamu tantance Yana Nan Yana functioning ko Yayi dissol
ving, amma Zan Dan Kara mata da wasu antibiotics din Wanda zasu taimawa jikinta in Sha Allah".
"Ok Dr nagode kwarai".
Tambaya likitan ya jefowa zahrar.
"Ko kina amfani da irin maganin Islamic chemist ko na gargajiya haka? Ma'ana kike Sha da sunan magani k
o kuma haka Nan amma