Showing 225001 words to 228000 words out of 295116 words
aikin Dana kasa yinsa a Cikin kankanin lokaci meya rage kuma? sai mu tattara mu tafi inda mukafi wayo Nima nasan nayi aure na huta da ragaita mu fuskanci rayuwa kuma, badan nayi alkawarin kawow
a Ammi ke a yarinyarki ba Aida yanzu muna Shirin tarbar babyn mu ko ba haka ba?"
Wannan furucin nasa shi ya ankarar da ita akwai fa sauran Rina a kaba, Nan da Nan wani tsoro ya kamata Nan ne fa karshen maganar, a Nan ne me afkuwa fa zata afku,tunda gata a
sokoto har dakin mahaifiyarsa saura da me ya rage kuma?.
Cikin shagwaba ta Fara fadar "Ni dai ka daina wannan maganar gaskiya wallahi ni Ina Nan kusa da Ammina ai ba muyi haka da kaiba nifa tsoro nakejiiii..."
Wani special smile ya sakar Mata duk da dak
in dimmer light ce Bata hanata ganin yanda dimple dinsa ya lotsa ba.
"Wani abu nace zanyi Miki ne da zaki Fara tsorona? Ki zana feel free Dani har abada babu cutarwa a tsakanin mu, kin manta Abba da Baba Malam Amanarki suka bani?".
Kai gyada Masa alamar eh
.
Cikin jikinsa ya sakata Yana fadar muyi barci da sauran lokaci duka yanzu one thirty five am".
Kafada ta make tana kallonsa ta gefen ido ita fa da abinda yake figitata gaskiya.
"Dan Allah ka tafi kada kaja mini Ammi fa tana Nan kada ta ganka nidai babu r
uwana wallahi".
"Nace Miki ki kwantar da hankalinki Amma Bata Nan fa tana gurin mijinta itama to Kinga Kota ganni ai ba wata damuwa ko?".
Ita dai barci rabi da rabi tayi a kunnenta aka Kira sallar farko data biyu tana jinsa ta tashi ya shiga toilet ya fito
ya zura jallabiya Daya zo da ita Cikin ledarta ya Dan shafi gefen fuskarta wadda tayi fayau a Cikin Dan hasken dake dakin.
"Tashi lokacin sallah yayi, Zan wuce masallacin daga can zanje gurin Hajiya inna, jiya Baki ganta ba ko lokacin kin gudo tazo gidan
Nan Wai zata tasani a gaba mu tafi Wai na daina zaman nan. Kin amince nayi nesa dake?".
Jin za'a tada sallah yasa yayi sauri ya fice daga dakin, Karan rufe kofa yasa Ammi dawowa ta bude kofarta wadda shigarta dakin kenan Dan yallabai na tafiya masallaci t
a nufo part dinta, bayansa kawai ta iya gani saboda saurin da yakeyi na kada ya rasa raka'ar farko, jinjina Kai tayi tana fadar.
"Dole ayi yanda za'ayi ku tattara ku Kama gabanku badani za'ayi wannan dibar Albarkar ba, wato abinda general ke nufi kenan Day
a tilastani zuwa gurinsa"
Sallah ta tayar ta zauna zaman azkar da lazimi Ala ala take shida da rabi tayi ta Mira Niger, Saida ya dai daici lokacin dawowa daga masallacin yayan nata sannan ta Kira shi.
Yana ganin Kiran yasan ba lafiya ba Dan Yana dagawa ya
Bai saurari gaisuwar da take masa ba ya Fara fadin.
"Zainab lafiya? Meya faru kuma?".
"Wallahi ba komai Yaya sai Alkhairi".
"To Alhamdulillahi, lfy kalau ya yaran da Mai gida"
"Kowa lafiya, daman Mira nayi na fada maka danka ya dawo harda tsarabar Mata ak
a Mata aka bashi tana nan sunzo ita da 'yar uwarsa can ya Kai Mata ita"
Sai kuma ta dauko masa Asalin dalilin kiran nasa shima supporting dinta yayi harma ya Kara da fadin dole a hada da babbar mace su tafi tare kamar zefi girma da daraja a gurin Iyayen na
ta, sunyi sallama akan idan an samu tickets dinsu damagaram to sokoton zasuyi waya wata irin nutswa taji ta saukar mata, gara ayi a wuce gurin.
Da gari ya Fara haske zahra ta tashi daga Kan sallayar da tayi sallah ta ninke ta kintsa gurin wanna tayi ta shi
rya Cikin rigar material Mai budedden dinki San rigar Bata Kama Mata jiki ba tayi rolling da gyalen material din Nan da Nan ta gyara dakin ta fesa roomfreshner ta fito Cikin so take ta gaishe da Ammi Amma Bata San takamaimai Ina ne dakinta ba sannan kuma B
atasan da wane Ido zata dubeta ba, tana kokarin juyawa ta koma kenan kofar dakin Ammi ta bude ta fito Shar da ita tana baza kanshinta da mamaki a fuskaerta ta fito tana fadin.
"Masha Allah, harkin tashi kenan?"
Ta tambayi Zahra.
Da sauri Zahra ta tsuguna
tana fadin.
"Ina kwana Ammy".
"Lafiya kalau ya bakunta?".
"Lfy kalau".
Ta fada tana Wasa da gefen gyalen da tayi rolling, ta kasa hada Ido da Ammi din.
Ciki Ammi ta koma tana fadin
"Shigo nan magana zamuyi dake"
Zahra ji tayi gabanta ta yanke ya fad'i, j
iki ba kwari tabi bayan Ammi ta shiga gefen gado Ammin ta nuna Mata ta zauna amma ta Kiya ta zauna a Kan carpet din dake gaban gadon tana jiran taji abinda za'a fada Mata.
Zama Ammin tayi tana karewa zahra kallo yarinyar tana wani irin kyau Mai daukar hank
ali.
"Kina jina Fateemah number mamanki Zaki bani ina son nayi magana da ita".
"To Ammy gata"
Ta Fara karanto Mata harta cika.
"Tashi kije zuwa anjima Ina Jim zakuje unguwan insha Allah Amma Bari nazo muje ku gaisa da Abbie dinku".
Ammi na gaba zahra na bi
nta a baya suka nufi katafaren part din Abbie compound din ba kowa silent da alamar gidan bashi da yawan hayani kowa Yana gurinsa a kame sai munafurci fall a cikinsa a parlour suka sameshi tunda suka shigo zahra ta sadda Kai kasa har kusa da inda yake zaun
e zahra ta karasa ta tsuguna har kasa ta gaishe shi, Cikin muryarta Mai nutsuwa, albarka dai zahra Tasha ta gurin Abbie da godiyar abinda iyayenta suka yiwa gudan jininsa, cewa yayi ta zauna sosai ta zauna ya ringa yi Mata tambayoyin tun tana dari dari das
hi harta dan sake dashi, lokacin da zasu dollars din America ya Bata raffer biyu ya Bata a Leda.
Ammi ta karbar Mata Tama godiya.
Har suka dawo Basu hadu da kowa ba ba Karamin Dadi Ammi taking da faruwar hakan ba, suna shiga suka samu masu aikin girki da s
hare -share.
Zahra Bata koma sama ba gurin Aunty Aishat ta wuce yayinda Ammi ta nufi kitchen.
Auntyn kawai ta Sami ta tashi yaran duk Basu tashi ba, waya takeyi saida taji tace gata Nan ma Bari na Bata, wayar ta mikawa Zahra tana fadin
"Bari nayi wanka tu
nda Allah ya kawo min ke bana son na shiga wanka ba kowa a Musa dasu*
Wayar ta Kara a kunne tana sallama, amsawa yayi Yana fadin.
"Pls My preccious Kina jina, dan Allah anjima da yamma ki biyo Sister Aishat kuzo tare ki gaishe da Hajiya inna Kuma na cika w
ani alkawarin Dana dauka tun ranar Dana bar gida nayi shi to shine nakeson cika shi ai asan zaki tayani mu cika alkawarina ko?".
Ya fada da sigar rarrashi.
I *AUREN HUCE HAUSHI*
09061432330
Or
08055362975
AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fa
teemah
Page 77
.............karfe bakwai dai dai mahmud ya baro gidan Hajiya Inna, bayan yayi wanka,dole tasa yazo gidan tunda a gidan Ammi baya da kayan sakawa ya duba baiga komai ba be sani ba ko canza musu guri akayi ko bayar
wa tayi abinda be bi ba'asi ba kenan yaga gara ya taho Nan ya shirya kawai, shigar kananun Kaya yayi ya fito Shar dashi, Bai koma gurin Hajiya Inna ba duk da albishir din da tayi Masa na sinasir da tasa ayi Masa da pepper soup din kafafuwan shanu.
Yaso
ya shiga gurin Abbie Amma gurin Amminsa zaya har yanzu bakinsu Bai Saba ba jiya da zummar suyi kwanan zaune ya shigo sai kuma aka samu akasi ya bige da allurar barci.
Ta kofar baya ya shigo part din Ammin har ya Haye sama Bai hadu da kowa ba dakin da
Zahra ta kwana ya bude ba kowa sai kamshinta Wanda har ya Fara kama dakin, komai tsab ba tamkar ba'a kwanta gadon ba, kofar ya janyo ya nufi dakin Ammi yasan a irin wannan time din Bata ciki turo kofar yayi da sallama shiru sai kamshi kawai ke tashi a daki
n.
Wani sanyin dadi ya ratsa shi jinsa yake kamar an sauke Masa wani katon dutse daga kansa, a tsakiyar dakin ya tsaya Yana tuno wasu lokutan baya da shigo cikinsa tamkar mahaukaci Yana magiya Amma ko gezau Ammi Batayi ba Saima tsallakewa da tayi ta wuce t
a barahi a durkushe, Amma yau gashi ya shigo cikinsa da walwala da Aminci ba bacin Rai ba tashin hankali.
Kwanciyarsa yayi a Kan sofa Yana fashi "Alhamdulillahi Ala kulli halin".
Yayi zaman kusan minti talatin kafin yaji alamun bude kofar a Hankali ya cira
Kansa daga wayarsa da yake duba sakonnin whatapps, Ammi ce ta shigo tunda ta shigo master parlourn ta tasan ya shigo gurin Bata Kara tabbatarwa ba Saida ta hauro saman Dan kamshinsa na daban ne.
Tsayawa tayi a gurin tana Kare Masa kallo, Masha Allah gani
tayi ya Zama Babba ya cika Ido kenan jiya ganin tsoro tayi masa gashi ya Kara yin wani fresh dashi da gani ya samu nutsuwa ba kadan ba.
Aje wayar yayi ya taso ya nufota inda take tsaya murmushi yaki barin Bakinta ta Kuma kasa dauke idanunta daga kansa.
Ba
wata wata mahmud na zuwa ya shige jikinta Yana fadin.
"Ammina fushi kike Dani ko? Nasan zakiyi fishi dani, gani Nazo kiyi min duk hukuncin Daya Dace Dani in dai Zaki yafe min, Dan Allah kiyi hakuri Nima bansan me yake faruwa Dani ba, Sam bana kaunar ko sun
an garin nan naji an fada bana Kuma son naji ko sunan Wanda na sani in dai Yana Cikin family wallahi".
Zamewa Yayi ya tsuguna ya rike kafafunta sai hawaye.
Dan duk'awa tayi ta kamo hannunsa ya taso jansa tayi kamar Karamin yaro har gefen katafaren gadonta
ta zaunar dashi itama ta zauna.
"Waya fada Mata Ina fushi da Kai? Ko alama dama ma banyi fushi da Kai ba sai yanzu da Ubangiji ya amshi rokona ya share min hawayena, bakayi min komai ba ko kayi ma na yafe maka duniya da lahira, Allah yayi maka albarka ya b
aka kariya daga sharrin dukkan wani abunqi, yanzu Ashe kana Bauchi state kayi zamanka akayi ta nemanka a turai da kasashen larabawa?".
"Ammi Nima fa wayar gari kawai nayi na ganni a garin bansan ta Yaya naje ba, Saida Habib Wanda ya ganni a yashe a kasa ka
rkashin bishiyar gamji ya fada min a halin daya ganni nayi mamakin to ta Ina nabi naje can? da kafata naje ko kaini akayi? duk ban sani ba, Ammi Ina jinfa na rasa hankalina na wasu kwanaki ko watanni, Ammi hatta magana fa daina yinta nayi sai dai Ido Ina J
in abinda ake fada Amma bana iya bude bakina na mayar mutanen Nan ba Karamin jihadi sukayi ba gurin ceto rayuwata, Idan malam dawo har Azare Zan kaiki ki yiwa Baba malam godiyar abinda sukayi min kudi dai bazasu iya biyansu ba sai dai Allah mutane ne su ma
su karamci". Nan ya zazzage mass
Mata duk irin rayuwar da yayi a Azaren har ya zauna a dakin waje na amajirai.
Baiyi zato ba yaji shashshekar Ammi.
"Subhanallahi ! Haba Ammi me yasa Zaki Bata hawayenki abin fa ya Riga ya wuce, Ina fada Miki ne kawai saboda
ki Kara yi min addu'a saboda bamu San me goben zatayi ba".
Knocking din kofa akeyi mahmud ya bada izinin shigowa.
Aishat ce da suhailat suka shigo itace Mai bin batool.
Da murnarta ta Karaso sai Kuma tayi turus tana kallon Ammi dake share hawaye Aishat m
a jikinta sanyi yayi.
"Meya sameta take share hawaye?
Aishat din ta jefawa mahmud din tambayar.
Ammin ce ta Bata amsa
"Ba komai Hussein ne yake fada min halin rayuwar Daya shiga tamkar marara gata harfa so akayi a haukata min d'a a banza wallahi Ina isti
gifari ga Ubangiji kafin na fada, dama wani Allah ya bawa dukiyar Nan bashi ba da yake da kananun shekaru irin haka, wallahi da nasan wannan condense milk din itace sila Dana yiwa jama'a unguwa rabonta an wuce gurin,to ba haka zanen kaddarar take ba sai ha
kuri".
Suhailat ce ta dan matso kusa da mahmud tana fadin.
"Sannu Ya Mahmud ya jikin naka?"
"Jiki da sauki suhailat ya karatun kin Gama ko?".
"A'a da saura sai next year in Sha Allah".
"Allah ya taimaka".
"Amin"
Suka fada gaba daya.
Aishat ce tacewa mah
mud "kaje Abbie Yana nemanka a parlournsa na part din nan, Ammi kema yace a Kai masu abin break fast can kamar na mutun bakwai".
Mikewa yayi yana fadin "Bari naje Ammi".
"Jeki ki fara hada abinda za'a shigar part din Abbie din keda sauda da Batool Kice i
ya Halima ta Zuba pepper soup din kayan Cikin Nan a babban warmer sauran ta saka a fridge".
"To Ammi"
Waje suhailat din tayi da sauri.
Saida suhailat din ta fice shima ya nufi kofar Yana Daf da ficewa Aishat tace masa.
"Ka fada Mata wacece zahra a gurinka
Naga alamar ba iya playing match din zakayi ba".
Tsaye yayi shi Bai fice ba shi kuma bai juyo ba, sai Kuma ya juyo ya dawo a Hankali ya zauna a gabanta ya sadda Kai da gaske wani irin nauyinta yakeji Wanda Bai taba tunanin zeji kwatankwacinsa ba a tare da
ita, a Hankali kamar baya son yin magana ya furta.
"Ammi ga zahra Nan an bani aurenta a Azare, tun watannin baya nace saina kawo Miki ita idan ta kwanta Miki a matasyin suruka ki saka Mata albaka ki kaita dakinta da kanki idan Bata yiiki ba ki saka a may
arwa da iyayenta ita a Basu hakuri, duk hukuncin da Kika yanke na karba da hannu bibiyu".
Yana gama fada Bai jira yaji abinda zata fada ba ya tashi ya fice da sauri Dan ba Karamin kokari yayi ba gurin kinar bakin waken fada Mata ba.
"Eh to da dai hakan ya
fi a mayar musu da yarnyarsu tunda akwai alkawarin da nayiwa fulani, Ina ga sai dai suyi hakurin gaskiya"
Abinfa ya iya jiyowa kenan daga bakin Ammin tasa bai it's cewa komai ba ya fice.
Daga shi sai Wanda ya halicce shi suka San abinda yake ji a kasan Z
uciyarsa.
Aishat zatayi magana Ammi ta daga Mata hannu dole ta kame bakinta daga abinda tayi niyyar fada.
"Kuje kiyi serving din ku kafin na fito, idan kun Gama ki hadawa yarinyar Nan kayanta Wanda kikece min tsaraba yasa akayi Mata nafi son tabar gidan Na
n kafin wani tsegumin ya fito".
Sororo Aishat tayi tana duban Ammi wadda ta tashi ya shige toilet kirjinta na bugawa da sauri da sauri.
"Allahumma Ajirniy fiymusibati, wannan wane irin tashin hankali ne Kuma? Allah ka kawo sauki".
Fita itama Aishat din tay
i jikinta a mugun sanyaye, bedroom dinta ta nufa ta yiwa Zahra magana suka fito tare, da kyar Aishat tayi ta maza ta danne zuciyarta sukaci abincin tare da su suhailat duk da basa cin abinci da wuri Amma dole tasa tunda Umarnin Ammi ne.
**
Ammi najin fit
ar Aishat ta fito daga toilet din ta dauki wayar ta Kira number data karba a gurin zahra, Bata so Kira a irin wannan lokacin na safiya ba amma dole tasa hakan.
Lokacin Ammah na kitchen Musaddiq ya kawo Mata wayar yace kiranta akeyi, tana wanke hannunta wa
ni Kiran ya shigo Saida ta goge hannunta ta karbi wayar, bakuwar number ce.
Dauka tayi tana amsa sallamar tana ficewa daga kitchen din ta barwa Alawiyya aikin, gaisawa sukayi da Ammi kafin Ammin tace.
"Ko Hajiya Asma'u ce maman Fateemah Zahra?".
Sai Ammah
taji gabanta ya Fadi ana ambatar sunan zahra.
"Eh nice, Allah yasa lafiya?".
Dan murmushin da Bata shirya ba ya kwacewa Ammi.
"Lafiya kalau sai Alkhairi,sunan Hajiya zainab daga Nan sokoto mahaifiyarsa Mahmud mijin Fateemah".
Cikin nuna jin Dadi da tsantsa
r fari ciki Ammah ta Fara fadin.
"Masha Allah! Hajiya ya gida ya akaji da jama'a ai jiya ta fada min suna Nan naso na karbi number ki mu gaisa sai tace min wai bazata iya tambayar mi ba, to yau naso na karba a gurin shi mijin nata mu gaisa".
"Kai haba babu
komai muya Kamata mu tako muzo muyi godiya yanzu ma bamu fasa ba wata dai Alfarma nake nema akan 'yata yau komai dare suna Nan bisa hanya zasuzo tare da 'yan uwa na sai anzo daga Nan an daukar min ita an kaita dakinta kamar kowace Amarya ba Wai a wayi gar
i a ganta a matsayin matarsa ba bana son ayi Mata wani duba na daban kinsan Yana yin kowa ne family da irin nasu matsalolin,duban irin kalubalen da aka fuskanta a Nan din kafin barinsa gida, naso ace wani nawa yayi Miki wannan bayanin to basa kusa kiyi hak
uri nayi rashin kunya akan Dan Fara".
Ta fada tana 'yar dariya irin gentle din Nan.
Itama Ammar yin tata tayi, tana fadin.
"Na fashimta kina dai son kankarowa diyar taki mutunci ne ko?"
"Gaskiya dai Kam Allah dai ya saka Miki da Alkhairi kinyi abinda duk u
wa ta gari zata yiwa yarinya mace Hussein ya fada min komai, mun gode da Karamancin ku garemu kin dauki yarinya kamar wannan kin bashi ba tare da kunsan asalinsa ba, sai nazo har gida nayi godiya in Sha Allah".
Sukayi sallama kasake Ammah tayi tana lissafo
maganganun su da mahaifiyarsa Mahmud daga ji ba wata Babbar bace sosai sai dai tasan kanta da alamar Allah ya karbi Addu'oin ta Wanda take ba