Showing 87001 words to 90000 words out of 295116 words
ya canza salo. Harta dauko wayar ta Sai ta ma
yar idan tayi gigin fadawa Mama kwabarta zatayi ruwa Dan a yauma Saida Mana ta karo kudi masu nauyi tace a bawa Mai gadin yanda duk abinda za'a saka shi yaji baze iya gardama ba, to idan ta koma Mata da wannan labarin amshe kudin zatayi tasan halinta kayan
ta, data Bata naira dubu gara ta bawa Dan tsubbu dubu hamsin, Sam Bata karuwa da ita saita wadannan hanyoyin idan ta aiketa tunda itace amintacciyarta ta Nan takeyin nata duk rintsi bazata so ta rasa wannan mafakar ba Dan Kusan da ita ta dogara gurin kwar
amniyar yau da Kullum nata.
*******
Saida Zahra tayi barci Mai isarta sannan ta farka lokacin biyu har da minti ashirin da hudu, da sauri ta Mike tana addu'ar tashi daga barci tayi mamaki ita fa gani tayi kamar barcin minti goma Sha biyar tayi Ashe lokac
in ya ja haka, alwala tayi tazo ta Fara sallah bayan ta idar wayar ta da dauko Ummee ta Kira cikin shauki tun dazu ta nemeta network din na garin ba kyau sai hakura tayi, Bata jima ba tana ringing aka daga ba Ummeen bace wata ce ta daga tana ta yi Mata lar
abcin gargal ita kuwa zahrar na language yafi kwarewa a Dan daburce tayi Mata bayini ta gane Ummeen ta fita masallacin Annabi sallah tunda har lokacin suna Madina basu tafi ba Kuma a yanda sukayi daga Saudi Arabia Nigeria zasuyo gurinta, sallama tayi wa ma
tar ta kashe.
Number sajida ta lalubo ta syprus tasan zata Sha mita tun ranar da sukayi ways da wayar Amatu tayi Mata buyagi ta kashe Basu Kara waya ba, har tayi ringing ta katse Bata dauka ba, Bata hakura ba wani Kiran ta karayi shima Yana daf da ze katse
aka daga.
"Haba bestie Ina ta kira kin shareni ko har yanzu fishin ne?"
Mai makon taji bestien sai muryar Fatima taji tana kwallawa Sajidar kira tana fadin "ku taho ga Amarya Zahra! Zahra" ta kirata da karfi tana murna kamar zata tsaga wayar, daya bayan d
aya suka dunga gaisawa suna ta korafin amarci Dadi ta Kama waya ta rufe wato Bata so a shigar musu rayuwa ko? Hakuri ta Basu tare da fada musu tayi missing din waccen wayar ne har sim din, sai daga karshe sajida ta karbi wayar.
"'yar duniya wato kinji dadi
n lamarin ko Kika wani shareni, ni yanzu ai yallabai Mahmud ya fiki kirki kinsan ya kirani Kusan sau uku? Daman ko Baki kirani ba Zan kiraki dazu wurin Sha daya ya kirani Wai na kiraki na lallasheki yayi tafiya ya baroki kina kuka?".
Ya fada tana kunshe da
riyar ta.
"Malama ki fito kiyi dariyar ki sosai kada ta kume Miki a ciki,da kike wani kunsheta".
Dariyar tayi da gasken sai tayi Mai isarta tace. "Dan Allah bestie mekika bawa wannan guy din Kinga yanda yayi masifar macewa a Kanki? Wlh har tausayi yake ba
ni Ni har mamaki nake idan ya kirani Yana min maganarki ranar Nan fa cewa yayi na bashi labarin zamanki a Nan syprus din wlh nayi zaton da Wasa yaki tunda nasan ba Karamin cajin kudi za'ayi ba. Amma haka na ware na rinka bashi labarin har na Gama ko a jiki
nsa, yanzu Ina aka tsaya da fatan komai ya dai daita? Dan nafi son dai dai lokacin ganawarmu muyi murna biyu graduation da naming ceremony".
"Wlh Zan kashe yaushe Kika zama haka Mai bin kwakwkwafin jama'a? to bazakiji ba an fada Miki kowa ma irinki ne ai
wlh ya Abdul Hakeem ya debo ruwan dafa kansa Dan nasan Dan bawan Allah saiya rinqa guduwa daga gidan"
Wata irin dariya ta saki tana fadin "billahil Azeem gara wata wainar data wake yarinya gyara zancen ki idan ana cin baure ba'a tona cikinsa Kuma idan ana
sallah ba'a magana".
"Wlh sharri zakiyi Masa Amma shi dai salihi ne".
"A inda salihai sukayi karanci ba".
"Mubar zance kawai tunda abun ya Zama haka".
Zahra ta fada tana cire hijabinta daga jikinta vest ce Fara Kal sai wando shima fari ai pink din kananun
flowers gashin tayi parking a tsakiyar Kan ta kashe da band shima pink, sai fito baby sak.
Gyara kwanciya tayi, tayi ringinnine da wayar a kunnenta Hira sukaci gaba da sajida yawanci duk akan auren zahrar ne. Sun dauki lokaci Mai Dan tsawo suna tattaunawa
akan bututuwa da dama kafin suyi sallama, ta nufi toilet wanka take son yi kafin ta fita cin abinci.
********
Jirginsu Mahmud a Addis Ababa Bole international airport yayi landing, daki biyu Sameer ya kama musu Nan kusa da airport din tunda a kalla za
suyi Kusan three hours.
Saida ya kaiwa Mahmud jakar laptop dinsa sannan ya nufi nasa dakin, bayan fitar Sameer Mahmud wanka yayi sannan yayi sallah maimakon ya kwanta ya Dan huta sai kawai ya bude wayarsa so yake ya ganta duk wani matsi da yayi tana manne
da zuciyarsa so yake ya ganta kafin ya kirata. CCTV ya shiga ta wayarsa duk abinda akeyi ya rinka bi Yana gani yasha dariyar karon Zayyan da wannan matar wadda ko sunanta Bai sani ba, shi yasa ya dauko shi yasan shi kadai ne cikin amuntattunsa Wanda ze Mas
a wanna aikin ba tare da an samu matsala ba.
Saida ya gama kallon ko ina na gidan yaga ba wata matsala, sannan yayi zooming din cikin bed room dinta daga ita sai vest purple da wando skintight kanta tayi parking da purple din band sai tayi wani irin kyau n
a musamman, kura Mata ido yayi Kamar ya warto ta yakeji, turare ta dauko tana fesawa a jikinta. Nan ya shiriri ce Yana kallonta knocking din da akayi Masa ya katse Masa abinda yakeyi, umarni ya bada a shigo Sameer ne sai ma'aikaciyar hotel din dauke da tr
ay na abinci sai karairaya take shi har dariya abin nata ya bashi, me Kamar zahra yaushe irin wadannan zasu burge shi, bayan ta wuce ne ya dago ya dubi Sameer "kada ka qara zuwar min da irin wannan a rinqa bawa maza suna kawo min kawai".
"Noted sir"
Ledar
dake hannunsa ya Mika Masa Mai tambarin wani boutique ne, sannan ya aje Laptop dinsa a kusa dashi Yana nuna masa wasu ayyukan da ya Gama yanzu, sun jima suna aikin kafin sameer ya fita saboda lokacin tashinsu ya kusa cika shi kuma Mahmud ya ciro kayan da
nufin sakawa.
Saida Zahra ta Gama feffesa turarenta sannan ta dauko after dress ta zura ta yane kanta da gyalen sannan ta nufo parlour, zalai ta samu tana 'yan goge goge duk da ba wani datti a gurin, gaishe da zilan tayi tana Mata sannu, ajiye mofar tayi
"Allah ya taimaki uwar dakina ga abincin can nayi Miki abinda kikeso faten dankalin turawa da pepper soup din kifi"
Zama Zahra tayi tana fadin "Kai Amma wlh na gode kwarai da gaske shi yasa nake yinki kinsa favorite Dina wlh".
"Ai shi yasa na cewa Ammah k
ada a wani dauko yarinya tun daga Mubi Nima na isa na zauna dake saina kirawo Kanwata Alawiyya ta cigaba da yiwa Ammar kafin Allah yasa yallaban ya dawo, ai ni har zaman wanka ni zanyi Miki Koda kuwa bakwa garin Nan ne".
Dan smile tayi kawai bata ce komai
ba saima ta canza akalar zancen.
"Ni Kuma Aunty zilai kin mikawa mutumin Nan abinci kuwa?".
"Ai tunda na Gama na zuba na hada harda ruwa da lemo na mika Masa. Naga Dan gayu ne beyi kalar masu gadi ba".
Dariya zahra tayi tana fadin "Aunty zilai kenan shi M
ai gadi har Kama gareshi".
Yana da kama Mana Wai Kinga wannan din?"
Na ga wani dai dazu ban sani ko shine Wanda aka Kira jiya cikin dare".
" Cikin dare Kuma?"
Kai ta gyada "Mata kusan Hakan tunda Sha biyu ta wuce ya kirawo wani kawai umarni ya bashi yazo
garin Nan da safe kinsan bakwai a Nan tayi mass nifa mutumin Nan wlh tsoro yake bani na kasa gane kansa".
Dan murmushi zilan tayi tana kallon Zahra "kiyi hakuri uwar dakina a hankali Zaki San komai a kansa badai Kuna tare ba da sannu Zaki gane shi din waye
, kici abincin sai muci gaba da hirar idan kin gwma".
Bata k'i Shawarar zilan ba ta tashi ta nufi dining ita Kuma zilan ta nufi dauko Mata ruwa da mutuniyarta farm fresh, sai da ta Gama cin abincin sannan ta dawo parlourn gurin da tabar Aunty zilan sukaci
gaba da hirar su, amma Kusan hankalin Zahra yana Kan Mahmud haka Nan sai taji ya fado Mata ta yarda da ake cewa sabo turken Wawa, yanzu da baya Nan sai taji duk kewarsa ta kamata, tun dazu take duba waya ko zataga kiransa Amma shiru tasan tsakanin Nigeria
da inda zasu indai da gaske chinan zasu da nisa a kalla jirgin zeyi landing a Ethiopia da India yaci ace ya kirata Amma shiru har Yanzu ko lfy? ta ayyana a cikin zuciyar ta.
Ganin tunanin Zahra yayi zurfi yasa zilan ta tashi tana fadin Bari nayi wanke wan
ke tunda kin Gama da kwanukan"
Tayi hanyar kitchen, ita kuma ganin tunanin ze dameta yasa ta kunna tv ta kamo MBC MAX tana son finafinan su sosai,Aunty zilan ma data Gama Zama tayi sukaci gaba da hirar jefi jefi har aka Kira magariba suka shiga sallah. Tan
a addu'oin yaumiyya na cikin du'aul mustajaba ne kira ya shigo wayarta da sauri ta dauko tana duba Mai Kiran Ummee ta gani da sauri ta daga tana fadin "Ummeena"
Amsawa tayi suka gaisa Ummeen ke fadar an fada Mata ta kirane nan tayi Mata fadan rufe layi da
tayi,nan Zahra taji kuka yazo Mata, Nan da Nan Ummeen ta rude tana tambayar ta ko tana da damuwa ne ta fada Mata cikin kukan tace "Ummee Shima fa wannan daga kawo ni gidansa ko sati daya ban rufa ba ya tafi ya barni Wai aiki zejeyi uk" shiru Ummee tayi k
afin ta shiga rarrashinta da kalamai na kwantar da hankali da nuna Mata ba lallai ne hasashenta ya kasance gaskiya ba, kada ta damu saboda ita har Umara tayi bayan auren tayi mata addu'oin samun nasara akan dukkan lamuranta, sannan ta yi mata fadan ta k
iyayi yawan kukan Nan bashi da ma"ana, daga karshe tayi Mata albishir zawan su next week harda Mama Hanifa da Aunty Nawwara duk suna hanya Daman ko Bata sameta a waya ba zata kira Hajiya Asma'u tasa a fada Mata. Murna ta shigayi Kamar tayi me har Ummee na
Mata dariya Nan da Nan ta ware ta shiga lissafo abinda takeso Wanda za"a taho Mata dashi.
Bayan maga wayarsu da Ummeen Ammah ta Kara kira lokacin tana tare da Abba.
Tana zubawa Abba Dan fruit salad wayar ta dauki ringing Abban ne ya dauko ya duba 'yar dar
iya yayi Yana mikawa Ammar wayar tare da fadin.
"Uwata ce ke kira". Ganin Kiran ze yanke yasa Abban karbar fruit salad din yaci gaba da zubawa Yana fadin "A dauki Kiran uwata kada ya yanke".
Daukar tayi tana amsa sallamarta da gaisuwar da take mata.
"Ammah
yanzu Dan Allah bazakizo ba Kuma Aunty Hasana ma fa batazo ba fa Kuma Ni sonake na ganki".
"Ikon Allah yanzu ke saboda Allah sai a ganni a gidanki a irin wannan kwanakin ai sai a dauka ba lafiya Auntyn taku dai zatazo Daman jiya take fad'a zata shigo ta g
anki tunda mijin naki baya Nan, ai Mahmud din ma ya turowa Abban ku da sako ba dadewa ta whatapp yace sun sauka lafiya, ke dai abinda nakeso ki kwantar da kiyi Masa biyyayya kinji".
Ta fad'a tana rarrashinta.
"To Ammah, daman kira nayi na fada Miki Ummee
tace next week zasu shigo Nigeria nasan zata fada Miki".
"To Allah ya kaimu Daman munyi maganar shekaran jiya har take tambayar meya faru da taki wayar? Nace ta Dan samu matsala ne, ga Abbanku yace a gaishe ki"
"Lah! Ammah Daman yana Nan amma ba'a fada mi
n ba Bashi na gaishe shi"
Sun gaisa da Abban har Yana Dan tsokanar ta, tunda a wani bangaren kakace a gurinsa, Nan yake fada Mata mijinta yace ya tafi da motarta Kano tana airport Dan haka daga nan Zuwa jibi za'a kawo Mata daya motar ta gurin Muttaka, godi
ya ta yiwa Abban sannan sukayi sallama.
Ta jima Bata aje wayar ba, tana juya maganarsu da Ammah Wai ya fadawa Abba sun sauka wato ita da bayaso Bata da matsayin da ze kirata ko sako ya fada Mata sun sauka, kenan Daman duk abinda yake Mata a 'yan kwanakin N
an yaudara ce Dan ya lasa Mata Zuma a baki ya gudu ya barta da kewarsa inda ta godewa Allah be lalata mata rayuwa ta gudu ya barta ba wlh duk rintsi sai ta bar Kasar Nan ta koma Jordan, Dan tasan Allah kadai yasan halin da Ammah zata shiga idan bawan Allah
n Nan yaqi dawowa....
✨✨✨
✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI.
✨✨✨
✨✨✨
Story
&
Written
by
Naman Fateemah.
page 31
______________Har aka Fara Kiran sallar insha'i tana zaune tana faman tunanin makomarta, tashi tayi tayi
sallah, nan Kan sallayar ta kwanta tana lazimi a haka har barci yayi awon gaba da ita.
Tun zilai na saka ran fitowa Zahra har ta hakura ta shige ciki duk da ba barci take ji ba, tun yamma take ganin zahrar wani sukuku Kamar marar lfy.
Zahra ba ita ta farka
ba sai Kusan daya da kwata, tashi tayi tana mik'a tare da salatin Annabi, duk jikinta ciwo yake Mata hijabin ta cire tare da after dress din ya Zama daga ita sai vest da wandon toilet ta shiga Bata Dade ba ta fito canja kayan jikinta tayi da rigar barci t
a Kashe wutar Mai haske ta kunna bed side camp tayi shiru tana istigifari ga Allah s.w.a da Salati ga fiyayyan halitta Annabin Rahama duk yanda tunani yaso ya bijiro Mata saida ta kawar dashi kawai ta fawwalawa Allah lamarinta tasan duk rintsi Yana tare da
ita, a haka har barci yaci karfinta.
Da safe har zulai ta Gama share share da mofin Zahra bata fito ba ganin shirun tayi yawa yasa tayi tunanin buga Mata kofa kada ta Zama babbar banza zuwanta ya Zama marar amfani rabonta da yarinyar nan tun magaribar jiy
a Bata Kara sakata a idonta ba, kofar bedroom din ta nufa tayi knocking taji shiru lokacin Zahra na Wanka, Kara bugawa tayi still dai shiru taji Nan da Nan hankalinta ya tashi kada fa wani abu ya Sami yarinyar Nan ta shiga uku.
Tana Nan tana shawarwarin t
a bude ta gani ko lafiya? taji alamun motsin tafiya daga ciki da sauri ta Kara knocking din, Zahra da towel a jikinta ta nufo kofar ta bude.
"A'a Aunty zilai kece? Ina kwana?"
Ta fada tana goge gashinta daya jike gurin wanka.
"Lafiya kalau, naji ki shiru n
e tun daga shiga sallah jiya harna gaji da zama Baki fito ba, gashi yanzu ma naji shiru har Ina kokarin Kiran Ammah na sani koba lfy ba".
Ta fada tana kokarin barin gurin "na gode da kulawar ki Aunty zilai wlh jiya barci ne ya daukeni a nan Kan sallaya ban
i na farka ba sai Kusan karfe biyu na dare".
"Ikon Allah kice kwanan kasa kikayi da sanyin tayis Bai Kama ki ba, tunda Naga gidan naku ko Ina sanyi Kamar gidajen larabawa".
Sai Kuma ta rufe bakinta da hannu.
"Kin jini ba wlh na manta Ashe gidan nasu ne".
D
ariya Zahra tayi "Kayya Ina wani balarabiya anan ai da uba ake ado Ni bafulatana ce kalarce dai na dauko tasu Amma idan masu abun suna yarawa wani abun sai kallo Dan ma Allah ya hadani da jarimin uba da yayi tsayin daka gurin ganin na iya yaren saboda na s
amu saukin mu'amala da dangin Mamana".
"Wannan gaskiya ne Allah ya sakawa Alhaji da Alkhairi ya biya Masa bukatunsa na Alkhairi"
"Allahumma Amin".
Zahra ta fada.
"Me za'a dafa miki? Mu dai nayi Mana nida bakon ku".
"Wai bakon mu wato dai bazaki ce Mai gadi
n ba ko?.
Dariya tayi. "Wlh baya Kama da masu gadi Kinga kuwa ai bana ce Masa ba".
"Haka ne ki dafa min indo mie da cooker oat kawai".
"To an gama sai kin fito".
Ta fada tana juyawa zuwa main parlour din yayin da Zahra ta koma ciki.
*************
DAMAGAR
AM NIGER REPUBLIC.
Cikin takun ta na nutsatstsiya kuma wayayyar mace 'yar gayu ajin karshe ta shigo parlourn tana sanye da doguwar rigar madam gezber kalar peach sai gyalen kalar light yellow touching din flowers din dake jikin kayan sai takalmi plat Mai
azabar kyau shima light yellow din tun kafin ta karaso kamshinta ya hade gurin.
A hankali ya dago ya dubeta har ta karaso gurinsa, tattara aikin da yake yayi ya Maida hankali a kanta lokacin da take Zama a kujerar dake gefen da yake.
"Sannu da aiki Yaya b
arka da Asuba".
Ta fada tana sadda kanta kasa Bai amsa ba Jin shirun yayi yawa yasa ta dago kanta ta dube shi, ita yake kallo.
"Yanzu abinda Kika zaba kenan Zainab da girmanki da hankalinki ki zazzage jiki ki baro dakin mijinki kizo ki nemi guri ki zauna m
ijinki yayi rarrashin duniyar Nan kinqi ki saurare shi daga karshen ma Kika zabi ki dawo Nan Damagaram saboda a Yamai uncle Yousoufu ya nuna Miki rashin kyautatawar abinda kikayi shine kikayo yajin Nan ko?.Ni tunda tubus ne