Showing 234001 words to 237000 words out of 295116 words

Chapter 79 - AUREN HUCE HAUSHI COMPLETE

fadin.

"Gashi Aunty Aishat tace zakuyi waya".

"Ok Nagode, bazaka shiga ku gaisa da Ammah ba?"

Yar dariya ya

yi.

"Na nawa kuma? Na shiga mun gaisa".

Dan murmushi tayi ta nufi Cikin gida.

Ba zato tayi arba da Aunty Hasana da gudu ta shige jikinta tana fadin.

"Aunty kin manta Dani wallahi, laifin me nayi Dan Allah".

"Kuji mun yarinya ! Sai Kuma nayi ta kiranki a wa

ya har mijinki ya Raina ni ya daina Jin 'yar kunyar tawa da yakeji ai yawan damun kani ko d'a da Kira a waya bini-bini Yana kawo raini da rashin ganin kima a tsakani gara a ringa daukar lokaci yanda duk lokacin daka Kira ya Zama ana marmarinka ku rabu ana

kewarka da Jin ba'a gaji da Hira da Kai ba".

"Wannan maganar taki bisa hanya take, haka ake son Babba yaja girmansa".

Hajiya kaltume ta fada.

"Ah to Mamma fada Mata dai so take girma ya Fadi a gurin kanin nawa yanzu kuwa Aunty sama Aunty kasa duk bayan kwa

na biyu saiya kirani ya gaisheni".

"Aunty Ina zuwa".

Zahra ta fad'a tana nufar bedroom din data yiwa kanta masauki, Bata Jima ba ta fito da abinda Ammi ta Bata ta mikawa Aunty Hasana tana fadin.

"Gasu Nan na manta dasu Ammi ce ta bani jiya da zamu taho".

B

ata zauna ba daki ta jiya tana rike da hannun Autar Aunty.

Aunty Hasana ce ta cire rapping sheet din na madaidaicin, white gold din ne yayi musu maraba, da sauri Hajiya kaltume ta matso tana fadin.

"Masha Allah girma sai Dan girma wani kayan sai amale wane

jaki,lallai babban goro sai magogin karfe, irin wannan kyautar girma haka, 'yan biting bude sauran muga abinda ke ciki".

Wata ubansun Alkyabba ce baka da ratsin zare golden sai turarika masu azabar kamshi a ciki.

Jim maganar Hajiya kaltume yasa Ammah fito

wa daga daki taga menene ake dagawa murya haka?

Sarkar Hajiyar ta mikawa Ammah.

"Duba kiga Karamar arziki irin wannan daga uwar mahmud, Ashe dasu tazo gidan ta aje ta shiga tata sabgar, inga fa sarkar Nan ta tasamma wajen fifty millions wallahi Dan kwanaki

mun siyar da wata Bata Kai wannan ba wurin forty seven milion aka sayar".

Ammah rasa abin fada tayi saboda abin ya Bata mamaki to su wane irin dukiya garesu mutanen nan?.

Nan suka zauna suna ta maida yanda akayi har kusan la'asar duk abinda ya kamata sun

yi yi an bada aikin kayan garar da za'a Kaiwa Zahra Dana Iyayen mijin duk wata al'ada da ake a sokoton Ammah ta tambaya an fada mata, da yammaci suna zaune Abba ya shigo Yana fadin.

"Asma'u ku tanadi abun tarbar Baki gobe in sha Allah bakin sokoto na Nan t

afe yanzu ba dadewa Kanin Alhaji Muhammad ya kirani yake fada min zasuzo naso na hanasu duba da nisan dake tsakanin Bauchi da sokoto Amma ya nuna min a'a idan ma yafi haka zasuzo godiya ce zasu zo tunda ba aure za'a sake daurawa ba inaga ko maza ne ko kuma

Mata da maza ne ban sani ba dai sai ayi dai abinda ya kamata nace Abdul Hakeem suje da magaji a debo zabi sai a Kara Dana gidan idan yaso sai a kawo sabo Naman na gida.

"To Allah ya kaimu, ya Kuma maganar furniture's din da za'a tafi dasu daga nan?".

Sai

goben insha Allah za'a had a da kayan da kikace za'a kawo daga Bauchi Sai a tafi dasu gaba daya ai inaga hakan yayi ko?"

"Eh hakan yayi Allah ya saka da Alkhairi ya jikan mahaifa".

Ameen su Hajiya da Aunty Hasana suka fada ciki ya shige Aunty Hasana ya ta

shi tabi bayansa.

Aiki su Ammah suka Fara babu kama hannun yaro auta Ammah ta turo makota tace ya fada musu su shigo gobe za'a karbi Kaya Kuma ya fadawa mamansu mujiba idan Abbansu yana gidan ta tambaye should ta shigo zasuyi aiki.

Hajiya kaltume Bata bar

gidan ba sai kusan Tara na dare, taso a Kara yiwa Zahra gyara Amma Aunty Hasana tace a karba a tafar Mata dashi tunda Hasanarsa ta kaita gurin masu gyaran Amare a India a barta haka Nan tunda Abu ne a duhu ba'asan yanda abun yake ba".

"Eh to kema da gaskiy

ar ki Naga 'yar tawa har yanzu zubin 'yan Mata gareta babu kamar cikakkiyar mace a tare da ita".

Da haka suka rabu haka Nan taji Bata son a Kara Bata komai idan ba fruits ba gaskiya Bata son wannan tonon sililin duk da bata da tabbas na wani Abu be shiga t

sakani ba duba da tun lokacin da akayi bikin to sai dai a yanda zilai ta fada Mata bayanin da likitar Nan tayi Mata Lamarin abun dubawa ne kwarai, ita fa tausayin Zahra takeji yanda taga anyi Mata wannan gyaran tasan sai yanda Hali yayi kawai Amma da Qura

a gaba.

Washe gari da sakkon aiki suka tashi Dan tun shida Maman mujiba ta shigo ita da Aina'u makociyar itama suna gaisawa sosai da Ammah din, duk bidirin da akeyi Mama Bata fito ba ko kuma tace me akeyi babu Daya,itama Ammah ta bawa banza ajiyarta.

Karf

e Tara Mai kyau su Inna maimuna sun shigo gidan a Bauchi suka kwana saboda sunyi dare bana Wasa ba dole suka hakura suka kwana a can.

Wasu dunkuna ne aka kawo wanda Aunty Hasana ta bayar aka dinkawa Zahra express laces ne na manyan Mata Wanda suke ji da Ka

nsu na manyan kudi ta saya saboda yau masu kawo Kayan walau maza ne ko Mata ya Zama dai babu raini duk da babu inda makusa take ta ko ina kawai dai idan kana da kyau ka Kara da wanka ne.

Karfe sha biyu ta gota wasu lafta laftan motoci suka tsaya a kofar gi

dan Alhaji Jafar Mai yadi wa

Bata lokaci Mai gadi ya bude musu tunda Alhaji ya fada Masa za'ayi Baki a gidan to Yana ganinsu yasan bakinne.

Gate baba sani ya bude musu suka Sanya Mai cikn harabar gidan.

A can Kuma Zahra ce tayi make up simple ta saka fit

ted gown na rigar lace sai ta fito da ainihin structure din jikinta yake. Su dai su Hajiya kaltume dasu Inna mainuna suna zaune Basu yi aune ba sukaga an Fara shigowa da Kaya, tun suna girgawa har suka zubawa sarautar Allah Saida aka zube set goma Sha biy

u, sai kuma mata suka shigo bisa jagorancin magaji su kuma mazan suna gurin su Abba da jama'arsa.

Sannu da zuwa aka Fara jera musu mutanen Cikin parlour din tare da Basu girin zama, Aina'u ce ta ware murya ta zankada guda uku a jere abinda ya fito da su zi

lai da sahura daga Ina suke zaune a gidan, Mama ma fitowa tayi da Dan sauri tana fadin.

"Menene akeyi a gidan nan haka da uwar Rana ake ta rafsa guda.

Part din Ammah ta nufa da sauri su zilai duna biye da ita a baya, turus tayi ganin Iyayen akwatuna a zube

a parlourn,kasa daurewa tayi.

"Wannan kayan fa na waye haka?" Inna Maimuna ce ta Bata Amsa "na Amarya Zahra ne kin san mijin nata ya koma gida shine iyayensa suma zasuyi nasu bikin".

Taku biyu tayi sai ganin ta akayi a kasa ta fadi jikinta na wata irin

karkawa Nan da Nan aka yo kanta da sauri Dan Bata taimakon gaggawa.

*AUREN HUCE HAUSHI*

AISHAT ISAH MUSAH

Maman Fateemah.

08055362975

Or

09061432330

Page 80.

.....



.



.. Subhanallahi mutanen dake parlourn suka dauka, da sauri Ammah da Aunty Hasan

a suka matso gurin da Mamar ta Fadi Ammah tana fadin..

"Ikon Allah har yanzu jikin ne kenan da Baki fito ba, Hasana maza Nemo Abdul Hakeem ko Hamza aje asibiti"O.

"Gaskiya dai Kam tunda abun Yana neman ya Zama wani Abu daban".

Hajiya kaltume ta fada yayind

a wata daga cikin bakin tace.

"Anya Bata da hypertension kuwa?".

"Nima abinda nake tunani kenan gaskiya".

Ammah ta fad'a.

Cikin kankanin lokaci Hamza da imam suka shigo yayin da a waje Abdul Hakeem ta fito da mota, zilai da sahura ne suka dauketa suka nufi

waje da ita, Aunty Hasana ta rufa musu baya suka fice.

Saida komai ya lafa sannan su Hajiya kaltume suka samu Damar fuskantar bakinsu,nan da nan aka Fara sauke musu ashirin ta arziki Alawiyya da magaji Wanda Bai bi Yan asibitin ba domin yasan tsabar tashi

n hankali ne ya haddasawa mama wannan abun ba komai ba, duk Wanda yace ruwan wani baze tafasa ba nasa ko zafi bazeyi ba.

Abinci bakin waje suka ringa fita dashi, sai da bakin sukaci abinci sukayi sallah sannan Aunty Surayya ta gabatar da Kayan lefen gasu H

ajiya kaltume dasu Inna maimuna wadda tun faduwar Mama taja jikinta gefe tasan mugun nufinta ne ya Fara tambayarta tunda taga duk yanda ta dunga dakile Lamarin Zahra Ubangiji ya nuna Mata shine Arrazzaqu shike daukaka bawa duk kuwa yanda makiya suka so su

dankwafe mutum sai ya nuna karfin ikonsa a Kan abun, gashi an waya gari Zahra tayi musu wata irin tazara tamkar tsakanin sama da kasa haka tazarar take,abinda ko a mafarki ko a hasashe babu Wanda ya taba kawo hakan.

Sun godiya sosai, sannan Aunty Surayya

r ta dauko key ta mikawa Hajiya kaltume tana fadin gashi inji Ammi tace a kawowa Ammah tana gaisheta kafin komai ya lafa tazo su gaisa ace ayi Mata godiya sosai da sosai.

Duk gurin ba Wanda baiyi mamaki ba na wannan kyautar girman da aka yiwa uwar Amarya.

Matan makotan da suka shigo suka Fara bude kayan ana gani ana Sanya Alkhairi a ciki.

Aunty Mahafuza Matar Ya Ibrahim ce tace .

"Wai ina amaryar tamu ne a rakamu mu gaisa da ita kafin a kaimana ita".

Inna maimuna ce tace "tashi muje ai ba nisa tayi ba tana

Cikin dakin nan".

Tashi tayi tana fadin gara muyi sabo tun daga Nan na Zama ta farko da zata sani a cikin matan yayun mijinta".

Inna maimuna na gaba Mahafuza na binta a baya har kofar bedroom din dasu Zahra suke ita da mujiba da Yan uwanta da sukazo dasu I

nna maimunar Salima da Ibtihal, salima ce ta bude kofar su Inna maimunar suka shigo idon Mahafuzar Yana Kan Zahra wadda take zaune a Kan sofa Tasha ubansu lace Wanda ya amsa sunansa tayi wani irin fitinan nan kyau a cikinsa tana daddanna iPhone sixteen plu

s dinta tana daga sexy eyes dinta sukayi four eyes da Mahafuzar, ba shiri ta hadiye wani Abu Daya sille ya wuce Mata Bata shirya ba.

"Tabarakallahu Ahasanul kaliqin, Masha Allah" ta fada a zuciyarta, ai ita a yanda Habibinta ya fada Mata yarinyar Daya gani

a part din Ammi da yake tunanin ko budurwar mahmud din ce sai taga Bai iya bada bayanin mutum ba Sam.

Da fara'arta ta shigo tana musu sallama da fara'a Suma su salima suka amsa Mata suka gaisheta, Cikin nutsuwa da Jan ajiya da nuna sanin ciwon Kai Zahra t

a gaishe da Mahafuza din.

Gurin Zama su mujiba suka bawa Mahafuzar suna fadin.

"Ki zauna Mana ga guri Aunty".

Gefen gadon ta zauna tana duban zahra a kaikaice, haka Nan yarinyar tayi Mata kwarjini sosai sai taji duk ta Raina kanta duk da itama 'yar gayu ce

kuma ba laifi da nata daidai kyawun Amma ganin zahra sai taji tayi lakwas tunda da biyu ta nace akan saita biyo masu kawo lefen duk da mutum hudu kawai ake bukata Mata Saida tayi yanda tayi Dan taga kul uwar daka, tunda daga waje taji gwiwarta ta sace tas

an wannan da alama tafi gaban raini, to Kuma sai gashi taga itama Zahrar zahra ce ga Jan aji da alama bazata dauki raini ba..

Ganin shirun ya yi yawa yasa Mahafuza tace Amarya zamu tafi "Ni sunana Mahafuza matar Ibrahim Dange yayan mahmud".

Dan murmushi z

ahra tayi.

"Na gode Aunty Mahafuza".

Tashi tayi tana fadin.

"Nima na gode Amaryar mu sai kin Karaso naso ace Ina Cikin masu kwana mu tafi tare".

'yar dariya zahra tayi wadda ta Kara fito da sirrin kyawunta.

Bayan ta fita Ibtihal tayi wani tsalle tana fadin

.

"Yessss! Adda zahra haka nake son Kama Kai da nemawa Kai mutumci".

Wayar hannunta ta aje tana fadin.

"Ibtihal Baki Jin magana wallahi me Kuma nayi?".

"Meye ma bakiyi ba irin wannan jam class haka kamar wata saraunya fa haka kikeyi acting".

Dan murmushi z

ahra tayi tana tuna hudubar Hajiyar makwarari lokacin da take Mata karatun dangin mijinta da yanda zata zauna dasu da yanda zata kama kanta kada ta bada fuskar da za'a Raina ta, wato ta yarda da maganar da Hausawa ke fada na cewar duk abinda Babba ya hango

yaro baze hango ba ko ya hau itace rimi sai yau ta yarda da hakan, da gani wannan da salon nata rainin hankalin ta shigo Sai kuma taga an fita iyawa.

Suna Nan suna maida yanda akayi Su Aunty Surayya suka shigo Zahra ta gaishe su, Nan Aunty Mahafuza ta gab

atarwa Zahra Aunty Surayya da kanwar Abbie maman ya Abbas surukar Aishat sai 'yar kanwar Hajja kakar su Mahmud ta wajen uwa, sun yaba matuka da zabin mahmud sosai, sunyi musu Addu'ar Albarkar Aure sannan suka fita.

Aunty Surayya ce ta dawo ganin ta dawo ya

sa su salima suka fice daga dakin.

Kusa da Zahra ta zauna wadda ta sadda Kai saboda wani nauyinta taji ya kamata niyyar zamewa tayi kasa Aunty Surayyar ta hanata.

"Zauna magana zamuyi dake, kina jina Zaki shiga sabon guri da wasu mutane Wanda zakiyi rayuwa

ta har abada dasu in Sha Allah,to ki nutsu ki fashinci kowa kada kiyi garaje a cikin tafiyar ki saka hankali sosai gurin wadanda Zaki mu'amalanta babu ruwanki da kowa babu ruwanki da 'yan matan family din Nan duk yawancinsu burinsu Kan mijinki yake kada w

ata ta dauko Abu ta kawo Miki da sunan kyauta naci Kona Sha kiyi amfani dashi idan Kika cire Amminsa to sai Hajiya Inna, koni idan ban Kwanta Miki ba kada kiyi amfani da abunda Zan Baki kinji ko".

Kai Zahra ta gyada mata.

"Naji Aunty nagode in Sha Allah Za

n kula da abinda Kika fada mini".

"Yauwa Kinga pass na dinner ko? Aishat tace zakuyi waya ki bawa kawayenki na kusa wadanda Kika San zasuje tunda abune da anan ya Riga ya Dade da wucewa mu a canne yake sabo, Kuma

gobe insha Allah zaku taho mu yau zamub

i jirgi daga Bauchi zuwa sokoto tunda mu duka har mazan mu bakwai ne, Kuma anan zamu bar Hajiayarsu Abbas da Hajja Asiya tare dasu zaku wuce goben, ki kula ki daraja Ammi tana sonki matuka kinji".

Kai ta gyada Mata sai taji matar ta burgeta sosai domin a

zamanin Nan babu Mai fada maka irin wannan sai mai kaunarka.

Alawiyya ce tayi knocking ta leko tace "ana jiran Aunty Surayya". Sallama ta yiwa Zahra ta fice da sauri.

***

Tun kafin aje asibitin Mama ta dawo hayyacinta abun nata kamar iska haka Nan suka

karasa a A/E suka dubata, tambayoyi suka shiga Jero Mata akan wane abune ya daga Mata hankali har BP dinta ya Mai dari da tamanin kasan ya Kai dari da goma, dagewa tayi ita babu abinda ya tada Mata hankali, su dai su Aunty Hasana Ido ne nasu, Mama taso su

barta su dawo gida Amma suka riketa saboda sunga karfin Hali ne kawai takeyi Amma Bata da lafiya sosai zuciyarta ma tana neman kamuwa da ciwo matukar ba'ayi controlling din jinin ba, dole ta hakura aka saka Mata magani a kasan harshe aka Kuma saka Mata Kar

in ruwa aka saka Allurar barci dole tanaji tana gani barci yayi awon gaba da ita, Ammah ta kirawo Aunty Hasana ya Kai sau uku tana tambayar ya jikin nata.

Daga karshe Aunty Hasanar gida Abdul Hakeem ya dawo da ita ta baro su zilan a can, lokacin data dawo

bakin da zasu tafi sun tafi sai mutum biyun da zasu kwana suma Sana can bangaren baki.

Kayan ta tarar Makota sun shigo an bude iya Wanda za'a Iya budewa sauran kuma an tattarasu gefe guda Dan bazasu ganu a Kan kanin lokaci ba.

Yawan akwatunan Aunty Hasana

ta tsaya kallo, Saida ta shiga dakin Ammah ta tsinkayo zancen motar da Ammi ta aikowa da Ammah.

Washe gari tun sassafe motocin Kaya biyu suka dauki hanyar sokoto.

Tun dare Mama ta dawo daga asibitin, matsa musu tayi akan a sallameta dole suka sallameta du

k da Abba yace ta hakura ta barsu suyi aikinsu ta matsa ita dai babu abinda yake damunta.

Zahra har dakin bakinsu salima da Ibtihal suka rakata ta gaishe dasu Cikin ladabi da biyyaya, shi Albarka dai zahre ta shata.

Lokacin da meyin makeup ne tazo Zahra Id

o ya Raina fata da duk gani takeyi kamar wasa ne babu inda zata tafi shi dai ya dawo ya same ta kamar yanda ya Saba.

Nan da Nan taji wata irin karaya da tashin hankali ya saukar Mata ai ji tayi wancen wasan yara ne yanzu ne dai za'ayi maganar gaskiya,Cikin

abinda be wuce minti talatin ba aka gama komai tayi kyau kamar me, sai Zuba wani kamshi take na musamman, ita kanta Ammah dauriya kawai takeyi Dan ganin abun tayi kamar yanzu ne take bikin wancen Wasa tayi duba da yanzu yanda ake komai da dangin mijinta b

a kamar wancen Karon ba da su kadai su kayi budurinsu, ga tashin Hankali Sam babu nutsuwa haka tana gidan Kullum tana zulumi akan yaron kada ya gudu da yarinya ko Kuma ya gudu ya barta da ciki ba Kuma asan asalin inda za'a nema shi ba, Amma yanzu Allah s.w

.a ya gama Mata gata ya juya Lamarin 'yar marainiyar Allah ya share Mata hawayen data Dade tana zubarwa akan tozarcin da ake Mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login