Showing 177001 words to 180000 words out of 295116 words
bawa kofar shigowar.
Har kusa da iya Abu ya zagaya ya gaisheta tare da Kara jajantawa juna tana fadin.
"Kaji sabon kinibibi g
urin zahra'u ko? Wai nice mamarta saboda ta aure min da shine zata Fara ladabin gangan".
Dan kallonta yayi a fakaice, baice komai ba ya tashi ya fita waje.
Bata Jima sosai ba ta fito can ta hange shi suna magana da wasu matasan unguwar, wucewa tayi ta nufi
gidansu Yana kallon yanda Idanu sukayi Mata caaaa kamar yaje ya boye abarsa.
Lokacin data shiga Abba na kokarin fita a mota shi da Bala driver.
Yana ganin zahra ya saka Balan tsayawa harta karaso inda suke cikin murna take fadin.
"Abbana ka manta dani ko?
".
"Haba uwata kin taba ganin da ya manta da uwarsa kina raina Kullum ai muna waya da mijin naki Yana kirana ya gaisheni yaron kirki wallahi malam Bala sai yanzu nake ganin alfanun had a uwata da yaron Nan, tun ranar da muka ganshi nasan Mai nagarta ne"
"To shike nan tunda ya kwace min kai Abbana".
'yar dariya yayi kawai wato halinta yana nan.
Tsugunawa tayi tana gaishe da Abban sannan ta jajanta masa jikin Baba malam, ta gaishe da malam Balan ma, Abban ne yace
can ma zeje Asibitin jiya Daya shiga gurin
likitan dake kula dashi ya fada Masa Wai Sameer ya Barbi komai qungiyoyin dake bada tallafin makarantu da dalibai zasu fita dashi zuwa India, shine Zan koma na bibiyi lamarin kada abin ya Zama wasa tunda ciwon bana Wasa bane".
"To Abba saika dawo Allah ya
bashi lafiya".
"Amin" suka amsa.
Suka fice ita Kuma ta shige.
Suna fita Mahmud na kawo Kai a motar zahra, parking suka gyara su Abban, Mahmud ya fito ya nufosu da Dan hanzarinsa suka gaisa da Abban ya jajanta Masa Matsalar Baba malam din sun Dade suna mag
anar fita wajen inda Mahmud ke bashi assurance Kan fitar, inda yake fada Masa yana Jin Nan da kwana uku zasu iya samun Visa tunda emergency issue ne na Asibiti.
Sukayi sallama su Abban suka wuce shi Kuma ya karasa gidan, very luckily Yana shiga Abdul Hakee
m na fitowa cikin Shirin fita Yana ganin Mahmud ya karaso da sauri Yana fadar.
"Yanzu nake tunanin kiranka a waya za muyi wata magana da Kai Ina fatan ban takura maka ba? idan babu damuwa ka hakura da shiga cikin muje Asibitin daga baya sai mu dawo nan din
tunda gaiswa ce kawai zakuyi dasu".
"Ok ba damuwa muje kawai next time na shiga".
Front seat ya bude ya shiga Yana fadin.
Ai dama nina karb'i tukin.
Suna tafe suna Hira wadda ta dangance su irin ta abokai aminai.
Kiran Sameer ne ya shigo wayar Mahmud suka
Fara wayar yayin da Abdul Hakeem ya shiga duniyar tunanin yanda sukayi da Ammah dazu da da safe bayan su magaji sun dawo labarin da Musaddiq ya Bata yayi matukar daga hankalinta sosai da kyar Abdul Hakeem ya tausheta akan tayi hakuri yayi Mata alkawarin b
incikar Mata waye Mahmud tun daga Nan har sokoton da yake Fadar can ne mahaifarsa,to gudun kada a samu subutar bakin Ammar ta kasa hakuri tayi Masa maganar yasa Abdul Hakeem dafe shi ya Hana shi shigar.
Suna shiga bangaren da aka kwantar da Baba malam din
sukaci karo da Habib sun taho da Dr Omole da sauri wasu likitocin biyu suna biye dasu da gani dai akwai abinda ya faru.
Suma su Mahmud da sauri sukabi bayan su.
* AUREN HUCE HAUSHI*
MAMAN FATEEMAH.
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da dauka
ka da Aminci su tabbata ga shugaban mu Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w.
Page 60.
_____Suna biye da doctors din har suka shiga dakin abinda suka gani ya daga musu hankali, jikin Baba malam ne yake wata irin jijjiga Kamar Wanda yake ciwon tsintsinko irin
na Mata masu haihuwa Abba dasu Abubakar suna ta faman tofa Masa addu'a, ganin lotoci sun shigo yasa su Abba suka matsa suka Basu guri, tamabaya likitan ya jefo musu.
"Ko akwai abinda ya faru Wanda ya haddasa Masa hakan ko Kuma an fada Masa abinda ya tada
Masa hankali ne?".
"A'a Babu komai doctor daga barci ya tashi da wannan abun".
Abubakar ya fada, yayin da Abba ya Kara da "kwarai kuwa muna zaune ya farka da wannan shivering din".
Jinjina Kai doctor Omolen Yaya Yana faman gwaje-gwajensa, rubuta yayi a tak
arda ya Miko Yana fadin.
"Ayi maza a kawo wannan alluran yanzu za'ayi Masa".
Habib ne ya karba ya nufi kofa,mahmud ne ya ya biyo shi da sauri suka fito, sun Fara tafiya mahmud yaga jikin Habib sai tsuma yake tamkar ze Fadi shima, rikeshi Habib yayi Yana f
adin.
"Wallahi kaina juyawa yake yi".
Ya fada Yana dafe Kansa.
"Haba Mana Habib take it easy, kada ka jawowa kanka wani problem din, zauna a Nan Ina zuwa".
Ya nuna Masa wani Dan bencin a gefen baranda da sauri yayi gaba da takardar a hannunsa, maganar Abdu
l Hakeem yaji daga bayansa Yana fadin.
"Muje kawai Naga Habib ma Kamar Baya cikin nutsuwarsa".
Tare suka jera har pharmacy suna tattaunawa Kan yanayin lalurar malam din.
Allurai biyu aka samu a cikin ukun Daya rubuta, a Nan pharmacy din suka fada musu daya
r tana da wahalar samu sai dai su duba a manyan chemist cikin gari ko za'a dace, biyun suka Fara kaiwa suka fadawa doctor dayar babu amma zasu duba a cikin gari ko za'a samu, wani chemist ya fada musu yace suje in dai Babu a can su dawo kawai ba za'a samu
ba a ko Ina.
Tare da Abdul Hakeem suka tafi shi yake driving din, sunje babu sun basu tabbacin sai dai a kano ko Bauchi.
Lokacin da suka dawo doctor Omolen suka samu shi kadai saura doctors din ya sallame su, shima Baba malam din ya Sami barci jijjigawa ta
lafa.
Bayanin da masu chemist din sukayi musu suka fada masa, Abba ya kalla yace Yana son ganinsu a office.
Ya fita da sauri irin Basu na likitoci, Abba da mahmud da Abdul Hakeem sukabi doctor yayin da Habib da Abubakar suka rufawa doctor baya.
Ya rigasu
shiga office din suna zuwa suka same shi a tsaye Yana kaiwa da kawawa, shigowar su yasa ya dakata ya nuna musu resting chairs na office din yace su zauna, bayani ya Fara musu Yana kallon Abba.
"Alhaji dole a samo wannan allurar yau ayi Masa Kuma yanda ka'i
darta take dole Wanda za'a yiwa Yana kusa ma'ana ba'a fito da ita daga fridge har sai Wanda za'a yiwa Yana kusa Bata minti biyar a zafi zata lalace Dan haka dole mu turaku Kano ko Bauchi a yau din Nan saboda idan aka dauki lokaci ba'ayi Masa ita ba za'a sh
iga want condition din Kuma Wanda bama fata tunda Kansa ne ya bugu lokacin Daya samu tsautsayin munga casa din to munyi zaton minor case ne, saida hakan ta faru Kuma muka tabbatar da abinda muka gani, yanzu Shawara ta rage taku sai ku zabi Inda kuke ganin
yafi dacewa sai ku tafi kafin visa din ku ta fito ana son ayi Masa wannan allurar Kamar sau hudu duk bayan Twelve hours are yinta" .
Kafin Abba ya samu zarafin magana mahmud yayi saurin fadin.
"Ina ganin doctor gara muje kanon tunda ta kanon zamu tashi, id
an mukaje Bauchi Kamar mun koma baya kenan, ai kace ko gida za'a iya Zama indai akwai Wanda zeyi allurar?"
Kai ya gyada masa alamar tabbatarwa.
Abba ne yace "Mahmud Ina ganin Kamar abin zeyi muku yawa abin fa bana Wasa bane kana ganin su mutanen naku zasu
yi abinda ya kamata? Dazu yaron Nan Sameer ya kirani yayi min bayanin komai har booking din Asibitin ya fada min ya gama komai Yana ganin daga nan zuwa gobe ko jibi za'a iya samun visa, ya fada min wait uwata Bata samu visa ba yaso ya hada da ita saboda la
lurar ta, nace Masa ba komai hakan ma Allah ya saka muku da Alkhairi, na saka Masa wani Abu a account dinsa kafin na biyo ku muga abinda Hali yayi, yanzu ma Abdul Hakeem ze saka Mata kudi account dinka saboda wannan data taso".
Godiya mahmud da Abdul Hakee
m sukayi Masa sannan suka fito suka bar Abba da docy Yana Kara fada Masa irin yanda yanayin ciwon yake.
Har suka dawo dakin da Baba malam din ke ciki suna tattaunawa dai Kan fitar da za'ayi da baba malam din.
Suna zuwa Mahmud ya cewa Habib da Abubakar su m
aza su koma su shirya zasu wuce Kano yanzu su taho da Iya Abu, key din motar da mahmud yazo da ita ya mikawa Habib yace suje a ciki,sai bayan sun wuce ne Abba ya shigo tare da wasu manyan mutane suka jajanta musu jikin malam din tunda barci yake, kudi masu
dama suka mikawa Abdul Hakeem suka fita suna masa fatan samun lafiya.
Malam Bala ne ya shigo da sauri ya mikawa Abba waya Yana fadin.
"Yallabai gashi Ina ganin bakin sun karaso gidan gonar".
Wayar ya amsa yaga sune, kafin ya Kira an Kara Kira..
Dauka yayi
ya amsa sallamar kafin ya Dora da fadin.
"Dan Allah ki jira Ina da patient ne a Asibiti".
Ya kashe Kiran.
Mahmud ya duba Yana fadin.
"Mahmud Bari naje nayi Baki daga Abuja Wadanda zasuyi aikin titina da office dina ya kawo cikin gari da Kuma gyaran gadar
jama'are, yanzu malam Bala ze dawo saiya kaiku kanon ya tayaku neman gurin Kwana kafin ku tafi sai kuyi amfani da wannan kudin idan Basu Isa ba kayi min magana kada kaji nauyi na Nima mahaifinka ne".
Cikin ladabi Mahmud din yace.
"Nagode Abba Allah ya Kara
sutura, basai Malam Balan ya dawo ba akwai motar da oga Sameer ya Bari jiya sai Habib ya tukamu a ciki kawai, Kuma akawai gidan da zamu zauna a Nan kusa da Asibitin malan Aminu kanon tunda doctor yace suna da allaurar a can".
"To babu laifi Allah yayi Alb
arka yasa a Dace"
Su duka suka amsa da "Amin".
Har gurin motar mahmud ya rako Abba, tare da Abdul Hakeem suka wuce saboda yawanci idan irin wannan project din yaso Abdul Hakeem keyi Masa monitoring na aikin.
Su Habib Basu Bata lokaci ba suka dawo da Iyaye
n jakunkuna take mahmud yace ba Wanda ze dauki kaya, Dan murmushi Abubakar yayi yasan za'a Rina babu yanda beyi da Habib akan kada su dauki Kaya yayi Masa musu Dan haka ya biye Masa suka dauko, tare sukazo da iya Abu, Mahmud ya gaisheta ya Kara jajanta Mat
a jikin malam, daidai saitin kansa taje ta tsaya tana kallonsa, Fara matse hawaye tayi tana fadin .
*Malam haka Allah yayi da Kai? Ubangiji ya baka lafiya idan na tafiya ya kaika da sa'a ya baka ikon cikawa da kalmatushshahada , na yafe maka duk abinda kay
i min da gangan ki da gaske Allah ya yafe maka, saita fashe da kuka sosai, Habib ne ya janyota gefe Mahmud Kuma ya fita da ita Yana fadin.
"Kiyi hakuri cuta ita ke shiga Nan da Nan sauki sai a hankali, kici gaba da yi Masa Addu'a kawai ita yafi bukata a ya
nzu".
Gefen hijabinta ta saka tana share hawayenta tana fadin.
*Kayya Dan nan malam sai abinda Allah yayi dubi fa yanda yake Sambal a kwance Kamar gawa ga want numfashi da yake da sauri da sauri ".
Sai wasu hawayen, bai Bari ta koma ciki ba key kawai yace
Habib ya Miko Masa, ta tasata gaba suka bar Asibitin.
Har cikin parlourn ta Mahmud ya rakata shida Bilyaminu daya samu a kofar gidan Yana bawa wasu Yara wani aikin gyaran itacen da aka kawo Wanda ake musu girki dashi, sun Jima suna Bata Baki kafin ta hakur
a da kukan da take kudi mahmud ya aje mata Wanda har sukazo su taoratata, sannan yace .
"Ga Bilyaminu Nan shine zeci gaba da kula da komai na gidan duk abinda babu shi za'a tambaya Kuma idan mun Isa India Zan Kira shi ya ringa kawo Miki wayar kina ganin ya
nda jikin nasa yake".
Godiya ta dunga Jero Masa da addu'ar fatan Alkhairi har suka fice.
Directly gidan su zahra ya wuce, magaji ya Nemo a waya yayi sa'a Yana gida yace ya fadawa Ammah ze shigo ya gaisheta.
Lokacin da suka shiga ciki,Mama na kofar main kit
chen dinsu tana yiwa sahura magana, a mutunce mahmud ya gaisheta sahura ta garzayo ta gaishe shi, har suka shige part din Ammah kamshinsa Yana gurin da Ido Mama ta bisu. Saida suka bacewa ganinsu sannan sahura ta matso kusa da Mama tana fadin "Wai Mama Bak
i gane wannan yaron bane Naga kin bisu da kallo".
Lemon da take Sha a cup ta kurba tana duban sahura.
"Ina fa na wani gane shi nasan 'ya'yan manyan kasar Nan ne dubk yanda yake Mana ko Ina magaji ya samo shi Dan shishshigi har gurin uwa aka kawo shi to dai
Babu 'yar da za'a lika Masa Daya ce agola Kuma ta bige da yaron malam".
Ta fada tana cigaba da Kora ruwan lemon ta.
"Mama Wai kina nufin Baki gane mijin Zahra bane ba?".
Ai da fadin da kwarewar Mama ba'afi minti Daya ba, Nan da Nan sai tari Kamar zata sik
'e da gudu sahura ta dauko Mata ruwan ta watsa gishiri a ciki ta Bata Tasha.
Magaji na gaba Mahmud na bayansa suka shiga parlourn Ammah, komai tsab ba abinda kakeji sai sanyi AC da sansanyan kamshin turaren wuta Mai Kama daki da freshner, gurin Zama magaj
in ya nuna Masa ya wuce corridor da ze sada shi da bedrooms dinta,a Kan carpet Mahmud ya zauna, tare da magajin suka fito Ammah tana sauko steps din tana Masa sallama.
Cikin nuna tsantsar girmamawa mahmud ya amsa sallamar Yana fadin.
"Barka fitowa Ammah".
"Barka kadai , an shigo kenan ya wajen Mai jikin?".Ta fada tana Zama a Dan nesa dashi.
Gaishe ta ya farayi sannan ya amsa Mata da.
"Mai jiki Alhamdulillahi, yanzu ma zuwa nayi nayi Miki sallama zamu wuce Kano dashi, jikin ne babu Dadi Kuma a Nan Basu da a
llurar Daya kamata ayi Masa shine zamu wuce yau Ina Jin gobe in dai visa ta Zama ready zamu wuce Indian in Sha Allah".
Tunda ya Fara Kora Mata bayani take jinjina Kai daga ita sai Allahn Daya halicceta suka sa me take kissimawa a zuciyarta.
Cikin nuna alhi
nin abin Ammah yace.."Ikon Allah kowa da irin tasa kaddarar, Allah ya yayewa muslmi wahala yasa kaffararsa ce wannan".
"Allahumma Amin".
Mahmud ya fada, sai Kuma parlourn yayi tsit, ga magana a bakin Ammah amman sai taji yaron yayi Mata masifar kwarjini, y
anda ta kare Masa kallo yau ita abin har tsoro ya Bata yanda ta ganshi, da ganinsa kasan ba mutumin banza bane.
Da gyara Zama Mahmud yayi ciki karfin Hali yace.
"Ammah gata Nan Dan Allah zata zauna a garin Nan Bata son Kano ko kadan naso tayi zamanta Amma
ta nuna Bata so, sai su zauna da matar da sukaje Kano tare kafin muga abinda Allah zeyi akan lamarin, Kuma Dan Allah Ammah a kula da Wanda ze Bata Abu taci a cikin gidan nan in da hali ma ke kadai Zaki Bata Abu taci itama Matar a fada Mata ta kula kada kow
a ya Bata Abu ta bawa zahra Dan Allah".
Ita Ammah duk ya sakata a duhu, to meya kawo wannan maganar da gani har cikin zuciyarsa abinda ya fada, Bata zafafa ba tace.
"In Sha Allah za'a kula, Allah ya tsare".
"Allahumma Amin".
Ya fada Zama ya gyara, ganin ha
ka yasa Ammah mikewa tana fadin.
"Ka Karasa tana wancan dakin ta nuna Masa da hannu tayi gaba wurin hanyar kitchen.
Cikin nutsuwa ya ratsa parlourn ya nufi bedroom din da Ammah ta nuna masa, a hankali ya Kama handle din kofar ya shiga, idonta a rufe da ear
piece a kunnenta be Karasa Inda take ba jikin kofar ya jingina ya Zuba Mata idanun dake Bata tsoro a da.
A hankali scent dinsa ya shiga hancinta da sauri ta juyi Inda take jiyo shi carab idanunsu ya sarke, tashi tayi zaune da sauri tana rarraba sexy eyes d
inta.
Hannuwa ya bude Mata alamun ta taso ta tazo gurinsa.
Ita fa tsoro ne ya kamata kada fa Aljani yayi siffarsa ya biyo ta, to ta Ina ma ze shigo har nan.
Wani killer smile yayi mata.
"Kina mamakin yanda akayi na shigo ko? To Ammah ta turoni nazo na samu
lada".
Dan turo baki tayi irin na shagwababbun yaran nan.
"Wallahi ka bani tsoro, ta Ina ka shigo Nan? Ina Ammah?".
Takowa yayi a hankali ya karaso Inda take ya zauna very close to her ya cire Mata dayan earpiece din daga kunnenta.
"Ki daina sakawa Yana d
amage din ear drum na kunne kinji kada ki tashi hankalina, yanzu ki taso mu tafi Kano zamu wuce da Baba malam daga can Kuma zamu wuce Indian din, naso mu tafi tare to duk iya kokari Sameer yayi Amma abun yaki yuwuwa, taso muje kiji dani".
Ya fada Yana kwan
tar da Kansa a jikin wuyanta,ya saka hannu ya tallabo fuskarta ya hade bakinsu, da sauri ta janye tana nuna Masa kofa tana fadin.
"Ammahhhh..."
"Da saninta na shigo ba satar guri nayi ba, taso muje lokaci Yana tafiya".
Narai narai tayi da ido.
"Dan Allah k
a barni na zauna a Nan wallahi tsoron gidan nan nakeyi yayi min girma ga unguwar babu mutane da yawa".
Tashi yayi ya nufi kofa Yana Fadin.
"Ina jiranki a parlour ya fice, har lokacin ba kowa sai kayan Abinci da fruits a Kan table mat a tsakiyar parlourn.
Z
ahra ce ta fito tana Dan gyara rolling din kanta bedroom din Ammah ta nufa ta fito da handbag