Showing 228001 words to 231000 words out of 295116 words

Chapter 77 - AUREN HUCE HAUSHI COMPLETE

dare ba Rana akan Zahra na neman dace da kwanciyar hankali a gidan Aure, sai Kuma tayi murmushi wannan sirikar ta

Zahra za'a da ita tasan ta Kan duniya wato sai ansan yayi aure ba Wai yazo da Matar ba kamar Auren bariki.

Part din Abban ta nufa na bangaren ta, tana shiga Yana aje wayarsa da ya gama. Ganin fuskarsa da wani irin annuri yasa ta fasa fada Masa abinda taz

o dashi gara ta Fara Jin nasa tukunna.

"Wane irin albishir akayi maka haka Mai Dadi Daya saka Zuciyarka a irin wannan Nishadin haka?".

"Zoki zauna yanzu muka Gama waya da sirikin uwata Wai ashe yaron Nan mahmud Dan wajen General Muhammad Dange ne, Saida ya

kirani yanzu na gano inda nasan fuskarsa Kullum na kalleshi sai Naga nasan fuskarsa ko a wani gurin ne daban Ashe fuskar mahaifiyarsa nake gani a tasa fuskar, kinsan kuwa waye General Dange? To babu abinda zewa Ubangiji sai godiya ya sakawa uwata da abind

a hankali da tunanin mu Bai taba kawowa ba mijinta fa shine Dan general din Wanda ake hasashen Yana Daya daga Cikin matasan masu kudin Africa sahun farko duk fa yanda family dinsu sukayi popular a kasar nan ta fuskar arziki yaron yayi musu wata irin tazara

, Abu Daya yake bani mamaki yanda ya iya jure rayuwa irin ta Cikin Almajirai ba kyamata ko kadan Abu Daya ne dai kawai ya ringa sani a tunani yanda tun bayan samun lafiyar yaron komai na makarantar ya canza akace NGOs sun shigo suna wannan mahaukatan ayyuk

an Wanda ba'a yinsu a sauran makarantu Dan ma daga baya sun canza salo sun shigo da wasu makarantu harma Dana Karkara".

Jinnina Kai kawai Ammah takeyi tasan wannan ba tsuminta ba ba Kuma dabararta ba Rahamar Allah ce ga bawa kawai da yake yinta ga wanda ya

so a lokacin da yaso, lallai sun kunshi takaici da yawa a baya Amma Cikin Rahamaniyya ta Ubangiji sai gashi abun ya zamo wani haske daga karshe abinda babu Wanda ya zata Koda kuwa a Cikin mafarki ne.

"Abban Yara Nima abinda ya shigo Dani kenan na fada maka

munyi communicating da mamansa yanzu".

Nan ta fede Masa daga biri har wutsiyar yanda Sukayi da Ammin mahmud.

Dariya Abban yayi yana fadin "Nima ya fada min har Yana bani hakuri da halin Mata na bidi'a Wai ita uwar sai tayi bikin danta kowa yasan yayi au

re"

Sun Dade sun tattaunawa na Suma dole su nuna Mata gata tunda inda Allah ya kaita ba gurin Wasa bane na take Abban ya turawa Ammi makudan kudi ayi abinda ya Kamata Dan ma da furnitures a aje Wanda Ummee suka turo ba'a sakaba saboda babu guri Kuma Kaya

ne na garari.

******** Tunda su zahra suka Gama Break fast suka koma parlour na uku suka zauna suhailat ta kunna musu tv ana yin wani series na 'yan Lebanon, manyan jakunkuna taga masu aikin Ammi suna fita dasu daga dakin da aka aje kayan da suka zo da

su ba dadewa Kuma taji maganar mutane daga dayan parlourn, sai kuma taga suhailat ta tashi da sauri tana fadin.

"Kai su mummy Badi'a ne yanzu da safen Nan haka kamar Wanda suke daga wata unguwar"

Ta wuce ta nufi inda suke.

Da gudu suhailat ta fada Kan mum

my Badi'a tana fadin.

"Sannunku da zuwa mummy keda Hajji zuwaira, ina kwanan ku Ya hanya? Amma zuwan Cikin dare kukayi ko? Naga duka yanzu Sha Daya fa".

Gaisuwar suka amsa sannan mummy Badi'ar tace "ko kadan dazu muka zo wurin karfe Tara da rabi ta baya m

uka shigo muna sama ne gurin Ammi itama yanzu zata sakko".

Aishat ce ta shigo daga wata kofa wadda zahra Bata San ko Ina bane, ranta a hade ta cewa Zahra ta taso suka nufi gurinsu su suhailat.

Suna shiga bakin suka fara fadin.

"Masha Allah, wannan ce Fatee

mar? Matso mu gaisa Hajja zuwaira na fadin "nice dai ta karfen keta katako ce" mummy Badi'a na tare mata, cikin Jin nauyi zahra ta tsuguna ta gaisheni su Cike kunya da girmamawa.

Aishat sai taji tana jin haushin maganar Hajja ita ana ga yaki tana ga k'ura

, Ammi na maganar a mayar da Zahra gurin iyayenta a Basu hakuri ita Kuma tana maganar wani itace ta karfe. Ammi ce ta shigo rungume da wani Abu anyi rapping dinsa tazo ta zauna kusa da mummy Badi'ar tana fadin gara ku tashi komai ya Zama ready kada kuyi da

re tunda tafiyar mota ce".

Tashi tayi tana fadin .

"Hasana kuje kofar baya gamu Nan zuwa".

"Taso sister muje"

Ta fada tana taba kafadar zahra.

Ita fa Bata gane ba an sakata a duhu Ina zata kuma taji ana fadin kada ayi dare to suwa zasuyi Daren? Ita Kuma me

ya hadata da bakin Ammin da taji kamar da ita zasu tafi.

Ita dai bin Aunty Aishar takeyi wadda taji kicin kicin da rai kamar ta fasa kuka.

Wata lafceciyar GLK Mercedes-Benz 2024 model Parke a kofar baya sai daukar Ido takeyi Baba Habu drivern Ammi na Aman

a Yana gefe Yana jiran Umarnin Ammi.

Da saurinsa ya matso Yana gaishe dasu zahra, fa sauri zahra ta Dan duqa ta fadin.

Lafiya kalau Baba"..

Su Ammi ne suka fito har inda su Zahra suke tsaye Ammi ta Karaso, ta Kamo hannun Zahra ta dankata a hannun Hajja zuw

aira tana fad'in.

Gata Nan Hajja na Baku Amana ku damkata hannun mahaifiyarta Dan Allah, Allah ya tsare hanya".

Kunshin abinda ke hannunta da wani gidan sarka White gold Mai azabar kyau sarkar kudinta sun tasarwa milion hamsin ta mikawa Zahra tana fadin "A

llah ya tsare hanya ki gaishe min da mamanki".

Ta bude motar ta sakata ta juya ta koma Bata Kara kallonsu ba saboda ji tayi kamar rabuawar kenan.

Wasu hawaye Aishat taji sun cika Mata ido da gudu tabi bayan Ammi tana fadin .

"Why! Why! Why! Ammai kin kashe

min farin Cikin bros wallahi".

Mahmud ne ya fito daga part din Abbie yaji wannan kalaman daga bakin twin sister dinsa.

Yayin da a waje itama Zahra data Gama fuskantar inda aka dosa ta kifa kanta a gefen kafadar mummy Badi'a tana sakin wani marayan kuka ta

na ayyana shikenan ta faru ta Kare wata sabuwar matsalar kuma.

A Hankali zahra ta bude idanunta sharaf da hawaye Jin motar ta harba da wani irin speed ta nufi main gate, ta juya ta yiwa gidan kallon karshe gidan data kwana Daya Tak a cikinsa da sunan matar

dansu wadda a yau kuma bata San wane suna zata Zama ba, wata Kika sunanta ya tashi ya koma bazawa kuma, Dan rashin 'yanci ko Jakarta ta hannu ba'a Bata dama ta shiga ta dauko ba.

* AUREN HUCE HAUSHI*

AISHAT ISAH MUSAH

Maman Fateemah



99061432

330

Or

08056362975

Page 78

.............

Cikin wani irin karsashi mahmud ya riko Aishat Yana fadin.

"Meye haka kikeyi? Kinfi Ammin sannin abinda ya Kamata tayi ne, Ni ne nace Mata idan zahra Bata kwanta Mata ba tayi abinda ya Kamata, ina cewa a gabank

i komai ya faru? to meye kuma na daga hankali Allah yasa hakan yafi Alkhairin".

Ya juya ya fice daga part din gaba daya, mota ya shiga yabar gidan gaba daya, isolation yake bukata a yanzu Dan Kansa babu abunda yake sai Sara Masa besan me yasa Ammi tayi hak

an ba amma jikinsa be bashi Wai an rabashi da precious bane har abada, akwai wata manufar yin hakan duba da zuwan gaggawa da yaga su mummy Badi'a da Hajja zuwaira matar kawu yusufu sunyi yasan da magana a kasa Kuma ga tafiarma a sirrance akayita ta kofa

r baya motarma Mai duhun glass ce,

Duk abinda mahmud ya fada Ammi taji shi sarai Amma tayi gaba dole ta nemarwa matarsa uwar 'ya'yansa Qima da mutumci bazata biyewa yarintarsu ba a haifi Dan da babu idanu.

Sama ta Haye tana lalubo number Aunty Surayya mat

ar uncle Mustapha.

Daki Aishat ta koma ta dubo ko Afnan ta tashi tunda Abulkhairi Yana gurin Batool, Amma fa hankalinta yaki kwanciya so take taji daga bakin Ammi din dole su zauna.

Kwanciya tayi tana lalubo number sweet heart dinta dole su ta fada Masa ha

lin da ake ciki saboda a gabanshi Komai ya faru akan yanda ya gigice daga yi masa fushin d'an lokaci to Ina ga anyi Mai dungurungun kuma, ai sai yanda Hali yayi tasan abinda ya fada kawai dauriya ce bawai har Zuciyarsa haka abin yake ba.

*******Tunda su z

ahra suka dauki hanya tayi shiru mummy Badi'a ke yiwa Zahra Hira da hannunka Mai sanda akan abubuwan da suka danganci zamantakewar aure da irin 'yan dabarun rike miji yaji ba wata sai Kai, ita dai zahra daga eh sai a'a take fada ko hanyar Bata lura da inda

suke nufa,ita dai Hajja zuwaira barcinta take Sharawa tunda suka dauki hanyar dodar, tafiya Malam Habu yakeyi iya tafiya ga kuma lafiyayar mota, a Kano sukayi sallar azzuhur da la'asar suka dauki hanya zahra tayi mamakin yanda wannan bawan Allah yasan han

ya haka gashi dai ya fara manyanta.

Karfe shida da rabi suka shigo Cikin garin Azaren katagum, dan rage tafiya Malam Habu yayi ya Dan juyo Yana fadin 'ranki shi dade Ina muka nufa gamu Allah ya kawo mu Azare".

Hanya ta ringa nuna Masa Yana bi har kofar g

idan Abba.

"Masha Allah".

Mummy Badi'a ta fada a ranta ganin gidan da suka zo da gani Suma ba kashin yadawa bane da nasu rufin asirin daidai gwargwado dan ko makaho ya Shafa yasan da abun.

Horn biyu malam Habu yayi Baba sani ya leko ganin Bai sheda motar b

a ya fito ya nufo su dai dai gurin window din driver ya leko gaisawa sukayi kafin Zahra tace Masa.

"Baba sani nice zahra ka bude Mana".

Da sauri ya juya Yana fadin "sannunku da zuwa ai bangane ba sai yanzu".

Suna sako Kai Cikin harabar gidan magaji na fit

owa da sauri da alama wani uzirin ne ya taso masa ganin bakuwar mota Mata na fitowa yaja ya tsaya yaga su waye ganin Bai sheda su ya nufi hanyar ficewa yayi taku kadan yaji maganar Zahra daga bayansa tana fadin.

"Sulaimanu".

Da sauri ya juyo yana dariya.

"Kai Kice cere Bina ce ta shigo garin".

Mummy Badi'a bata san lokacin da dariya ta kubce Mata ba, tana kallon magaji Daya nufosu da sauri.

Gaishe dasu mummy Badi'ar yayi Yana fad'in.

"Sannunku da hanya Bismillah ku shigo, yayi gaba da sauri don ya isarwa d

a Ammah sako, haba Ashe da dalili shi dai yaga anata faman dafe-dafe Daya tambaya ba Wanda ya bashi amsa, Zahra na gaba su mummy Badi'a suna bayanta cikin gidan shiru ba kowa sai su zilai da sahura suna gyaran kitchen din waje daga nesa sahura ta hango su

zahra zasu shige part din Ammah.

"Kai zilai Kinga kamar uwar dakinki sa wasu mata sun shiga part din Ammah".

Banza zilan tayi Mata tana ganin tsabar gulmace kawai irinta sahura wace zahrar kuma wadda bata kasar ma gaba daya, jin tayi banza da ita yasa ta h

akura taci gaba da abinda takeyi.

Su zahra na shigowa Ammah da magaji suna fitowa daga kofar baya wadda aka Samar da ita saboda part din Abba.

Cikin farin ciki Wanda har ya bawa zahra mamaki, Ammah ta taresu tamkar tasan da zuwansu, Fadi take "sannunku da

hanya kunsha doguwar tafiya nayi ta neman zahra dazu network ba kyau sai hakuri nayi".

Zahra taso ta shige jikin Ammah kamar yanda ta Saba Amman sai taji nauyin yin hakan a gaban bakin Ido sai dai dan kwantar da kanta tayi a jikin Ammah nan da nan taji wa

ta karaya da tausayin Ammah ya kamata tunda ta Zama budurwa Ammah Bata huta da kwaramniyarta ba yanzu ma gashi ana murna anyi auren ga Kuma wata sabuwa ta bullo In "yan caca.

"Bismillah ku zauna Hajiya sannu sannunku fa"

Alawiyya ce ta shigo da katon tray

dauke da abubuwan sanyi ta aje tana gaishe da bakin nasu.

Mummy Badi'a ce tacewa Ammah.

"Yauwa sannu Hajiya ya muka sameku".

"Lafiya kalau Alhamdulillahi"

Ammah ta gaishe da Hajja zuwaira.

Ruwa kawai suka Sha kafin a rakasu dakin da akayi musu masauki a Na

n part din Ammah din Amma Yana daga can gefe daban ba'a fiye amfani dashi ba tunda da wadatar dakuna.

Magaji ma fita yayi da ruwa da kwalin exotic da Coke na gwangwani yaje ya budewa Baba Habu dakin Baki na waje lokacin Yana gurin Mai gadi suna Hira.

Kayan

dake Cikin motar malam Habu ya Fara fitowa da magaji yana fadin.

"Dan Allah shigar musu da kayan nan".

Zahra dakin da take Zama ta shige tana mamakin yanda Ammah Bata nuna tsahin hankalinta ba duk da Batasan dalilin zuwansu ba ita da 'yan uwan Ammi.



Cik

in Kan kanin lokaci magaji ya Gama shigo da kayan ya zube su a parlour ya shiga ya fadawa Ammah.

***

Su zahra basu fi minti ashirin da tafiya ba Part din Ammi ya fara karbar Baki matar Aliyu Halimatu ita ta fara zuwa Ammi batayi mamaki ba tasan karshen

maganar kenan duk wanda ya samu labarin mahmud ya dawo zaiyi kokarin zuwa ya gani da idonsa ballantana tasan maganar zahra zata karade dangi shi yasa tayi wannan Kandagarkin ta turata gida duk masifar mutum da iya gulmarsa Saida ya koma da gwiwa a sage Da

n Mai Kama da itama baze gani ba, kafin azzuhur part din ya dinke da jama'a 'yan taya murna, na gida Wanda suka Isa sai yan leke-leke sukeyi basa sama basa kasa, irinsu Habiba matar uncle saminu har gidan Hajiya Inna sukaje ita da Matar Ya Abdallah first b

orn din Abbie, tasu tazo Daya da Habiba itama 'yar adawar mahmud ce ta gaske sai dai ita ta iya takunta ba lallai ne lokaci Daya ka ganeta ba,haka suka dawo ba wani labari sai Kuma suka shiga kokonton gaskiyar maganar yarinyar da aka fada yazo da ita.

Aish

at na kwance Kiran Aunty Surayya ya shigo.

"Wai kina Ina ne tun Dan hantsi nake gidan Nan sai yaran nake gani Amma ke ko duriyarki Babu".

Yunkurawa tayi ta tashi zaune tana fadin.

"Ina masaukina a kasa bana Jin Dadi ne shi yasa, Aunty Ina wuni".

Dariya Amm

i tayi saboda wayar a speaker take, tana ayyana kina min dacin Rai dai na tura muku Mata gida,Baku San nemar muku daraja nake yi ba duk wannan taruruwar murnar da ake zuwa ba domin Allah ake yinta ba saboda aga yarinyar da aka Kai musu labarin ta.

" Lafiya

kalau, kizo sama yanzu Ina bedroom din Ammi".

Ta kashe wayar, saukowa Aishar tayi ta zura takalma ta fice tana hawan strains taji Kira ya shigo Mata tana dubawa Sameer ne.

Ta daga da sallama suka gaisa sannna ya Dora da fadin.

"Dake da waye zakuzo gidan o

ga na arkilla zaku duba wani Abu kuga Koda abinda za'a gyara".

"Ok Bari na fadawa Aunty Surayya sai muzo tare".

Ta fada tana tura handle din kofar bedroom din Ammin.

A zaune ta samesu su Aunty Surayya nata faman rubutu a Cikin wata jotter.

Da sallama a bak

inta ta shiga ta gaishe dasu Ammin ta nemi guri ta zauna, Saida Aunty Surayya ta Gama rubutun ta dago tana kallon Aishat din.

"Ungo duba kin gani Koda gyaran da za'ayi".

Jotter ta karba ai Bata San lokacin da tayi super ta Haye jikin Ammin su ba.

"Allah ya

Kara sutura Ammi, ya jikan mahaifi yanda Kika faranta Mana Allah ya haskaka qabarin Alhaji Haroona ya yalwata Masa, mun gode Amminmu sai yanzu na samu kwanciyar hankali wallahi".

Murmushi Ammin tayi.

"Allahumma Amin, da kin dauki fushi Dani Dan Ina nemar

muku daraja da kima kinsa yau har sama Hajiya Babba ta hauro saboda taga kwakwaf tunda nasan yayan ki Ibrahim ya fada Mata komai har dakun Nan ta shiga Wai sau Daya ta taba shigarsu Ina jinta dasu Batool Suma da Taya bera Bari har kciki suke shiga Kuma jik

in ba kwari ta sauka da kyar fa take taka kafar Amma gulma ta hauro da ita saman Ina jiyo wash wash dinta tana sauka".

"Allah ya kyauta ai ba Karamin Basu kafa mikayi ba Ammi sai yanzu na gane plan dinki na gaggawar ficewa da zahrar daga gidan Kinga kin ka

she bakin tsanya babu batun mutum ya bugi kirji yace ya ganta da idanunsa, yanzu Sameer ya kirawo ni yace muje gidan bros na Arkilla muga wani Abu ko da abunda za'a gyara".

"To Kuma da boutique dina zakuje a hado lefen da za'a Kai musu can nasan ba wani ab

un azo a gani akayi Mata ba duba da yanda abun ya faru kinsan halin kayanki Kuma".

"To Bari mu Fara zuwa Arkillar in yaso sai mu wuce can din ko Aunty Surayya?".

A gidan suka Sami mahmud da wasu abokansa biyu sai sameer.

Suka gaishe da Aunty Surayya har ta

na zolayar mahmud.

Sameer ne ya shiga ya bude musu inda kayan da suka zo dasu daga Dubai da Kuma akwatunan.

"Auntyn mu gasu Nan ku duba idan da abinda babu ko za'a canza ko karawa sai a fada"..

Ya ja musu kofar, kayan suka Fara dubawa ba karya komai yayi h

arda abinda ma ba'a sakawa an saka sunyi santin kayan kamar me Dan naira da taci gidansu a gurin ba Bata lokaci suka shiga zubawa a Cikin akwatunan abinda ya daukesu kusan awa hudu suna Abu Daya.

Saida suka Gama komai sannan Aunty Surayya ta Kira Ammi vide

o call lokacin Ammin tana gurin Hajiya Inna Dan ana shiga magariba ta fice ita da suhailat wadda ke driving dinsu suka nufi mabera gidan Hajiya Inna taje ta fada Mata komai ake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login