Showing 282001 words to 285000 words out of 295116 words
Kiran meeting na duka family a Babban h
all din Nan da kukayi walima.
Mutane sun amsa Kiran kamar ba gobe Dan sun San da walakin goro a Miya, Uncle Mustapha ne yayi Addu'a da jawabin maraba ga jama'a sannan yace wani Abu yakeso kowa ya maida hankali ya saurara yaji sai mu yiwa kanmu adalci a cik
i game da maganar Mahmud da yarinyar Nan safna, Jin haka yasa su Aunty Sameera da uncle saminu zasu tada Zaune tsaye, Abbie ne ya taka musu birki yace ko shi baisan menene ba tosu meye zesa su tada hayaniya Kan abinda bakasan menene asasinsa ba, dole suk
a hakura Amma zuciyar Safna kamar ta fito Dan mugun bugawar da tajeyi.
*_AUREN HUCE HAUSHI_*
AISHAT ISAH MUSAH.
(Maman Fateemah).
09061432330
Or
08055362975
Page 95.
______Ba'a dauki dogon lokaci ba ma'akacin kamfanin wayar ya hada komai ya saka
microphone yanda na nesa zasuji magana, cikin abinda Bai wuce minti biyu ba maganar Aunty Sameera ta karade gurin ita ta Kira uncle saminu ta nemi ganinsa a lokacin take tamyarsa yaje gurin data fada masa a Nan ya fada Mata yaje har ya bada turare Wanda s
afnar zata shafa taje gurina idan na shaqa ban Isa nayi Mata musun duk abinda ta buqata Koda kuwa kwanciya da ita ne, shine suka hada tazo da system tayi min wannan shishshigewar Dana kasa hanata a Ranar da uncle saminu ya samemu Ni da ita da yamma Wanda y
aso tun a Ranar ya hada min gwarama sai Kuma Allah ya Kare abun ya shashance, sai kuma sauran maganganu Wanda Basu shafeni ba, haka aka dunga sauraren yanda suka ringa kulla makirci kala-kala ita da uncle din har turo min Safna daki, Ashe duk setup ne.
Sai
Kuma wayata da Safna a mabanbantan lokuta babu komai sai gaisawa da zumunci da Kuma requesting na kudi da dai sauransu sai Kuma wayar Safna da number din da Batool ta bada,a Nan kowa ya shiga shock Dan abin ba tsabta Dan duk abinda sukayi tun daga chart d
insu har Kira da voice note har video call ba'a rage komai ba Abu mafi tada hankali a cikin wayoyinsu sunyi maganar zubar da ciki ya Kai sau biyu, da irin yanda suke shirya haduwa a lokutan da take zuwa makaranta, a lokacin ne aka gane Ashe duk lokacin da
tace ta tafi Niger state saurayin nata take bi har outside country suke fita, ta Nan aka gane tana amfani da layukan waya hudu da wayar ta yanda idan ta fita makaranta take rufe wayar tace saboda suna lectures ne.
Daga karshe aka dawo kansu uncle inda aka
dunga sauraren makirci abun dai babu Dadin ji, har na karshen nan Wanda suka hada karfi sukaje har okene gurin wani matsafi suka karbo abinda aka turara min a daki da wasu tsubbace_tsubbacen da akayi Dan kowa yayi min naqi, duk ta waya suke shirya komai D
an a zahiri bazaka tab'a cewa da wata alaqa irin haka a tsakaninsu ba, a Ranar da abun ya faru sun jima suna waya da hada yanda abun ze kasance Dan turaren maganin da aka saka Aunty Sameera ce ta shiga da kanta tayi lokacin yaran sun fice sallah sannan Saf
na da uncle saminu suka shigo dakin lokacin da uncle din yayi waya da security din gidan Hajiya Inna yace Masa mun fito da zayyan, shine fa suka shirya min wannan makircin Wanda kowa ya kasa gane meye gaskiyar Al'amarin sai batool da Allah ya tsareta ita d
a uncle Mustapha, tunda aka Fara wannan fallasar su Safna da Sameerar ke zufa Shima uncle sadda Kai kasa yayi, mutane kuwa Nan da Nan guri ya kaure da hayaniya masu Ala tsine nayi masu sharben hawaye nayi masu Ala wadarai nayi, cikin borin kunya Aunty Same
era ta tashi tana zazzaga masifa da hawayenta bibiyu tana fadin wallahi shirya wannan abun akayi ita ba ita bace wadda take magana inpersonate ne akayi Mata bazata yarda ba sai tayi shari'a da masu kamfanin wayar, uncle Mustapha ne yayi Mata zabu -zabu aka
n idan Bata yiwa mutane shiru ba ze saka a tafi da ita a sakaya masa ita ta jira ai da saura.
Computer aka hada wadda akayi connecting da CCTV tiryan-tiryan aka Fara nuna duk abinda ya faru a part din su Mahmud a Ranar tun daga safe har dare,duk shige da f
icen kowa gashi Nan kowa ya gani har abinda ba'a fada ba a wayar Saida aka gani in da uncle saminun ya fasa interlock din kofar shiga part din mu ya binne wani Abu da turaren da akayi da shiga cikin dakin da wayar da yayi lokacin da Mahmud ya taho da shiga
rsu dakin har da Wasan banza da sukayi kafin suji shigowar su Mahmud, sai lokacin akaga Ashe uncle bayan curtains ya shige ita Kuma ta tsaya gefen da kofa zata karareta idan ya bude kofar, duk abinda ya faru kowa yaga zahiri Nan da Nan hankalinsu ya Kara t
ashi Dan An yanka ta tashi abinda hankali da tunaninsu Bai tab'a kawo musu ba kenan, Abbie ne ya taso idanunsa sunyi jajur sai huci yake Yana fadin Sameera tazo su fice Masa daga gida ya saketa saki uku minti biyar ya Bata idan suka wuce haka sai sunga kas
kancin da Basu tab'a tunanin ana yinsa ba, Nan Sameerar ta Fadi tana birgima tana tuma da fadin ta shiga uku wallahi saminu ne ya sakata yace Dan mu mallake dukiyarsa idan mukayi haka Dole sai yanda mukayi dashi da kowa ma Tunda babu Wanda ze iya bude Baki
yace Mana ba haka za'ayi ba.
Kan uncle saminu Abbie ya juya ya nuna Masa hanya Yana fadin ya fita kada ya Kara ganinsa a gidansa yaje yaji da kunyar tonon sililin da akayi masa, Safna kuwa a Nan da sume Saida aka yayyafa Mata ruwa ta farfado tana sambatun
ita babu Mai rabata Dani Tunda an daura Aure take Abbie ya rattaba saki ga safna a madadina Tunda Daman bansan da masaniyar Auren ba.
Hajiya Turai ce matar Autan su Alhaji sa'id tasa aka fita da Safna da Aunty Sameera.
Saida aka wuce dasu sannan Ammi ta t
ashi wadda tun lokacin da aka Fara bayanin take hamdala ga Ubangiji Daya wanke Mata yaro daga zargin Zina Daya karade a cikin family.
A hankali ta ratso mutane ta fito tsakiya ta Fara fadin ta godewa Allah ko yanzu ta koma ga Allah Bata da sauran bakin cik
i saboda Allah maji rokon bayinsa ya amsa Mata addu'arta wadda take yinda babu dare babu Rana, saukar Al'quran ma anyi Mata babu adadi Tunda abin ya faru tana addu'ar Allah ya tona asirin duk Mai Hannu a cikin Lamarin, sannan ta juya ta dubi Abbie tana fad
in daga yau kwanan gidan Nan ya qare min abinda nake jira kenan Daman gaskiyar tayi halinta, to Kuma yau Alhamdulillahi gaskiya tayi halinta Dan Haka Nima hanya kasan fita ta. Ta juya ta fice itama, abinda ya tada hankalin Abbaie din kenan ya bita da sauri
ya fice shima, Dan Tunda yake a zamanzu magana makanciyarta haka Bata tab'a hadasu ba. "To fa kinji dalilin Daya mayar Ammina niger. Hakan ne ya Kara harzikani saboda anyi min rashin adalci, lokacin fa Sameer yazo min da bayanin na jinjinawa Batool matuk'
a yarinyar tayi min bazata Sosai, Abu kamar Wasa Duk Wanda sukabi Ammi babu Wanda ta yarda ta biyo da suka Fara rinjar Hajja ne bayan zuwan Hajiya Inna Ammi ta dawo Damagaram gurin Yayanta kafin ya Yanke Mata hukunci dawowa sokoto dole, hummm Amma fa Ina b
iyiye da duk motsin Ammina Dan Yanke huldar da nayi ta zahiri ce Amma a badini Ina cikin duka lamuranta Dan Ina zuwa Yamai duk lokacin danaso ganinta sai dai su nemeni su rasa a can garin, ganin nesa ta tazo kusa yasa nayi zamana a garin ku dankwali yaja h
ula, sauran bayanai da yawa Kuma sirrina ne. Kinji kadan daga abinda ya sameni Dan ma na takaita Miki wasu abubuwan da uncle saminu ya ringa nuna min ke dai abar kaza cikin gashinta kawai, idan ana cin B'aure ba'a tona cikinsa Kuma idan ana sallah ba'a mag
ana, wani sanin sirrin cikin ciki sai dai hanji kawai, Dan haka ban Hana ki gaisa da zuri'ar uncle saminu ba Amma na yanke Hulda dasu har abada kamar yanda mahaifina ya cire Shi a cikin duk sabgoginsa sai dai abinda ba'a rasa ba Dan masu iya magana na cewa
hannunka baya ribewa ka yanke kayar,to kinji summary na abinda ya faru Dani ya Zama sanadin da yasa na fito a wancan lokacin sai dai ni Alhamdulillahi hakan wata Rahama ce daga Allah.
Jinjina abin Zahra take a cikin zuciyarta ace duk wannan masifa ta dumf
ari mutum Daya ai sai Wanda Allah ya bawa karfin zuciya da imani ace duk girman family Kamar wannan duk sun maka nak'i Sai mutum biyu kawai lallai anga taskun rayuwa.
A hankali ta sauke numfashi tana kallonsa Banda tasan baya son kuka ba da wallahi saita m
atse yanda zuciyarta ke Mata zafi, Dan ji tayi ta tsani safnar da yayarta tsana Mai zafi wadda ita dai ko Mama da Salma da suka nuna Mata qin jini bataji su kamar wadannan ba.
"Me amorrrr....".
Ta fada a hankali.
Gyara Mata kwanciya yayi a cinyarsa Yana ka
llonta cikin Ido.
"Umhummm.... Fadi ya akayi?".
"Allah ya Kara maka juriya da hakuri kaga jarabawa ta rayuwa, lallai Ubangiyi yayi gaskiya da yace shin bazan jarabceku ba?. Amma taka dai Kam sai Mai karfin Imani Dan Mai karamar kwakwalwa sai kansa ya buga
koya fada wata harkar Tunda babu ni'imar da Ubangiji Bai maka ba, Allah ya hore maka amma ya baka kariya daga fadawa mugunyar rayuwa, ya tsare min kayana Alhamdulillahi Allah abin godiya".
Dagota yayi daga kwancen ya kafa Mata idanunsa da suke razanata a w
ancen lokacin Wanda Kuma suke tsumata a yanzu.
"Kice Kayan naki ne ke kadai, to ya za'ayi da sauran dake kokowar shigowa Kuma?".
Wani warrrr tayi masa da sexy din ta Wanda wani irin Abu yake walainiya a cikinsu.
"Ai dagani babu wata a yanzu dai saina cinye
na sude kayana tas sai dai su samu sudin kwano".
Rike Baki Yayi Yana wata dariya kasa-kasa.
"Kai yarinyar nan yaushe kikayi Baki haka? "Wato kin Fara gane garin ko?".
Dariyarta Mai shagaltar dashi ta Fara tana nuna shi da hannu.
"Ni Kuma wane garin na Far
a ganewa?".
Ba zato yayi Mata daukar jarirai yana fad'in Bari na nuna Miki garin".
*****Tunda su Ammah suka shiga garin Miya kukan Salma ya tsananta tamkar zata shide, Banda aikin lallashi babu Abinda su Ammah keyi daga karshe ne Aunty Hassana ta rufeta
da fada ta inda ta shiga ba tanan take fita ba. Shi dai malam Bala ko tari Bai kubce Masa ba Dan yasan sakayyar Allah ce kawai ta sauka akan Mama da 'ya'yan ta Dan dashi wani Maci Amana ne da Allah kadai yasan abinda suka shuka shida ita to tun tayin farko
ta taka Mata birki da barazanar sanar da Alhajin shine abinda ya kawo basa ga maciji a tsakaninsu.
Ba laifi gidansu Anas din da nasu rufin asirin sai dai da alama rayuwa ake ta babu kwaba a gidan Dan yanda kannensa Mata suka ringa yatsina fuska ga babu t
arbiyya Kota sisin kwabo a gidan saboda da kyar kanwarsa Haulatu ta bayar da key din dakinta a sauki Baki cewa tayi ita da kayanta kada a Bata mata, sai wani kanin Anas din yayi Mata Jan Ido sannan ta bada, aka bude suka shiga inda aka kawo musu Abinci ba
laifi ta Nan sun yaba, amma dai uwar tasa basuga fuska a gurinta ba, sun dai gaisa shima ganinsu Ammah da tayi ba karya sun jiku da naira gayu ya zauna dole ta mayar da makaman yakinta ta Bari idan sun wuce ta baje kolin abinda ta tanadarwa daga salmar har
Anas din tunda 'yar kanwarta yake aure Bai Kuma fada Mata ze auro Salma ba saida iyayensa maza zasu tafi daurin auren suka shigo suka fada Mata Tunda Babansu ya rasu.
A dofane suka wayi gari inda tun karfe bakwai motar Kayan ta sauka a Miya Dan tun dare A
bba yasa akayi lodin Kayan abinda babu yasa su sahura da makotansu suka shiga stores suka sawo, Kayan toye-toye ma gidan masu yin na sayarwa akaje aka sawo saboda Basu da matsalarsu a unguwar da Kuma can bakin kasuwa.
Kafin azzuhur gida ya kankama na amary
a, Ammah ta saka Salma tayi wanka wadda har lokacin kuka takeyi ga azababban Zazzabi Daya rufeta, a irin kayan da aka dinka na Zahra Wanda magaji ze tafi dasu Ammah ta debo Mata kala kusan goma ta taho Mata dasu Tunda babu Abinda aka tanada bagatatan abun
yazo.
Su Ammah sun Kara Kai Salma gurin surikarta sun bada Amanarta sannan suka mikata dakinta tare da yayar Baban Ana's din, tana gunjin kuka suka barota Dan abinda Bata tab'a kawowa bane ko cikin mafarki akayi Mata taci burin auren miji na kece raini ta
shiryawa kanta rayuwar Jin Dadi da walwala Amma sai gashi ta Kare a auren yaron kamfanin nefa Zama a inda ko cikin hasashe Bata tab'a kawowa ba, haka su Aunty Hassana suka wuce.
Saukinta Daya gidan da abunda aka zuba Mata ze kankaro Mata mutunci ko banza t
a Nan fannin dai babu raini.
***
A cikin sati daya Zahra da Mahmud sunyi wata irin shak'uwa ta ban mamaki,Dan Daya ji yake baze iya rayuwa ba Saida dayan Zahra ta Zama 'yar gari sai tsula shagwaba take Masa shi Kuma duk ya susuce a kanta, ga wani irin f
resh da sukayi dan dole idan ka kallesu ka kara, Saida hankalinsa ya nutsu sannan ya zauna dasu Salis da Bashir ya nemi shawararsu akan idan suna ra'ayin aiki dashi to suyi Shawara da gida akan Nan gida suke son Zama suyi aikin ko a waje sannan ya bawa kow
a gida a acan Azaren Saida ya fada musu inda gidajen suke Salis yayi murmushi Shima Mahmud din yayi wani Abu suka tuna, lokacin da Mahmud yaja Salis din sukaje ana yiwa gidajen pop Salis ke tambayar ko gidan waye haka sai Mahmud din ke fadin na wani abokin
Sameer ne yasa shi ya dube Masa har yake cewa Salis din ko gidan ya burgeka ne Naga kamar kana sonsa? Dariya lokacin Salis din yayi Yana fadin wa zeba Dan rogo rumfa? ai irin wannan gidajen sai wadanda sukaci suka tada Kai. Dariya kawai lokacin Mahmud yay
i baice komai ba kawai dai yace Masa ya Taya shi a duba abinda baiyi ba Mai gidan ne yace ayi hakan Nan Salis din ya zage Yana ta fadin Nan kaza ya kamata ayi nan ayi kaza haka suka zagaye gidan har suka Gama bada gyaran, haka suka shiga dayan ma aka rubu
ta komai, to sai yanzu da yake fadar inda gidajen suka Salis ta tuna da abun, sunyi godiya kamar su Ari Baki Dan Dadi Bashir baisan lokacin da hawaye ya zubo masa sai gani sukayi Yana share hawaye, saboda Tunda ya Gama Karatu Bai Sami aiki ba gashi Dan Mai
karamin karfi kullum Yana yawo neman aiki sauda yawa Mahmud Kan fada Masa yayi hakuri da lokaci, in dai aiki ne Saiya zab'a, a lokacin jinsa kawai yake Ashe da gaske yakeyi saiya zaba din tunda gashi ya Basu options na zabar Ina suke da muradin yin aikin
.
Dariya sosai Mahmud ya ringa yiwa Bashir ganin yanda yake shafe Ido kamar Mace.
"Haba bash meye haka be strong mana Dan Allah, kuka kuma? To in banyi muku ba suwaye Zan yiwa kun riqeni Amana lokacin da bakusan daga wace duniyar nake ba, kun ciyar Dani ku
n dinka mun suturar sakawa, kun bani kudin da kuka nema da karfin jikinku, kun tsaya a gurin jinyata lokacin dasu Habib ke yinta ga abin Hawa an sakar min babu shamaki duk inda zani, an bani Mata kunyi uwa kunyi makarbiya gurin hidima da jikinku da aljihun
ku to ni kuwa ai bani da abinda Zan biyaku dashi sai dai nace Ubangiji ya biyaku da madaukaliyar Aljanna wallahi tuni na cireku daga abokai kun zamar min 'yan uwa yanzu ga wannan" ya mikawa Bashir Daya fi kusanci dashi E.passport ne yace su saurari visa
Sameer ze kawo musu ta umarar Azumin nan Mai kusantowa, yace Kuma kowa ya duba akwai sako a wayarsa, sunyi tsaraba ya Kuma fada musu tickets dinsu na zuwa Bauchi Yana hannun Sameer, bakin godiyar ma rasawa sukayi Dan wata kyautar tafi gaban godiya, Dan ya
gigita musu lissafi ba Dan kadan ba.
Sameer ne ya shigo da sallama lokacin kwanansa biyu da dawowa daga Egypt gurinsu Mama Dan Saida akayi Mata aiki sannan ya juyo ya barosu a can, Mama tayi kuka tayi kuka akan wautar datayi a baya na nuna hassada da ganin
kyashin yarinya marainiyar Allah wadda aka mutu aka Bari ko kanta Bata sani ba Amma shedan yayi Mata katutu a zuciya ta dunga kulle-kullen mugun Abu Tunda masu dubanta suka barbasa Mata yarinyar tana tare da wata irin sa'ar rayuwa duk sai ta rude tana gan
in ta Yaya hakan ze faru gata Mai kyau na ban mamaki sannan ace sa'arma tatace tun daga lokacin zuciyarta Bata huta ba, to gashi Alkawarin Allah ya tabbata gata a gadon asibiti a wata k'asar tare da ciwon zuciya Wanda bakin ciki da hassada sukayi sanadinsa
, ga Kuma wadda take abun a kanta taje inda Ubangiji ya nufa taje din,tunda Alkawarin Allah baya tashi ga shi Kuma mijin da taketa kangewa kada yazo gurinta shine ya Zama silar samun waraka ga ciwonta, ga mijinta Tunda sukazo bai Kira ba ya bawa banza ajiy
arta Bata Kara Jin ko duriyarsa ba tun lokacin da yaje sokoto