Showing 207001 words to 210000 words out of 295116 words
cikin tashin hankali ba Wanda yaga hawayenki
sai yanzu da asking ya I gaban gashi".
Share hawayen tayi tana fadin "
dole nayi kuka ni kadai nasan dacin Dana ci a lokutan baya da dararen Dana Raya akan ubangijina ya dubi Lamarin yaron nan ya juyo min da hankalinsa gida".
"To godiya ya kamata ki yiwa
Allah Daya amshi addu'ar ki ba kuka ba".
Wani murmushi general yayi yana duban Mustapha.
"Ni bansan lokacin data aje karar 'ya'yan fari ba da ko me zakayi musu Bata daga Kai ta dubeka amma yanzu dibi yanda take Kora bayani Kamar ba ita na".
"Kan barta tayi
Yaya ai taking jarunta ma ba uwa duka ba, yanzu Yaya kenan za'ayi? Da nida madam zamuje next week amma dole mu raba tafiyar a yau Zan shiga neman visa ko nawa Zan bayar saina samu nan da jibi in Sha Allah Zan tafi Indian Zan kadi shi mu taho gida da izini
n Allah. Amma dan Allah kada a fadawa Hajiya Inna wallahi idan taji cewa zatayi kafarta kafa ta".
"Kaje kayi shiri zanyi magana akan visar taka, ka Zama cikin shiri kawai".
Tashi Ammi tayi ta shiga ciki ta barsu suna tattaunawa akan Lamarin.
*****
Saida z
ahta tayi barci Mai isarta sannan ta tashi, wanka ta shiga tana fitowa lokacin magariba ta kusa kawo jiki, tayi mamakin dogon barcin da tayi.
Lotion kawai ta shafa sai roll-on da tasa sure sai body midt da normal turaruka da take amfani dasu designers na k
amfanin Alharamaini, rigar atamfa ta saka simple style A shape ta yafa Karamin gyale sai tayi wani sansanyan kyau, a hankali ta bude kofar ta fito tana takunta gentle ta shigo parlourn Aishat ta gani a zaune da Abulkhairi a gefenta tana koya masa homework,
kafin tayi sallama har sansanyan kqmshinta ya jewa Aishat.
Dago Kai tayi tana amsa sallamar da Zahra tayi.
"Masha Allah!"
Abinda Aishat ta fada kenan Dan babu karya yarinyar ta hadu ta ko Ina macece ga asalin kyau Dan gaske, murmushinta Mai kayatarwa zahr
a tayi Mata tana fadin.
"Sannu da hutawa Aunty".
Hannu Hanan ke dagowa Zahra tana zillo daga cinyar mamanta.
Daukarta tayi tana Zama daga dayan gefe Kan wata kujerar.
"Yauwa sannu, Zahra ko?"
Kaita gyada Mata alamar eh.
"Kinsha barcin gajiya, ga abincinki
can Kan table muje kici kin kwanta da yunwa, bro yace na fada Miki yaje Asibiti sai dare ze dawo".
"Ok, nagode kiyk zamanki Bari muje da 'yar gidana Aunty ki bani ita Dan Allah Ina sonta".
Dan murmushi tayi idan mijin da Zaki aura ya amince ki dauka Ni taw
a Mai sauki ne na Baki".
Gaba tayi tana dariya kasa-kasa ta nufi dining din save da Afnan.
Sun Dade suna Hira da Aunty Aishat har barci ya Fara Kama Zahra sannan tayi Mata sallama ta nufi inda akayi Mata masauki, bayan ta wuce Aishat da Dade tana auna La
marin Zahra a zahiri Sam batayi Kama da yarinya marar tarbiyya ba ko masu budedden idanu Amma tayiwa tafiyarsu da Dan uwanta Question mark, idan ta tuna da irin warning din da yayi Mata kafin ya bar gidan.
"Gata Nan amanace a gurinsa shi yasa na kawo ta Na
n inda zata zauna safe, ki kula sosai nasan halin sayyid a Kan mata duk da kince yayi tafiya to Koda za'a samu akasi yazo bana nan, to ki fada masa yarinyar nan da mijinta Dan muna komawa za'ayi bikinta ya dauke idonsa daga kanta idan Kuma ba haka ba za'a
iya samun matsala.
"Maji ma ganj, an binne tsohuwa da Rai"
Ta fada a fili.
A Nan taci gaba da Zama tana jiran ta inda Dan uwanta ze bullo, wurin Sha Daya da minti goma ya bude ya shigo gidan, ya yi mamakin ganin Aisha Ido biyu.
"Ashe dai Hali yana nan, yan
zu Dan Allah bakiyi barci ba".
"Naka wasa ne kana tunanin Zan iya barci banji komai daga gareka ba Nima ban Amayar maka da abinda ya faru bayan baka nan ba".
"To ai shikenan Bari nayi wanka na fito inaga kwanan zaune zamuyi yau".
Ya shige ainihin dakin da
yake sauka idan yazo wani aiki kasar bata yarda ya sauka a hotel ko Daya daga cikin gidajensa, inda Allah ya taimakesu Abbas Dan kanwar Abbie ne Kuma sa'anni suke da yayunsa gashi tasu tazo Daya da mahmud sosai Dan kusan tare suke aiwatar da ayyukan kamfan
onin Abbie.
Bai Dade ba ya fit Yana baza natural kamshinsa ya zauna yana fadin hada min coffee sai zance yafi tafiya dai dai".
Ta tashi ta nufi kitchen tana fadin. "Bari na hada coffee maker yanzu na kawo maka".
Tashi yayi ya nufi dakin da Zahra take, a ha
nkali ya tura kofar a kwance a tsakiyar bed din ya hangota da wayar ta a yashe a gefe da gani batasan lokacin da barci yayi awon gaba da ita ba.
A hankali ya tako har gaban gadon Yana Kare Mata kallo a cikin dim light din dake dakin, Dan sunkuyawa yayi dai
dai lips din ta ya Bata light kiss ya shafa gashin kanta a hankali, wayar ya dauke ya Dora Kan bed side ya gyara Mata blanket din ya rage karfin A/Cn ya tofa Mata Addu'oi ya ja Mata kofar ya fice yana Jin wata irin kewarta.
A tsaye ya samu Aisha da kallon
tuhama ta bishi, yana kallonta Sarai yayi Mata fuska.
"Bani idan ya Zama ready".
Ya fada yana Mika Mata hannu.
Kada hakuri tayi ta kalleshi idi cikin ido.
"Wai wacece wannan yarinyar a gurinka? Kuma meye dangantakarka da ita Naga ka shiga inda take alhalin
ba muharraminta bane Kai?".
Ta fada tana tsare shi da Ido amma zuciyarta sai dokawa take Bata fatan abinda take sak'a Mata ya kasance gaskiya.
"Ple Aisha zauna ki nutsu ki tambayeni duk abinda ya shige Miki duhu".
Bataki tasa ba zaman tayi tana Kara jadda
da Masa tambayarta akan dangantakarsa da Zahra.
"Wai meye damuwar ki da ita ne na fada Miki 'yar uban gidana ce, daga haka me kike son ji Kuma?"
Lokacin da suke wannan maganganun ita Kuma Zahra kishirwa ta tasheta Karamin fridge din cikin dakin ta duba Bab
u ruwa a ciki Wanda Kuma Auntyn ta shigo Mata dashi dazu ya huce bazeyi Mata dadin Sha ba. Kofa ta bude ta fito da niyyar zuwa kitchen ta dauko ruwan ta saka ma a fridge din dakin, maganganu ta rinka jiyowa kasa kasa da farko har tsoro ya kamata sai daga b
aya ta ringa jiyo maganar Mahmud ne da 'yar uwarsa.
Abinda taji ya masifar daga hankalinta.
"Na fada miki babu komai a tsakanina da yarinyar nan kina ganin Zan iyayin gaban kaina nayi Aure ba tare da sanin iyayena ba? ki rubuta ki aje duk abinda Ammi ta ya
nke a kaina na karba ita zata nemar min matar aure da kanta, idan kin tuna ta taba fada tayi min Mata a Niger,Wadda har aka kawota tayi sati biyu a lokacin Abbie ya Hana maganar to yanzu zanje natsuguna a gabanta na nemi yafiyar abinda nayi Mata Kuma ta z
abar min duk wadda tayi Mata Zan karba da hannu biyu tunda ni dai babu Wadda na gani ta kwanta min da sunan Aure, Kinga gara ita ta zabar min da kanta"..
Ai jikin Zahra karkarwa ya fara me yake nufi duk abinda yake Mata pretending ne ba gaskiya ba kenan? D
a kyar ta Kai kanta dakin Dan tana shiga ta zube a kasa tana fadin .
Naga ta kaina Ni Zahra Ashe ni kadai nake kidin girbina bani da wata kima da daraja a idanun Dan tahalikin nan?.
* AUREN HUCE HAUSHI*
MAMAN FATEEMAH.
09061432330
Or
09055362975
Page 71
..
…
....
Sai da Zahra tayi kukanta ta bawa uku Lada sannan ta share hawayenta tana hakurkurtar da kanta, lallai irin wannan cin fuskar da ciwo ita meta rasa da yake gudun nunata a matsayin matarsa? Wai 'yar ubangidansa, To ita Kuma zata Kama Kanta
in Sha Allah ba Kuma zata nuna taji hirar nan tasu ba.
"Ya ubangiji ka shiga cikin lamarinta ka Bani hakuri da dangana bisa jarabawar da kake jarantata da it's Dan isar fiyayyan halitta Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w.".
Ta fada a fili tana tashi daga ind
a ta zauna tana kissima abubuwa da yawa a wannan karo.
Amma dole ta nemi tudun dafawa dole ta iya Kanta tunda abun yazo da cin fuska har ze ringa gudun hada kansa da ita.
Ranar barci dai sai barawo, kwana tayi tana nafilfili da rokon ubangiji mafita.
Baya
n tayi sallar Asuba ta koma ta kwanta lamo batajin zata iya fadawa kowa wannan maganar zatayi hiding din kayanta taci gaba da addu'ar samun mafita a gurin lillahil wahidul Qahhar ya shiga duk lamuranta.
Da safe kin fitowa tayi har Aunty Aishat ta biyota da
ki, Tana ganinta Zahra ta tashi zaune tana fadin.
"Ina kwana Aunty, Ina Afnan da Abul?"
"Lafiya kalau, ya bakunta Kuma? Afnan Kuma Bata tashi ba sai takai twelve tana barci in dai ta farka da Asuba, shi kuma Babana ya tafi school"
"Ok. Allah sarki".
Zahra
ta fada tana Dan Jan blanket din zuwa jikinta saboda yanda rigar barcin take sai a hankali.
Dan zama Aunty Aishat din tayi gefen gadon.
"Ki tashi ki shirya kiyi break yau zamu shiga Asibiti a duba ki,tun jiya nayi Mana booking na ganin doctor din, kinsan H
ussein sai a hankali idan yaso Abu to babu sauki bare Naga ya dauki lamarinki ba Nan kusa ba".
"Nifa Aunty ki fada masa na warke tun a Nigeria fa,na biyoshi ne kawai saboda na duba jikin Baba Malam,Kuma wallahi azumi nakeyi yau".
Tsare Zahra tayi da Ido sa
i taga yanayin yarinyar ya canza ba kamar jiya ba, Amma dai batace komai ba ta tashi tana fadin.
"Bari na fada masa".
Ta fice duk zuciyarta babu Dadi da gaske yarinyar tayi wani irin collapse Wanda Bata San dalilnsa ba.
Tunda Aishat ta wuce yace duba tsade
dden agogo Rolex dake hannunsa, shifa jiya da kyar ta iya barci ba tare da ita ba a jikinsa sau uku Yana zuwa kofar yana jinta bam da key a rufe.
Sai Zuba Ido yake yaga ta bullo, Maimakon ya gansu su biyu sai yaga Aishat ita kadai ta dawo.
Kasa hakurin ta
karaso yayi ya tashi ya nufi inda take.
"Tana Ina Kuma? Lokaci fa Yana tafiya nifa tun seven thirty na shirya".
Wani kallo tayi masa ganin duk ya wani rude.
"Tace ita babu inda zata ita ta warke, kuma da azumi ta tashi bazatayi break ba".
"What!! Bata da
hankali ne? wane irin ta warke duka last week fa tayi ta fama da bleeding duk ta daga min hankali, shine yanzu zata fadi haka, salon mu koma Kuma wata matsalar ta taso, tasan halin Dana shiga a wancan lokaci Bari naje na sameta".
Ikon Allah Aishat ta tsay
a tana kallo, lokaci Daya ya daga hankalinsa ya wani birkice, Wai me taji Yana fada ne? Me kalamansa suke nufi idan ba Rami me ya kawo zancen Rami.
Da sauri ta rufa Masa baya duk ya wani susuce lokaci Daya ita ba taga abin daga hankali ba tace Bata so Amma
lafazinsa sun sakata a kokonto ba Dan kadan ba.
Da zafinsa ya Kama handle din kofar sai dai tayi locking dinta, a zafafe ya Fara dukan kofar Yana fadin.
"Precious me kike nufi da baza kije Asibitin ba? kina son ki tayar min da hankali ne ko? maza bude ki
fito mu tafi tun jiya aka Gama komai".
Tsayawa Aishat tayi turus Jin kalaman da yake fada Wai ko ya manta a Ina yake ne?.
"Previousss...."
Ta fada a hankali tana girgiza Kai komawa tayi tunda Allah baisa ya ganta ba.
Ita Kuma Zahra tana jinsa yanda ya amba
ci precious sai taji wani irin bacin Rai ya lullibeta wata harara ta zabgawa kofar tana gunguni a ciki.
"Saina shayar da Kai ruwan mamaki saika karyata kanka da kanka Wallahil Azim, Ni Zahra nafi qarfin cin fuska gurin 'yan uwanka saina saiwa kaina kimar d
aka Zubar min sai ka nunawa duniya ni wani bqngare ce ta rayuwarka".
Toilet ta shige taba iska ajiyarsa.
Kasa hakuri Aishat ta dawo, Bata karasa inda yake ba daga dan nesa dashi ta tsaya tamkar a yanzu ne ta biyo shi. "
"Wai menene na tada jijiyar wuya, ta
ce bataso ka qyaleta Mana ba lafiyar jikinta bace, ka wuce kawai Nima Ina son na shiga kasuwa saboda wasu Abubuwan amfanin sunyi kasa".
Wani duban Baki da lissafi yayi mata.
"Wai kinsan wahalar da Tasha kuwa, Kinga yanda ta daga min hankali kuwa? Kin..."
A
i baisan lokacin Daya ci wani burki ba shaf ya manta Aishat fa Bata San komai dake tsakaninsu ba.
Tahowa yayi ransa a hade ta rufo Masa baya, Zama yayi ya dafe Kansa.
Daga sama ya tsinkayo maganar Aishat.
"Wai meya jawo dacin rai haka daga fadin Bata zuwa
Asibiti,Kuma sai sakin magana kake kamar da wani Abu a tsakaninka da wannan yarinyar ni ka fada min kamanta bama rufewa juna damuwa ko farin ciki tare fa muke sharing".
Bai dago ba Bai Kuma tanka Mata ba.
"Miskili kawai".
Ta fada a zuciyarta.
Itama Bata K
ara tofa tata ba tayi wucewar ta sama.
Da Ido ya rakata Yana ayyana subul da bakan da yayi.
Lokacin da Zahra ta fito daga wanka Bataji motsinsa ba, ta kuduri aniyar sai dai wani tsautsayin idan ya gotta ya ganta Amma ta haramtawa kanta haduwa dashi.
Yafi z
aman awa Daya da rabi ko motsinta Bai Kara jiba ya koma kusan sau uku, amma babu canji dakin dai a rufe.
Dole da yaga Babu sarki sai Allah ya hakura ya wuce Asibitin gurin Baba malam.
Yana ficewa Aishat ta sauko kasa ta nufi dakin da Zahra take knocking t
ayi Tana Kiran sunanta.
Lokacin tana chart da sajida tana fada Mata next week zasuyi graduation, taji kiran da Aunty Aishat din ke Mata, tsam ta taso ta bude kofar arba tayi da Afnan wadda akayi Mata gayu sosai sai kamshin Bom-bon tajeyi zallo ta Fara tana
dariya, hannu Zahra ta Mika ta amsheta tana matsawa daga hanya.
"Sannu Aunty,ko fita zakiyi ne?"
Zahra ta fada tana Zama a gefen gado ita Kuma Auntyn ta zauna a Kan sofar dake dakin, kallon Zahra tayi Ido Cikin Ido.
"Me yasa Kika rufe daki kina Jin bro Ya
na Miki magana kikayi kunnen uwar shegu dashi ko da wani Abu a tsakaninku dashi?".
Girgiza Kai tayi.
"Ba komai Aunty Ina wankane Kuma na rufe jacuzzi din shi yasa ban jiba, Kuma maganar asibiti mijina ne yace na Bari ba sai naje ba tunda an tabbatar da na
rkewar ciwon kada a jogalo min wani Abu daban, lokacin da muka taho Baya nan sai Abbana ya hadoni da Ya Mahmud tunda Shima zezo India din, sai a dubani sosai to jiya bayan na shigo ya kirani yace sunyi magana da doctor Hajara tace babu komai kawai dai nazo
yawo ne, shine yace to kada naje wani asibiti zeyi magana da Ya mahmud din Ina ganin ya manta ne ko sai yau ze fada Masa".
Ta karasa maganar kamar Dade duniya haka akayi ta.
Kallonta Aishat keyi tunda ta ambaci mijinta ita fa nema suke su caza Mata Kai k
owa da nasa salon, shi yana wani furuci dake nuni da ita din kamar suna da wata alaka da daf da daf Dan yanda ya ture dazu ita ya saka Mata shakku a cikn furucin nasa, itama kuma gashi tayi wata magana wadda tayi karo da zarginta kuma.
Nisawa tayi tana fad
in "Allah ya rufa asiri".
"To Zaki zauna a gida ne keda Afnan ko kuma Zaki bini muje kasuwa? To ai Kuma kina azumi kada ki kwaso kishirwa".
Zubut Zahra ta Mike da Afnan a hannu tana fadin.
"Muje Aunty Nima Ina son nayi sayyaya Naga gari Kuma".
"To kin fad
awa mijinki zakiyi yawo ko?"
Dan murmushi tayi tana wasa hannun Afnan.
"Ai ban tare ba, Kuma yace duk inda ya Kama naje yasan bazanyi rashin gaskiya ba".
"A'a Kice aikin gyaran amare ya sameni kinzo inda ake bidi'ar gyaran aure".
Dariya tayi tana fadin.
"
kaji Aunty Ni wane gyara za'ayi min kawai ki Bari".
Ta fice daga dakin bayanta Aunty Aishar ta biyo.
Ita ke driving din motar Zahra na gefenta rike da Afnan.
Basu Dade a kasuwar ba suka dawo Zahra laffaya ta dauko tsaraddu masu kyau da tsada a gurin biya A
unty Aishar ta hanata ta biya ta biya Mata.
Ba zato suka tarar da mahmud a parlour Yana ibadar kallon ball ana Asian cup, Zahra you tayi kamar Bata San Allah yayi ruwan tsirarsa a gurin ba ta wuce da Afnan a kafadarta Wanda tayi barci, har ta kule ganinsa
Yana kallonta a zuciyarsa ya Fara tunanin Wai to meya shiga Kan yarinyar Nan ne haka totally ta canza Masa yanda ta nuna tamkar Bata taba saninsa ba ko gaisuwar Daya Raina ta Hausawan baici arzikinta ba.
Remote ya dauka ya kashe kallon Yana fuskantar Aisha
t.
"Shatu Wai me yake damun yarinyar Nan ne ko magana fa batayi min ba ta wuce, kota fada Miki wani Abu da nayi Mata, wato Naga alamar raini ya Fara shiga tsaninmu.
Zama tayi daura dashi tana fad'in.
"Toni Ina Zan sani ne dazu dai ta fada min mijinta ne ya
hanata zuwa Asibitin Wai yace kada a jankwalo Mata wani Abu tunda a Nigeria sun Basu tabbacin babu sauran ciwon".
A zabure ya gyara Zama Yana wani kankance idanu.
"Kikace menene ? Mijinta kome?"
Gyada Kai tayi tana bashi assurance na abinda ta fada.
"Mij
inta fa kikace? Haka ta fada Miki?".
"Eh haka ta fada min dazu kafin mu fita kasuwa, harma tace min Bata tare ba sai ta komai gida, gaskiya mijin yarinyar Nan yayi Dace da