Showing 147001 words to 150000 words out of 295116 words

Chapter 50 - AUREN HUCE HAUSHI COMPLETE

bari ta duba Koda kayan amfanin kitchen Dana abinci tasan abinda ya kamata tayi kada ta Zama sakarya wadda ta rako Mata. Plat shoes

ta saka fari tas dashi ta nufo down stairs din cikin takunta mai daukar hankali, Bata ankara da mutum a zaune ba Saida ta ahigo tsakiyar falon taja ta tsaya tana rarraba idanu tana son tantance ya fasalin ginin yake da inda ya Kamata ta dosa,.

Carab suka

hada Ido dashi ya aje abinda yakeyi ya Zuba Mata idanu irin kallon Nan na wuce shari'a Yana tsarkake ubangijin da ya yi wannan halittar da take gabansa.

Dan zabura zahrar tayi ganin mutum ba zato ba tsammani.

Aje abinda yakeyi yayi ya taso har lokacin Yan

a kallonta Dan ja baya tayi ganin ya nufo ta.

"Ina Zaki Kuma nida na taso na gaishe da Aunty na".

Ya fada Yana murmushi, saida ya matso ta Dan gane shi, shine jiya ya rungume Mahmud a kofar store din da yayi sayayya.

Sai lokacin ta Dan nutsu amma da tana t

unanin ta Ina zata fece ta Koma saman tasan ko banza tana da mafaka a can.

Dan murmushi tayi itama tana fadin "Yaya sunan bakon da babu sallama? Kawai na wayi gari da ganin mutun ai dole na rasana".

Dariya yayi Yana fadin "Good morning Aunty".

"Morning".

T

a amsa masa a dan darare din nan ba wani sakewa, tana kallonsa.

"I am Faruq Dange".

Ya fada Yana juyawa zuwa inda yake aikinsa.

A hankali ta bude bakinta tace Masa.

"Sunana Fatima Zahra Muhammad Sani, Ina maka.barka da zuwa".

Tana Gama fada ta wuce can ind

a ta hango Kaya akan dining table.

Sakato yayi Yana kallonta Bai taba tunanin tana Jin yaren ba, Kai kawai ya girgiza Yana dan murmushi Yana fadin "wato Ya Mahmud sai a barshi kawai sannin inda ya dosa sai Allah, shi yasa kenan duk yayi d'iban Karan mahauk

aciya da matan daketa rashin hankali a Kansa yayi tafiyarsa ya kyale kowa da nata salon rashin hankalin".

Ledojin ta shiga dubawa taga Dame Dame Nene a ciki, Wanda su Fateeha da mommy ta Bata ta cire ta aje a gefe sai Kuma Wanda ya sawo jiya ta cire na ki

tchen, kofar data gani a tufe taje tadan tura ga mamakinta a bude ta ganta shiga tayi kitchen ne modern sosai babu abinda babu a cikinsa tsayawa tayi tana nazarinsa kafin ta juya ta koma dauko Kayan.

Saida ta aje komai a muhallinsa sannan ta bude freezer d

ata gani ta kwance, nama ne dasu kifa da kayan miya a Nike cikin manyan bikitin roba, kaji biyu ta Ciro da Zuba a roba ta tarasu a famfo saboda kankarar ta saki.

Filawa ta diba ta kwaba da yeast da barking powder ta rufe ta koma ta gyara Naman ta Dora a wu

ta.

Wani ruwan ta Dora daban ta dauko Madara ta bude ta diba Mai yawa ta dama Zuba akan ruwa data Dora ta Dan zame murfin sannan ta ciro hollandia custard ta fasa ta dibi yanda take ganin zata ishesu ta dama ta aje a gefe. Plates da cups da duk abinda tasa

n za'a bukata ta dauko ta wanke ta aje a muhallin Daya dace.

Filawar data kwaba ta dauko taga ya tashi ta ringa murzawa round sai ta Gama ta shafa Mai a frying pan ta rage wuta ta shiga gasawa tanayi tana juyawa.

Biyu ta raba Naman ta dattaka rabi tayi sou

rce Rabin Kuma tayi pepper soup dashi ta dama custard din ta dafa coffee Kuma.

Tun daga sama Mahmud ke jiyo wani irin kanshi girki yayi tunanin ko da wani sabon restaurant a Nan kusa dasu, Saida ya fito yana saukowa yaji kamshin ya cika gidan.

Shigar kanan

un Kaya yayi yayi masifar kyau, yau shigar da yayi ta fito da ainihin ko waye shi Dan ba karya kana kallonsa kasan matashi ne Mai cike da Jin Dadi da wadatar arziki Dan agogon dake hannunsa kadai na millions of naira ne, shigar da ya Jima da daina yinta Na

n gida Nigeria rabon da ya fito haka tun kafin ya shiga rubibi.

Hannu Faruq ya shiga tafawa Yana fadin "perfect match, wallahi kun Dace Ashe haka Auntyn tawa take? Haba shi yasa baka sauraren masu yi maka rawar Kai, ya Mahmud Ashe da abinda ka taka shiya

sa kayi shuru ka kyale kowa, Mai irin wannan matar mezeci da tarkace irinsu Safna, wallahi na Dade Banga ma'auratan da suka tafi da imanina kamar kai da Aunty na ba, Dan Allah ka tsaya min na auri kanwarta pls

🙏

".

Ikon Allah Mahmud ya tsaya yana kallo loka

ci Daya faruq ya gigice masa wato yaga zahrar kenan tunda ya sauko yaji gidan ya hade da kamshin girki yasa itace a kitchen, ko ba komai yasan Allah yayi Mata baiwar iya abinci a Dan zaman da sukayi ya fashimci hakan.

Shi rasa abin cewa ma yayi a Kan kalam

an Faruq, Dan uwansa ne na jini, amma ya gigice da ganin matarsa, tab lallai da matsala Babba.

Bai nuna Masa komai ba sai Dan murmushi da yayi Yana fadin. "Ai mata ta ita kadai ce Bata da Kani ko kanwa, nine wanta nine komai nata Sai dai ka duba ko a Ina n

e Zan shige maka gaba in Sha Allah".

"Dan Allah nidai ka taimaka ko cikin family dinta ne ayi min wanna alfarmar ka shige min gaba".

Kyale shi yayi ya nufi kitchen din lokacin ta Gama hada komai ta juyawa kofar baya tana cire jan bayan kwakwa zatayi amfani

da ita in anjima.

Kamshinsa ya Fara fada Mata ya shigo gurin a hankali ta juyo, Yana tsaye ya harde hannuwansa a kirjinsa ya zubawa bayanta Ido,yanda ta juyo din nan shi Kansa da take halalinasa Saida yaji wani yarrr a jikinsa Dan gani yayi gaba Daya ta c

anza Masa ga wani irin cikowa da kirjinta yayi sosai.

Lumshe Ido yayi Yana tunanin lallai dole addinin musuluci da yayi Hani ga mutum baligi ya shiga gurin macen daba muharramarsa gaskiya. Yana can Yana tunani ya tsinkayi muryarta tana fadin "Ina kwana" b

atare data Kara kallon inda yake ba.

Bai amsa ba ya danyi gyaran murya.

"Meye Kuma Ina kwana? Na fada Miki ki iya tarairaya ta wallahi, kada garin kallon ruwa kwado yayi Miki Qafa, kina da kishiya fa kinsan idan ta fiki iya lafazi da tarairayata can Zan ta

re a gurinta".

Warrr tayi masa da sexy eyes dinta tana Masa wani kallo.

"Yes ko Baki yarda ba? yanzu na Kira Miki ita ku gaisa".

Kai ta girgiza Masa alamar A'a.

"Come on, zo Nan ki fada min bakya son kishiyar?"

Ya bude Mata hannuwansa alamar ta shigo, kaf

ada ta make ta aje kwakwar ta nufi famfon cikin sink ta Fara wanke hannunta.

Cikin takunsa na nazantaka ya shigo ciki directly gurinta ya nufa Yana fadin "Ni gani na shigo sai nazo ki bani hot one tunda ni ba'a son nawa".

Bai jira tace komai ba ya saka ha

nnunsa ya rungumeta ta baya Yana shafa cikinta.

Shiru tayi Masa kamar ruwa ya cinyeta, Jin hannun nasa ya nufi wata jihar yasa tayi saurin rike Masa hannu tasan idan ya karasa akwai damuwa sosai.

"Pls Dan Allah ka Bari kaga da bako a gidan kada ya jiyo mu

fa".

Ta fada tana kokarin kwace kanta.

"Ok saboda shi Zaki hanani na sake kenan? To Bari na sender shi inda yafi wayo".

Dayan hannun ya saka ya ciro wayarsa yayi dialing din number Faruq, Sam batayi zaton kiransa zeyi ba, Saida taji Yana fadar "Faruq kaje

wancen part din ka qarasa aikin gani Nan zuwa".

Bai jira yaji abinda yake kokarin fada ba ya kashe wayar ya Dora a gefen cabinet din kitchen yana fadin "to saiki sake ki bani hakkina tunda sirikinki yabar gurin".

Juyota yayi ya hade bakinsu ya cire rollin

g din, yana shafar gashin da yaji gyara ga qamshin hair spray sai tashi yakeyi ya jima Yana yamutsata kafin ya janye Dan Kansa yana Maida numfashi.

Tsugunnawa yayi ya dauko Mata veil din ya rufa Mata a Kanta Yana fadin "dauko wasu flask din ki zubawa Faruq

nasa ki saka a basket na Kai Masa can idan ya gama ya tattara ya tafi gurin bikin da yazo".

"Me yasa? ba yace min shi qaninka bane".

"Ok. Dan Yana qanena saina zauna dashi gida Daya Yana kalle min Mata ko? Ai ya tafi shine mafita Dan akanki zamu iya bata

wa da kowa to maganin Kar ayi kada a fara, Dan Allah ki ringa saka hijab idan munyi Bak'i ba kowa ne ze iya kawar da Kai a kanki ba Kinga kuwa yanda Faruq ya gigice min na Nemo masa sister dinki, na fada masa babu Amma ya kasa fahimta sai rokona yake na sa

mo Masa mace ko cikin family dinku ne"

Ya fada a Dan zafafe.

Shiru tayi ta nufi abinda ya sakatayi Saida ta Zuba Masa komai ta saka basket din ta aje a gefe ta dauko Wanda ta zubawa Mai gadi ta aje a kusa Dana Faruq din.

Malam Musa ya Kira yace yazo kofar

parlourn su hadu, dauka yayi ya fice daga kitchen din yabar zahra da dogon tunanin akan abinda yace Faruq din yayi.

___

Tunda garin Allah ya waye Ammah ke faman neman number zahra abin yaci tura, a yau dai hakurinta ya Gaza Dan tun Daren jiya da zilai

ta Kira Ammah tana fada Mata yanda fasalin gidan da suke yake da kuma kudin da tace an Basu dubu ashirin da safe da yamma ma an kawo musu wasu kudin dubu dari-dari ita da iya Rahane ga turamen atamfofi guda hudu hudu da lace bibiyu, Kuma ta fada Mata tunda

su zahrar suka fice Bata Kara ganin giccinsu ba ga wayar ta ma a rufe.

Akalar Kiran Ammah ta canza ta shiga lalubo Number Abdul Hakeem.

Ringing din farko ya dauka yana Fadi "barka da Asuba Ammah, an tashi lfy?.

"Alhamdulillahi, idan ka tashi ka shigo In

a son ganinka" ta fada cikin damuwa.

"To in Sha Allah, gani nan shigowa"..

Ta kashe wayar, ta ajiye a gefe tana fadin "kazo ka nemomin wannan yaron ya fada min waye shi Ina Kuma ya Kai min 'yata ko waya ya Hana muyi da ita inji meye dalilni Daya hana ta a

mfani da wayar, tunda Naga Abban ba wani Abu zeyi ba, ga wannan kinibabbiyar matar tasa da koma sai taji Masa kwakwaf".

Tsaki tayi tana Jin duk Zuciyar ta ba dadi ko kadan, tana Nan zaune Abdul Hakeem din ya shigo sanye da jallabiya coffee colour a jikinsa

ya gaishe da Ammah ya nemi guri ya zauna Yana fadin "lafiya kuwa Ammah?".

"Da sauki, Nemo min mijin Zahra a wayarka naji dalilinsa na yanke ma'amalarta Dani tunda suka bar garin Nan ban Kara Jin duriyarta ba".

Shiru Abdul Hakeem din yayi kafin yace "ba h

aka za'ayi ba, Zan kirasa na saka handsfree sai kiji yanda zamuyi dashi idan munji da alamun rashin gaskiya sai a San abunda ya Kamata tunda ba'asan dalilinsa. Ba na hanata amfani da wayar, ke uwace kiyi hakuri babu abinda ze Samar Miki 'ya da izinin Alla

h, in Sha Allah sai kinyi alfahari da Auren Nan Muhmud mutumin kirki ne bashi da wata alama ta rashin gaskiya, kinsan ya fada min shi Dan Sokoto ne,.har unguwar su da iyayensa duk ya fada min lokacin da zeyi tafiyar nan, yace saboda halin Rai Koda be dawo

ba na nemi Sameer ko sabon mai gadin Daya kawo a can gidansu na hayin banki, ko Binya na gidan Baba malam duk mutanensa ne. Bari na kirasa Dan hankalinki ya kwanta".

Ya Fara dialing din number sa.

Sun Gama break fast din kenan wayarsa ta dauki slow music d

aga kitchen inda ya barota tsam ya tashi ya nufi kitchen din kafin yaje Kiran ya yanke, sunan Abdul Hakeem ya gani, kafin ya Kira wani Kiran ya shigo.

Saida ya zauna daf da ita ya daga kiran.

"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu babban yay

an mu, barka da Asuba".

Ya fada Yana murmushi.

"Wa'alaika Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu barkamu kadai, ya iyalin?" Dariya abin ya bashi "Gasu Nan muna ta basu hakuri kasan Mata sai a hankali".

Ya fada Yana Dan Jan tsunin hancinta, Batasan dawa

yake wayar ba.

"Wai meya samu wayarta ne Bata shiga kwata-kwata duk hankakii Ammah fa ya tashi, Jin kwana biyu shiru ba suyi magana ba idan tana kusa ka Bata suyi magana Dan hankalinta ya kwanta".

"Ya salam Dan Allah ka bawa Amman mu hakuri laifi tayi min

na karbe wayar, amma Zan Bata ita yau in Sha Allah, ai Zan shigo garin gobe ko jibi".

Tunda ta fashinci da Ya Abdul Hakeem yake wayar taji hankalinta gaba Daya yayi gida Jin cewa zeje Azaren bada ita ba sai taji duk ta shiga tashin hankali da gaske gida t

ake son komawa, ta dauka da Wasa yake Mata lokacin da yace ze dauko Mata Rukayya idan zasuje Azare.

Wayar ya Mika Mata ya Mike ya fice daga parlourn gaba Daya.

Sallama tayiwa ya Abdul Hakeem din sannan ta gaishe shi.

Sannan ya dora da fadin "ga Ammah nason

magana dake".

"Dan Allah Ya Abdul Hakeem ka Bata hakuri wallahi saboda bansan abinda Zan fada Mata ba na kashe wayar Allah ba yaji nayi ba, kaina ne yayi zafi gurin fa buduwarsa ta turoni Asibiti ita Kuma ta shiga wulakantani, Dan Allah ka rokarmin shi ya

maidoni gida wallahi na gaji Ni tsoro nakeji bakaga irin gidajen da yake kawoni ba kamar baza'a mutu ba fa". Ta ida fada tana kuka.

Duk abunda ke wakana Ammah na zaune tayi tagumi tana Jin wani sanyi da tausayinta a Zuciyar ta, amman koba komai ta samu nu

tsuwa taji lafiyar ta sauran Kuma tasan shegantake ce kawai.

Wayar Abdul Hakeem ya mikawa Ammah ya tashi ya fice shima gara ya Basu guri su tattauna.

"Wai kukan Kuma na menene haka? ai kowa ya gyara ya sani kowa ya Bata ya sani, kiji tsoron Allah ki rike s

irrin mijinki kinsan baqi kinsan fari keba karamar yarinya bace,saboda me Zaki tafi wani guri har ki nemi kwana bada izinin mijinki ba, haka kawai kin tashi hankakin jama'ar da suka daukeki da mutumci kin kyauta kenan? To wallahi kada na sake Jin wani Abu

makamancin haka daga gareki ki nutsu ki rike aurenki kada na Kara Jin kin ambaci ya dawo dake nan, kinsan dai ba'a nan zaku dawwama ba ina cewa ya fada Miki garinsu wata Rana dole ze koma gida sai kice bazaki bishi ba? Akul na karajin magana makamanciyar w

annan daga bakinki".

Tunda Ammah ta Fara magana Zahra ke shashsheka a hankali.

"Kiyi hakuri wallahi na daina bazan Kara ba, wallahi bansan laifin da nayi Masa ba ya dauke min wayar da passport dina har da kudi da ATM duka".

Salati Ammah ta dauka tana fadin

"Ni Asma'u yanzu harda passport dinki Kika dauka dole ya kwashe wato guduwa kuka shirya zakiyi kibar kasar ko?"

Cikin gigita Zahra ta fashe Mata da kuka sosai tana Fadi "wallahi ba guduwa zanyi ba Daman suna cikin jakar fa".

Ji tayi an zare wayar daga han

nunta Batasan lokacin daya taso ta shige jikinsa ba tana fadin "Dan Allah ka fadawa Ammah abinda take zargina dashi ba haka bane".

Ai Jin wannan furucin na Zahra yasa Ammah yanke Kiran cikin gaggawa.

Jin alamun yanke Kiran yasa shi Kara sakata a jikinsa b

aya son kukanta ko misqalazarratin.

AUREN HUCE HAUSHI.

(Maman Fateemah.

Page 51

🖋



___Dan murmushi Ammah tayi,koba ba komai ta Sami peace of mind, yanzu Bata da wata fargaba,zata Kira zilai ta fada Mata ta kwantar da hankalinta babu wata damuwa

Zahra na Nan lafiya kalau ita dai tayi zamanta sai lokacin Daya bukaci su dawo sai su taho din kawai.

Tashi tayi da wayar a hannunta ta wuce Ciki tana Jin wata sabuwar nutsuwa tana shigar ta. Addu'ar da takewa yarinyar Allah ya Zama gatanta a dukkan al'a

mura.

***

Sun Jima a yanda suke ita Bata janye ba shi Kuma be saketa ba, ajiyar zuciya kawai take saki a hankali.

"Wai me kika yiwa Ammah ne haka da zafi har kike neman bayi Miki shaidar zur".

Tsuntse idanu tayi sai wasu hawayen. "Ya salam! Pls bana son

kuka sam, ki adana abinki Mana Yana da lokaci, ai kin gane?".

Shiru tayi masa, me zata fad'a Masa tace Ammah tace Mata niyyar guduwa take yi.

"Pls ki fada min Mana ko saina Kira na tambayeta laifin da kikayi Mata sannan zanji Kan maganar?"

Da sauri ta shi

ga fadar "wai fa Dan naje gidan su bestie shine take min fadan me yasa nayi yaji, shine na fada Mata ba haka bane".

Dago fuskarta yayi yaga yanda idanunta suka sauya kala daga farare zuwa ja.

"Shi kenan ai komai ya wuce tunda Nina janyo akayi yajin tunda n

a turaki gurin Haseena, nayi zaton zuwa yanzu ta aje maganar soyayya a tsakanin mu sai zumunci kawai, kiyi Hakuri nayi Mata last warning akan shirmen da tayi".

"Ni dai dan Allah ka maidani gida na gaji da garin kwata kwata".

Ta fada tana turo baki.

Baice M

ata komai ba ya nufi one seater ya zauna ya dorata a cinyarsa suna facing din juna.

"Ki cire ranki da komawa Azare Saida ganin gida daga Nan sai Sokoto birnin shehu, kina tunanin Zaki koma can ne? Ai shi yasa nace a hadoki da house maid wadda take da Amana

tunda a yanda Naga takunta zatayi amanar, shine dalilin da ze kaini can na fadawa Abban mu da malam Zan koma gida tunda the game is over, na samu a binda nake nema ai saina koma ayi wadda za'ayi ko?".

Ya fada yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login