Showing 198001 words to 201000 words out of 295116 words

Chapter 67 - AUREN HUCE HAUSHI COMPLETE

duk su Ya Abdul Hakeem basu shigo ba".

"A'a yau inaga basu da fita ko ina kamar Abban nasu".

Ta juya ta koma zahra ma ta gyara rolling dinta

ta fito tamkar dawisu tana tafiyar nan das-das.

Basket din ta dauka ta fice bata bi ta kan dan gidanta ba dayake ta zuba mata zance, wani lokacin har mamakin yawan maganar Magaji take shi sam baya gajiya da magana.

Da sallama a bakinta ta shiga parlourn k

asancewar a bude ta sameshi, suna dining area sanda ta shiga, directly gurinsu ta nufa,Abba na ganinta ya fara murmushi yana fadin.

"Masha Allah, uwata ba raguwa bace har kin fito? Haka akeso ki zama mai himma".

Itama murmushin tayi tana karasawa gurinsa

ta tsuguna har kasa.

"Abbana ina kwana?". Ta fada tana aje basket din.

"Lafiya kalau uwata".

Basket din ta dauko tana fadin.

"Yau dai abincina Abbana zaici gaskiya Ammah".

"Gaskiyarki uwata ai babu wanda zaiki abincin babarsa zuba mini Allah yayi Albarka y

a baki masu yi miki kema"

"Allahumma Amin". maganganu yake mata masu harshen damo daga karshe ya rufe da kara jaddada mata mahimnacin hakuri, sannan ta baro sashen nasa duk jiki a mace.

Lokacin data shigo mutumin ya kunna tashar restling yana kallo.

Tana s

higowa ya taso.

"Daman ke nake jira kizo na saida miki wannan jaridar".

"Jarida kuma".

Tsaki yayi yana tabe baki kamar mace.

"Ashe ke bakya daukar haske, to labari zan baki".

"Ok. Sai yanzu naje Ghana, bani na sha".

Zama sukayi nan kasa kan carpet.

"Kina j

ina wai dan Allah me yasa kikace kada na kawo sahura gidanki? Kinga yanda Mama ta damu kuwa akan nace mata kuna kano kamar zata fasa kuka fa, ke bar wannan kada na manta abinda zan fada miki, dazu da Asuba nayi shirin masallaci na saka J/C dina a leda na n

ufi kofar baya na aje idan an dawo daga sallah na sulale ta baya na wuce training din ball, kinsan tun lokacin dana samu karaya Abba ya hana ball, ni kuma idan babu ita da matsala gaskiya shine nake fita ta baya har na dawo babu wanda ya sani, to dazun ina

nufar gurin naga Mama da Ya Hamza da wannan 'yar rainin hankalin tana rusa kuka sun fice ta kofar bayan ita da Ya Hamzan ita kuma Mamar ta dawo ta wuce ta gefen inda nake tana shafe hawaye da gefen hijabin dake jikinta, harta wuce bata ganni ba nasan duk

yanda akayi da magana a kasa tunda babu wanda yasan da zuwan salma gidan nan".

Zuru zahra tayi masa tana kallonsa.

"Tab Allah ya kyauta can gasu gada, wai zomo yaji kidan masu farauta, ai idan kace ruwan wani ba zai tafasa ba to in sha Allah naka ko zafi b

azeyi ba, ayi dai mugani karya dai fure take bata 'ya'ya, ba dai mugun abu suka zaba ba da saura ma basuga komai ba, kace kai baka son cigaban kowa to kaima yaushe zakaga dai dai".

"Haka ne kam ai so nake Abba ya gama break naje na fada masa ya kira Ya Ham

zan yaji meya faru kuma ina suka tafi ko kuma nace Abban yaje makarantar da kansa ko daga can ne aka samu matsalar".

"Kai magaji ina ruwanka da sagbarsu,kasa ido idan tayi wari kowa zeji ne har wani zaka fadawa Abba meye naka a ciki, ka manta hadisin Annab

i Asalihissalam wanda yake cewa yana daga kyawun mutum ya bar abunda babu ruwansa? To ka kyautata musulincinka kaima, ka nuna kamar baka san anyi ba idan wani dalili yasa anzo gabar da zaka iya fadin abinda ka gani falillahil hamdu saika fada din".

"To shi

ke nan bari naje nayi wani aiki kinsan mun fara project".

"Masha Allah Allah ya taimaka, ya dai fiye maka da guzirin tsegumi"

.

"Allahumma Amin, gaskiyarki yallabiya"

Yayi waje.

Ita kuma zahra ta tashi zata koma ciki taji ana knocking din kofa ta nufi gur

in, tana budewa taga Hajiya Amina mutuniyar Ammah ce sosai, tana sayar da turarika na jiki dana daki da kayan gyaran Aure dasu dilkar Amare. Jakar hannunta zahra ta karba tana bata hanya tare da fadin.

"Sannu da zuwa Hajiya"

"Yauwa Amarya ya gida?".

"Lafi

ya kalau Hajiya, ina kwana?".

Lafiya kalau Alhamduliahi ya mai gidan naki?.

"Lafiya kalau" ta fafa tana sadda kai kasa.

"Bari na fadawa Ammar kinzo"

Kafin ta bata amsa har Ammar ta shigo, tana fadin.

"Lale marhabin da Hajiyar kamshi, lallai kinaji da wann

an 'yar taki, nan da nan haka har kinzo".

."Ai ba'a bori da sanyi jiki" ta fada tana dan murmusawa".

"Haka ne kam"

Ammah ta fada sannan suka gaisa.

Tashi zahra tayi zata tafi ta basu guri.

"Dawo ki shiga da wannan jakar, ki bude ki dauki fallan sabon zani

ki cire kayan jikinki ki dauwa shi gani nan shigowa".

Dauka tayi tayi gaba da jakar babu halin tambaya tunda ita dai bataga wani dalilin da ze saka ayi mata wani gyara ba tana zaman zamanta ita da ko mijin baya kusa bare yaji ko kamshin ne.

Saida ta bacew

a ganinsu sannan Ammah ta bawa Hajiya Amina hankinta sosai.

"Kina ji abun ne yazo a gurarran lokaci wai gobe zatabi mijin india sai jiya da dare Abbansu ya fada min, shine na tura kizo kiyi mata dan abunda ba za'a rasa ba, to kuma sai a dazu Zilai ke fada

min wata magana, na rasa ta inda zan bullo mata, wai sunje asibiti an tabbatar wa da zilan wai zahra har yanzu wani namji bai santa a diya mace ba, dan da farko an dauka ciki ne ya lalace sai da akayi bincike aka gani fibroid ne ya narke a sanasiyyar magan

in da tasha, shine zilan tace wai ko mijin ne bashi da lafiya sukayi shiru ko asibitin da sukaje hanawa tayi a fada min wai kada hankalina ya tashi".

Jinjina kai hajiyar tayi.

"Babbar magana dole ayi bincike gaskiya, bari na shiga naji yanda abun yake daga

bakinta"

Ta mike ta nufi dakin, a zaune ta samu zahra tana lallatsa wayarta.

Da sauri ta aje tana gyara zama.

Gurin da aka aje jakar ta nufa ta bude ta fara ciro kayan aikinta ta shinfida table mat a kasa ta fita ta dawo da cups da cokali, hada wancan zu

ba wannan tana zuba madara tana bata tana shanyewa sai da tazo kan wani bakin magani sannan ta dago tana fadin.

" Wamnan saidai na baki ki tafi dashi dan buduruwa bata sha sai matar auren da suke haduwa da mijinta kinga ke dai ba zakiyi amfani dashi ba tun

da naga ke har yanzu baki fara naki amarcin ba ko?".

Hannu tasa ta rufe fuskarta shike nan tasan ko rantsuwa tayi babu kaffara Aunty zilai ce ta fadawa Ammah shine aka biyo mata ta nan gurin.

Shiru zahra tayi in dai ita zata bada amsar tambayar za'a shekar

a ba'aji amsar ba.

"Kinyi shiru baki bani amsa ba? Ko mijin naki bashi da lafiya ne akwai irin nasu magaungunan sai a baki ki tafar masa dasu".

"Hjy shifa lafiyarsa kalau wallahi".

"To ai shikenan daman ana gudun kada kuyi yarinta wannan shine zaman auren"

..

Kayan hadin data hado ta shiga shafa mata dilkan dasu kurkur, bayan ya bushe aka murje ta shiga wanka tun a toilet din taga an samu banbanci yanda jikinta ke fitar da wani irin shining ga wani irin kamshi mai saka nutsuwa, data fito ta samu an hada burn

er kan wata kujera ta zauna Hjyr ta tufeta da blanket tace ta cire towel din ta bata wani magani me azabar kamshi tace ta zuba ta bude kafarta sosai ya shigeta, a dan kunyace tace mata

"Ina period fa".

Dafe kai tayi, kafin tace ba komai ki barshi ya shiga

jikinki kawai, daya gama haka ta ringa bata kalolinsu tana turare jikinta dasu har aka gama wasu mayika da humra ta aje mata ta fice tace ta shafe jikinta dasu. Lokacin data fito ko amma kasa dauke idonta tayi daga kan zahra.

"Tabarakallahu Ahsanaul khaliq

in"

Ta fada a hankali dan wani irin kyau tayi na ban mamaki.

Tana karasa shigowa cikin parlourn kanshin jikinta ya canza yanayin gurin gaba daya.

Sannu ta yiwa Ammah ta shige karamin parlour tayi zamanta saboda taga alama maganar sirri sukeyi da Ammah.

Ya

Imam ne ya shigo parlourn da sallamarsa yana dauke da manyan ledoji guda biyu, ya aje yana gaushe da Hajiya Amina, sannan ya yiwa Ammah sannu da gida.

"Wannan kuma daga ina?".

Ammah ta tambaya, baki ne daga kano gasu nan shigowa".

Ya fada yana juyawa, taso

wa zahra tayi da sauri tana fadin.

"Ya Imam ina yini?"

Dawowa yayi yana fadin.

"Lafiya kalau zahra ashe kina gidan na shigo dazu banganki ba, ya gida? Ya kuma jikin baba malam? Jiya na kirasu na duba shi lokacin ana masa aiki sukace".

"Eh wallahi anyi aiki

n sai fatan samun lafiya".

Ai kafin Ya imam ya fadi abinda yayi niyya yaga zahra ta kwasa kamar wata.'yar baby ta nufi wata fattijuwa da suka shigo da wata budurwa sai magaji daya riko sauran wasu kayan, tana zuwa ta shige jikinta tana fadin.

"Wayyo dadi y

au ga Hajiyarmu a Azare, wallahi nayi zaton da wasa kike min".

Dariya Hajiyar tayi tana fadin.

"Kada ki kadani tsohon rai ki ida laifin daba naki ba fa".

Dariya itama zahrar tayi, tana rike hannun Hajiyar makwarari, sai data dago taga Aunty Rukayya na musu

dariya.

Hajiyar zahra ta saki ta nufi Aunty Rukayya da saur tana fadin.

"Kin shammaceni Aunty Rukayya sai ki fada min gaku nan zuwa".

Su dai sauran na parlourn kallon ikon Allah suke tunda basu san bakin zahrar ba.

Tasowa Ammah tayi tana fadin.

"Sannu da

hanya Hajiya karaso ki zauna ki rabu da shiriritar zahra".

Gurin zama Ammah ta bata ta zauna suka gaisa da Hajiyar sannan Hajiya Amina ma ta gaisheta tare da yi mata sannu da hanya,su zahra ne suka karaso Rukayya ta gaishe dasu Ammah zahra ta matsa ta gais

he da Hajiyar makwarari, sai kakabin abun takeyi.

Alawiyya dake aiki a kitchen ce ta fito da tray babba da ruwa da drinks dasu snacks a kai ta kawo ta aje tana gaishe da Hajiya da yi mata sanni da hanya, sannan suka gaisa da Rukayya.

Hajiya Amina tashi tay

i tana fadin.

"Zan tafi Hajiya duk komai suna gurinta na nuna mata yanda zatayi".

"To nagode in sha Allah sai munyi waya".

Hajiyar makwarari ta yiwa sallama ta tafi.

"Hajiya kusha ruwa sai kuyi sallah kafin kuci abinci ko?"

Ammah ta fada tana tashi ta basu

guri.

"Zuba min ruwan nasha kinji zahra'u, kinga Rakiya nan sai dacin rai take mini dan nace zanzo naga jikin naki, kinsan kirkinta kadan ne, banda barbada har yaushe zata nuna adawa a zuwa gurin matar mahmud yaron daya zamar mana fitilar daya haskemu da

ita yo ko ubanta ai da tallafin mijinki yake juya tashi kasuwar".

"Ayi hakuri Hajiya banda gori, ina laifi tunda ta rakok".

Ammah ta fada lokacin ta shigo parlourn daga kitchen.

Baki Rukayya ta zunbura.

"Wallahi da nasan haka zakiyin da ban fadawa Ya samee

r ya taho dake ba na barki wanda ze kawoki ya kawoki ku gama bulayinku ku koma tunda ba sanin inda zaku kukayi ba".

"Kar nan 'yar Ashatta, ai wannan yarinyar babu irinta a garin nan dana kwatanta za'a kawoni gareta ko kinji".

"Hajiya rabu da ita, zahra ku

shiga can dakin kije ki dauko mata nata ruwan a kyale Hajiya ta huta".

Tsam suka mike kamar daman jira sukeyi suka wuce ciki.

Magaji ne ya shigo yana kara gaishe da Hajiya, sannan ya fadawa Ammah a kawo abinci da ruwa a mikawa Oga sameer shiya kawo su.

Kit

chen suka shiga tasa Alawiyya ta hada abinci da duk abinda ya kamata magajin da Alawiyya suka fita kai masa.

A dakin Ammah Hajiya tayi sallah sannn suka kara gaisawa, Hajiyar ke fadin.

"To barka fa anyi ta barka da wannan ciwo ya rabu da yarinyar nan, ina

amfanin ace sai an yanka yarinya ace za'a cire ciwo".

Kasake Ammah tayi wato abinda Hasana da zulai suka fada haka yake ita kawai taki fadawa wai kada ta tada mata hankali.

"Eh wallahi Hajiya anyi ta barka kam babu abinda zamuce sai dai Allah ya saka da Al

khairi yasa a gama lafiya, mun gode kwarai da gaske".

"Kai! Kada na karajin godiyar nan daga bakinki, ai duk abinda zamu yiwa yaron nan bazamu biya shi ba,yanzu fa Allah ke rike damu amma da bazarsa muke rawa, sau biyu fa yana kaini masar akan lalurar ido

data kafa ya, kaini umar sau biyu ya gyara mini gida ga jikana ya janyo shi jikinsa duk inda ya aje kafa sameeru yana maida tasa ko wannan fushin zuciyar da yayi babu wanda yasan inda yake sai sameerun, su iyayen sunfi maida karfin nemansa a kasashen turaw

a da larabawa basu san yana nan ba,ai wannan yaron uwarsa tayi farar haihuwa gashi Allah ya bashi mata wanke hannu daka taba, gaku kuma mutanen arziki kun bashi irin wannan yarinya ba tare da kun dubi halin da yake ciki ba sameeru yace min Almajirin malam

ya zama a nan gurin ku, duk da irin dumbun arzikin da Allah yayi masa, kinga yanda iyayensa suke da arziki kuwa duk sokoto basu da na biyu, amma sai nasa yacewa na iyayen kau ban guri, ki dafi yarinyarki da kirki dan inda zata shiga bana wasa bane, yanzu h

aka na taho mata da sakonni daga gurin dan uwana malam na sanka, dan ma yace Alhamdulillah yarinyar jikinta da tsari na gaske".

Tunda Hajiya ta kama zuba Ammah ke binta da aikin kallo wasu maganganu take fada wadanda ko cikin mafarki bata taba hasaso irin

su ba, ita fa ta kasa gane wai akan waye Hajyar ke magana ma tukuna.

"Wai Hajiya waye wannan din da kike bani labarinsa ne ban gane ba".

Wani kallon ina hankalinki yake Hajiyar tayi mata.

"Yo maganarwa zan zage ina miki in ba ta sirikinki mijin diyarki za

hra'u ba, ai dalilin da yasa na taso takanas nazo kenan na fada miki ki koyawa yarinyarki iya zama da mutane duk da naga da wayonta yarinyar taki,amma ta koyi kamewa sosai dan naga alama sai kin kara mata karatu sosai na yanda zata rike mijinta sosai dan r

irribinsa mata keyi kamar kudi shi kuma dan arzikin ko kallonsu bayayi tunda ya kyalla ido yaga taki 'yar tunfa wata tafiya da inaga mai gidan nan ne ya taba kaita wata kasa ko ina? na manta sameeru dai ya fada min to a tun lokacin yake bibiyar yarki idan

ma baki sani ba".

Ruwan mamaki ne ya gama cinye Ammah a zaune yanda Hqjiya ta bude aiki gaba daya, nan da dunga zayyano mata ko waye mahmud har abinda ya shafi uwarsa da inda ta fito saida ta zayyane mata tas.

Godiya dai Hajiya ta shata gurin Ammah, kayan

da Hajiyar ta kawo ta bukaci a shigo dasu, Alawyya Ammah ta kira a waya ta fada mata ta shigo da kayan baki sukazo dasu bedroom dinta, ba yanda Ammah ba tayi da Hajiya ba akan tabar bude kayan sai taci abinci amma tace a'a sai tayi abinda ya kawota tukunna

.

Bayan ta gama nunawa Ammah komai da yanda za'ayi amfani da komai sannan suka nufo parlour Taci abinci.

Abdul Hakeem ne ya rako sameer suka gaisa da Ammah, ya fada mata zasu yau zasu wuce tare da Zahra saboda an samu canji tashin flight din dole ta Abuja

zasu tashi saboda yana yin weather ta kano bata da kyau jirgi baze iya tashi ba, dan haka flight bakwai zamu mu kwana a gidan kanin mommy.

Hajiya ce tayi tsagal tana fadin .

"Wai ku bazaku daina tafiyar katangatse ba sufa mata 'yan tsiri ne bazu fadawa mu

tum abu ba sai yanzu yanzu a gurguje".

"Ayi Hakuri haka umarnin suke".

"To ni zan fadawa mahmudun yanzu da dah ba daya bane garin irin wannan shima wata rana zata shafeshi dan za'a manta abu mai mahimmanci daya kamata a dauka".

Ammah da kanta ta shiga inda

su zahra suka baje kolin hira, fada mata tayi tazo ga sameer ya shigo ta juya.

Tare suka fito da Rukayya, zahra ta gaishe shi yace tazo ya kaita gida ta shirya yau zasu wuce kano, nan yayi mata bayanin canjin da aka samu.

Kamar zata fasa kuka ta tashi ta

ahige bedroom din Ammah.

"Tashi kije gurinta abun ne yazo mata bazata".

Ammah bataki ba ta tashi ta nufi gurinta din, samunta tayi ta hada kai da gwiwa tana shsshsheka, dafata tayi a ka tana kiran sunanta, dago sexy eyes dinta tayi wanda suka jike da haway

e, girgiza mata kai Ammah tayi alamar ta bar kukan, tashi tayi ta rungume Ammar tana fadin.

"Ammah wai fa india zan bishi, kuma wallahi bai fada min an samu visar ba".

Bayanta Ammar ta dan bubbuga.

"Kiyi hakuri wasu mazan haka suke ba komai suke fadawa mat

a ba, kuje da yarinyar nan ta tayaki ki shirya sai kizo nan ma kafin ku dawo na hada miki abunda ya kamata,ke dai kiyi masa biyyayya duk abinda ya sakaki kiyi masa matukar be sabawa Allah ba, duk ida rayuwa ta kaiki ki zama mai hakurin zama da jama'ar da A

llah ya hadaki dasu, ki girmama masa iyayensa ki daraja masa 'yan uwansa, kada ki bari kema a raina ki kada ki zama mai nuna halin ko in kula akan lamarinsa ko kiyi farin ciki lokacin da yake cikin halin damuwa, ki zama jaruma mai dauke masa bukatunsa kiyi

juriya akan duka binda ya bijiro miki dashi, ki zama mai kauda masa Qishirwa duk lokacin daya bukata. Allah yayi miki albarka ya albarkaci aurenki, kuje kada kuyi dare a hanya".

* AUREN HUCE HAUSHI *

0906143233

My

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login