Showing 120001 words to 123000 words out of 295116 words

Chapter 41 - AUREN HUCE HAUSHI COMPLETE

rufe wannan gashi c

an a kitchen a waje ki diba harda snacks din duka, Amma ki Fara karbo Mata sakon a kasuwar tukunna kuje da sadiya ta rakaki ku shiga a dai daita tunda ba nisa ga cunkoson cikin kasuwa Kuma kinsan Sameer baze Baki motarsa ba, wadda mukazo da ita Kuma Aliyu

yayi nasa gurin da ita".

Basu dauki minti talatin ba suka dawo da sakon har lokacin Zahra barci take sai da jama'a sun Fara taruwa a gidan duk dangi need sai dai-daikun Yan uwan mahaifar mujahidar.

A blender hajiyar taba mommy ta nika Mata masoron ta juyo

mata shi a cikin robar da Hajiyar ta bada a zuba a ciki.

Lokacin da mommy ta kawo Mata Hajiyar da kanta ta nufi dakin mujahidar tana fadin "Ina matar Mahmudun take?.

Barcinta take sadidan Dan tabata Hajiyar tayi tana fadin. "Tashi 'yar nan ga maganin lalu

rar ki da izinin Allah".

Tashi zahrar tayi tana bin Hajiyar da kallo lokacin data aje robar kusa da ita.

"Bude ki gani sai nayi Miki bayanin yanda za'ayi dashi".

Batayi musu ba ta bude robar taga garin masoron.

"Kina jina? Abinda za'ayi dashi ki ringa dib

a Kashi Daya bisa hudu na karamin cokalin shayi kina zubawa a ruwab zafi tafasashshe cikin kofin ok ki barshi yayi minti ashirin a ciki sai ki tace ki Shanye ruwan,haka Zaki ringa yi har ya Kare in Sha Allah ze narke yabi jinin al'adarki ya fice, ki rabu

da wannan shirmen komai ace za'a yanka mutum kamar kabewa"

'yar dariya Zahra tayi tana fadin in Sha Allah zanyi na gode madallah Allah ya saka da Alkhairi".

"Allahumma Amin. Allah ya Baki lafiya,ayi ta hakuri irin mijinki Mata Ido rufe suke nemansu sai kin

kauda Kai zaki

ç

i ribar zaman aurenki. Amma kada ki kuskura ki yarda a nuna Miki San iyawa akan mijinki, ki kula da sukarki Bata da damuwa ko kalilan ki girmama Masa danginsa da kakarsa jiya ya wannan suna gidan Nan sunzo ganin Mai sunan mijinki na wurin S

ameeru, Ni cewa nake can wurinku zasu sauka ma sai naji Sameeru na maganar su fito zasu koma a jiyan kinsan sha'anin tafiyar iska, ba wani nisa ke gareta ba".

Ita dai Zahra Jin Hajiyar take Dan ba komai ta fashimta ba.

Rukayya ce ta shigo da Abinci dasu s

nacks a babban tray tana fadin " Ai tunda naji shiru Hajiya Baki fito ba nasan kin hanata barci kawai wallahi ke idan Kika so Abu ba sauki saina Allah idan kinyi hakuri zata tashi ki bata".

"Ke tafi can waya fada Miki ana bori da sanyin jiki Baki San hadar

in wannan abun bane baya barin haihuwa fa ba dole a tari abun ba tunda wuri, wannan yarinya tubarakallah haka ai ba'aso a samu abinda ze kawo Mata cikas a zaman aurenta ba, ni tunda na ganta ta kwanta min har maganin tsarin jiki Zan karbo mata a Sanka, nan

babban gida".

Baki Rukayya ta rike tana kakabin Abun "Ikon Allah to ke Hajiya fada Miki tayi tana son na tsarin jikin? Da kike faman fadin Zaki karbo Mata".

Kafin Hajiyar ta Kara magana Zahra ta rigata.

"Haba Aunty Rukayya Ina laifin Hajiya kuwa tunda n

a sako Qafa gidan Nan Bata huta ba hidimata takeyi".

"Eh haka ne kam tunda har kasuwar kurmi ta aikeni, da girnana da komai nace bazanj ba tace nayi mata kiwa dan rabon da naje cikin kurmi tun Ina secondary Dan ma ban manta shogon ba"

Ficewa Hajiyar tana

fadin kyaji dashi idan Kaya ne".

Tashi zahrar tayi tana fadin Bari na dawo, ta fice daga dakin.

Toilet ta shiga ta Kara gyara Kanta, lokacin data fito dai dai lokacin masu kawo lefen suka karaso suma Nan da nan gudan ya dauki jama'a Dan makota ma Wanda suk

a makara suka ringa shigowa.

Ganin gidan ya kacame da jama'a yasa Zahra tayi amfani da wannan damar ta nufi hanyar soron gidan, a soron ta tsaya ta Ciro wani face mask da yake cikin jakar ta da eyeglasses dinta ta saka ta fice daga gidan.

Ba Bata lokaci ta

na fita Dan sahu Yana kawo Kai, ta dafe shi ta shige, tana fadin "Janbulo zaka Kaini".

"Hajiya sai dai drop gaskiya Dan hanyar ta baude ni rimi na nufa".

"Muje Zan baka kudin drop din".

Ta fada tana Dan leken gefenta kamar narar gaskiya, hankalinta be kwan

ta ba sai da taga sunyi nisa da unguwar, ajiyar zuciya ta sauke tana "na barka da Dr Sai ku cinye kanku haka kawai za'a sabautani saboda Kai,Wanda har yanzu bansan daga wace bahiyar ka bullo ba, ayi min sakiyar da Babu ruwa a cuceni a cuci rayuwata shi yas

a na taho da hirina idan tayi ruwa rijiya idan batayi ba ta Zama Masai"

Kafin su karasa layin su Ssjida tacewa Mai adaidaita din ya taya gurin me P. O.S zata ciri kudi.

Har kiofar gate din gidan ya kaita 10k ta bashi, cikin mamaki ya dubeta "Hajiya kudin s

unyi over dari bakwai ne kudin, Hala ke bakuwa ce?"

Gaga tayi Tana fadin na sani kaje kawai nagode Allah ya tsare".

"Na gode Allah ya rufa asiri ya kara Miki daukaka".

Tana tafiya tana fadin. "Allahumma Amin".

Ta shige gidan shi Kuma ya juya Kan mashin din

sa ya wuce Yana Fadin "Bari na koma na sallami gidan sai na Kara fitowa".

***********

Bayan tafiyar masu kawo lefen an baje anata kallon kayan arzikin da suka kawo Masha Allah kayansu sunyi kyau sosai Dan akwatuna set hudu suka kawo da manyan jakunkun

a uku har da adudu biyu.

Saida komai ya lafa sannan hankalin Rukayya ya dawo jikinta ta shiga neman zahra, abin mamaki ba zahra ba alamarta Abu kamar Wasa ya Zama gaske Nan da Nan tashin hankali ya wanzu a gidan Dan mantawa akayi da murnar wani lefe Nan da

Nan Rukayya ta Fara share hawaye.

Mommy ce ta Farayi Mata fada "Haba Rukayya menene haka Zahra Karamar yarinya ce ku shiga makota Mana ko taron jama'a ne bataso ta shiga can ta zauna ba kince toilet tace Miki zata shiga ba? Kafin ta fito Kuma bakin sun sh

igo?"

"Eh haka ne Amma Naga fitowarta harta tsaya a can daga Nan mutane sukayi yawa ban sake ganinta ba".

"Ke Zubaida maza ku shiga gidajen kusa ku duba ko can ta shiga ku kirawota".

"To mommy". Ta fada sukayi waje su uku.

Hajiyar makwarari kuwa cewa take

"Ina yarinyar nan ta shiga ko masu kawo kayan tabi suka tafi".

Wani kallo Rukayya tayi Mata "kaji Hajiya da wani zance kamar wata 'yar baby ce zahrar da zatabi wasu mutane".

"Ungo Nan".

Abu kamar Wasa karamar magana tana neman Zama babba, duk kukkuken bab

u it's Babu dalilinta komai Kama da Zahra Babu.

Mommy da Kanta ta Kira Sameer tace duk inda yake yazo yanzu tana son ganinsa.

Daman ba nusa yayi ba Yana tare da abokansa na unguwar Dan a hannun Hajiyar ya girma harya Gama secondary school dinsa.

A tsakar g

ida ya samu su mommy anyi cirko-cirko.

"Gani mommy lafiya na ganku haka?".

Hajiya ce ta Fara fadar "Ina fa lafiya ba'aga matar Mahmudu ba har makota anbi baku ko alamarta".

Mommy ya kalla. "Kamar ya ba'a ganta ba? To Ina ta shiga?"

"Allahu A'alam, da farko

abin ban dauke shi haka ba sai yanzu da naga da gaske ne yasa nace Bari na Kira ka".

"Ok, Bari naje Nan Ina zuwa"

Ya juya ya fice da sauri, cikin tashin hankali me ze fadawa Mijinta Ina ta tafi?.

Tambayar mutanen kusa masu sana'a a kofar gidan ya rinka yi

, har ya juya sai wani Mai sayar da Mai yace yaga fitowarta da face mask da glass a Ido ta hau a dai- daita sahu sunyi hanyar nan ya nuna hanyar gidan shatema.

Dafe Kai yayi cikin tashin hankali, "wannan wace irin masifa ce haka kawai an tadawa yarinya han

kali har ta yanke Shawarar tayi tafiyar ta, to tana Ina? Ina ta tafi? Ba wani ta sani a garin Nan ba ga Babu waya a hannunta, Saida ya fada masa ya fito Mata a mutum sak a wuce wannan wasan yaran ya kaita inda ya Dace a duba Masa ita amma ya gano ya yiwa H

aseena waya ta a duba Masa ita yasan karshen film din ba Mai kyau bane"

Jiki ba kwari ya koma ciki..

***** ***** *****

Hankalin Zahra be kwanta ba so sai Saida ta ganta a cikin falon gidan su Sajida, Mai aikinsu ta bude Mata parlourn tana fa

din "A'a marhabin maraba da Amarya sannu da zuwa".

Ta fada tana murmushi, tare suka shigo ciki.

"Yauwa Mama Hauwa sannu da gida, ya naji gidan naku Shiru ko su Mamar basa nan ne?"

"Wallahi sunje Rimin sumaila duba kanin Baffa bashi da lafiya,a nan ya kwan

ta a Asibitin Murtala to shine sukaje su Kara duba shi da jikin".

"Allah sarki ko kawu Musa?"

"Shine Ashe kin sanshi".

Eh nasan shi Mana, har a gidansa mun kwana lokacin da mukaje da sajida. Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne"..

"Allahumma Amin, Bari na

bude Miki dakin mutuniyar ki shiga na kawo Miki abinci can, inaga sai dare zasu dawo tunda suka Kai har wannan lokacin".

Wanka ta shiga ta Dade a toilet din kafin ta fito tana tsane jikinta da towel, lotion ta shafa ta dauko Rigar material marar nauyi ta

saka a cikin kayan sajida.

Jallop din kuskus aka kawo Mata wadda Tasha kayan lambu da pepper soup na kayan ciki da kunun aya Mai sanyi da ruwa.

Abincin taci ta koshi ta dora da kayan sanyi tayi hamdala ga Allah ta kishingida jinta take fresh idan Allah ya

kaimu safiya ta karawa motarta Mai, ganinta a araha yasa ake garata kamar kwallo.AUREN HUCE HAUSHI.

MAMAN FATEEMAH

Page 42.

_______Abu kamar Wasa har kusan karfe taran dare ba zahra ba labarinta, iya Rahane mommy ta Kira tana tambayarta kosu Rukayya s

un dawo? Dan bazata fada ba direct tace ana neman zahrar hakan dabara ce ta tambaya a fakaice.

Amsar data Bata ita ta Kara tadawa kowa hankali cewa tayi "Basu dawo ba tun fitar safe da sukayi ga zulai ma duk ta shiga damuwa tace tun yamma Ammarta ke Kiran

wayar zilan tace wayar zahara'un Bata shiga".

"Yanzu ya za'ayi kenan?"

Rukayya ta tambaya.

"Ni damuwa ta Daya kada ta fada mugun hannu Dan ma dai ba lallai ansan matar waye ba Amma yau abin tsoro ce kiransa zanyi kawai na fada Masa halin da ake ciki ko ya

san wasu 'yan uwansu a nan kanon, tunda barin Kashi a ciki baya maganin yunwa gara ya fada kawai asan Yanda za'ayi tun guri be kure ba.

Number dinsa yayi ta try Amma amsar Daya ce a rufe take.

Da kyar ya mayar dasu mommy gida har Rukayya a gidansu ta sauka

, to ta koma tacewa baiwar Allah da sukazo tare zahrar ta Bata ko me?"

Duk wani lissafi ya gama suncewa Sameer, duk wannan Abu be tashi faruwa ba Saida sukazo gidan kakarsa, ita kanta Hajiyar makwararin tashi Dan kukanta tana mitar yarinyar Nan Bata kyauta

Mata ba ta rasa a inda zatayi irin wannan shegantakar sai a gidanta.

Jiki ba kwari Sameer ya shiga gidansa, sau Daya Fateeha ta kalleshi ta dauke Kai ta cika fam da fushi tun safe Daya fice Bata Kara sakashi a idanunta ba, ta kirawo shi ya Kai sau biyar s

ai dai yace Mata gashi Nan Amma bezo ba sai yanzu wurin Sha dayan dare.

A kusa da ita ya zauna ta kauda Kai, hannu yasa ya dauki yaron a Kan cinyarta, yasa hannu Daya ya tallabota ta hada da babyn ya rungumesu, Jin ajiyar zuciyar da yake saukewa a jajjere

yasa Fateeha ta gane da matsala.

"Wai menene?"

Ta fada cikin damuwa.

"Bari kawai wlh hankalina a tashe yake, tun bayan Azzahar Zahra ta fice daga gidan Hajiyar makwarari bamu San inda ta nufa ba, duk inda muke tunanin zataje munje Bata nan".

Itama mantawa

tayi da fushin da takeyi dashi ta Fara sallallami "Yanzu Ina ta tafi? Kadafa wani Abu ya sameta kasan mutane yanzu gaskiyar su kadan ce".

Dafe kansa da yake Sara Masa yayi "Bana tunanin haka gaskiya da Kanta ta fita ta tafi kawai dai an Bata Mata Rai ne b

an Kuma yi tunanin abin yayi Mata zafi haka ba da bazan barta a gidan Hajiyar ba, amfani tayi da masu kawo lefen mujahida ana can gurin karbar lefe ita Kuma ta fice daga gidan Dan akwai Wanda ya fada min Yanda ta fito nasan da niyya ta fice abunta".

Zuru F

ateeha tayi tana sauraren mijinta.

"Ka Kira ka fada masa?"

Kai ya girgiza Yana fadin na kasa samunsa nafi one hour Ina nemansa ban same shi ba".

*** *** *** ***

Karfe Tara su Umman sajida suka shigo gidan lokacin Zahra na parlour suna hira da Mam

a Hauwa, turus Maman tayi ganin zahra ko rantsuwa tayi Babu kaffara, wannan ba zuwan arziki bane amma sai ta share tana fadin "wa nake gani haka?"

Dariya Zahra tayi tana fadin "Umman mu sannunku da hanya".

"Yauwa sannu,aike za'a yiwa sannu kin sha

doguwar tafiya".

Shiru zahrar tayi batace komai ba, kannen Sajidar ne suka Fara gaisheta suna fadin "Aunty kin rigamu zuwa munata cewa idan Ya Abba ze Kai Miki sakonki da Baffan Rimi ya bada a Kai Miki zamu bishi sai gashi Kuma kinzo"

Karamar kanwa

rsu ta janyo tana fadin "ai zakuje ko mutuniyar tunda anyi min Alkawarin zuwan".

"Eh zamuzo Aunty zahra".

Nusaiba ta fada suna Zama kusa da zahrar, yayin da Maman su ta wuce bedroom dinta tana cike da tunani barkatai a zuciyar ta.

Tana shiga jakar hannun

ta ta zuge ta Ciro wayar ta, Ammah ta Kira Dan bazata Zama uwar banza ba da alama gudowa yarinyar Nan tayi.

Lokacin da Kiran ya shigowa Ammah tana duba wasu kaya da Hajiya kaltume ta Aiko Mata dasu ne.

Ganin Umman sajida ne yasa ta aje kayan ta dauki wayar

tare da sallama.

"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".

"Hajiya ya gida ya wajen Amare? Ina ta son na Kira mu gaisa Allah Bai nufa ba sai yau, itama zahrar mun kwana biyu bamu gaisa ba".

"Wallahi kowa lafiya, Amare Kuma suna nan kusa daku

Bata jin dadi ne mijin ya matsa suzo Nan Kano a dubata ni tun safe da muka gaisa da wayar zilai ban Kara samunta ba, na Kirawo zilan ma tace min har yanzu Basu dawo ba duk ta tada hankalin ta, nace ita da ba ita kadai ta fita ba tare suke da amininsa da ka

nwarsa, Kinga duk inda suke ai suna tare".

Shiru Maman tayi kenan hasashenta ya kusa Zama gaskiya Kenan.

"Hajiya ga zahrar a gidan nan,yanzu muka dawo daga Rimi Sai na tarar da ita Ina ganinta nasan ba lafiya ba Ashe garin sukazo ta kawo min ziyara".

Jim A

mmah tayi tana jinjina lamarin.

"Anya kuwa ki dai saka Mata Ido zuwa safe kome ke nan sai ki fada min idan anzo daukarta to da sanin mijin tazo idan Kuma tace zata tafi ki hanata ki fada min na gode kwarai Allah yayi Mana jagora ya Raya Mana zuri'a".

"Alla

humma Amin". Sukayi sallama.

Zuciyar Ammah sai bugawa takeyi a hankali ta furta "meke Nan Kuma? Ni Asma'u Allah ka taimaki 'yar marainiyar Allah, matsaloli daga an toshe wannan sai waccen ta bulle Allah yayi Mana maganin wannan matsaloli yanzu kuma ko me

nene damuwar datasa ta tsallake tabar inda suke gashi ta Kama wayar ta rufe Dan ma kada a San inda take,ai kuwa zamu gauraya bazan dauki shashanci ba".

Ta hada duk kayan ta zuba a ledar da aka kawosu ta fice daga dakin ta nufi dakin Abban Yara tunda ita ke

da girki.



Saida Umman sajida tayi wanka tayi sallah sannan ta fito har lokacin suna falon da yaran direct dining ta nufa taci abinci sannan ta dawo falon.

Gaisheta zahra ta Karayi tana tambayar ya Mai jikin,

Dasu Baffa.

Sun dauki lokaci suna hira kafin

Ummar tace "Wai daga Ina kikazo ne daga can Azaren ne ko Kuma kinzo nan garin ne?"

Shiru zahrar tayi kafin tace "ganin likita nazo akan wannan ciwon marar da bakeyi duk wata".

"Ikon Allah kuma ke kadai Kika taho ganin likitan kamar marar gata".

"A'a bani k

adai nazo ba tare da Aunty Zilai Mai aikin Ammah mukazo tana can a Nasarawa G.R.A".

"Ok, to mryasa baku taho tare ba Nan din".

Shiru tayi Bata ce komai ba, ganin da Yara yasa itama ummar tabar zancen.

Kafin kowa ya tashi Zahra ta tashi tana fadin "Umma Bar

i naje ba kwanta barci nakeji"

"To Allah ya tashemu lafiya.

Basu Dade ba Suma suka shige daki Daman duk sun gaji.

Lokacin da Ammah ta shiga dakin Abban samun Mama tayi kane -kane tana ta zuba zance da kudi a hannunta masu Dan yawa da gani a gurin Abban ta

Karba, cikin alamun rashin gaskiya mamar ta Fara fadin. "Aina leka parlourn ki naji Shiru nayi zaton kina Nan wallahi Ashe Baki shigo ba"

Fuska ba annuri Ammah tace. "Eh ban shigo ba idan kin gama na dawo ta juya har Takai kofar ficewa Abban yayi gyaran

murya Yana fadin "dawo ki zauna Ina Kuma Zaki ita ta tashi ta tafi tunda ta gama abinda ya kawo ta"

Jiki ba kwari Mama ta tashi tana fadin "ai Kam na Gama Allah ya tashemu lafiya nagode Allah ya Kara arziki".

Ta nufi inda Ammah ke tsaye tana fadin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login