Showing 138001 words to 141000 words out of 295116 words
tana rike
da Ayyan sunan da ake fadawa yaron kenan, Fateeha na fadin " Masha Allah, Amarya kin Sha kamshi sai yau Allah yayi haduwarmu?".
"Wallahi kuwa Aunty, barka Allah ya Raya Mana".
"Amin ya Rabbi, nifa na dauka da Rana zakizo mu yini muna hira Amma sai naji sw
eetheart Yana fadar Wai gaku Nan a harya".
Da gyarawa Ayyan riko tayi tana zame rolling din kanta. "nima bansan da fitar ba sai dazu da yamma yace zamuzo nifa naso ya barni nazo suna lokacin Amma yace a'a saiya dawo zamuzo".
Har Fateeha ta bude Baki zatayi
magana ta tuna gargadin Sameer akan sakin bakin magana yace ta iya bakinta akan abida Zata fadawa zahrar.
"Kinsan komai nufin Allah ne sai yau ne ya kaddari mu hadu,munga sako Allah ya saka da Alkhairi yabar zumunci, Kaya irin haka kamar za'a bude Masa Bo
utique dasu, wasu ai har ya shekara biyar sannan yayi amfani dasu, Kinga wannan material din da Kika sako min me kalar peach wata sister dina da za'a yiwa biki ta kwallafa rai a kansa tana son tasa ranar dinner da taje kasuwa kasa sayensa tayi 350k 4yrd, s
aita gano na sayar Mata da nawa tunda suna gidan safwan ya kawo kayan".
Ita dai Zahra Shiru tayi Dan ji tayi wani bambarakwai tunda ita dai bataga wasu Kaya ba, amma saita wayance da fadar "lah ba komai ai dan "komai nayiwa d'ana ban fad'i ba, Allah dai ya
Raya Mana yayi musu Albarka".
"Allahumma Amin".
Knocking akayi daga waje, umarni Fateeha ta bayar wata yarinya 'yar matashiya ta shigo da babban tray da kayayyakin motsa Baki a Kai ta aje ta gaishe da zahra ta juya ta fice.
Suna cikin hira Sameer ya Kira
yace zahra ta fito zasu wuce.
Har gurin mota suka rakosu suna ta godiya, jikin window din da zahra take ta Dan leka tana "Fadin zamu mu shigo in Sha Allah mu yini a gurinki tunda ni bakizo Mana da rana ba".
"To ai ba laifina bane Kinga niba sanin garin n
aku nayi sosai ba sai a yanda akayi Dani".
Dariya Fateeha tayi "to ai kin Zama 'yar kanon kema tunda gaki a cikinta Baki San ranar barinta ba".
Sameer ne ya yiwa Fateeha magana ta yiwa zahra sallama, ta bude back seat ta saka ledar dake hannunta.
Direct ga
ndun Albasa suka nufa gidan mommy, zahra Bata tashi Jin abinda tayi da Bata kyauta ba Saida suka shigo harabar gidan mommy din.
Dan marairaice Masa tayi da fuska a Karon farko ta riko hannunsa.
"Please me amor ka shiga Kai kadai wallahi kunyar mommy nakeji
bazan iya shiga ba".
Ta fada a shagwabe kamar zatayi Masa kuka.
Saida ya gyara parking sannan ya maido hankalinsa gaba Daya gurinta.
Meya hadaki da mommy Kuma da kike Jin kunyar haduwa da ita?".
"Jiya fa harda ita a gidan Hajiyar oga Sameer".
Mai gadi ne
ya karaso Yana gaishe da Mahmud tare da jera masa godiya wadda zahra Bata Dan isalinta ba, fitowa Mahmud yayi suka gaisa da Mai gadin,abinda ya tilastawa Zahra fitowa, gaishe da Mai gadin tayi ta Dan Fara tafiya duk da Batasan inda kofar shigar take ba.
Gu
rin wasu kujeru data gani ta nufa ta zauna da alamar Kamar Baki ne suka tashi daga gurin.
A Nan ya sameta ya Mika Mata hannunsa ta kama ya mikar da ita tsaye, "zo muje ciki dare Yana karayi kin zaunar damu a gurin Fateeha kome kuje fada ma oho Allah yasa d
ai ba gulma kujeyi ba".
Kafin tayi yunkurin bashi amsa daga bayansu sukaji maganar Rukayya "lah wa nake gani kamar Ya Mahmud da Auntyn mu?"
Da sauri zahra ta zame hannunta ta juya baya tana Fadin "wallahi Aunty Rukayya nayi fushi saboda Allah saiki taho b
ako sallama".
"Ayya sorry wallahi Nima karfina akafi dole tasa na taho kinsan Ya Sameer ba sauki shine ya tattaroni ko wanka fa sai a gidan Nan nayi".
Ta juya ya Mahmud Ina yini an dawo lafiya?".
"Lafiya kalau Ruky ya kikaji da 'yar rigima Ashe Kuma yaji
tayi muku ta gudu".
"Wallahi kuwa ya Mahmud ai jiya nayi kuka kamar ba gobe tashin hankalina Daya idan ta B'ata me za'a fada maka idan ka dawo Ashe kana hanya".
Baki zahra ta zubura tana kiftawa Rukayya Ido.
Kafin yayi magana sukaji magana daga bayansu.
"
Waye nake gani kamar DANGEN SHUNI!?"
Da sauri Mahmud ya juya itama zahra juyawar tayi Jin kamar muryar data sani ce take Fadin hakan.
"Lah! Lah! Lah! Wa nake gani haka? Zakariyya Daman ana ganinku, rabon da mu hadu tun zuwana na karshen kontagora".
Zahra c
e ta Matso tana Fadin Lah Ya Abba, Kaine ina yini?"
"Lafiya kalau ya kukaje gida? ai da safe na Kira Rukayya take fada min bakwa tare ta dawo gida".
"Eh wallahi, yasu Umma?"
"Suna lafiya daga Ina haka?"
Dan kallon Mahmud tayi kafin tace Masa "daga gida mu
ke Mommy mukazo gaishewa".
Kusa da Mahmud ya matso Yana Fadin "DANGEN SHUNI! Allah ya taimaki manyan kasa. Daman ana ganinku haka available? Gaskiya na zama lucky. Daman wallahi neman number ka nakeyi nayi interview da kamfanin ku na Nan Kano last two wee
ks Amma har yau ban samu number ba, kasan lamarin kasar Saida wakasani,to ya akaji da jama'a?"
.
"Lafiya kalau Alhamdulillahi, Rukayya ki bashi number ta zamuyi maganar later, ko kana Shirin Zama sirikina ne?".
'yar dariya yayi "Hakan nake fata ai zuwan z
ahra jiya Ni Alkhairi ya zamar min".
Dan Jim Mahmud yayi, me kenan zakariyya kenan brother din sajida ne?
"Anyway we'll talk later in Sha Allah, madam let's go".
Sukayi sallama da Ya Abba suka nufi ciki zuciyar zahra fal murna wato duk abinda Allah yayi ak
wai hikima a cikinsa, wannan dalilin ne yasa ta tattara ta nufi Janbulo Ashe ita zata Zama dalilin haduwarsu.
Saida suka gulewa ganinsu sannan Ya Abba ya kalli Rukayya, "Daman Kuna da relation da DANGE?".
"Eh aminin Ya Sameer ne tun suna secondary School,
yanzu haka shine P.A dinsa ai jiya zahra da muka dauko daga can wife dinsa ce an samu wani incidence ne tayi tafiyar ta can Janbulo din".
Baki sake yake kallon Rukayya abin jinsa yake kamar Almara badan ya gansu tare ba baze taba gaskata zance Rukayya ba,
gaskiya he's surprised to ai shi ba haka maganar tazo Masa ba daga bakin sajida.
"Wai kina nufin DANGE ne mijin zahra?"
"Eh Mana shine, Wai Daman Kasan Ya Mahmud din ne?"
"So sai kuwa farin sani, muna haduwa da a kwantagora a unguwa Daya ma kuwa, ai kak
arsa ta wurin Babansa 'yar can ce Nima kakata 'yar can ce Ummar mu kadai ta Haifa a Rimin sumaila Aurenta ya mutu ta koma gida, duk 'yan uwan Umma suna can kwantagoran na Niger state da Abuja, kinsa meya daure min Kai kuwa?"
Girgiza Masa Kai tayi alamar A
'a.
"Cewa fa akayi ita zahrar an aura Mata Almajirin wani malami da yake a unguwarsu saboda duk Wanda yazo ze aureta sai an fasa Auren"
"Nima naji kadan daga labarinta gurin ya Sameer to ga dai mijinta Nan sauran bayanin Kuma ban San yanda akayi ya faru b
a, tunda ya Sameer ba fada mana zeyi ba".
A parlour suka Sami mommy da kannan Rukayya Mata Bilkisu da Husna sai karamar yarinya 'yar Auntyn su Sameer Afra.
Tunda suka shigo zahra ke sadda Kai kasa da gaske nauyin mommy take ji, gaisuwar yaran suka ringa
amsawa da gudu Afta ta nufo zahra tana Fadin "welcome Aunty" ta shige jikinta tana tattabata.
Hannunta zahra ta riqe suka karasa gurin da mommy ke zaune yayin da su Husna suka koma dayan parlourn.
A kasa Kan carpet suka zauna, a tare suka gaishe da mommy
din, ta yiwa Mahmud sannu da dawowa sannan ta Dora da godiya, hidima da akeyi da Sameer. Zahra ta kalla ganin sai sadda Kai tajeyi yasa tace.
" 'ya ta ko jikin ne Naga bakya walwala sosai?".
Yana ji yayi fuska Bai tankaba ba dai iya shegen da tayi ba kena
n jiyan saita magantu da bakinta.
Bata yarda sun hada Ido ba tace.
"A'a ba komai mommy lafiya ta kalau".
"To Masha Allah haka nake son ji, kina jina ki saki jikinki Dani ki daina Jin nauyi na kinji, ni uwace idan kina da damuwa duk da bama fatan hakan ki
sameni ki fada min ki daina yanke hukunci da kanki".
"To in Sha Allah bazan qara ba na gode". Ta fada tana Wasa kitson Afra kanana Yar dasu.
Tashi mommy tayi tana fadin "Bari na fadawa Alhaji kunzo sai ku shuga ki gaisa yaga 'yar tasa wadda bai sani ba".
T
a nufi nufi wani corridor dake hannun dama.
Bata dade ba ta dawo tana fad'in "Mahmud kuje Yana parlourn kasa". Saida aka yiwa Afra wayo da chocolates sannan ta yards tabi mommy dakinta ita Kuma zahra suka nufi bangaren Abban su Sameer din.
A Nan suka same
shi a parlourn Wanda yaji kayan more rayuwa dai-dai da shekarunsa, babban mutum mai cikar Kamala, fari sosai kamar irin buzayen nan, a Nan zahra ta gano inda Aunty Rukayya ta samo farin ta dan mommy dai irin wankan tarwada din nan ce shi yasa tayi mamakin
Jin Rukayya kanwarsa ce uwa Daya uba Daya.
Da madaukakiyar fara'a ta taresu Yana fadin "Masha Allah sannunku da zuwa, ka kyauta Mahmud daka kawo min yarinyar nan kaga na Riga Alhaji Muhammad ganinta ko? masha Allah ku zauna".
Ya fada Yana nuna musu seat d
in Zama, basu zauna ba a kasa suka zauna suna gaishe shi, ya amsa cikin sakin fuska, da gani shi mutun ne Mai yawan fara'a.
"Allah yayi muku Albarka ya kade fitina a tsakaninku naji Dadi kwarai daka kawo min ita, yarinya ayi hakuri da juna kinji, mijinki
na jama'a ne Saida hakuri kiyi Masa biyayya gwargwadon iyawarki, Kai Kuma ka kula da lamarin ta kada ka yarda wani ya wulakanta maka ita amana ce suka baka, a yanda kaje musu ba kowa ne ze dauki yarinya kamar wannan ya baka ba, to ka kula da ita sosai ka B
ata dukkan farin ciki tayi rawar gani, daga karshe Ina rokonka abinda ban taba saka Baki a cikin duk kwaramniyar da akayi a baya ba sai yau, kayi hakuri ka koma gida ba girmanka da mutuncinka bane haka ai ba'a fushi da iyaye duk rintsi albarkarsu ake nema
kome ka Zama indai kana da iyaye yaro ne Kai, nasan an bata maka Amma idan ka duba ko tukwicin wannan yarinyar da Allah yayi Maka ai sai ka huce ka nuna godiyarka ga Allah Daya baka ita, Kai ba karamin mutum bane a kasar Nan Koda kuwa a shekaru kake da ka
rancin girma, kaje gida ka hada hankalin ka guri daya, Allah yayi Albarka ya Kara daukaka numa ganin sakonni mun gode kwarai da gaske, idan Kuma naji Shiru baka koma ba da kaina zanyi abinda baka so ayi din, Dan ko shekaranjiya Saida Hajiya Inna Tasha kuka
nta a dakin Nan Ina amfanin irin haka ai musulmin kwarai da yafiya aka San Shi kaji Mahmud ayi hakuri ayi afuwa Allah yasa son masu yafiya".
Tunda Alhajin ya Fara magana jikin Mahmud yayi sanyi da gaske duk badak'alar da akayi ko uffan Bai tofa ba sai yanz
u Kuma yasan baya raba Daya biyu damuwar da yaga hajiya Inna a ciki ta Dame shi.
Cikin ladabi Mahmud ya Fara magana. "Nagode Abba in Sha Allah Zan koma, Nima nayi wannan tunanin ba fushi nayi dasu ba sune dai sukayi fushi dani, Ina son su huce ne tukunna
kada na koma a maido hannun agogo baya".
"Kai haba wannan maganar ai babu ita to ai itama zahara'u ta zamar maka garkuwa, ki tashi ku tafi dare ya Farayi ga yanayin sanyi Allah yayi Albarka ayi kokari ayi yanda nace".
"In Sha Allah Abba".
'yar karamar Leda
Fara Alhajin ya mikowa Mahmud Yana fadin "ungo rikewa 'yata".
Godiya sukayi Masa Sosai suka nufi kofa Yana saka musu Albarka.
Lokacin da suka fito Rukayya ta shigo suna tare da mommy.
"Aunty Rukayya har Ya Abban ya tafi?". Zahrar ta fada tana nufar inda R
ukayyar take.
"Eh ya wuce tun dazu".
"Ok shikenan da sako Zan bashi gurin Ummah Amma na Kirata a waya".
Sallama sukayiwa Mommy Rukayya ta rakosu har gurin mota da ledar da mommy ta bawa zahra kyautar dangin turaren wuta dasu humra.
Da sukazo fita kudi masu
yawa taga ya bawa Mai gadin gidan sannan suka wuce, tunda suka fito daga parlourn Alhaji Abban su Sameer Mahmud yayi dif da alamar anyi Masa famin wani Miki a zuciyarsa.
Ganin haka yasa zahra ta Kama kanta itama.
Titin gidan Bashir tofa suka fito gasu ca
n sun fita gidan Buhari, sahad store taga ya shigo ya nemi guri yayi parking sannan ya bude Yana Fadi ki jirani ina zuwa ya wuce ciki.
Bai Dade da shiga ba wata mota tayi parking kusa da tasu, gurin akwai wadatar hasken da yasa kana iya ganin Wanda yake c
ikin mota.
Ba zato ba tsammani kawai idanun Zahra suka sarke Dana Musbahu Wanda ya fito daga gurin driver suna tare da wani Guy da alamar dayan irin ya'yan hutun Nan ne, da gani Suma sayyayar sukazo, da sauri ya nufo gurinta jikinsa har rawa yakeyi Yana fa
din "Zahra!" dai-dai lokacin Kuma Mahmud ya fito tare da ma'aikatan gurin sun dauko Masa Kaya sun nufo motar, shi Kuma wannan gayen Yana ganin Mahmud yayi wata irin zabura ya nufeshi ya rungume shi jikinsa na wata irin tsuma Yana fadin "Ya Mahmud Ina ka s
higa ka barmu".
✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
MAMAN FATEEMAH.
Page 48.
___ Rungume juna sukayi sosai, kuka ya saka Masa kamar karamin yaro da gani ba karamin missing dinsa yayi ba , Shima Mahmud Jin wani Abu yake yi a zuciyarsa badan n
amijin duniya bane da Babu abinda ze hana shi zubda hawayen shima, yayi kewar Faruq sosai saboda sunyi wata irin shaquwa dashi ta ban mamaki,duk da ba uwa daya ta haifesu ba Kuma kusan sa'anni ne Dan baifi wata hudu Mahmud ya bashi ba, Amma Yana bashi gi
rma sosai,duk abinda yakeyi hankalinsa dari bisa dari Yana Kan musbahu Wanda yayi mutuwar tsaye shi Bai karasa gurin zahrar ba, shi kima bai dawo baya ba, me yake Shirin faruwa ne? wannan din meye dinta yasan dai tayi aure ance wani k'olo aka aura mata, t
o Ina auren kada dai gudowa tayi ta shigo yawon duniya?.
Ita ma zahrar ji tayi komai ya tsaya mata, har wata zufa taji tana tsatstsafo Mata a jikinta abun kamar a mafarki, gurin da su Mahmud suke ta kara kallo still suna yanda suke Saidai gaba Daya hankali
nsa Yana gurinsu fuskarsa ba annuri ko misqala zarratin kamar dade duniya be taba dariya ba, sadda Kai zahra tayi dan ji tayi wani irin tsoronsa na shigarta tuna karonsu tayi wanda ya kusan cinye mata lebe, kasa tayi da kanta jiran taji ya zata kaya.
Bayan
sa ya Mahmud ya ringa Dan bubbugawa da tafin hannunsa Yana fadin.
"Haba Faruq meye na kuka da girmanka da komai Kai ba mace ba, ka nutsu ka share wannan hawayen, akwai mace fa a kusa damu tana kallonka, wallahi wata Rana sai tayi maka gorin ragon maza"
Ya
fada Yana sakinsa da sauri yama duban masu rike da kayan daya saya a hannu "sorry na barku da Kaya kuyi hakuri Dan Allah mu karasa ku saka a mota"
Yayi gaba yana yiwa Mushahu wani shegen kallo, Faruq na rike dashi ram Kamar Yana gudun ya bace Masa.
Back
seat Faruq ya bude suka zuba kayan,Faruq din ne ya curo kudin da baisan yawansu ba ya Mika musu sukayi godiya suka wuce bakin aikinsu.
Jikin motar Mahmud ya tsaya Yana facing din musbahu da fuskar shanu.
"Dan Allah Ya Mahmud kana Ina ne duk tsawon wannan l
okacin? Kuma wacece wannan da kuke tare?"
Fuska Babu annuri Kona sisin kwabo ya Maida dubansa Kan Faruq din "Idan ka Gama abinda kazoyi ka sameni a Bawo road komai dare Ina jiranka". Ganin yanda mahmud ya daure fuska yasa yaja bakinsa yayi shiru be kara t
ambayarsa komai ba.
"Ok. Zan shigo yanzu ma in Sha Allah, Nima yau na shigo around four thirty, yanzu ma uncle mushahu na rako, dan yayar Mamee ne gashi nan,bari nayi masa magana ku gaisa be ganeka bane".
Da hanzari Mahmud ya daga masa hannu "pls Faruq no
need". Ya fada yana dhugewa motar, abinda ya daurewa Faruq kai kenan, wai Ya Mahmud ne yake driving da kansa, sai yake ganin kamar an canza masa Ya Mahmud dinsa da wani.
Saida ya fice daga harabar gurin sannan Faruq ya karaso gurin Uncle dinsa yana fadar
"Yanzu fa a hanya muke maganar Ya mahmud da kai ashe yana kusa damu wallahi ba wanda ya zaci yana kasar nan, abinda ya bani mamaki wannan Babyn da suke tare a sanina da Ya Mahmud baya harkar mata gaskiya, sai dai ban sani ba ko bacin rai ya saka shi yin hu
lda irin wannan dasu".
Faruq be ankare da shi kadai yake zubarsa ba sai da ya kai aya yaji Musbahu be tofa masa ko A ba sannan ya dan taba shi.
Firgigit yayi alamun yayi zurfi a cikin dogon tunani.
Dogon numfashi yaja yana yiwa Faruq duban tsanaki, kafin y
ace.
"Faruq waye wannan nake gani kamar Mahmud?".
"Shine mana baka ganeshi bane?".
Wani gumi yaji nan da nan ya rufe shi tabbas Shiya gani a cikin hotunan da Najib ya turo masa na daurin Auren zahra, ya dade