Showing 60001 words to 63000 words out of 295116 words
ya rufe laptop din ya Miki, gu
rin da take zaune ya nufo yana zuwa ya Dan tsuguna kusa da ita Yana fadin "taso muje kada nabar 'yar amanata da yunwa na amsa query a gurin su bestie ko?"
Ya fada Yana murmushi.
Hannunta ya kama ya dagota tsaye suna shakar numfashin juna Amma ita kanta ya
na duban kasa, dayan Hannun yasa ya dago fuskarta as usual yanda ya saba.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali Amma bata rufe idon ba kamar yanda ya hanata a jiya Bata manta ba amma ta kauda Kai gefe dan da gaske Bata iya had a ido dashi.
Dan kwanto da ita ya
yi jikinsa Yana juyo da fuskarta yana fadin.
"Wallahi kada ki rusa min budget dina kisa na kwashe kunyar nan daga idanunki tun banyi niyya ba matukar zakici gaba da irin wannan dabi'ar".
Das das girjinta ya kara bugawa akan wadda yake, tana fadin "oh ni Z
ahra tawa ta sameni shi Wai wane iri ne haka? sai yayi ta sakin magana ko kunya babu".
Saida ya matsa mata taci abincin kirki bayan sun Gama ne suka dawo parlor suka zauna Sam Babu sabo ko kalilan a tsakaninsu kallo ya kunna a Nile sat ya kamo super suppor
t suna kwallo live.
Ganin ita ba wani gane kan ball din take ba yasa ta Mike zata koma daki ta kira Sajida taji ya maganar tafiyar Dan tun jiya da Abba yace a jiya zata tafi gidanta sajidar tace itama sai gida ta.
Takunta biyu taji ya janyo ta ta fada jiki
nsa ba Shiri ta zaro ido waje hura kata iskar bakinsa yayi a fuskarta dalilin yasa ta rufe idonta kenan a hankali yace "Ina Zaki ki barni a zaune alhalin saboda na tayaki Zama yasa naki fita ko ina".
✨✨
✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
✨✨
✨✨
💎
PAGE TWENTY
💎
(20)
_______"ya Salam". Zahra ta fada a hankali jin yanda yake hura mata iskar bakinsa a fuskarta, yasa hannuwansa duka biyun ya tallabo fuskarta yana kallon face din very cute da ita, shifa baya gajiya da kallonta komai nata burgeshi y
ake yi Dan bakinta ya kalli 'yan kyawawan lips din ta pink, gdy yake yiwa buwayi Gagara misali daya mallaka masa ita a lokacin da bai taba zato ba, tunda ya kafeta da ido Bata yarda sun hada ido ba, ba Kuma tayi gigin dogowa ba.
Qaran da door bell din tayi
shiya kawo karshen 'yar tutsiyen da yayi Mata wani soft kiss ya yiwa gefen wuyanta Wanda har Sai da ta zabura tana fadin "wayyo Allah!".
A shagwabe ta janye jikinta daga rikon da yayi mata, shi Kuma ya tashi ya nufi kofa, Bata jira taga waye ba tayi wuf t
a nufi ciki jikinta kamar mazari.
Tana shiga ta zube a gado tana fitar da numfashi da sauri da sauri kamar wadda tasha gudu, jin alamun bude kofar yasa tayi saurin duba gurin Sajida ta gani tsaye ta tsura Mata ido tana Mata wani kallo cikin mutukar tsantsa
r farin ciki zahrar ta taso tana fadin "haba bestie kin wani tsareni da ido kina min kallon qurillah irin wannan ko Kinga wani abu a jikina ne?".
Ta qarasa fada tana karasowa kusa da ita 'yar madaidaiciyar ledar hannunta tana fadar "Wai meye Kika wani yi s
hiru kina kallona ne Dan Allah talk to me Mana pls".
Biyo bayan zahrar tayi har gefen gadon kafin ta samu kuzarin fadin "Bestie Kinganki kuwa just one day Amma har kin Fara canzawa, Fadi min meye sirrin gaskiya, na tafi jiya da zulumin ki a Raina yau kuma
nazo na sameki haka kin wani Kara Zama fresh dake".
"Bestie tsakanin mu harda 'yar zolaya zakice Wai na Kara zama fresh?"
Zama tayi gefen zahrar tana fadin "wallahi I am serious kin canza a idona gaskiya Kinga ai dole na fada ko?".
"To shikenan kin fada b
azan hanaki ba, wai da gasken yau Zaki wuce?"
Kai ta gyada Mana kafin tace "In Sha Allah meya rage kuma ai gara naje na fuskanci karatun ko tunda na samu nutsuwa kin shigo gidan ki. Alhamdulillahi, ga sauran abubuwanki na wajen Baffan rimi kici baga da am
fani dasu dazuma munyi waya da safe yace na bawa Ammah abinda ya Aiko dai ya Kara jardada Mata na a fada Miki kada wani ya kawo Miki abu kici Kuma yace a tura a karbo Miki sako Nan da sati daya".
Dan langabar da Kai tayi tana Kara ganin kimar Sajida ta dau
ki matsalar nan tata bada wasa ba.
Godiya sosai Zahra ta yiwa Sajida akan abinda suke mata, sun Dade sajidar na yiwa Zahra nasiha akan ta rike aurenta da kyau ita bataga wani abun ashsha ba gurin Mahmud idan. Nan da Nan idon Zahra ya kawo ruwa ta shiga sha
rewa da hannunta tana fadar "wallahi bestie na rasa dalilin da yasa nake jin wani abu a tare dashi tun ranar Dana Fara ganin shi naji abun ko kallonsa fa nayi sai naji gabana Yana faduwa heart beat Dina Yana karuwa, kinsan ma inda matsalar take?"
Kai saji
dar ta girgaiza tana fadar "sai kin fada".
"Kinsan haduwar mu ta farko rungumeni fa yayi a cikin jirjinsa tsam kamar.wata baby amman Kamar an dinke min Baki na kasa ko fada Masa magana ne saima wani azababben kwarjini da yayi min harda fadar na ringa ku
la kada nayi musu asara'.
Ai Sajida Bata San lokacin da wata dariya ta kubce Mata ba tana fadar.
"Babbar magana kice da wata tsumammiya a tsakani ku tun tuni har kika dauki alhakina gurin hanani kwanciyar hankali tun jiya Allah barci ma ban samu na kirki
ba Ina zulumin abinda kaje yazo, Dan ba kowa bane za'a aje masa mace kamar ke ya iya kauda Kai gaskiya"
Wani duba zahrar tayi Mata tana fadin "ban Gane ba me kike nufi da maganganunki?.
Wata dariyar tayi tana fadin "A'a ba mefa nake nufi kawai dai......
"
Sai tayi shiru.
Wani zancen ta dauko Tana fadin "Zahra ki tsaya ki nutsu a gidan aurenki ki gyale kowa duk wanda ze raina Miki miji kada ki amince ko waye kuwa Koda ni da nake Miki wannan maganar, Kuma game da Hameeda ki kula sosai Dan a jiya ta nuna Mik
i jiya ba yau bace, jini kuma yafi ruwa kauri, Koda ta dawo tana neman Kara shiga jikin ki da wata manufar tazo, Dan Allah kiba marada kunya duk yanda ake son ganin lapses dinki kada ki bada damar hakan".
In Sha Allah zan kula nagode Bestie Allah yabar zum
unci. Zahra ta fada
"Ameen" sajidar na ta fada, suna cikin hira akayi knocking din kofar ba'a bude ba Zahra ce Mike tana fadin "ina zuwa, tana kokarin yafa gyale ta rufe gashinta Sajida ta warce ta aje gefen ta tana fadin "haba ke kamar matar liman a da
ki na da Bata ja ba tayi gaba saboda an Kara buga kofar, budewa tayi Mahmud ta gani Yana tsaye ya canza kaya ya saka Riga da wando na wani yadi light brown dinkin buda yana baza kanshi sa na ibada.
Matsawa tayi daga jikin kyauren ganin alamar shigowa zeyi
Amma fa Saida yadan shafi fuskarta kadan sannan ya ida ahigewa ciki, tsaye tayi tana binsa da ido tana ayyana "Wai meye ne yake faman shafa mata fuska har a gaban mutane ko kunya bayaji tasan wlh sarai Sajida ta gani sai dai ta basar kawai gashi ta wani ri
ke mata gyale ta wani barta tsurarta".
Direct gurin mirror ya nufa ya zauna a Kan stool, Yana fadin "Bestien mu zuwa nayi muyi sallama naji Abdul Hakeem yana maganar Zaki wuce yau ko".
Ya fada Yana murmushi, itama murmushin tayi masa tana fadar.
",In Sh
a Allah yau sai kano tunda Allah ya cika min burina Zahra ta shigo gidanta fine".
"To mun gode kwarai Allah ya saka da Alkhairi sai munzo visiting idan madam zata dauki nauyin zuwan mu Kinga Nima sai Naga duniya ko madam?" Ya zubawa Zahra narkakkun idanun
sa Yana Mata wani kallon qasa qasa.
Shiru Zahra tayi tana yafa gyaren a kanta, Sajida ce tace "gaskiya Kam haka za'ayi".
Tashi yayi ya Dan tako kadan zuwa gaban Zahra kamar ze hadeta da jikinsa da sauri tayi baya tana turo Baki yi yayi kamar Bai gani ba, e
nvelope ya Mika mata Yana fadin ki Bata sskonta ne na jiya data Bari nayi niyya bazan canza ba sai dai idan bataso ta bayar, nizan shiga gurin su malam".
A hankali tace "an gode madallah a dawo lfy".
"Amin to bestie sai munzo ko".
Bai jira abinda zata ce
ba yayi ficewarsa.
Ajiyar zuciya Zahra ta sauke tana Zama kusa da Sajida Mika Mata envelope din tayi tana fadin "yaushe ya Baki kikace bakya so?".
"Jiya Mana lokacin da zamu tafi sanda wannan jikar marokan ta zubar da darajarta ta rokeshi, yanzu Dan Alla
h me Hameeda ke nema? wane irin rufin asiri ne Allah Bai mata ba. Amma ta lalace gurin roko? shi yasa na aje masa kudin sa nayi gaba kayan ma nace bana so su rike".
Dan murmushi Zahra tayi tana fadin "Saji danger wato halin na Nan ko? To nidai gashi nan t
unda a gaban ki ya bayar saiki karba".
"Bude mu gani to"
Sajidar ta fada.
Stalling founds ne na ingila musu yawa a ciki kallon kallo sukayiwa juna kafin Sajida tace wallahi bestie akwai kukus a shinkafa zakice na fada Miki, Wai kuwa kin tsaya kin Kare guyn
nan kallo kuwa?". Kinga ya Miki Kama da Wanda baida abinyi ko wanda ya tashi a cikin rashin wadataccen ilimi da mugu? Dubi muhallin daya ajeki, ance malam ya bashi gidan sai kungiyar da yakewa aiki sukayi renovation din gidan ki kiyasta nawa yaci gurin ai
kin kinsan da an kashe abinda yafi kudin ginin duk yi Masa akayi? Ki tuna Nan fa ba garinsu bane ance bako ne kuma yaki fadin garinsu anyi magana ance yace ya manta komai sai a hankali idan ya tuna hankali ze yarda da hakan? Kuma kina tunanin Abba ze dauk
eki ya bashi ba tare da yasan wani Abu a tare dashi ba? Kiyi nazarin abin Mana ni dai ina fada Miki kibi komai a hankali kuma yanda na fashimci wani Abu a maganar da Kika fada min kinfa kamu da son guyn Nan tun sanda kuka hadu ba tare da kin sani ba, Kuma
Shima Naga yanda yake shige Miki ko kunya ta Bai jiba kinsan sai a hankali kawai kwanan Nan labarin ze sauya irinsu basayi da wasa fa".
Ta garasa fada tana dariya kasa-kasa.
Suna cikin tattaunawa Kira ya shigo wayar sajida "Ya Abdul Hakeem ne" ta fadawa Z
ahra kafin ta daga.
"To"
Kawai tace ta kashe Kiran tana fadin.
"To bestie ya Abdul Hakeem Yana jirana Wai a she shine ze Kaini nifa daya fada na dauka da Wasa yake lokacin da Ammah tace Magaji ko Malam Bala dureba zasu kaini sai kawai yace su Bari Shima
Yana son yaje kanon Sai ya tafi Dani".
Dariya Zahra tayi tana fadin "idan tayi wari munji batun, yanzu ba fa Naga Ya Abdul Hakeem Yana dama dama dake ba bai fada min ba Amma zakice na fada Miki Ina ga target dinsa kenan yau yake son ya yad'a manufarsa s
hi yasa yayi Riga malam masallaci yace Wai daman kanon zaya".
Kin magana sajidar tayi sai murmushi kawai. Zahra tace "bestie ko dai komai ma ya kankama ne ban sani ba Ina shirme?".
Kafin sajidar ta Bata amsa wani Kiran ya shigo da sauri ta dauki jakarta ta
na fadin "To bestie sai gani na gaba Allah ya bada zaman lafiya ya kade fitina, sai anyi ta hakuri kafin komai ya dai daita ki kwantar da hankalin ki zakiji dadin Zama dashi in Sha Allah".
Har gate ta rakata babbar ledar dake hannunta ta Mika mata tana Mat
a addu'ar sauka lfy. Amsa tayi tana Mata godiya ta bude gate din ta fita, ya Abdul Hakeem Zahra ta gani a mota a zaune cikin mamaki tace.
"Ya Abdul Hakeem daman kana Nan waje Amma baka shigo ba?".
Fitowa yayi ya karaso gurinsu Zahrar ta gaishe shi, sannan
ta juya ta koma ciki duk zuciyarta ba Dadi Kamar ta Hana sajidar tafiya amma ba hali.
*********
Mahmud Yana fitowa direct Famfon shanu ya nufa tunda lifan din Habib a gurinsa ya kwana, tun jiya daya karba da yamma Bai koma unguwar ba.
Lokacin daya kara
sa yayi arba da motar Sameer wani murmushi yayi Yana fadin. "magulmaci kawai".
Kafin ya shiga Saida suka dinga gaisawa da jama'a anata Allah sanya Alkhairi, Binya ya tambaya Ina Habib yace yaje Kai wani sako da malam ya tura shi ya Kai gidan sarki.
Gurin M
alam din ya shiga shi dasu Sameer ya samu suna magana da malam din Yana shigowa da sallama mlm din yace.
"Yauwa Dan halak yanzu nake cewa bazaka jima ba zaka shigo, mutanen ku ne sukazo da wasu ayyuka gasu nan dai zasuyi maka bayani. Ya wajen iyalin naka!
?"
Dan sosa kansa yayi Yana Dan sadda shi qasa yace "Lafiya kalau tace a gaisheka" .
"Masha Allah. Allah yayi Albarka"
Gurin su Sameer ya juya suka gaisa, kafin suka fita zuwa inda suke meeting.
Stepdown training zasuyi da school base management committee
Basu tunda tsarinsu ya koma sun bin tsarin makarantun government ne sai kuma officially da suka gayyaci Mahmud zuwa gurin taron da zasuyi a Lagos nan da kwanaki biyar masu zuwa. Bayan Gama taron Sameer ya dauki Mahmud a mota suka fita hotel din suka nufa
a hanya Sameer ya kalli Mahmud Yana fadin "yallabai meye labari naga text dinka komai an sawo zuwa anjima motar zata karaso amma sai nake ganin kamar kayi tafiyar nan da ita tunda zaka jima a can Kuma kaga duka kwanan ta nawa zaka tafin baka ganin abin ze
iya Zama na surutu ko ace ma guduwa kayi amma dai ya kake gani?".
Dan Jim yayi kafin yace.
Tafiya da ita ba shine solution ba na dauketa na kaita Ina ko Kuma nace Mata wanene ni Nan nace Lagos zani can Kuma taga sabanin hakan ya kake tunani ka tuna fa sh
e's educated, zatayi saurin gane komai ni kuma nafi son na Gina soyayya ta a zuciyarta ba tare da tasan who I am ba, I hope you understand?".
Kai ya gyada Masa alamar eh.
Sun Dade suna tsaya yanda program din ze kasance da abinda za'a batar da abinda za'a
kashe a makarantar zuwa lokacin da zasu dawo suna cikin aikin direban daya dauko kayan ya Kira Sameer ya fada Masa ya shigo Azaren ya fada Masa inda yake tattara komai sukayi suka wuce gurin da direban yake, Sameer din ne ya shiga gaba direban na binsa a b
aya har zuwa gidan Mahmud din.
Mai gadi ya taya direban sauke kayan, kayan abinci ne da sauran tarkacen girki hatta nama da kifi daga can aka kawo kayane masu matukar yawa.
Ciki Mahmud din ya shiga tararwa ya yi tayi Baki har su zulai da sahura, a tsaitsay
e suka gaisa yayi gaba zuwa bedroom dinsa.
Ganin idon su zilan yasa zahra mikewa tabi bayansa dai dai lokacin Kuma Yara suka Fara shigon kayan masarufin da aka kawo, ganin zahrar Bata Nan yasa su sahura shiga dasu store din kayan abincin suka hada da wanda
Abba yasa suka kawo dazu da kayan gara su gireba dasu dublan da alkaki.
Sunyi mamakin yanda yara ke shigo da kayan abincin basu Kara Shan mamaki ba Saida aka Fara shigo dasu Nama da kifi ga drinks Nan ko ba'a fada ba Wai ance ido ba mudu ba amma yasan kim
a sun San kayan na manyan kudi ne, ko wacce da magana a bakinta Amma bata furta ba.
Zahrar na shiga corridorn ta waske zuwa nata dakin.
✨✨
✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
✨✨
✨✨
💎
PAGE TWENTY ONE
💎
(21)
...............
…
... Sai da su zulai suka gyara
Mata komai yanda ya kamata sannan suka gyara parlourn,lokacin da Mahmud ya fito bedroom dinta ya nufa baiyi wani knocking ba ya tura kofar a gaban gado ya ganta ta cire bedsheet din ta zubo da pillows din da alama wani Abu take nema sallama yayi mata cikin
muryarsa Mai nutsuwa yana kallon ta, cikin takunsa na cikakken namiji ya karaso Yana tambayarta "lfy me kike nema ne haka Kika birkita gurin haka?".
Jiki sanyaye tace Masa "wayata nake nema tun safe banganta".
Dan matsowa yayi kamar ze tayata dubawar Yana
fadin "Kuma tun safe Baki ganta ba Kuma Baki nema ba sai yanzu, to su waye suka shigo dakin ne?".
"Shiru tayi kawai tunda tasan daga ita sai sajida ne a dakin Kuma tun bayan tafiyar ta ko Baki ne 'yan ganin daki Bata ahigo dasu Nan Dan gani take yaushe z
a'a dinga shigo da jama'a har dakin barcin mutum su dai dayan tunda ba a ciki take ba.
Dagowa tayi ta Dan kalli gefen shi da gani wanka yayi ya canza kananun Kaya tana mamakin sa ita tunda take ganinsa Bata taba ganinsa da shiga irin wannan ba Kullum manya
n kaya ne Amma daga jiya zuwa yau ya zamar Mata wani daban, Sam ba wancen bane take gani.
Kamar ze wuce ta bayanta sai Jin Hannun Mutum tayi ya zagayo ta cikinta ya manna bayanta a kirjinsa ya kwanto da kansa dai dai saitin kunnenta iska yadan hura Mata ka