Showing 243001 words to 246000 words out of 295116 words
tsare,dan Aishat ce tayi Mata tsegumin abinda take zaton ze aikata Dan taga dazu ya birkice da yawa idan aka barshi ko budar Kan baza'ayi ba ga momin Kano kuma ta shirya masa Dan lokacin
da akaje da maganar ko a hakura dayin wunin tsalle tayi ta dire akan babu fashi sai anyi me zata yiwa mahmud ta biya shi kaunar da yake yiwa Faruq ya dauke shi tamkar uwa Daya ta haifesu ya bude Masa yanda ya kamata hatta karatun da yayi mahmud ya zabar M
asa saboda ya ringa yi Masa ayyukansa.
Mahmud yana ji yana gani Sameer ya wuce dasu zahrar ita dasu sajeeda da Amatu.
Zahra a gurin su Ummee ta zauna sun Kai kusan biyu Aunty Nauwarah na saka Zahra a wasu irin ruwan magunguna masu azabar kamshi ga turaren
jiki Wanda sai da kamshimsa ya game part din gaba daya, abin isar Zahra yayi Dan idan ba so suke yayi Mata lahani ba ya kamata a kyaleta haka ita kadai ranta sai abubuwa ake Mata Babu sasaauci,ko Dan Basu San abinda idanunta suka gani bane. Kawai a Riga s
uke ganin mutum Basu San sirrin dake lullube bane.
Gado Daya suka kwana da Ummee Zahra nata mitar Ummee ta manta da ita, data isheta da magana Ummeen ta fada Mata Abbu ne bashi da Lafiya ai mijinta ya sani Dan yaje har London ya duba shi, shine yayi blocki
ng din layinta a wayoyinsu yace idan aka Bari Kika sani Zaki tada hankalinki gashi kema lokacin yace Baki da lafiya.
Gyara kwanciya Zahra tayi tana mitar abun, kamar ta hakura sai kuma tacewa Ummee.
"Wai Dan Allah Ummee a Ina Mika san...."
Sai Kuma tayi sh
iru.
"A'a Fadi Mana a Ina nasan mijinki".
Dariya tayi tana rufe Ido.
"Makocinmu ne a can Jordan gidansa Yana kallon namu".
Tashi zaune Zahra tayi tana duban Ummee.
"Badai wannan gidan da nake cewa yayi min kyau ba gashi Naga an saka Masa suna a samansa GID
AN ZAHRA".
Dariya Ummee tayi to ai daman gidan na zahrar ne haka Shima ya fada min tun kafin nasan ke zahrar tawa yake nufi, ko aikin gyaran gidan Abbie ne ya samo Masa masu yin duk sadda ya shigo Jordan Yana gidan mu, Bai Kuma taba fada Mana ya sanki ba K
oda wata manufar da take kawosa gidan, sai bayan an bashi ke ya kirani yake fada min an bashi Mata idan ya shigo ze kawo min hotonta na gani.
Ranar Daya zo da yammaci ya shigo yaci abinci sannan ya bude ya ringa nuna min hotunanki tun kina 'yar matashiyar
ki har na girmanki, ba Karamin mamaki hakan ya bani ba Daman yasan kina da alaka da Dani ko Kuma arashi ne kawai.
Dana tambayeshi ba wani rufa-rufa ya fada min yasan matsayinmu a gurinki.
Zahra tayi matukar mamaki Amma Dan tahalikin Nan Bai taba nuna Mata
yasan su Ummee ba Koda Wasa, Sai dai Daman tayi matukar mamakin yanda taga suke mu'amala abun kwarai ya bata mamaki babu wani bakunta a tattare dasu.
Sun Jima Ummee na Bata labarin yanda suka shaku da mahmud din sai taga ita ai ya fita shiga jikinsu ma sos
ai.
Washe gari da wuri Aunty Hasana dasu Aunty Nauwarah da sauran mutanen Ammah Hajiya kaltume ta turasu tare da Aishat wadda zatayi musu jagora suje a duba abinda ya kamata a gyara a gidan da za'a Kai Amaryar tunda company ne sukayi jeren kayan da akazo d
asu na zahrar duk da mahmud yace ba gurin saka komai, dole ya bada part dinsa na gidan Hajiya Inna aka zuba kayan tunda baiyi niyyar saka masa komai ba a lokacin domin guda biyu aka Gina Daya na zahrar to an Riga an saka masa furnitures sai dayan da dole t
asa aka yi Masa paint da abinda ya kamata aka saka kayan a can. Basu wani Dade ba suka baro can din tunda babu bukatar yi masa komai sai dai turarukan daki da aka saka, Basu dawo gida sai da aka kaisu gidan da za'a Kai Zahra, permanent gidanta gidan Hajiya
Inna temporary ne na week end da yada zango Idan an dawo daga tafiya Dan Alkawari ne duk inda yaje ya dawo gidanta ne farkon sauka.
Sunyi santin gidan tamkar ba'a Nigeria mutum yake ba Dan Maman mujiba kasa shiru tayi da bakinta lokacin da Aishat ke shiga
dasu guri guri a kasa taga parlours sun Kai hudu ga sama sun hau taga common karfen dake Jikin stairs shi Kansa tamkar na zinari sai daukar Ido yakeyi ga gidan ko Ina daukar Ido yakeyi ga haukatan bedrooms ga toilet ga gani na fada Dan wani abun ko a hot
o Bata taba ganinsu ba. Ja tayi ta tsaya tana kallon Aunty Hasana.
"Dan Allah Hasana Wai Yaya Aljanna take ne?"
Ba Wanda baiyi dariya ba a gurin kuma ita har zuciyar ta tayi tambayar.
Ganin suna dariya yasa ta Kara fadin.
"Wallahi da gaske nake tambayar Na
n, ki dubi gidan Nan Wai a sokoto yake? Ni tunda Allah ya halicceni ban taba shiga makamancinsa ba, Nan gidan zahra ne wadda ake tsegumin an aurawa Almajiri kolo marar galihu marar komai, ana ta zunden Alhaji idan ya wuce a unguwar, a cikin gidan Kuma ana
sakin habaici an ce kyau ya Kare a Wanda ba'asan asalinsa ba, to yau kowa yazo yaga inda Allah yasa Alhaji Jafar ya kawo marainiyar Allah gidan da hasashe be taba hasasowa ba, tunani Bai taba tunanowa ba, Hasana saka wayarki ki daukar min gidan Nan ciki da
waje sai masu tsegumi sun gani da idanunsu, 'yan bakin ciki kuma su mutu tunda Alkawarin Allah baya tashi idan yace Kaine sai kakai, lallai Dan tsiron da Allah keso ko babu ruwa saiya rayu, yau Zahra ta Zama farin wata Sha kallo. Masha Allah Arzikin mutum
a jikinsa yake Kuma dare ga Mai rabo hantsine".
Guda ta rangada har sau uku tana Kara fadin . "Idan Rana ta fito tafin hannu baya kareta, walkiya inta haska wanene ze iya kareta? Hadari In yayya tsawa rufe kunne baya Hana jinsa ga Zahra ikon Allah sai kal
lo".
Kudi Aunty Nauwarah ta Ciro dollars ne saura Wanda ta zubawa Zahra ta Zubawa maman mujiba Dan ko Bata Jin abinda take fada tasan kurare 'yarta takeyi, ko ita da suke a kasashen da sukaci gaba gidan Zahra ya tafi da ita Dan babu karya anyi gidan tamkar
baza'a mutu ba Dan dukiya dai an kasheta tamkar ba'asan ciwonta ba.
******
Saida zahrar tayi barci Mai isarta sannan ta tashi, lokacin wurin Sha Daya. Wanka ta shiga tayi data fito tayi break fast sannan ta shirya, Aunty Nauwarah tayi Mata makeup mai d
aukar hankali. Doguwar rigar atamfa green Mai milk din fulawoyi ta saka tayi amfani da gyale milk da takalma plat milk, wayarta ta dauko wadda ta sakata a silent tun daren jiya saboda message din data gani na mahmud da yake son dole ta fito Yana ta bayan p
art din Ammin, idan ta fita akayi Dace wani ya ganta ai noway out, cewa za'ayi har satar jiki take tana zuwa gurinsa, dubawa ta shiga yi na meu amor ta Fara bi kasancewar Aunty Nauwarah Bata Jin hausa yasa hankalinta kwance ta kirasa.
Harta yanke be daga b
a sai taji wani irin ba Dadi a zuciyarta.
Ya Abdul Hakeem ya Nemo wayar taji a Ina suka kwana.
Dauka yayi suka gaisa kafin ta Dora da fadin.
"Ya Abdul Hakeem a Ina kuka kwana ne? Kuma Ina Abbana wallahi kunyi surprised dina banyi zaton zakuzo ba wallahi".
"To Ni dai gani Nan a wata unguwa Wai kome? Na manta Abba kuma sunbi jirgin bakwai da rabi yanzu haka ya sauka a Bauchi sun dauki hanyar Azare".
Wayyo Ya Abdul Hakeem yanzu Abbana yazo garin Nan na kasa gaisawa dashi".
"Kinsan halin Abba ai yace ze dawo sp
ecial yaga masaukin ki, kinsan ya w
Sun jima suna waya daga baya sukayi sallama.
Aunty Hasana ce tazo ta raka Zahra Dakin Ammi ta gaishesu sannan ta mayar da ita masaukin da Ammi tayi mata.
Sai wurin karfe biyu mai yin makeup wadda momin Kano ta dauko taka
nas tazo Shirya Amarya, tayi Mata makeup light, ta Zuba Mata wani material Mai ubansun kyau ta daura Mata head sai zahrar ta fito a tauraruwarta dan komai hassadar mutum ya kalleta ya Kara kallo Dan da gaske zaharar ce.
A Hidima event center Wanda ke bodin
ga road, behind Nipost sokoto south za'ayi yinin, lokacin da aka shiryata photographer yazo anyi hotuna kamar me sunje part din momin Kano ma anyi hotuna a Nan Zahra taga kanwar maman Musbahu Aunty batayi mamaki ba tunda taga musbahun da Faruq tare a Kano
da alamar sun jada relation dasu.
Daga bangaren Momin akazo tafiya da Zahra gurin da za'ayi event din Mai gayya Mai aikin ya Kira momin da Kansa yace suje za'a kawo ta.
Abinda yaso ya Zama na magana a Cikin family kenan sai da momin ta tsawatar saboda momi
ba Wasa tasan kanta yanda ya kamata Bata daukar wargi domin itama daga babban gidan sarautar Kano aka daukota, shi yasa tasu tazo Daya da Ammi ma Dan itama Ammi tasan ciwon kanta Kuma da fadarta gurin miji, Sam Bata shiga shirgin tsugune tashi na family d
in.
Sameer yazo ya tafi da Zahra su Amatu sunso subi Zahrar Amma Sameer yace ba can suka nufa ba yanzu da inda ze kaita, dolensu suka hakura da bin motar Amaryar.
Direct kalambaina road suka nufa ita dai Zahra ikon Allah take kallo.
Gaban wani plat house m
ai wani irin gini na daukar hankali taga sameer ya tsaya Yana yin Horn har suka Karads shiga ciki wayar Sameer ta dauki kida da sauri ya dauka Yana fadin.
"Har munfa karaso".
Da yake a handsfree take sai Zahra taji yace .
Ku wuce kawai akwai mutane a gidan
".
Wani sanyin dadi ne ya rufe Zahra Daman tunda suka taho addu'a take haka Nan Bata San kebewarsu a tsakanin Nan dan salon da yake fito Mata dasu yafi karfin dan Karamin tunaninta.gaskiya, hamdala dai tayi tafi ciki carbi.
Guri yinin ya hadu ya kuma Tara
matan da suka amsa sunan su mata, Dan momin kano ba Karamar gayya tayi ba tunda ita Ammi ta bawa wannan bangaren, mutanen Ammi na Niger sunzo kamar Gori, gurin ya dinke da matan gayu sai sabgogin arziki akeyi an sakata Zahra a wata kujera a tsakiya hall d
in ga kidan wakokin bikin na tashi Dan a kalla su Kai kala biyar Dan ma abun ne yazo a Qure.
Kafin yamma an sakewa Zahra dress ya Kai sau biyar da mahaukatan laces na makudan kudi duk karkashin momin kano tunda itama 'yar kasuwa ce ta gaske Dan wasu abubuw
an ma tare da Ammi suke juyawa irin kayan da ake shigo musu dasu daga kasashen dasu mahmud suke da kamfanoni a can.
Da yamma Zahra na Dakin da ake Mata canjin dress Hajiyar makwarari ta shigo iita da Aunty Rukayya, Hajiyar Tasha wani ubansun lace tayi gwag
qgwaron tsofaffi ga jaka da takalmi da gyale duk iri Daya.
"Ina zahara'un take? Zuwa nayi na tofeki da lahaula saboda naji bakin mutane yayi yawa a kanki to kada aje ba'a sani ba Koda Mai kambun baka, gara ki shiga gidanki salin alin salamun qaulin, yo Ina
dalili! A sakawa yarinya Idanu kowa wuwww,haba surutu ake caca
*AUREN HUCE HAUSHI*
AISHAT ISAH MUSAH.
Maman Fateemah
09061432330
08055362975
Wannan littafin ba MALLAKIN kowa bane gurin juya shi ko sarrafi shi Audio ko wata sigar Saida izinin marubuciy
ar.
Page 82.
....... Mahmud na tsaye a compound din gidan motar Alhaji Muhammad ta shigo a hankali har ta tsaya a dai dai steps da ze sadaka da babbar kofar shiga ciki, da sauri mahmud yaje ya budewa Abbie kofar dake tsakiya ya fito yayin da Malam Haruna
ya budewa Zahrar kofar karshe ta fito, mahmud ne yaje ya bude kofar Abbie na gaba Zahra na biye dashi.
Suna shiga Cikin Zahra taji wata irin karaya tasan karshen tika tik, duk wani zagaye zagaye yau dai ne final, gata a sokoto a gidan mahmud inda ya ta'al
laka duk wani burinsa da yake kanta.
"Ya Ilahiy!"
Ta furta da siririn sauti.
Har bedroom dinta Abbie ya kaita yayi Mata umarni data zauna a Kan gadon ta, ba musu ta dosana tare da Bismillah ta zauna a darare, Abbie din da Kansa ya dunga kwararo musu Addu'o
i Cikin harshen larabci mahmud na fadin Amin.
Abinda ya karyawa Zahra zuciya kenan shaukin mahaifanta ya taso Mata yanzu da itama nata suna Nan da watakila shine a tsaye yake kwararo masu wadannan Addu'oin, duk da su Ammah da Abbanta Basu taba Bari tayi ku
kan maraici ba,amma masu iya magana na fadin gurbin idon ba Ido bane, ita kaunar d'a da mahaifi daban take Allah s.w.a. ke sanyata a tsakaninsu, ba zato sukaji saukar siririn sautin kukanta.
"Haba Fateemah ya zakiyi kuka Kuma? keda nake ganinki jaruma, ai
masu babban suna basa kuka, ko su Abban naki da Malam dole sukayi Miki suka hadaki da Hussein? fada min yanzu na koma dake kije ki zabi Wanda kikeso na aura Miki kinji 'yata".
Zuru mahmud yayi yana kallon Abbie din yasan da a wancen lokacin ne irin wannan
ranar da Abbanta da Abdul Hakeem suka Kai Masa ita ta samu irin wannan damar babu abinda ze hanata fadar Bata sonsa, sai dai yanzu yasan ko tana Shan giyar wake bazata Fara ba Dan shi Kansa yasan ya Bata darussan da barinsa ze Mata wahala duk talauci kuwa
Dan yasan duk shegantaka ce ke sakata wannan koke koken Bata ji dai dai ba da tuni labarin ze canza.Amma a juri zuwa Rafi da sannu za'a fasa tulu.
Shiru Zahrar tayi tana ajiyar zuciya, dan murmushinsu na manya yayi ya nufi kofa Yana fadin.
"Kiyi hakuri ha
ka shine girma kinji Diya ta,idan yayi Miki ba dai dai ba ki fada min nine Zan hukuntashi Allah yayi muku albarka ya Albarkaci aurenku da 'ya'ya masu Albarka ya kade muku fitina ya Baku Zama lafiya ayi ta hakuri kinji 'ya ta Zan tafi, ki yiwa mijinki biyay
ya ki bashi girmansa da Allah s.w.a ya bashi kinji'.
Kai kawai ta iya gyada Masa saboda kukan da takeyi. ficewa yayi daga dakin Yana Jin wata nutsuwa ko ba komai Dan nasa yayi dacen da kowane uba ke fatan dansa yayi, yasan in Sha Allah za'a samu nagartacci
yar uwa a gurin Nan.
Da sauri mahmud ya biyo shi a baya sai ganinsa yayi.
"Yaya ka fito ka barta kaje ka lallasheta Mana kasan mata 'yan lallashi ne".
Sunkuyar da Kansa yayi sai yaji Yana Jin nauyin hada Ido da Abbie din nasa, Dan shafa gefen fuskarsa yayi
, Shima Abbie din murmusawa yayi ya nufi mota Yana kissima yanda Dan nasa yake Cikin farin ciki Dan masu iya magana suna cewa labarin zuciya a tambayi fuska, Sai dai yana nuna kawaici ne a gabansa.
Abbie na barin gidan Shima ya shiga motar da yazo da ita y
a fice Yana fita motocin Ammi suka doso gidan Daya Aishat ke ja sauran Kuma be tantance ko su waye ba, fitila Aishat tayi masa tayi gaba itama ta gane shi.
A Cikin motar Aishat su Ummee ne sai Mama sauran Kuma su Hajiya kaltume ne 'yan tawagar Ammah sai ta
wagar Ammi dai saura motocin gidan Kuma jama'ar su Mahmud ne da matan gidan.
Tun a kofar gate din gidan Mama ta Raina kanta balle da aka shigo ciki, take taji kirjinta ya Fara ciwo har wani jiri yake daukarta a daddafe ta shiga ciki a Nan Kuma taga abin al
'ajabin Daya so ya zautata Dan abinda Bata taba tunanin ze faru bane take gani. Wai wannan gidan na zahra ne itace mamallakiyarsa ita zata rayu a cikinsa. Lungu da sako ba inda Aishat Bata shiga dasu ba,master bedroom dinsu ne kadai Bata bude ba,da yawa su
n Zama 'yan kauye a gidan, dan sunga abinda Basu taba gani ba, dakin Zahra da kawayenta Wanda suka shigo Babu dadewa suka shiga suna ta rarinarsu da dauke dauken hotuna. su Hajiyar suka shigo ai ganin da gaske Zahrar ce a zaune a Cikin dakin Kuma da sunan
mamallakiyarsa.
Wani Abu Mama taji ya soketa a kahon zuci da kyar ta iya sulalewa ta zauna a bayan wata Mata tana dafe kirjinta.
Babu Wanda ya lura da halin da Mamar ta shiga tafi minti uku a haka kafin ta samu rangwamen ciwon ta Mike ta fice tana Jan kaf
a Dan ji tayi sunyi Mata wani irin nauyi.
Har goma da rabi gidan da jama'a Amma da yawa bakin sun wuce sai danginsu na Cikin garin sune suka nemi gurin suna baza hajarsu ta yin hotuna, sai Aunty safiya wadda gidansu babu nisa da unguwar da aka Kai zahrar.
Yawancin kawayen duk kasa suka sauko ya rage daga Zahra sai sajeeda da Amatullah. Aunty safiya Batasan lokacin yaja haka ba Saida ta duba wayar hannunta taga quarter to eleven sannan ta ankare ta cewa Amatu ta taso su wuce.
Sallama suka yiwa Zahra Amatu na
fadar.
"Kiyi Masa biyayya dai yauwa kada naji kada na gani, ko Aunty safiya?"..
Ta fada tana kallon zahrar wadda ta sadda Kai kasa tana Wasa da siririn zoben gold da yake hannunta.
"Dan Allah Amatu ki rabu da ita tun safe kika damunta, ba gara ita ba Dan
an kusa shatanta ta warke ba, ke kuwa kece a kwana Dan Naga wannan Tajuddeen din da yake dama-dama dake guda ne da alama kema garin namu Zaki shigo".
"Ki rabu da ita Aunty safiya Zan rama ne, wallahi yanzun ma Ina Jin kunyar Aunty na ne baiwa bani da bak
in magana ba ki Bari dagani sai ke kiji magana, Naga alamar ko irin Jan aji Nan bazakiyi ba