Showing 186001 words to 189000 words out of 295116 words

Chapter 63 - AUREN HUCE HAUSHI COMPLETE

/>
mar baki da wayo da dabara Dan Allah wuce a gurin".

Kayan ta dauka ta nufi kofa tana fadin.

"Bari naje na gani ko Yana nan din".

Ta wuce ta fita.

Zugum Mama tayi tana nazarin yanda abubuwa suketa lalace Mata, Wai yarinyar Nan me take takama da shine? duk a

binda za'ayi da sunanta sai ya lalace,ko da tsiya-tsiya yau sai sakon Nan ya shiga gidanta duk Inda ta koma ma saina lalubo shi Dan wallahi bazanga bakin cikin da ze hanani barci ba.

Duk iya kokarin sahura na taga magaji abun ya gagara wayar zilan ma an r

ufe ta, ko Kuma network yaki bada hadin Kai.

Wata dabara ta fadowa sahura, da sauri ta nufi gurin Bala driver tana fatan samun mafita a gurinsa saboda Bata fatan ta rasa abinda Mama ta kwadaita Mata zata Bata.

Yana aikin goge mota da alama fita zasuyi da A

bba, sallama tayi Masa suka gaisa sannna tace Masa.

"Dan Allah malam Bala ko zaka taimaka ka kwatanta min gidan da yarinyar Nan zahra suka koma naji ance sun tashi daga Nan hayin banki,Kuma na nemi duka lambobinsu ban samu ba".

Ta fada tana fatan samun abi

nda take so.

Tunda ta fara Kora bayani malam Bala ya dakata da aikin da yakeyi Yana kallon ta Saida ta Kai aya sannan yace Mata.

"Haba sahura yaushe Zan dunga bin diddigin yarinyar da take gidan mijinta, ai wannan rashin lissafi nema ma wallahi ai da kunya

ki fito neman gidan Zahra a Nan gurin mu alhalin ga uwarta can a cikin gida, to ke me zakiyi a can Wanda Baki son uwarta ta sani".

Cikin rashin yarda da Kai ta Fara fadin.

" A'a wallahi kasan wani abun alherin idan mutum zeyi baya son a gani sai dai shi y

aron ya fadawa uwar tasa daga baya".

"To shiga ciki ki nemi bayani dole"

Ya juya yaci gaba da aikinsa ya bawa banza ajiyar ta, it's Kuma ta koma ciki da ledarta a hannu, mita yake shi kadai.

"Haba mutane sai halin tsiya, Nan gaba kadan wallahi wannan mijin

nata ze shayar da mutane mamaki Dan naji Alhaji Yana wani furuci jiya bansan dai dawa yake waya ba Amma Ina ganin da bincken da yake yi akan yaron Nan Kuma jiya Wanda ya saka shi ya dawo Masa da amsa".

Shi kadai yaci Baga da Yan maganganunsa.

Duk iya dab

ara Mama tayi Amma babu wani cigaba dole ta nufi bangaren Ammah.

Cikin iya makirci Mama tayi knocking a kofar falon Ammah.

Autane ya taso ya bude mata kofar, parlourn yasha gyara sosai sai kamshi ke tashi da sallama ta shiga, duk sai ta Raina nata dakin Da

n babu karya ko yanayin gyaran da banbanci.

"Mama Ina yini".

ba zato Mama taji muryar magaji yana gaisheta daga bayanta.

Da sauri ta juya tana fadin.

" A'a Magaji! Daman kana gidan Nan tun dazu nake nemanka na rasa, Dan Allah tashi ka taimaka ka raka sahur

a gidan Zahra akwai wasu Kaya Dana saka a kawo Mata Amma shiru basuzo ba sai yau da safe shine nake son a Kai Mata su banso ko Ammah ma ta sani ba, sai dai zahrar ta Bata labari, to anje ance Wai basa gidan".

Zama magajin ya gyara, Yana kallon Mama Ido cik

in Ido.

"Wai Mama kina maganar zahra ne?".

"A'a to da maganar wa nake maka".

"To ai Bata garin nan tun jiya suka wuce Kano, kinsa mijin nata baya kasar suna tare da Baba malam a India, to yafi son ta zauna a ca gaskiya, kin San manya Basu fiye son zaman ge

fe ba gara gurin da yake da kyakykyawan tsaro"

Rasa abin fada tayi, ta rasa zancen wa zata Kama na magaji Kona zilai data ce Bata San unguwar da suke ba, kenan ba'a garin Nan ba kenan take nufi,ai da mamaki Daman Ace Wai zilai Bata San sunan unguwa a garin

Nan ba, to Wai waye ma babban da taji magaji ya fada shi yaron ko Kuma waye?.

Tunda magaji ya Gama fada Mata abinda zahra ta fada masa ya koma yayi kwanciyarsa, yaci gaba da latsa wayarsa.

Fita tayi daga parlourn ta koma nata part din duk dabara takwance

mata Kuma Bata taba zaton wankin hula ze kaita dare ba sai yanzu, tana fita Ammah na shigowa.

Magaji Ammah ta kalla tana fadin.

"Waye ya fita yanzu?"

Tashi zaune sosai magaji yayi haka Musaddiq ma matsowa yayi tana fadin.

"Ammah Wai Ya magaji yaje ya raka

sahura gidan Adda Zahra".

Gyara Zama magaji yayi sosai Yana fuskantar Ammah.

Kinsan wani Abu Ammah Anya zahra Bata San wani abu ba game da maganar zuwan da sahura ba zatayi ba? saboda ina zaune Zahra ta kirani ta kada min warning akan kada na kuskura na ka

wo sahura inda take, tace min na fada mata Bata Nan sun koma Kano, to yanzu magamar ce ta kawo ta wai na dauki sahura na kaita gidan zahra zata kai Mata sako shine nace Mata ai sun koma Kano".

Jinjina Kai kawai Ammah tayi tace.

"Allah ya kyautata".

A bind

a ta iya fada Kenan tayi gaba abin ta, ita lamarin Mama har ya daina ma Bata mamaki tausayi take Bata hassada ai mugun ciwo ce.

*

Sai kusan Sha biyu na agogn kasar India Habib ya tashi, yayi mamakin yanda lokaci yayi gudu haka, da sauri ya nufi

toilet Yana yiwa Kansa fadan me kenan yayi shida ya biyo marar lafiya Amma ya bige da dogon barci irin haka, "ko Yaya Baba malam din yake?" Ya yiwa Kansa da Kansa tambaya.

A gaggauce yayi wanka ya fito, Bai wani Bata lokaci ba ya shirya ya fito yana ayyana

Allah yasa Mahmud ya dawo Dan jiya sun Dade suna dakon zuwansa Amma shiru dole suka hakura suka kwanta.

A parlour ya iske mahmud Yana ta faman aiki a cikin computer desktop wadda take girke a parlourn, daga gefe Kuma wasu indiyawa ne su biyu Yana musu mag

ana da harahen indianci suna amsa masa, da alama Kamar Umarnin wani Abu yake basu, har Inda yake zaune Habib ya Karasa yayi Masa sallama ga mamakinsa sai yaji gaba Daya sun amsa masa, Shima Mahmud barin abinda yake yayi ya juyo Yana sakin murmushi ya mikaw

a mahmud hannu sukayi musabaha, sannan ya mikawa bakin mahmud suka gaisa, ganin Kamar Habib na dari-dari dashi dan Yana kula da yanda yake tsare shi da ido, sai idan yaga zasu hada Ido yayi saurin janye nashi, tashi muhmud yayi daga Kan computer ya riko ha

nnun Habib Suma sauran biyun suka rufo musu baya.

"Bakon india, nasan ka gajine shi yasa na Hana Abubakar tashinka nace ya barka kayi barcin gajiya tunda ka gaji da yawa".

Ya fada suna Zama a kujera two seater,

"Bari kawai ni kaina nayi mamakin barcin da

nayi, Ina Abubakar ne?".

"Sun fita da Mr Ajey kasuwa, inaga sun kusa dawowa ma yanzu, ga abinci nan kaci idan ka gama zaku fita dasu Mr Salman zasu rakaka kuje a Sami kayan sakawa tun dazu suke jiran ka fito ku tafi baka tashi ba, ga abincin can ka duba W

anda zaka iyaci sai ku wuce, nima Zan shiga naga doctors din dake kula da Baba malam yanzu suka nemi ganina tunda tun jiya suka shiga dashi dakin bincike na musamman sai gobe za'a fito dashi, kasan tsare-tsaren Asibitocin su da banbanci da namu na Nigeria"

..

ATM mahmud ya mikowa Habib na bankiya juya Kuma yayiwa su Mr Salman maganar da Habib besan me aka fada ba, ya wuce ciki Yana fadin.

"Kada ka dauko kaya kadan Dan bamu San how long samu zauna a Nan ba sai yanda Hali yayi".

Shi dai Habib kasa cewa komai y

ayi Dan ya gama Shan ruwan mamaki ba kadan ba, Mahmud din da suke kwana su tashi tare ne wannan? ko a mafarki be taba kawo haka ba".

Cikin abinda be wuce minti latatin ba Mahmud ya fito cikin kananun Kaya yayi fresh dashi ya fice daga gidan, har lokacin s

u Abubakar Basu dawo ba, da kanshi yake driving din, da Dan hanzari yake tafiya saboda gaba Daya hankalinsa yayi Asibiti.

Lokacin Daya shiga direct office din consultant din ya nufa, be same shi a office ba Yana cikin ward inda yake duba patient dinsa, bai

fi zaman minti goma ba doctor din ya dawo da zugar wasu dalibai a bayansa Yana ganin mahmud ya gane shi, tunda yaji yana Jin yaransu yake Nan Nan dashi.

A cikin office din wasu hotuna ya dauko ya aje a Kan table dinsa yace mahmud da sauran daliban su matso

.Dalla Dalla ya shiga Yi musu bayanin yanda ciwon yake da yanda yake yiwa mutum illah idan har ba'a Farga an kawo mutum Inda za'ayi Masa aikin gaggawa ba saboda yanda spinal cord din ta matse to komai ze iya faruwa za'a iya rasa kafa da amfanin kasan Jiki

na har abada, Dan haka daga Nan zuwa Kwana uku za'ayi wannan aikin, Amma dole charges zasu karu tunda sun Kara gani karaya a kashin hakarkarinsa na hagu guda biyu sai kashin mukamikinsa Daya goce".

Take a Nan mahmud ya nemi a bashi bill na Karin charges di

n da aka samu, yaje ya biya komai ba damar ganin Baba malam haka dokar take,yana tafiya a Kan barandar Asibitin Yana sauri ya Karasa gurin Daya aje mota yaji daga bayansa ance.

"Waye nake gani Kamar Mahmud Dange".

Da sauri ya juya Yana mamakin waye wannan

yayi Masa farin sani haka.

Faisal ya gani kanin Aunty Surayya matar uncle Mustaphan zasuyi sa'anni da mahmud din, cikin fara'a Mahmud ya Fara fadin.

"Faisal bungudu Long time, Daman talaka Yana ganinku?".

"Kaji ka da wani magana Kai ganin ku ai sai Mai sa

'ar gaske, Nigeria kun Mata tawaye ma kwata-kwata yaushe ake ganinku, meya kawo ka Nan ne haka ko patient gareka".

"Eh wallahi wani Babana ne ya samu spinal cord injury muka kawo shi Nan, Kai Kuma meya kawoka?"

"Wallahi Alhajin mu ne ya samu accident tun

kusan wata hudu da suka wuce, karaya ya samu a cinya, anyi gyara har sau uku abun yaki shine, wani doctor da muke gani a wani private orthopedic hospital a Sokoto yayi Mana hanya mukazo nan, kaga jiya uncle Mustapha ya bar Nan kasar tunda shine ya kawo mu

sai da ya Gama Mana koma".

Jinjina Kai Mahmud yake kafin yace.

"Allah ya bashi lafiya, ga jikin girma ga lalura muje na ganshi na duba shi".

Tare suka juya Faisal din Yana fadin.

"Wallahi Rabon mu hadu ne nace Bari na koma masaukina nayi wanka na huta tun

da ba wata damuwa a tare dashi sunce sai Nan da sati uku zasuyi Masa aiki sai sunyi treating din gurin da infection ya Kama sannan zasu sake Masa aiki"

"Allah yasa ayi aikin cikin sa'a yasa da nasara yasa a dace.

"Allahumma Amin" Faisal ya fada.

Lokacin

da suka shiga Alhajin Yana zaune a gadonsa Yana lazimi da casbaha dinsa.

Ganin Faisal ya dawo da wani yasa ya maida hanklinsa a Kansu, har suka karaso yana kallonsu.

Sallama Mahmud yayi masa ya amsa sannan Mahmud din ya gaishe shi da jiki.

Faisal ne ya yi

wa mahaifansa bayanin Mahmud, cikin nuna Jin Dadi mahaifan na Faisal ya shiga jorowa mahmud godiyar abinda akayi masa, Basu jima ba Mahmud ya aje Masa Dala dubu yayi masa sallama, Mahmud yasha shi Albarka Kamar ze Bari Baki gurin godiya.

Shima Faisal godiy

ar ya dunga jerawa Mahmud Kamar me, shiya dauki Faisal ya Kai shi har masaukinsu sannan Shima ya hada shi da dala dari biyar yayi gaba, wani irin shauki ke dibarsa akan yaje gidanta tunda gari ya waye yaji ba abinda yakeso irin yaje ya ganta ita da yaran,

amma wata zuciyar na fada Masa kada kaje akwai k'ura Kuma wannan match din bazaka iya playing dinsa yanzu ba, kwabarka ce zatayi ruwa, dole ya karkata Kan motar ya dauke daga direction din da ze Kai shi gidanta, Amma fa dole yaje gareta duk rintsi Dan yan

zu ma yasan Yana zuwa wani labarin za'ayi ba wannan ba Dan dole ballin ya tashi.

__

Har dare Zahra Bata Jin dadin jikinta Sam da mahmud ma ya Kira Basu Dade ba yace Yana da wani uzurin da zeyi sukayi sallama.

Wurin karfe biyu da rabi ta farka sai taji Ka

mar an Zuba Mata ruwa, da sauri ta yunkura ta tashi zaune abunda ta gani ya sakata tashin hankali ta sauko a zabure tana sallallami jikinta sai rawa yakeyi, period ne yazo abinda Bata taba yiba kenan ai sai kowa yasan da zuwansa Amma wannan sai ganin Abu t

ayi da wata irin Zuba ta tashin hankali.

"Na shiga Tara mezan gani haka?".

Toilet ta nufa tana cikin rudu ba kadan ba data shiga ta cire nighty din ta sakarwa kanta Ruwa ta wanka Yana bin kafarta Zuba yake sosai har da guda guda, ganin abin bana hankali ba

ne yasa ta fashe da kuka, da kyar ta samu ya Dan tsagaita da Zuba ta hada pad biyu ta saka ta fito ta kunna wutar dakin yanda taga Kan bed din sai hankalinta ya Kara tashi cire bedsheet din tayi tana share hawaye.

Cikin washing machine ta saka bedsheet din

ta fito da towel a bucket da detergent ta Fara aikin gurin tana cikin aikin tayi wata irin Zuba wadda har Saida ya biyo kafarta saboda yawa hannu ta Dora a ka ta fasa kuka tana fadin.

"Na shigesu shikenan mutuwa zanyi".

Wayarta da dauko ta lalubo number M

uhmud ta Kira ba tayi tunanin ko karfe nawa bane a can.

Yana zaune yana aiki a laptop dinsa yaji Kiran ta ya shigo agogon dake parlourn ya duba yasan yanzu a Nigeria tsakar dare ne to lafiya yasan ba gwanar chart din dare bace bare yayi tunanin kiransa tay

i suyi Hira.

Yana dauka yaji shashshekar kukanta.

Cikin kidima ya tambayeta.

"Menene? Meya faru? Keda waye a dakin?" Kiyi min magana Mana ".

Duk ya jero Mata wadannan tambayoyin, Bata bashi amsa ba sai faman fadin ta shigesu take.

"Wai precious so kike Ni

ma na fasa kukan ne? na tambaye ki kinyi min banza kina ta kuka, ko wani ne ya mutu aka fada Miki kike wannan kukan ko wani Abu yake damunki ne?"

Ya fada Yana kwantar da murya Dan so yake tadan samu nutsuwar da zatayi masa bayanin damuwar data saka tayi ma

sa Kiran tsakar dare.

"Pls precious tall me menene Mana?".

Cikin karaya da sallamawa ta bude bakinta da kyar tana shashsheka.

"Wallahi me Amor jinane ze Kare bleeding nake kagan shi Nan sai Zuba yake duk na Bata bedroom din Nan Ni dai ka yafe min nasan mu

tuwa zanyi ta fada wani kukan Yana kwace mata.

Jin abinda take fada ya daga Masa hankali sosai, saima ya rasa Yaya zeyi Mata wani tunani yayi, saiya aro jarunta ya yafa yace mata.

" Pls haba my angel ki nutsu babu abinda ze sameki kinji maza kirawo Matar n

an tazo ki hadani da ita.

Kai kawai ta gyada Kamar Yana kallonta, Kiran number Aunty zilan tayi, tana cikin barci taji Kira figigit ta tashi ta dauka sunan Zahra ta gani da sauri ta dauka cikin kuka Zahra tace Mata.

"Kizo Aunty zilai zan mutu".

"Innailaihi

wa innailaihi raji'un! Na zilai na shiga uku meya sameki?".

Shiru tayi mata, da gudu-gudu zilan ta karasa bedroom din Zahra abinda ta gani ya daga Mata hankali.

"Na shiga uku Ni zalaihatu meya sameki wannan ai Bari ne, tun yaushe Kika Fara zubar da jinin

nan? Bari na fadawa Mai gadi ya kaimu Asibiti wannan ai ba abun Wasa bane, Kiran Mahmud ne ya shigo Aunty zilai ta mikawa wayar.

Jin muryar Mahmud yasa Aunty zilai Kara risunawa tamkar yana gabanta, magana ya Fara Dan ko gaisuwar da take masa Sam beji ba.

"Dan Allah ki taimaka Mata ta gyara jikinta ga zayyan can Yana jiranku zaku wuca Asibiti.

A&E sukaje anyi Mata tambayi daga karshe sukace sai nayi scanning da safe zasu tantance Dan Zahra ta kafe ita ba miscarriage tayi ba su Kuma sunce babu abinda ze kaw

o Mata irin wannan heavy bleeding din Sai shi, suna Asibitin mahmud ya sake Kiran zayyan ya tambaye shi me sukace ya sameta.

Yace Masa ance miscarriage tayi Amma da safe zasuyi hoto su duba.

Jim Mahmud yayi Yana tunanin meya hada zahra da barin ciki Kuma

? Sai dai wani abun na daban gaskiya.

Sunyi mata duk abinda ya kamata Kuma Alhamdulillahi zubar tayi sauki, wurin karfe hudu da rabi suka dawo gida sai da safe zasu koma za'a Mata scanning a ga menene mu"assasa na kawo zubar jini kuma ayi Mata pcv.

Bayan d

aqowarsu mahmud ya kirata yafi sau biyar Yana tambayarta ya jikin? Ba wata matsala? Meke mata ciwo?.

Haka yayi tayi ita har Saida ya koma Bata tausayi ma ya fita shiga damuwa ita keda Matsalar Amma ya fita shiga tashin hankali nesa ba kusa ba, ya fada Mata

yayi Dana sanin tahowa ya barta,Amma dole yasan abinyi tunda akwai matsala.

*AUREN HUCE HAUSHI*

08055362975

Or



09061432330

My WhatsApp number.

AISHAT ISAH MUSA (Aunty Uwani)

Naman Fateemah.

Page 64.

.............Sun koma asibitin sunga c

onsultant g

Gynecology doctor sabuwar ce tazo daga federal medical center Birnin kudu, Dr Hajara yqrinya ce karama Amma tasan aikinta, so sai ta duba zahra ta turata ayi Mata special scanning saboda taga history na ciwonta a cikin file dinta.

Basu Dade a g

urin scanning din ba suka dawo, tunda doctor din ta bude take jinjina Kai abun yayi matukar Bata mamaki, Saida ta aje result na scanning din sannan ta cire eye glasses din idonta.

"Dan Allah sister me ki kayi amfani dashi akan matsalarki ta fibroid? Ma'ana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login