Showing 66001 words to 69000 words out of 295116 words
yayi knocking wata Kuma na kwabarsa, juyawa yayi ya koma gurin dining din shi dai baze iya cin abinci Mai n
auyi ba, abincin ya dauka yabar pepper soup da hadin salad din tinda bashi da yawa.
Gurin Mai gadi ya nufa yana Fadin "Ga abincin nan a samu ayi amfani dashi yayi yawa".
Da hanzari ya taso Yana fadin "To yallabai ai dazu ma Mai gidan ta Aiko dashi har Said
a na bawa wasu Yara ma sauran, wannan kuma Bari na kira Mustapha yazo ya kai musu can gida madallah dai an gode da dawainya".
"Haba ba komai gashi idan yazo sai ya biya mashin dasu". Ya aje Masa 5k akan warmer din ya juya yabar Mai gadin Yana sheka Masa ad
du'a da fatan Alkhairi.
Saida yayi wanka sannan ya dawo dining din yaci iya Yanda yake ganin ya isheshi sauran ya Kara kaiwa Mai gadin sannan ya koma daki.
Kan kujerar desktop computer ya zauna Yana kunnawa da ita akayi masa connecting din CCTV din dake gi
dan, a hankali ya fara watching Yana kallon duk wani abinda ya faru a gidan wani irin murmushi yakeyi lokacin daya ke kallon dabin su da ita da yadda tasha kukanta, wani Abu daya ja hankalinsa shine yadda yaga su zilai da yadda yaga sahura tayiwa zilai da
bara ta turata ciki gurin zahra, ita Kuma tana waya bayan ta gama Kuma yaga ta shiga store ta fito tana kudundune Abu a cikin hijabinta wanda be San ko menene ba, take a Nan ya Dora mata question mark.
Saida ya Gama ganin komai Dan yanzu ma littafi ne take
karantawa har lokacin daya murda handle din kofar da Yanda ta wani zaro sexy eyes din ta Kamar zasu Fado kasa saboda razana, murmushi yayi Yana fadin "matsoraciya kawai wannan za'a Sha drama da ita Dan Naga alama shagwaba tabi jikinta Bata San wahala".
Z
ahra kuwa tunda ta shige ta rufe kofarta tayi duk abinda zatayi na al'adun kwanciyar ta, sai ta dauko littafin ta du'aul mustajaba tana karanta addu'ar barci, bayan ta Gama ta shafa shiru kawai tayi tana tunane tunanen zuci ba, memories na abinda ya faru t
sakanin ta da Mahmud ya shiga dawo Mata, Dan guntun tsaki tayi tasa hannu a kirjinta data wuni suna Mata zugi, a hankali ta Fara magana Kamar Mai gudun kada wani yaji ta.
"Jarababbe kamar maye duk ya cinye min labba da harshe ya shafeni tas yana wani gurna
ni kamar na zaki, da wasu idanunsa da gani na fitinannu ne! Ni Zahra na gamu da gamona na shiga Tara bama uku ba, shikenan na Zama nama sai Yanda hali yayi". Hawaye ne sharrr suka zubo Mata duk lamarin ya cud'e Mata ta rasa mafita, alwala ta shige ta daur
o tana ayyana gara ta kaiwa Wanda baya barci wani abu Kuma Bai taba boyuwa ba a gurinsa kukanta tasan shine sami'uddu'a.
Sallah tayi raka'a hudu ta zauna tayi istigifari da hailala da salati ga fiyayyan halitta Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w har Saida taj
i zuciyarta ta samu nutsuwa kafin daga karshen ta daga hannuwanta sama tana Fadi cikin raunin murya da Qasqantar da Kai ga Allah s.w.a
"Ya Ubangiji Kaine mafi sani ga abinda yake faruwa Dani, wani Abu Bai sameni ba sai da izininka na gode maka a duk halin
dana samu kaina a ciki, ka zama gata na,ka lullubeni da bargon Rahamarka, ka suturtani da suturarka, ka rufa min asiri da rufin asirinka, kada ka barni da iyawata ka iya min da iyawarka, Ubangijina ga wannan bawan naka Nan kasan ko waye shi lamarinsa Ubang
iji ka sani ba boyayye bane a gurina Idan Yana da wani kaidi kada ka Bari yayi tasiri a kaina Dan isar Annabi MUHAMMAD a gurinka. Ubangiji kajikaina ka duba raunina ka tausaya min kada ka Bari makiya suga wallena ka bani rinjaye a kan dukkan al'amurana".
Duka hannuwanta tasa ta rufe fuskarta kamar me shafa addu'a Amma kuka ta saki Mai tsuma zuciya tana ayyana "Wai fa ita Amarya ce wadda ya kamata ace a irin wannan time din ana can ana riritata kamar a hadiyeta dan so da kauna da tarairaya da kulawa. Amman
nata da haka yazo Mata, Astagafirullah Ubangiji ka yafe min zunubina daya janyo min irin wannan gararin rayuwar".
Ta dauki dogon lokaci tana shashhsheka a haka barci yaci karfinta ta sulale a gurin yayi awon Gaga da ita.
Bata farka ba sai kusan biyar da
rabi cikin sauri ta tashi tana fadin "subahanallahi!"
Da sauri ta nufi toilet tana addu'ar tashi daga barci, a gurguje tayi uzurinta tayi alwala ta fito sallah tayi ta zauna yin Azkar da karatun qur'ani har gurin takwas na safe.
Mahmud Bai dawo gida ba da
ga sallar asuba gurin Sameer ya wuce, so yake yi suyi duk abinda ya kamata a Nan tunda kwaso jiki ya taho, shi yasa jiya yaqi yin komai yayi kwanciyarsa kawai.
Ba karamin mamaki Sameer yayi ba ganinsa da yayi a irin wannan lokacin to ai ko lokacin da taye
single baya Masa sakko haka. Amma sai gashi shida yake expecting dinsa gurin one-two haka shine ya ganshi haka kamar an koroshi.
Cikin zolaya yace "My man ya naga haka ka duba time kuwa? Ka fito kabar 'yar mutane ko dai da matsala ne na fadawa Babanka ma
nya su shiga ciki, sun baka yarinya girma -girma kana neman ka bada musu yaji a ido duk Wanda ya ganka a irin wannan lokacin daya Kamata ace kana can kana Shan kafi tea, ai sai mutane su dauka fanko aka kawo maka, gaskiya ka yiwa Allah ka koma ni zan shig
o mu karasa aikin a gidanka daman meke kawo mu Nan? ba bukatar privacy ba? to yanzu muna dashi kaga no need sai munzo Nan Kuma kasan yanzu ba da bane ".
Ya fada ba alamar zolayar yanzu, ikon Allah Mahmud ya tsaya yana kallo kafin yace "ka Gama Alhaji muha
mmadu tunda Naga alamar roll din tsohona kake playing, to Wai Ina ruwanka da harkar Nan Ina cewa Mata dai tawa ce yanda nayi ra'ayi haka zan tafiyar da abina, ai dalilin daya kawoni kenan kazo mu ida duk Wani aikin da zamuyi kaje kayi sallama da malam ka k
ama gabanka".
Ya zauna Yana dauko laptop din Sameer Yana operatin dinta.
Kusa dashi Sameer din ya zauna Yana fadin "Allah ya huci zuciyarka angon Zahra da Safnah....." wani kallo Mahmud ya watsa Masa wanda yasa Sameer yayi shiru ba Shiri, shi kansa baisan
sanda bakinsa ya furta sunan safna ba ko alama.
✨✨
✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
✨✨
✨✨
Story
&
Written by
Maman Fatimah.
💎
Page twenty three
💎
(2 3)
________Zahra ba ita ta farka b sai gurin bakwai da rabi, sai lokacin ta tuna ta cewa Musaddiq
ya fadawa Ammah ta bar kawo abinci zata dafa tunda ba komai take ba, toilet ta fad'a ta Dan sakarwa kanta ruwa Bata jima ba ta fito Riga da Wanda na Pakistan ta saka tayi rolling da gyalen ta saka plat shoes na daki ta nufi falo Amma zuciyar ta tana ta dar
- dar kada suyi arangama da Dodon nata, falon ta shigo shiru sai sanyin A/C da daddad'an kamshin da yake ga curtains din duk a sake ga fitilu masu qarancin haske a kunne saiya bada wani irin yanayi Mai saka nutsuwa.
Dan waige-waige ta Fara Kamar tana neman
wani Abu gurin sai Kuma ta nufi gurin tv ta tsuguna tana hada socket din adapter din tv ta kunna ta kamo tashar Almajid, kokacin sun saka Qira'ar Muhammad Saddiqul minshawi a cikin suratul ISRA'I sai da ta dai daita volume din sannan ta nufi kitchen din a
nutse da takunta Wanda da yawa suke ganin yangace da jiji da Kai alhalin ba haka bane naturally haka Allah yayi ta.
Kitchen din ta shiga Kusan shigowarta ta uku Kennan, lokar da taga kayayyakin aikin ta bude ta dauko roba mai Dan Fadi ta nufi store ta deb
o Irish ta fito wanke shi tayi ta fere ta zuba a tukunya ta kunna gas, sai kuma ta dauko kaza guda ta yanka ta wanke ta zuba seasoning da spices ta rufe, ta jona egg boiler ta zuba kwai hudu a ciki.
A gefe kuma ta dauko attarugu da Albasa ta yanka kananu t
a aje a gefe Irish din ta Fara dubawa taga yayi ta sauke ta zuba a container Mai zurfi tasa fork ta murje ta dora frying pan ta zuba Mai kadan ta saya attarugu da albasar ta zuba a Kan irish din ta zuba magi da curry ta fasa ta yanka dafaffen kwan a ciki s
annan ta fasa danye ta zuga ta juya ta aje ta duba kazar itama tayi Nan da Nan ta hada pepper chicken sannan ta jona tanda electric ta Fara zuba hadin Irish din Nan tana soyawa Kamar masa, tana gamawa tayi pepper chicken. Dora ruwa tayi a karamar tunya ka
fin ya tafasa ta dauko madara ta bude ta diba a wani bowl ta dama sannan ta dama corn flour a cup, jikin kitchen cabinets din ta tsaya tana bin karatun da yake shigowa daga parlour har sun kai suratul D'AHA.
Madarar ta zuba taci gaba da tafasa sannan ta
zuba corn flour din ta daure da yayi dai dai yanda takeso ta sauke ta Kara Masa condensed milk a cikin ta juye, hadesu tayi a babban tray tayi ta nufi falon, Nan akan dining table ta jero komai sannan ta koma ta dauko sauran tarkacen su cups.
Kitchen din
ta koma ta gyara gurin tas, sannan ta koma daki wanka ta shiga, tana fitowa ta shafa lotion dinta tayi simple makeup ta saka saka turarikanta na jiki dasu humra Nan da Nan jikinta ya shiga fitar da wani fitinan Nan kanshi, doguwar rigar Dubai Mai kananun s
tones pink mai duhu ta saka rolling tayi dan Vail din
rigar milk colour sai ta fito balarabiyarta sak Dan idan ba kaji tayi maka Hausa ba bazaka taba cewa tasan ko zo da Hausa ba, tayi kyau matuka yarintarta ta fito sosai idan ka kalli fuskarta very cute s
ai wani annuri take fitarwa.
Parlour ta fito gurin dining din ta nufa cikin takunta das das. Tana mamakin Ina ya shiga Dan ko motsinsa babu har yanzu ita kuma bazataje bedroom dinsa ba, idan ya gaji da zaman dakin ya tunda ba yaro bane yunwar cikinsa ta f
ito dashi. Kunun madarar ta zuba da masar Irish din kwara biyu kawai ta dawo main parlourn ta zauna tana ci tana sauraren karatun, sai da ta gama ta Kai kayan kitchen ta wanke sannan ta dauko Wanda ta zubawa baba Mai gadi ta nufi kofa a hankali take tafiya
a cikin harabar gidan iskar bishiyoyin da sauran shuke shuken suna kadawa gwanin sanyi can gurin gate taga baba Mai gadin ya nufa da sauri da alama budewa zeyi.Dan tsayawa tayi daga gefe idonta Yana kan gate din Dan taji dirin mota zata shigo cikin kankan
in lokaci motar ta shigo ido cikin ido sukayi da shi shine yake driving din gabanta ne ya bada ras ras Kuma ya kafeta da fitinannun idanunsa cikin gwaninta ya nufi parking lot, Sameer kuwa Kamar wani sakarai haka yake kallon zahrar Yana tsarkake suna Allah
a zuciyarsa ya ganta har kusan hudu Amma da alama ganin tsoro yake Mata sai yau yaga zahirin zahrar, da sauri baba Mai gadin ya karaso yana gaisheta ta Mika Masa Dan Karamin basket din ta juya da sauri ta nufi kofar falon har Kamar tana dan sassarfa ta sh
ige ciki, harta wuce idanun Mahmud suna binta Nan da Nan yayi kicin-kicin da fuska daman ga Sameer ya tabo shi ga itama da kalar nata shirmen, cikin zafin nama ya kashe motar ya Kama kofar ze bude Sameer ya kamo hannunsa ya rike Yana girgiza masa Kai kafin
ya dungule dayan hannunsa irin na roko din nan yace.
"Pls Dan Allah cool your temper kada kaje mata a haka kayi Mata uzuri Batasan Kai ko waye ba, Kuma infact ma laifinka ne ka tafi ka barta a gida har zuwa wannan lokacin Kuma tana ganin hakan da tayi s
hine dai dai koni nayi supporting dinta hakan shine dai dai ta nuna maka tasan haqqin abinda ka bar mata amana" .
A Dan fusace ya kalli Sameer.
"Nine na Bata amanarsa da izuninwa ta fito nan wato. ya kalleta yanda yakeso ko? Matata take kaiwa Mai gadi abin
ci wannan wane irin zubewar aji ne a gurina? Dubi fa yanda ta fito? Ko baka gani ba?"
Ya fada yana kallon Sameer.
"Ni banga wani Abu na rashin kyautatawa ba a shigarta, kawai dai idonka wani Abu ya nuna maka na daban gaskiya".
Hannunsa ya zare daga cikin n
a Sameer din ya bude kofar a hankali ba Kamar dazu ba zagayowa Sameer yayi ya rufe motar yabi bayansa Dan Idan ya Bari ya shige irin na jiya ze masa ya ajeshi a waje, kofar ya bude wani sanyi da kanshin girki Dana turarikan daki sukayiwa Sameer sallama Bat
a Nan sai tv a kunne ana karatun har lokacin.
Direct gurin dining Sameer ya wuce yana fadin Bari na Fara da Nan Idan na gama ma gaisa tunda ba bako nake ba ya Fara budewa Yana kallon Mahmud Yana fadin.
"Tab da alama Allah ya tarfawa garinki nono irin wanna
n delicious".
Gaba Mahmud yayi Bai tanka Masa ba ya shige ciki.
Kofar bedroom dinta ya kalla har dariya take bashi bilhaqqi da gaske tsoransa takeji bare Kuma da jiya ya Dan motsa mata Jamiyya.
Ta Dan Dade a bedroom din nata daga baya ta bawa kanta kwari
n Gwiwar ta fita ko banza bazata bada kofar da wani na waje ze gane da 'yar tsama a tsakaninsu ba Kar a Raina Mata wayo, fuskarta ta Dan Kara shafawa powder kadan ta Dan Kara fesa mouth freshner Mai kamshi apricot ta nufi kofa tana budewa saura kadan yau m
a suyi karon, da sauri taja Baya. Shigar kananun Kaya yayi as usual dan zaman da sukayi ta fashimci kamat ya samu wani freedom ne na sakewa, trouser black da milk T-shirt ne a jikinsa hannunsa daure da agogo sai waya a hannunsa. Baya tayi da sauri tana Dan
zare idanu Dan ba Karamin tsoro taji ba, Shima kallon ta yake Kamar ya rungumota ko yaji relief na abinda yakeji a zuciyarsa, amma sai ya share ya Mika hannunsa ya kamo nata ya natso da ita kusa dashi Sosai Yana Fadin "kin tashi lfy?".
Ya shafi gefen fusk
antar, cikin siririyar murya tace masa
"Ina kwana? Shiru yayi Kamar beji ta ba, ya janyo ta suka Fara tafiya a cikin corridorn, sai da suka Fara gangara steps din taji yace waya Baki izinin fita gurin watchman din can?"
Ya Dan matse hannunta dake cikin na
sa.
"Wash!!! Allah ta fad'a ba tare data shirya ba. Dan da gaske matsewar ta shigeta dago Kai tayi cikin narke fuska Kamar zatayi kuka dai dai lokacin Sameer ya dago Kansa daga daddana wayar da yakeyi Jin maganarta Sam beji tahowarsu ba wani irin perfect m
atch couples ya gani sun masifar dacewa da juna ya Dade bega ma'auratan da suka burge shi kamar su ba, a zuciyarsa yake Fadin.
"Masha Allah".
Zahrar Tace masa.
"Ba kowa, Dan Allah ka sakar min hannu wlh zafi...."
Ta fada cikin shagwabar da Bata San tayi
ba.
Murmushi Sameer yake ta saki daga inda yake Dan ba karya yasan muhmud yayi dacen da Basu zata ba abun kamar a film yake ganinsa. Dan lokacin da suka Fara ganinta da Kuma furucin da shi Mahmud din yayi ashe Allah ya karbi addu'ar.
Dan gyaran murya Same
er yayi Yana kallon Mahmud din tare da fadar.
"Yallabai a bar madam ta karaso mu gaisa Mana ni ba mazauni babe gaba nayi daga Nan"
Ya fada da sigar zolaya duk yaga har yanzu kamar Yana Jin zafinsa tun maganar da yayi masa na Safnah.
Sassauta rikon hannau
n yayi suka ida gangarowa directly dining area ya nufa yana zuwa ya ja Mata kujera ya zaunar da ita sannan Shima ya janyo ya zauna.
Gurinsu Sameer ya karaso daga inda yake zaune Yana fadin.
"Madam barka da Asuba kingan ni sai yau ki?".
Ya fad'a yana Zama k
usa da Mahmud.
A kunyace ta amsa da "lfy kalau Ya Sameer ya kaje gida? Ina madam?"
"Komai lfy ya hakuri damu?".
'yar dariya tayi kafin ta Mike ta Fara bude abincin Wani daddad'an kamshin ne ya doki hancin Mahmud har Saida ya lumshe idonsa, Dan kallonsa tay
i sannan ta kalli Sameer tace "me za'a zuba?".
Kai Sameer ya girgaiza Yana fadin "ai ni na riga ku ci tun shigowarmu naji bazan iya jiran masu gidan ba saina shide Ina jin kamshin delicious Amma ace saina jira".
Ya fad'a Yana dariya.Dan murmushi Mahmud di
n yayi.
"Wato ko Ina saika nuna halinka ko?".
"Pls zuba min kawai".
Kallonsa tayi kasa-kasa, tace "Toh"
Masar dankwalin turawan ta zuba sannan ta zuba pepper chicken din ta tura Masa sannan ta zuba kunun Madarar sannan ta koma ta zauna a darare.
Wani cup d
in ya zuba kunun Madarar ya dauko da fork ya matso kusa da ita da plates din abincin yace.
"Oya saka hannu muci".
Ya wani hade gabas da yamma alamun ba wargi Kai ta shiga girgaizawa alamar ta koshi Shima ture abincin yayi Yana duban Sameer.
"Muje kawai"
Y
a fad'a yan Jan kujerar baya.
"Zanci".
Ta fada a gajarce.
Komawa yayi ya zauna Yana fadin "fine tunda zaki
ç
i gara Idan mutuwar zamuyi mu mutu tare Dan naga abinda Mata suke yayi kenan Idan