Showing 246001 words to 249000 words out of 295116 words

Chapter 83 - AUREN HUCE HAUSHI COMPLETE

Daya kiraki kike Fara tsuma kamar wata tsohuwar kilaki".

Ta saka gefen Alkyabbar ta rufe fuskarta dashi tana Mata dariya.

"Wallahi kinci bashi saina biya Shi kuwa D

an tsabar iya sharri Zaki wani ce Daya Kira nike kama tsuma".

Hannun Amatu Aunty safiya ta janyo tana fadin.

"Zomu tafi ramawa tayi tun farar safiya kike Mata Dan biki ai kadan ma tayi miki".

Suka fito parlourn farko na sama ba kowa a ciki sai wani irin ka

nshi da sanyi Mai kwantar da hankalinki a tsakiya Amatu ta tsaya ta rike Qugu tana karewa gurin zuwa dayan parlourn kallo ta Dan busar da iska daga bakinta tana kallon Aunty safiya dake tsaye tana kallon Amatu data ja ta tsaya.

"Wai lafiyarki Kika ja tung

a Kika tsaya?".

"Bari kawai Aunty aini lokacin da kike bani labarin Families din su mahmud jinki kawai nake gani nake kamar kina kurarasa ne kawai. Amma yanda Naga gidan kakarsa kadai sai Naga ai Bakima iya bada labarin ba ban Kara sarewa ba Saida na shiga

gidan mahaifiyarsa to ga Kuma Mai kankat, Dan Allah Aunty safiya waye mahmud din Nan nifa na sare da Lamarinsu gaba Daya dole kiyi kokontonsa a wancen gidan Daya sakani Santi Ashe akurkin kaji na gani".

Tafin hannuwanta ta bude ta Fara kwararo Addu'a.

"Ub

angijin sammai da kassai ka zauna da Zahra lafiya a gidan Nan Dan isar Annabin Rahama ka tsareta daga dukkan qalubale na rayuwar Aure ka dubi gwagwarmayar data Sha a baya ka Zama gatanta, ubangiji ka jibinci lamuranta Dan soyayyar ka da Manzon Allah ka dor

ata a Kan duk wani mahassadi da 'yan bani na iya ka dauwamar da soyayyarta a zuciyar mijinta, ubangiji ka dubi maraicin baiwarka ba Dan ta rasa gata ba".

"Allahumma Amin".

Sukaji an fada daga bayansu.

Da sauri Aunty safiyar da Amatu suka juya, Mahmud suk

a gani ya shigo ciki ta wani corridor Basu San ta Ina ya biyo ba.

Kunya Aunty safiya taji abinda take ta gudu kenan kada ya shigo da abokansa su sameta a gidan duk da ba wani girmansa tayi da yawa ba Amma ita ai Yaya ce".

Cikin daburcewa Aunty safiya ta ga

ishesa tayi Masa Allah ya Sanya Alkhairi, Amatu ma gashesa tayi.

Zasuyi gaba mahmud din yacewa Aunty safiyar.

"Auntyn mu ko ta Nan Zakibi sai zayyan ya mikaki gida mun gode kwarai".

Tana Jin haka tasan abokansa suna kasa da sauri ta juyo tana fadin.

"Nagod

e jazakumullahu khairan".

Saida ta gangara kasa sannan ya Ciro waya ya Kira zayyan.

"Ga Auntyn mu nan ka mikata gida a fadawa Sameer ya Bata itama".

Kit ya kashe wayar Yana kallon Amatu yana murmushi.

"Ashe dai sai wani yayi min iso gurin previous din kena

n,ai nayi zaton dukkan ku kuka yoye kun bar min ita kadai".

"A'a wane mu da barin sarauniyar Mata a daki ita kadai yanzu haka suna tare da sajeeda".

Gaba Amatu tayi ta nufi kofar ba wani knocking ta tura ta rike kofar tana kallonsu, sajeeda ce tace.

"To u

war iya wace gulmar Kuma ta dawo dake dakin Nan yanzu dai ba kyaleki zamuyi ba tunda babu idanun kunya".

Shigowa tayi tana fadin. "Alheri ya dawo Dani Mai gayya Mai aikin ne na rako dungurungun Dan haka kema tattarko ya naki ya naki Mai gurin yazo".

Wani

irin Ras zahra taji, Ita fa abun Nan ya Fara Bata tsoro Wai me yasa a baya Bata jin haka ne Sai yanzu? turo kofar da yayi ita ta datse Mata tunanin data fada.

Shine Cikin shigar shadda sky blue sai walkiya take tamkar a matse Mai a jikinta ga wani ubansu k

amshinsa na dindindin Daya kashe na kowa a dakin.idanunsa yana kanta wani irin azababben kyau tayi Masa Ganin ya shagala da kallonta kada a saki layi a gabansu sajeeda yasa tayi magana.

" Yallabai barka da dare, ya hidima? Allah ya Sanya Alkhairi ya bada z

aman lafiya da zuri'a d'ayyuba. To zamu tafi gata Nan Zan baka Amabarta a karo na biyu, kamar wancen karon, kaji tsoron Allah a Cikin zamantakewar ku ka tsare Mata mutuncinta a da Basu San waye Kai ba, Amma a yau ko baka fada Mana ba mun gani da idanunmu,

nasan bestie zata iya fuskantar hari daga masu burin samun matsayi irin nata a gurinka, ko ba'a fada ba tunda a Dan kwaramniyar bikin Nan naji views din Mata da yawa a kanka. Gata Nan Bata da kowa a garin Nan daga Allah Daya halicceta sai Kai daka kawota,

ka zamar Mata bangon da zata jingina dashi ka zamar Mata suturar da zata Kare Mata martabarta, kada ka cutar da ita Dan girman Allah Zahra marainiyar Allah ce duk da Bata rasa komai na gatan gidan duniyar Nan ba Amma tana bukatar samun nutsuwa tunda a can

akwai 'yar kasan da ake soya Mata Aya a tafin hannuwanta ba tare da an ankare ba Saida tafiya tayi tafiya, Allah ya amintar dake bestie a Cikin gidan Aurenki ya Baki kariya irin wadda yake Kare bayinsa salihai da ita, ya amintar dake kamar yanda ya amintar

da Annabinsa Ibrahim A.S daga wutar Namaruzu. Dan Allah kiyi Masa biyayya ki rufe masa sirrinsa kinji, Allah ya Baku zaman lafiya Mai dorewa ya kauda muku fitina"..

Sai Kuma muryarta ta Fara rawa, sai hawaye, da sauri ta nufi kofa ta fice. Zahrar ma share

hawaye take haka Amatu itama idanunta sun cicciko da hawayen,Shima Dan gogan tunda yarinyar ta Fara magana yaji kamar ta Dora Masa bulo inci Tara a kansa, ya yarda kaunar precious da yarinyar Nan ta gaske ce babu algus a cikinta saboda yayi wani Abu Wanda

ya gaskata hakan, Dan ranar Daya bijiro Mata da maganar soyyyarsa dan Karamin hauka sajeedar tayi Masa da kyar ya fahimtar da ita cewar gwaji ne yayi Mata ba Wai da gaske yake ba, duk da haka Saida ta nuna Masa kada ya karayi Mata irin haka za'a iya samun

matsala.

A can main parlour kuwa abokan angone tare da kawayen Zahra sai wasu 'yan Mata na family din, tun a can ya fada musu Bai Hana zuwa sayen Baki ba Amma babu Mai shigar Masa dakin barci babu Kuma Mai Kara gane Masa Mata Ganin gurin dinner ma Ala amf

ana.

Yasha caccaka gurin friends dinsa yayi kunnen uwar shegu dasu shine dalilin Daya saka yayi amfani da kofar baya ya hauro stairs din shi kadai.

A Nan su sajeeda suka Sami su Khadija dasu Aneesah da sauran mutanen, Tajuddeen ne ya taso ya nufi Amatullah

yana fadin. "Daman kina sama duk Kiran da nake Miki bakya amsawa?".

Dan bude hannunta tayi alamar babu waya a gurinta.

Jinjina Kai yayi suka nufi waje.

Addu'a sukayi aka shafa sannan kowa ya fito da wata Leda Mai shegen kyau a hannunta da alama kyautar gi

rma ce daga bangaren anguna.

Saida suka fito sannan salis ya Kira mahmud Yana fadin .

"To yallabai ango mu zamu wuce asuba ta gari".

Wani Abu mahmud din ya fada Masa ya fashe da dariya wadda ta janyo Hankalin da yawa daga mutanen gurin Yana fadin. "A'a kay

i zamanka wasu har sun Fara ficewa daga cikin gidan ka duba time lokacin yaja da yawa".

Tun bayan fitar su Amatu zahra tayi tsilli-tsilli, sai taga yau ya Kara Mata wani kwarjin da girma gani tayi kamar ya cika dakin, numfashi ma neman tsaya Mata yayi wal

lahi wani irin Abu take gani a cikin idanunsa.

Yana sauke wayar daga kunnensa ya nufo zahrar Yana sakin tsadadden murmushi, ya Dan tsuguna a gabanta ya saka hannu ya dago fuskarta wadda hawaye ya bata.

"Ya salam!"

Ya fada Yana Zama kusa da ita, tafin hannu

nta Daya Sha lalle ya rike Yana Dan matsawa kada dayan hannunsa ya saka ya zare Alkyabbar daga kanta Yana karewa fuskarta kallo, be tab'a Jin ya gaji da kallonta ba shi dai ya yarda Allah ya jarabcesahi da wata irin soyyaya a kanta shifa ji yakeyi ko baze

kusanceta ba ze iya rayuwa da ita har iya rayuwarsa.

Wani irin kanshi ne ke fita daga jikinta na musamman ba Wanda ya Zama constant ba a'a an samu Karin wani na musamman a Jikin.

"Welcome to Dange's house Mrs Mahmud Muhammad Dange, Alhamdulillahi bini'imat

ihi titummus salihat, Fateemah Allah yayi Miki Albarka yau gaki a gidan Mahmud Kuma gidanki da Zaki rayu a cikinsa ki dasa Mana bishiyar Zuri'armu a cikinsa ta girma ta yadu har asha inuwarta, Fateemah duk burina na duniyar Nan game da mace a kanki na ta'a

llaqa shi ki zamar min bargon daze lillib'eni ki hanani Jin sanyi sai dumin jikinki, ki daukemin duk wata kishirwar data addabeni akan diya mace kinji my princess, duk duniyar Nan da ke kadai na aminnta na bayyana Mata sirrina ciki da waje ke kadaice macen

data tab'a gani ainishin waye ni tunda nayi Hankalin kaina, ki tallafeni kada ki Bari na shiga rubibi a hannun Mata kinji my previous, na baki amanar kaina da kaina tunda ni babu Wanda ya Baki Amana ta amma ke kowa fada min yake gaki Nan Amana na kula dak

e to nima ki kula Dani Dan tamkar marayan da bashi da uwa bashi da uba haka nake a gurinki ki bani dukkan kulawa kinji, kuma Dan Allah ki daina tsorona nifa babu abinda Zan Miki na cutarwa idan na cutar dake Nina cutar da kaina, duk wani burina nandora shi

a kanki".

Ya fada Yana shigar da ita jikinsa Yana sauke ajiyar zuciya a jajjjere, lif tayi a jikinsa Amma fa yaji yanda heart dinta ke beating very fast. Lumshe ido yayi ya rasa meya canza Masa ita take irin wannan Jin tsoron nasa yasan ba dabi'arta bace

hakan ko ranar Daya Fara fito Mata a mutum sak ba tayi irin wannan tsumar ba kawai dai ta Dan rikice Masa na dan lokaci Amma Daya saka Mata pressure dole ta nutsu tayi Masa abinda yake so a lokacin harya saida ya samu relief, Amma yanzu duk ta rikice Masa

a Hankali yayi Mata magana a kunnenta.

"My previous me kike tsoro a tare dani, fada min kinji?".

Ya fada Yana Kara shigar da ita jikinsa yana kuma Dan shafa gashin kanta Daya Sha gyara na musamman, sanyi da salama da wata irin nutsuwa suna sauka a cikin z

uciya da gangar jikin a lokaci daya.

Lif ta qarayi a jikinsa dan da gaske tana Jin wani irin Abu da ada Bata jinsa a tattare dashi, sai yanzu take jin da gaske fa auren ne a kanta sabanin da da take jinta dai gata nan.

*AUREN HUCE HAUSHI*

_AISHAT ISAH MU

SAH

_*Maman Fateemah_*

08055362975

My

WhatsApps number.

*Page 83.

______Kara shigar da zahrar yayi jikinsa, nan da nan yaji labarin Yana neman canza salo shi Kuma harga Allah Yana bukatar privacy saboda matukar ya tab'a wannan shugwababbar 'yar ra

ki sai abinda Hali yayi. Don yasan za'a Sha danger da ita ga mutanen biki suna Nan yasan da safe baza'a rasa masu zuwa suyi Mata sallama ba, yafi son sirri gaskiya. Amma dai zasuyi nafilar da Manzon Rahama yayi umarni da ma'aurata su yita.

"Cikin nasa salo

n da yasan Yana yin rinjaye a kanta ya Dan fara shafa cikinta a Hankali.

"Da yunwa a cikin Nan gaskiya, Bari na kawo Miki abinda zaki

ç

i kada Nan gaba ayi min gorin ranar da akazo gidana ko abincin tarba babu Ina ta kurin sokoto aga nayi failing ko ba haka

ba?".

Ita dai zahra shiru tayi masa shi ya kasa ganewa yau jinta take tamkar Bata taba wata kebewa tare dashi ba,taga sai wani rawar jiki yakeyi abinda ba halinsa ba, duk wannan kanewar ta nemi nata gurin wani sabon mahmud take gani ba Wanda ta sani ba.

Y

a tambaya Yana kokarin zare Mata Alkyabbar gaba Daya daga jikinta wani fitinan kamshin ya mamaye shi, ga wani mahaukacin feeling da yaji Yana fusgarsa zuwa gareta, kankameta ya karayi a jikinsa da gaske ya shiga wani yanayi,ba Karamin yak'i yayi da zuciyar

sa kafin ya sassauta Mata rikon da yayi mata Yana maida numfashi.

Alkyabbar ya aje gefen gadon ya Zama daga ita sai wata rigar atamfa wadda akayiwa wani fitinannan dinki Wanda ya fito Mata da ikahirin halittarta ta kirji zahiri, yabi shafaffen cikinta abi

nda ya Kara fallasa asirin kirjin nata kenan da suke a cike tsan-tsan, ai baisan lokacin Daya Kara mannata a jikinsa ba Yana fadin "Ashe wannan abar ba Karamin sitirtamin kayana tayi ba" Yana Kai hannunsa gurin.

Dan zabura tayi ta rike hannunsa ta shagwa

b'e Masa fuska tare da juya Masa sexy eyes dinta

"Please meu amorrr.....ba kyaufa ka Bari Dan Allah".

Saitin kunnenta yayi magana a hankali..

"Meye ba kyau din fada min abinda nayi Daya sabawa shari'a? Ina son Jin tempareture din jikinki ne naji kamar t

ayi high".

"A'a...ni lafiya ta qalau".

"Ok, to bari nazo".

Ya fada Yana gyara Mata zip din rigar, fuskarta ya dan shafa kadan tare da Bata wani light kiss a gefen wuyanta Wanda yasa tadan fitar da wani Karamin sound da yaso ya Hana shi fitar.

Babbar rigar

ya cire ya aje a kusa da ita Yana nufar kofa ya fice, Dan kwanciya tayi a gefen gadon tana Jin wani Abu Yana circulating a cikin jinin jikinta.

Bai Jima ba ya dawo dauka da Leda Mai tambarin na Maru suya spots, da plates da sauran tarkacen su knife da cups

da su forks, a kan Karamin Conner table ya Dara idanunsa na Kan Zahra wadda ta lumshe Ido tana sauke numfashi a hankali,wani special smile ya saki yana godewa sarki buwayi gagara misali da yayi Masa irin wannan kyautar, Saida ya aje komai sannan ya nufeta

ya tsuguna dai dai saitin fuskarta Yana dan shafawa a hankali narkakkun idanunta ta bude tana kallonsa.

"Oya tashi kici abinci".

Ta lumshe idanun tayi. "I am ok fa, bana Jin yunwa barci nakeji".

Bai saurareta ba ya saka hannu ya dagota daga kwancen Yana f

adin "Ni nagano yunwar a tare dake".

Nama ne Wanda ita dai bazata ce ga yanda aka sarrafa shi ba, ya gyara hannun rigarsa ya Fara Bata tana mitar ita ta koshi Amma Bai barta ba Saida ya tabbatar da ta koshi sannan ya dauko Mata mutuniyar farm fresh ta stra

wberry ya cika cup ya kafa Mata a Baki ta Sha rabi ta kawar da Kai kamar yanda yaran goye sukeyi idan suka koshi da Abu.

"Pls precious ki shanye mana farm fresh ce fa, ko kin daina yayinta ne? Naga tunda mukazo kabi nema ba alhalin an cika Miki store da it

a".

A shagwab'e ta dago sexy eyes din ta tana Masa wani kallon Daya nemi jefa shi a wata nahiyar.

"Nifa na koshi kamar na cikin mafa ze dawo nakeji".

"Ok. Shike Nan Bari na dauke kayan sai ki shiga kiyo Alwala kafin na dawo".

Har ya kai kofa ya tsinkayo ma

ganarta tana fadar "pls naga zaka mayar Kai bakaci komai ba".

Kafeta yayi da Ido Yana nazarinta "Da kina son naci ai da kin bani, amma Baki bani ba tunda na dauke kuma sai wani jikon Wanda kikaci shikenan is enough for us, koba haka ba?".

Ya dage Mata gi

ra ya fice.

Tsam tayi da ranta tana hasaso mezeje yazo, ita fa duk lamuransa sun tsaya Mata a Rai yanda ya downgrade din kansa a Azare da yanda ya ringa mu'amalantar Almajiran malam, a yayin zamansa a can, ita fa gani take wallahi yanzu yafi karfin ajinta

nesa ba kusa ba duk da tasan itama yes ba karya Ubangiji ya Gama Mata gata ya dauke Mata iyaye Amma cikin Rahamaniyya tasa saiya saukake Mata duk wani tsananin rayiwa, duk da Tasha badaqala a baya sai gashi ya zama tariihi.

Allah be Bata ikon tashi ba har

ya dawo, ruwan dake hannunsa na laimar alwala ya Dan yarfa Mata sai tayi figigit tana sauke ajiyar zuciya.

Gaba yayi ya nufi kofar da take tunanin toilet ne, ta Mike a hankali tabi bayansa hanya ya matsa ya Bata tare da fadin "shiga kiyo Alwala Ina jirank

i".

Ya juya ya fice daga dakin, brush ta bude sabo ya wanke bakinta sannan tayi alwalar gurin mirror ta nufa ta karewa kanta kallo, wallahi tausayin kanta da kanta takeyi tasan sai yanda hali yayi Dan ita kadai tasan me take hangowa a cikin idanunsa.

Tana

tsaya taji alamun za'a bude kofar tayi saurin barin gurin, Yana budewa tana zuwa bakin kofar jallabiya ce sabuwa fara Kar a jikinsa sai Zuba kamshinsa nan nasa na musamman yakeyi, hannu ya Miko Mata yana sakin murmushi Yana fadin "inye 'yan matan gidan ma

hmud Dange, yarinyar Nan kina yanda kike so da Dan malam din Nan wallahi sai cika kike kina batsewa irin kada a kawo Miki wargi din nan ko?".

Kauda Kai tayi tana sakin murmushin ta Mai shagaltar dashi "Ni wallahi ka Bari idan wani yaji saiya dauka haka ne

fa".

Hannu ya rike ta fito daga toilet din.

"To da karya na fada ba cikar kike kina batsewa ba kawai Dan ki Sara min allo ki hanani rawar gaban hantsi ni da halaliyata za'a hanani dama daddawata da moda".

Ya fada Yana kafeta da tsumammun idanunsa, sadda ka

nta tayi kasa Dan abinda take gani a can baya ta gani yau muraran a idanun nasa ta rasa wane irin abu ne da yake sakata a rudu haka.

"Muje muyi sallar".

Hijab taga ya dauko Mata fari sol dashi Mai laushi irin na mutanen Indonesia din nan ya zura Mata,Yana

janye da hannunta suka nufi wani guri kamar space din da ake saka dining table suna zuwa taga an yi gurin ne domin ibada kawai ba Bata lokaci ya shige gaba yaja musu sallah, raka'a biyu yayi musu yayi sallama ya Jima Yana musu Addu'oi da harshen larabci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login