Showing 30001 words to 33000 words out of 295116 words
/>
a sa'a"
A kofa suka hadu da Sulaiman ya biyo ta tana fadin "Na rantsa da Allah zamu tafi mu barki ba Dan Abba ya fito ba da wallahi sai dai ki fito kiga bama gidan".
Kafin ya saki labulen ya juya Zahra ta Kai kofar da zata kaika compound din gidan.
Masha
Allah anyi jarabawa an Gama sai jiran sakamako.
A haka sukaci Baga da zuwa makaranta har suka Zama common enterence a matakin jaha.
Lokacin da suka dawo zaman gida lokacin ne Alhaji Jafar da kansa ya yiwa Zahra passport da visa Saida ya Gama komai sannan y
a fadawa su Ammah da Mama. Godiya Ammah ta shiga jerawa Mai gidan nasu,yayin da Mama tayi shiru Kamar bazatayi magana ba sai Kuma tace "yanzu Yallabai da kanka zaka rakata ai da Koda Hasana ko Hassan ka hadasu zasu kaita ko Kuma a fadawa cen kakanninta su
turo a tafi da ita ai cacar kudin Kamar yayi yawa".
Daga Ammah har Alhaji Jafar din kallon Mamar suke ita dai Ammah shiru tayi yayin da Alhajin yace.
Saboda ban San darajar 'ya'ya ba zan hada Yara a tafiyar uwa duniya daga Nan har Jordan na kwanta a gida
hanakli kwance ko?"
Kai ta gaigice tare da fadin "gani makudan kudi za'a kashe".
Wani kallo yayi Mata "kada ki kawo b'araka Rabi'a duk yaran dake gabana daya na daukesu yada zan yiwa abinda na Haifa haka zan yiwa marainiyar Allah. Da Kuma kike maganar cac
ar kudi idan zan jera shekara Ina Kai zahra Jordan kullum ba abinda ze girgaiza a cikin abinda na mallaka".
Ku tashi kuje.
Lokacin da zasu tafi anyi Mata tsara sosai Dan Nanna ma kilishi tasa aka yi Mai yawa na tsaraba.
Har kano su Ammah da yara sukayi mus
u rakiya.
Lokacin da sukaje Jordan din ba karamar murna kakanninta zukayi ba Dan Babu zato suka gansu, sun Kuma Kara yabawa da cika Alkawarin Alhaji Jafar Dan da kansa yayi musu Alkawarin ze kawo musu Zahra Dan ko a waya Bai fada musu zuwansu ba,sai addres
s dai daya taba tambaya can wani lokaci.
A ranar Zahra taga zallar soyayya a gurin dangin Najwa Dan gidan cika yayi da 'yan uwa aka dasa sabon kukan rashin Najwar da kyar Abbie da Abbanta suka dinga Basu hakuri Dan ma Alhaji Jafar ba larabcin yakeji sosai
ba saidai Wanda suke Jin turanci suka ringa magana dasu.
Lokacin da Alhaji Jafar din ze tafi masukin daya Kama a hotel Abbie hanawa yayi duk yanda yaso zillewa kin yarda yayi dole ya amince aka sauke shi a wani part dake kusa da nasa Ummee din, Dan ba kary
a dukiya dai Kam akwaita Dan shi kanshi Alhajin yayi mamakin yanda ya riskesu Bai taba kawo haka suke ba lallai yasan hadin Allah ne kawai da suka bawa Muhammad sani auren 'yarsu Dan tazarar Mai nisa ce a tsakanin su.
Kwanan Alhaji Jafar bakwai ya wuce Uma
ra yayin da Ummee tayi Masa Alkawarin zasu hadu a Saudiyyar tunda zata kawo Zahrar Nan gurin iyayenta da 'yan uwa su ganta a cikin garin Madinatul Munawwara.
Satinsa daya da zuwa Suma su Zahrar sukazo Saudiyyar ita da Ummeen da Aunty Nawwara.
A Nan ma Saud
iyyar Zahra taga gata iya gata Dan kowa Nan Nan yake da ita, Dan kanwar Ummee Hanifa sosai ta kafe sai dai a bar Mata Zahra ta tafi da ita Istanbul inda take aure Wai Bata yarda da zaman Nigeria ba.
Ankai ruwa Rana da ita kafin ta hakura Dan da gaske Alhaj
i Jafar ya bude Mata aiki Dan cewa yayi idan irin haka za'a ringa yi bazai Kara bawo musu ita ba saidai duk Mai son ganinta taje ya ganota Kamar yanda Ummee keyi, hakuri aka ringa bashi.
Saida aka Kai Zahra makka suyi kayi umara sannan suka fara Shirin bar
o kasar.l Sayyaya dai Zahra ta shata Dan wasu kayan sai a awon cargo akayo musu su.
Sarkar gwal da warwaro zobe kuwa kirar Saudiyya da Dubai zuwa kirar Bahrain sun Kai kala goma duk dai dai size din ta sai na Ammah biyu na Hasana ma biyu shi kanshi Alhaji
n anyone mass goma Sha Tara ta Arziki.
Ranar da zasu dawo Zahra Tasha kuka haka kakarta Ummee,har jidda sukayo musu rakiya Basu suka tafi ba sai da jirgin su Zahra ya tashi a sararin subahanahu wata'ala.
Saukar safe sukayi anan suka samu Bala direban Alhaj
i Dan Bai fadawa kowa sun taho ba sai Balan kawai, sau da yawa idan ya fada gashi Nan a hanya hankalin Nanna baya kwanciya har sai ya iso.
Lokacin da suka shigo harabar gidan suna tsayawa Zahra to garzaya cikin gida tana fadin "Ammah!!! mun dawo".
Da gudu
Hameeda ta fito daga part dinsu, rungume juna sukayi suna ta tsallen murna Sai jikin zahra Hameedar ke shafawa gani take kamar canza Mata Zahrar akayi.
Da sauri Ammah ta fito tana "fadin wa nake gani ne haka Kamar bakin saudiyya zuwa ba notice?"
Alhajin ne
ya Bata amsa.
"Surprised din ki mukayi ko Zahra na?.
Kai ta gyada masa.
Kayansu ne su Bala da Mai gadi suka Fara shigowa dasu kafin Alhajin ya nufi part dinsa na cikin gidan yayin da Ammah ta rufa Masa baya.
Har yayi wanka ya shirya Mama Bata shigo ba, h
ar ya tambayar Ammah yayi Ina Rabi'a ? Tace Masa tana ciki watakila ko barci take.
Kusan kwana su Zahra sukayi tana baiwa Hameeda labarin abinda ta gani da inda sukaje a Jordan da saudiyya, wurin karfe biyu Ammah ta tashi zatayi nafila ta jiyo su suna Hira
a dayan bed room dinta lokacin wuri biyu da rabi na dare, leko tace su kwanta basu san dare yayi sosai ba.
Washe gari an baje tsarabar Zahra an baiwa kowa dai dai gwargwado.
Amman tsarabar Hameeda daban take Dan har sarka Saida ta baiwa Hameedar.
Basifi
sati biyu da dawowa ba jarabarsu ta fito ta Federal inda Zahra ta samu F.G.G.C KAZAURE yayin da Sulaiman ya samu F.G.C DAURA, Hameeda F.G.C AZARE. Salma ce kawai bata samu ba a cikinsu.
Sunyi murna Kuma sunyi bakin cikin rashin samun makaranta daya duk an
watsa su Abban Kuma da ya Hassan sunce kowa ya tafi inda ya samu, ita Hameeda Bata da damuwa tana gida, su Kuma duka 'ya'yan Ammah duk sun fita waje danma hanyarsu daya sai an aje Zahra a karasa da Sulaiman.
Ranar da zasu tafi sun Sha kuka haka suka dauk
o hanya malam Bala da Ya Hassan ne suka kaisu.
Lokacin da aka Kai Zahra an tashi daga aji, wasu Yara House master dinsu ya kira da wata prefect yasa su Kai Zahra room din 'yan j.s one.
A cikin yaran da suka Taya Zahra daukar kayane wata yarinya tace Mata "
sister kizo ki zauna a kwana ta tunda ni daya ce saman gadona ba kowa".
Kai kawai zahra ta gyada Mata tana ta sauke ajiyar zuciya.
Ita ta taimkawa Zahra ta shirya komai a locker dinta, Saida ta Bari zahra ta HUCE daga kukan da tsaha sannan tace Mata "ni su
nana Sajida Musa ni 'yar kano ce unguwar Gwammaja kefa ya sunanki?".
Nan Zahra ta fada Mata komai nata tun daga Nan suke tare har suka Zama aminai komai nasu ya Zama daya banbanci su kawai Sajida na A Zahra na C.
Haka sukaci gaba da rayuwa a makarantar gas
u Kuma Yara masu kwazo barin zahra ga kyau ga ilimi Nan da Nan tayi suna a makarantar kafin hutu tayi popular sosai a makarantar, idan kace 'yar larabawa kowa ya santa ba Kuma Dan Babu irin jiinsin nata ba A'a farin jini ne daga Allah.
Lokacin da akayi hut
u Zahra ba karamar murna tayi ba Kuma cikin ikon Allah da wuri malam Bala yazo lokacin har ya dauko Sulaiman.
Bayan Azahar kadan suka shiga Azare sunyi murna sosai da ganin mutanen gida Dan Sulaiman har da kuka, Nan su Hameeda suka saka gaba suna tsokana.
Haka suka cigaba da karatunsu cikin amincin Allah, lokacin da sukazo hutun third term ne akayi auren Aunty Hasana aka kaita Jos, Ya Hassan Kuma Daman Yana karatunsa a Rasha.
Kowa inda yake yacigaba da karatunsa Salmace Allah ya taikata ta samu shiga FGC A
ZAREN itama a ss1.
A haka aka dunga juyawa har suka Gama secondary School dinsu suka dawo gida.
Dawowarsu ba dadewa Allah ya yiwa Nanna rasuwa rashin daya taba Abbansu sosai.
Dan ya Dade Yana fama da damuwa tunda a rayuwa da ita ya tashi baisan dadin uba n
amiji ba itace komai nasa.
Ganin abin nasa Yana neman yayi yawa yasa Abokinsa bakon malamin daya sauka Nan daura gidan Nanna da almajiransa dududu Bai zaifi sa'an Alhajin ba malam Bubar ya dukufa yi Masa addu'a tare da saka Yara kanana suna Masa addu'a, c
ikin ikon Allah sai komai ya daidaita.
Ranar wata laraba zahra ta shirya zata raka Hameeda duba Qawarta meenal gidan Dan majalissarsu Mai wakiltar su majalissar Jaha, wani material ta saka Mai ruwan sararin samaniya yayi matukar karbar jikinta haka dinki
ma ya Dace da material din, simple makeup tayi ta saka turarenta Amber oud new edition na kamfanin Al haramaini.
Tunda ta fito Mama ke Mata wani irin kallo Wanda har saida ta rinqa Jin ta takura kafin Hameedar ta fito.
A kasa suka taka suna Hira har sulaje
gidan,sun Dan jima suna Hira da marara lafiyar kasancewar breast lump ne aka cire Mata ba wani serious case bane.
Lokacin da zasu tafi suka Kara komawa gurin mamanta sukayi Mata sallama suna zaune ne da a falonta kafin meenal din tayi Mata magana ta fito.
Wani handsome guy ne ya shigo falon da sallama ya Dan jefa car key dinsa sama, kana ganinsa kasan hutu ya Kama jikinsa.
Ciki ya shigo lokacin da Suke amsa masa sallamarsa kujera two seaters ya zauna a Kai wadda ke facing dinsu Hameedar.
Gaishe shi sukayi
su Duke ya amsa Yana cewa "Hameeda daman kina Nan na Dade ban ganki ba gaskiya Ina ga tun kafin na tafi Colombia fa".
Dan rausayar da Kai tayi tana fadar "wallahi Kam Ya Sahal an jima Kam kune dai bakwa ganuwa Kuna uwa duniya kunyi shiru Kum barmu da zafin
Kasarmu".
Ta fada tana dariya.
Dai dai lokacin mommyn su meenal din ta fito kallon Sahal tayi tana fadar Kai Kuma haka mukayi da Kai?"
Kaisa ya Dan Sosa da key din hannunsa Yana fadi "Iam so sorry Mom kada ki damu yanzu zanje na kawo Miki in Sha Allah."
Ya fada Yana mikewa da nufin tafiya Meenal tayi tsagal tana fadin "Dan Allah Ya Sahal ka tafi dasu tunda cikin garin kayi.
Suka yiwa mommy sallama da godiya suka fito da leda Mai Dan girma a hannun Meenal wadda mommyn ta Basu.
Har kofar gida ya kawosu su
na tsayawa ya kalli Hameeda Yana fadar "Dan Allah ki bani aron sister din take Mana Kona ten minutes ne Mana".
Dan murmushi tayi tana fadar.
"Ka Fara yiwa Abban mu magana dai haka Naga anayi"
Ita dai Zahra ciki ta wuce Dan Kamar a kan.kaya take duk ya taku
ra Mata da wani irin kallo har a cikin mota ma saita mirror yayi sitinta tunda Hameeda ce ta zauna a seat din gaba tana Masa Hira Amman gaba daya hankalinsa yana kan Zahra.
Ita dai zahra Bata San yanda suka Kare ba taga dai Lokacin da Hameedar ta shigo ta
wuce dakin su.
Bayan kwana biyu da zuwa gidansu Meenal da yamma su zahra sun tafi islamiyya ne baki sukazo gurin Alhaji Jafar, ya sansu farin sani daya kanin Dan majalissar su ne dayan Kuma kanin Babansu.
Yayi mamakin ganinsu Saida suka gaisa ne suka biji
ro da abinda ya kawo su na yiwa yaron gurin Dan uwansu Sahal kidiba yaga yarinyar gurinsa Yana so. Shine mahaifansa ya turosu ya gabatar da maganar Yana neman izininsa na Fara zuwa gurinta Shira.
Alhajin yaji Dadi sosai na yanda suka zo suka memi izininsa
duk da Daman sharadinsa kenan, ya Kuma nemi Jin wacece daga cikin yaran suka gada Masa zahra ce, nan ya amince musu da addu'ar Allah ya hada kawunan su.
Tun daga lokacin Sahal ya Fara zuwa gurin Zahra cikin ikon Allah tayi na'am dashi Basu Dade sosai ba su
kayi wata irin shakuwa ta ban mamaki duk Wanda ya kwana ya tashi a unguwar yasan irin soyayyar da sahal yakewa zahra kusan Kullum da yamma Yana nan makale da ita, a haka har manya suka shiga maganar aka tsaida lokaci wata shida inda zasu tafi Colombia inda
yake hada masters dinsa ita kuma zata Fara nata degree din.
Anyi lefe na garari Wanda ya dauki Baki fiye da tunanin Mai tunani, an kashe kudi Kamar ba'a San zafinsu ba.
Lokacin da bikin ya rage baifi saura wata biyu ba sai lamarin ya Fara canzawa kwata -k
wata Sahal ya rage zuwa gurin Zahra haka ma sai a kwana a wuni Bai kirata ba, duk wani zazzari da yake na bikin su events din da yake ta faman damun zahra da maganar duk ya daina Kai tafi-tafi sai ayi kwana uku hudu har sati Bai kirata ba, da farkon abin
tana kiransa taji ko lafiya a yanayin yanda yake amsa Mata wayar saita hakura da Kiran nasa, tun Ammah na zuba ido har ta samu Zahra a wani dare ta tsareta da tambayar ko wani Abu ya hadata da Sahal ne? Ta Bata tabbacin ba abinda ya hadasu sai dai ta fada
Mata yanda suka ringa yi dashi a kwanaki idan ta Kira shi.
Addu'a Ammah ta Bata tace ta ringa yi itama zataci gaba da yi, Mata sannan ta umarceta da kada ta Kara kiransa a wayar ta zuba ido kawai.
Duk abinda Ammah take na shirye-shiryen Baki Bata fasa ba,
tayi waya mutanan Jordan ma sunce suna Nan tafe Amma a daure a turo Zahra Kamar saura wata data bikin.
Ba'afi sati daya da waya da kakanninta na uwa ba sakon kayan dakinta ya sauka Nigeria daga Istanbul kayan da suka gigita Mama Dan ba kayan Wasa bane se
t din gado har hudu kujeru set uku bayan electronics kuwa wasu har ba'a San amfaninsu ba sai dai idan an duba manual din.
Alhaji Jafar yayi fada Kamar ya Ari Baki lokacin daya Kira Abbie akan danme zasuyi Masa haka toshi meye amfaninsa da bazasu Bari yayi
Mata kayan dakin ba.
Hakuri Abbien ya shiga bashi akan su basuyi Dan su Bata Masa raiba, sunga abinda ya kamata suyiwa diyar Najwa kenan.
Ammah da Mama Alhaji Jafar ya Kira ya fada musu tunda an Riga an yiwa zahra kayan dakin da duk abinda ya kamata to ga
fifty million Nan ya baiwa Zahra idan komai ya nutsa saita Fara business na abinda take son sayarwa sannan ya Bata shanu biyar.
Kuka Ammah ta saka saboda Dadi ta rasa bakin da zatayi Masa godiya, yanda take dawainya da wannan marainiyar Allah Bai taba gaji
yawa ba.
Mama ce ta Ari bakinta tana ta yiwa Abban godiya da saka Albarka sai faman dariya tace bakinta yaki rufuwa, tun Ammah na ganin dariyar farin ciki ce har ta Fara wani tunani na daban, Nan da Nan ta Kori shaidan akan abinda zuciya ke sawwala Mata.
Lokaci na Kara tafiya daukewar ma'amala na Kara yawaita a tsakanin Sahal da zahra, yanzu ta Kai kwata-kwata sun daina waya dashi, ana saura kwana talatin da hudu a Fara biki Wanda yayi daidai da saura kwana uku zahra da Hameeda da Abdul Hakeem su tafi Ista
nbul. Dan direct gurin kanwar Ummeen Hanifa zasu tafi daga baya su Ummeen sun samesu a can, idan an Gama komai su rankato Nigeria Dan da gaske Ummee ta shiryawa bikin sosai.
Washe gari, tunda gari ya waje Mama ke Kai kawo tsakar gida duk da ba aikinta ba
ne ba Kuma halayyarta bane hakan. Yayin da a bangaren Ammah ta rasa me yake Mata Dadi duk kasala ta baibayeta jinta take Kamar ma zazzabi na neman rufata...
💋
❤
💋
❤
️
✨
AUREN HUCE HAUSHIN
✨
️
💋
❤
️
💋
❤
️
STORY
&
WRITTEN
BY
MAMAN FATIMAH.
🔷
✨
PAGE ELEVEN
✨
🔷
(11)
________Misalin Sha biyu da rabi na Rana kawar Mama kuma Aminiyar Asabe tazo gidan macece wayayya Mai kisisina Bata fiye zuwa gidan sosai ba sai lokaci lokaci, ta Dan jima a dakin Ammah suna hira har
tana tsokanar zahra da Amaryar gobe ana dariya.
Part din Mama ta shiga suka kule a master bedroom dinta.
Batafi awa daya da zuwa ba, wasu Mata suka shigo gidan lokacin Ammah tana bangaren Abba.
Zilai Mai aik cei ta leko tana fadin "uwar dakina a
nyi baki kuwa ko Ammah zaki yiwa magana Naga bakin nata be"
Mayafi karami ta Dora a saman gashinta da tayi parking dinsa har wajen kugunta Yana reto Baki sidik dashi jikin Nan nata Kamar ka taba jini fito.
Lekowa tayi tana musu sannu da zuwa tare da gais
he su tana fadar "ku shigo daga ciki Bari na Kira Ammar".
Ta fada tana zura silifar a kafarta.
Daya daga cikin su ukun ne ta tabe Baki ta kauda Kai tana fadar "kirawo ta tazo ba sai mun shiga ba tunda ba Zama mukazo ba"
Ita dai Zahra gaba tayi yayin da s
u Zilai masu aiki suka zuba musu idanu suna kallon kallo ya junansu Dan daga Jin lafazinsu