Showing 156001 words to 159000 words out of 295116 words

Chapter 53 - AUREN HUCE HAUSHI COMPLETE

yayi miki maganin wannan babbar matsalar?".

Dan Jim tayi tana tunanin to ko abinda Hajiyar makwarari ta Bata ne ya Fara aiki? Hannunta Mahmud da Dan murza kadan daga kasa ta dago ta kalle shi, Kai ya gyada Mata alamar tace wani Abu.

"E

h Dr kakata ce ta bani magani lokacin da aka gano matsalar shine nake amfani dashi".

Biron dake hannunsa ya aje a Kan table din ya gyara zama

"Kika ce kakarki ta Baki magani da aka gano matsalar?".

Kai ta gyada masa alamar tabbatarwa.

"Anyway ba damuwa Ba

ri mu gani daga Nan zuwa ending this month din Nan idan munga da progress shi kenan,idan Kuma Yana nan zamuyi surgery mu cire shi kawai, Allah ma yasa big brother dinki ya yi tunanin zuwa a duba da wuri irin wannan ba'a fiye ganewa ba sai anyiwa yarinya au

re anga Bata haihu ba sannan ake bincike a gano meye matsalar".

"Ok mun gode doctor, kome ke nan zamu dawo zuwa next month din in Sha Allah".

Mahmud ya fada yana mikawa Dr din hannu.

Tare suka fito da Dr din a haraba sukayi sallama shi ya shiga ciki ward

su Kuma suka fice daga Asibitin.

Sun dauki titin da ze fitar dasu HOTORO NNPC ne wayar Mahmud tayi K'ara alamar shigowar massage.

Ciro ta yayi ya duba, gefen titi ya gangara yayi parking.

Sannan yayi dialing din number da akayi Masa text din da ita, ba Ba

ta lokaci daga can aka daga.

"Yi min cikakken bayani".

Abinda Mahmud din ya fada kenan, daga can Daya bangaren aka Fara Masa bayani sai jinjina Kai kawai take yi har ya aka gama fada masa duk abinda ya nema a fada masan.

"Kana jina Zan fadawa Bilyaminu ya

kawota Nan Kano can sallari za'a ajeta zanzo in Sha Allah ayi Mata duk abinda ya kamata".

Ya yanke kiran, ita dai Zahra ido ne nata, wani zance yakeyi Wanda ta kasa fahimta, wacece me za'a kawota tayi shi me zeyi idan yaje gidan da yace a kaita? Nan da Na

n taji faduwar gaba kada fa ko Yana harkar mata, taga ba sauki idan ya rikice, ko zuwa zeyi yayi... Da sauri ta girgaiza Kai tana runtse Ido.

"Ya akayi ne 'yan Mata naga kin shiga dogon tunani?".

Kankance idanu tayi tana Masa wani kallo na tuhuma.

"Wa ken

an za'a kawo maka". Wata dariyar rainin wayo yayi Yana kallonta kasa - kasa.

"Mace Mana, tunda kin hanani ai gara na nemi mafaka inda Zan rage zafi, ko so kike na kasa amfanuwa, idan har ban samu nutsuwa ba saina kwanta gadon Asibiti, kinsan ya nakeji kuwa

?".

Ya wani Yi mik'a Yana kokarin janyota jikinsa.

Da sauri tayi baya tana fadin.

"Allah ya tsari gatari da Saran shuka,ni me Zan baka ai ban cika mace ba, Daman ni me zakayi Dani da aka k'ak'aba maka sadaka bani da wata qima ko daraja a gurinka tunda baka

san darajata ba, da bakinka fa kace an fada maka duk Wanda suka nemi aurena sai sun Gama Dani suke barina kaga kana min kallon fasiqa Mai ma'amala da maza kenan me ze Hana ka Kira a kawo maka mace a gabana, wallahi tallahi bazan zauna da fasiqi ba sai dai

ka rabu dani wallahi ban taba kebancewa da wani namiji ba a duniyar nan bayan Kai, bazaka shafa min wahala ba ka gudu ka barni, tunda har gobe ba Wanda yasan daga ina kake, Kuma rayuwar garin Nan ai mun santa komai ma na haya ne, haka kawai ka cuceni ka g

udu ka barni da Jangwam idan da gaskiya wa yake gudun asalinsa ai duk lalacewar gida yafi daji ka koma Mana idan ba fitsare gurin kayi ba da abin kunya ba ka gudo nan".

Tana kawowa Nan sai kuka, shi ikon Allah ya tsaya Yana kallo yanda ta zage tana tsula

Masa rashin kunya wato Mata ba sauki gurin kishi, Dan murmushi yayi yana ayyana 'yar daru kawai.

Dauko ta yayi cak kamar 'yar baby ya kwantar da kujera ya sakata cikin jikinsa ya zagaye ta da hannunsa.

Tana ta mutsu-mutsun kwacewa Amma yayi Mata kyakykyawa

n riko.

"Mai maita min abinda kikace waye Dan iskan? Ni zaki kalli idona kina fada min abinda ranki ya Raya miki? Idan matan zanbi kin isa ki hanani ne, nace a kaita sallarin Kuma Billahillazi mace ce kuma gurinta zanje ko Zaki hana ne, an fada Miki ina so

nki ne kunya da kawaici yasa na karba amma badan kinyi min ba, Kuma ki rubuta ki aje har abada bazan taba sakinki ba idan ma kinayi dan naji haushi na rabu dake ne ki sake dabara, Kuma dake zamuje can din na ajeki na shiga nayi abinda nakeso mu koma Kuma k

iyi min wanka, gida Kuma eh abun kunya nayi na gudo nan, yarinya na yiwa ciki Dan haka ki shirya rike yarinyar da aka Haifa min nan gaba kadan".

AUREN HUCE HAUSHI.

Naman Fateemah.

Page 54.

...........Sun Kai kusan minti goma a haka, tana jikinsa a

haka tayi kukanta Mai isarta, baris yayi da ita Yana Jin tana ajiyar zuciya, Shima da gaske ta tunzura Masa zuciya Wai "fasiqa"

kalma mafi Muni Daya tabaji daga bakinta, dole ta karbi hukunci Wanda ko Nan gaba ba zata Kara marmarin fada Masa makamanciyar i

rinta ba.

Sauke ta yayi daga jikinsa ya gyara kujerar ya tada motar, baiko Kara kallon inda take ba ta fisgeta da wani irin mahaukaciya gudu.

"Wayyo Allah Nan Dan Allah kada ka kashe mu, na shiga uku". Ta fasa masa kuka Dan da gaske ta tsorata da yanda ya

saki motar.

Bai tanka Mata ba amma ya sassauta gudun, shiga Nan fita can taga sun shiga wata unguwa Mai karancin gine-gine duk tayi zuru-zuru da ita kofar wani katafaren gida ya tsaya ya Danna horn da karfi da gudu aka bude gate din ba wata wata ya Danna

Kai cikin gidan.

A tsakiyar gidan ya Parker motar, wasu kartin maza ta gani sun nufo motar da sauri kusan su shida dukkansu majiya karfi, take jikin zahra ya dauki rawa, Yana kallonta ta gefen Ido yanda take mazari, Amma ya share ta.

Kofar ya bude dai dai

lokacin da suka karaso suna kwasar gaisuwa.

"Sagir tana Ina?".

Mahmud ya fada Yana duban Wanda ya kira da sagir.

"Tana ciki yanzu ba dadewa bilya ya kawo ta".

"Ok.kuna iya tafiya Amma kafin Nan ku sako min little da barbar tsakar compund din nan. Yayi gab

a abinsa ya nufi wata katafariyar kofar parlour.

Zahra tayi mutuwar zaune Dan gaba daya tsoro ya cika Mata zuciya ganin wannan mutanen kawai tasan ba abin arziki ake qullawa a gidan Nan ba, Wanda taga ya nufi wani guri can baya ya taho tare da wasu irin ka

rnunka masu wani irin gashi a jikinsu bula bula dasu, wani irin kara Mai Kama da fito yayi musu suka Fara zagaye motar suna wani irin gurnani, wata mota hilux taga sun shiga sai mutum biyu suka Bari a gidan suka wuce.

Zahra idanunta na ganin karnukan na za

gaya motar hantar cikinta ta Kama rawa, a duniya tana tsoron Kare bare wadannan data gani masu Kama da kura ai Bata San lokacin da jib'i ya rufeta ba duk da sanyin AC dake motar, wannan wane irin wulakanci ne yayi Mata Yana can Yana aikata masha'a ya sakar

Mata karnuka wadanda zasu hanata fita ko Nan da can.

Daya daga cikin biyun da suka rage a gidan ne ya nufi cikin gidan ya Zama daga Zahra sai Wanda take tunanin Mai gadi ne sai Kuma masu gadinta Dan taga alama saboda ita aka kawo karnukan nan, Bata San lo

kacin da kuka ya kwace Mata ba tana fadin.

"Wayyo Allah! Abba kazo kaga yanda ake wulakantani karnuka ke gadina Kamar wata criminal".

Motsin kirki ta kasayi gani take kamar idan ta motsa zasu fasa glass din su shigo ciki, ba abin tashin hankali irin gurnan

in da sukeyi.

**

Cikin takunsa na mazantaka ya shigo parlourn sai da yazo tsakiya yaja ya tsaya Yana karewa gurin kallo kamar yau ya Fara shigowa, ba motsin komai, da sassarfa ya Haye steps din da ze sada shi da dakunan barcin, kofa ta farko ya bude da ka

rfi abinda ya sakata zabura kenan ta Dora hannu a ka jikinta ya dauki karkarwa tana fadin.

"Wallahi Allah sani akayi bani nake Mata wannan abun ba".

"Shiii! Kept quiet!".

Ya daka Mata tsawa, Yana kusanto inda ta takure a jikin katafaren gadon, kafa Daya ya

Dora a Kan gadon dayar tana dire a kasa Yana Kare Mata kallo tun daga sama har kasa sai wani bashi yake tashi daga jikinta.

Sadda Kai tayi kasa tana tsuma.

Cikin izza da rashin son wargi ya bude bakinsa da kyar yace Mata.

"Meya hadaki da rayuwar iyalina?

Meta tsare miki? Keda waye kuka saka rayuwarta gaba? Waya sakaki bibiyar lamarinta gurin kawo sakonnin mugun Abu? Waye ya sakaki jefo abinda Kika jefa a gidan ranar da Zayyan ya kamaki? Kada ki kuskura kiyi min karya duk da kin haifeni Zan nuna mini true

colour din yanzun nan, sai kinyi Dana sanin sanin Wanda kikewa aiki wallahi Dan Allah sai nasa an wulakantaki".

Zayyan ne ya shigo.

"Sir akwai damuwa Naga hankalinta ya tashi kamar tana kuka, da alama tsoronsu takeji ko a mayar dasu ne?".

Wani banzan kallo

ya watso masa.

"Sorry sir".

Ya fada Yana sadda Kai kasa.

Kuka ta fasa tana fadin "Dan Allah kayi min Rai yallabai wallahi bani nake Mata wadannan abubuwan ba, wallahi Hajiya Mama ce duk Aurenta da ake fasawa ma ita ce take yin asirin da ake fasawar saboda

an fada Mata duk cikin yaran gidan Zahra tafi kowa sa'ar rayuwa,mijin da zata aura ba ita ba wani ma saiya huta a jikinta,uwa uba Kuma tafi duk yaran gidan kyau da cika irin ta Mata ga nasaba ta bangaren mahaifiyarta,ko rashin zuwan kakarta kasar Nan da h

annun Hajiya mamar a ciki, abinda nakai na farko Wanda wannan ya karba, ta nuna Zayyan, Shima maganine a cikin turaren wutar Wanda akace idan ta turara ka shaki kamshin bazaka Kara Zama a Azaren ba har abada, zaka kuma manta da ita Zahrar sai dai kotu ta r

aba Auren, na ranar Nan Kuma wallahi bansan Kona meye ba tace daga Jos aka kawo Mata wayata ma babu caji har gida tazo ita da dureba ta aikeni naje Tasha na karbo ta fada min duk yanda zanyi ta bani duba hamsin tace ladar aikina ce, wallahi iya abinda na s

ani kenan, kayi min Rai wallahi na daina har abada ka rufa min asiri wallahi na baro mahaifiyata babu lafiya ni nake kula da ita, kudin da nake samu a gurinta dasu muke cin abinci na Kuma sayawa tsohuwa ta magani".

Ta fada tana yarfe gumi daga fuskarta duk

da sanyin AC dake ratsa dakin.

Tsayuwarsa ya gyara Yana jinjina maganganunta a zuciyarsa, shi yana Jin chakwakiya kala kala Amma ta zahra ta bashi mamaki wannan wace irin kiyayya ce haka.

"Kinsan abinda yasa Zan kyaleki?"

Da saurinta ta girgaiza Kai.

"Sab

oda ke 'yar aike ce, shi Kuma jakada Bai taba laifi ba sai ke kin bada gudun mawa gurin cutar da marainiyar Allah Wadda bataji ba Bata gani ba, kunyi ta kokarin kada ta cimma abinda Allah ya hukunta a Kanta Ashe Taki kuke zubawa gonarta,ku Baku isa ku Hana

Allah s.w.a ciki Alkawarinsa ba a Kanta, hassada ga Mai rabo Taki ce, Kuma dare ga Mai rabo hantsi ne, duk da ta auri Almajirin malam baku saurara Mata ba dole sai ta wulakanta ko? To Allah ya nuna muku Kaidin ku ba komai bane da sannu zaku girbi abinda k

uka shuka, babu abinda zanyiwa Hajiya Mama taci darajar mijinta.Amma ke gargadi na farko Kuma na karshe da Zan Miki kada naji ko labarin ki a Azare duk ranar da naji labarin an ganki saina saka an batar dake har abada, ga Bilyaminu nan ze mayar dake kutatt

ara ku nemi wani gurin ko arear Bauchi kada naji labarin an ganki, na bashi sako ze Baki idan dan talauci ne kika Zama jakadiyar yada barna to ki nemi sana'a ki Kuma tuba ga Allah Mai gafara ne Mai jinkai".

Wani kukan ne ya kwacewa Asabe Bata taba tunanin

ze Zama me rangwame a gareta ba,duba da yanda Zayyan da bilyamu suka ringa surfa Mata Mari har Saida kumatunta suka Haye kamar ta kunsa biredi a ciki.

"Na gode! Nagode! Yallabai Allah ya saka maka da Alkhairi lallai ka cika mumini Mai imani ka saka sharri

da Alkhairi in Sha Allah gobe zamu koma gida Zuru daman nina Kiya da innata tace mu koma mahaifarta Ina kwadayin abinda nake samu da Mama".

Bai Kara tofa ko kalma daya ba ya juya ya fice daga dakin Zayyan ya biyo shi a baya.

Wani bangaren ya nufa yayin

da Zayyan yayi waje, har lokacin su barbar suna nasu aikin, sagir Zayyan ya kwalawa Kira ya taso daga bakin gate ya nufo shi.

"Dan Allah meyasa baka da lissafi ne Wai? Kasan wacece a motar Nan daka bawa karnukan ku umarnin nan?"

Motar ya kalla yana fadin.

"A'a ban sani ba".

Kwafa yayi to matar oga ce wallahi idan ta ganeka sai tayi maganinka, da alama wani abun tayi masa kasan boss ba sauki idan aka taba shi, kasan meye bani mamaki besa nayi bij-biji da wannan matar ba saima ma makudan kudi da ya bada a

bata".

Ya fada Yana tsaki.

"Kai rabu da wannan muyi magana Mai mahimmanci. Dan Allah da gaske ne da ake fadin oga yayi aure? Wallahi na dauka duk shafta ce kawai".

"Matsa Nan, naka Wasa ne yanzu ka janye su salin alin ka tafi dasu gurinka yanda baze gane

Kai ka janyesu sai yayi zaton sun gaji ne suka zo gurinka".

"Haka za'ayi Bari ka gani".

Ya juya da sauri Yana wani irin fito a hankali, da gudu sukayo gurinsa ya nufi gate suka bishi suna kada jela.

Wata ajiyar zuciya zahra ta saki Dan tayi kukan har ta h

akura ta zubawa sarautar Allah ido.

Bayan fitowar Zayyan Mahmud yakai minti Sha biyar sannan ya fito cikin sabuwar shiga ta wasu kananun kayan, ash colour T.shirt da black trouser Yana baza kanshinsa kamar ko yaushe.

Da sauri Zayyan ya nufo shi, ganin Basu

little a gurin motar yasa Mahmud din yiwa Zayyan Wani kallo, shafa Kai yayi yana fadin.

"Tuba muke oga, hukuncin yayi tsauri".

Be ce Masa komai ba har suka karasa gurin motar saida ya bude sannan ya dubi Zayyan din Yana Mika masa key.

"Ungo bari mu koma b

aya kayi driving din mu na gaji bazan iya mayar damu gida ba".

Ya zagaya ya bude side din zahra take zaune Yana fadin.

"Precious" ya Mika Mata hannu alamar ta kama ta fito...

Tun wayewar gari Hajiya Mama ke jiran Asabe ta kawo Mata sauran magungunan da za

tayi amfani dasu mahadin Wanda ta tura a jefa gidan Zahra, har akayi sallar azzahar babu labarin Asabe, la'asar shiru gashi har bayan insha'i babu ko duriyarta a gidan gashi wayarta a rufe. Ganin zaman tsammani baze yuwu ba yasa Mamar fitowa neman sahura,

can inda dakunansu suke ta nufa tana tufka da warwara, tashin hankalinta Daya Bata aiwatar da abinda akace tayi tun safe ba, a daki ta samu sahura ta Bata kudin adaidaita ya kaita gurin Asabe ta fada Mata tazo tana nemanta.

Labarin da sahura ta dawowa Mama

dashi yayi matukar daga Mata hankali, Dan 'yan gidan abokan hayarsu sun tabbatarwa da sahura tun fitar da sukayi Hajiya Mama Bata dawo gidan ba har lokacin.

AUREN HUCE HAUSHI.

Maman Fateemah.

Page 55.

_____Zayyan Yana fitowa yaga yan

da zahra ke tsuma sai yaji ba Dadi, gaskiya oga Bai kyauta ba, da alama ta hadosu ne yake horata ta wannan hanyar wato halinsa Yana Nan na rashin son wargi, itama Bata tsira ba saiya nuna Mata Hali.

Gurin sagir ya nufa, Yana Jin babu Dadi a cikin ransa

, ga wadda za'a hada da barbar Nan yayi kaca-kaca da banza, Amma ya wani kyaleta taci bulus sai wannan Mace Mai daraja ze hada da wadannan karnukan nasa masu kama da kuraye su tsare yarinyar mutane, shi ko tausayinta bayaji ya wani yi zamansa a ciki idan m

a sumewa zatayi bashi da damuwa, Allah idan ya wuce saiya casa waccan karamar 'yar iskar dan yaga alama tsohuwar Yar duniya ce ta kware a gurin munafurci.

A zaune ya samu sagir Yana jin wakar boda katsina.

"Dallah kashe Mana! Kai ko imani ma baka

dashi, ka sakarwa baiwar Allah karnukanku marasa mutunci kazo kana shakatawa,to Bari na fada maka, idan kayi Wasa ka kusa cin taliyar karshe a karkashin oga wallahi, dan ba kowa ka sakarwa karnuka ba sai amaryar oga, idan tayi marking dinka kana zaune za'a

ce ka Kara gaba".

Ya fada yana Jan tsaki yayi gaba abinsa. Sororo sagir yayi yabi Zayyan da kallo sai Kuma ya tashi da sauri yabi bayansa.

"Dan Allah Zayyan tsaya, fada min gaskiya wallahi na dauka irin masu kawo kansu din Nan ne yake so ya koya Mata hanka

li, tunda mun shaida oga baya harkar Mata, shi yasa nayi biris da lamarin su".

"Yayi kyau, wallahil azim nasan hankalinsa Yana Kanta dari bisa dari kawai dai so yake ya nuna mata shi din Jan wuya ne baya daukar shirme, tun wuri kasan yanda zakayi ka mayar

dasu muhallinsu kafin lokacin fitowarsu yayi su fito patrol"

Fitoh daya sagir yayi musu suka nufo inda suke tsaye, gaban sagir din suka turje gaba yayi suka rufa Masa baya.

Mahmud ne ya fito sharr dashi da gani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login