Showing 90001 words to 93000 words out of 295116 words
Bari kizo ki zauna ki Mike kafa
gashi nan har an Fara kawo Miki caffar ana son aurenki idan kin Gama idda wannan arzikin ki ne?".
Ya fada Yana kureta da ido, da sauri ta cira Kai ta dube shi. "Ni Kuma Yaya ake jawo min zawarci kawai daga ganin mace sai ace zawara ce".
"Kada kiga laifinsu
sun ganki yau sun ganki gobe Baki da niyyar tafiya,idan Badi'a zata fita ki wanke jiki ku kama tafiya ba dole ace Miki haka ba".
Idonta taf da hawaye ta dube shi "to Yaya ya akeso nayi kasan dai yanda abun Nan ya kasance duk yanda naso a saurareni idanuwa
suka rufe ba Wanda ya kula da abinda nakeso su gane Saida suka rabani da Dana yabar gida cikin bacin Rai Wanda har gobe ba Wanda yasan inda yake, gaskiya Kuma tayi halinta yanzu za'a matsamin da zarya na fada musu niba yaji nayi ba duk ranar da yarona ya
dawo Zan dawo".
"Zainab a gabana kike fadar danki, Dan farin ba zakiyi min Kara ba".
"Kayi hakuri Yaya na Bari d'anka to" ta fada.
'yar dariya yayi na nawa Kuma sai dai a koki gaba, yanzu Dan Allah Alfarma zakiyi min kiyi hakuri ki koma dakinki Suma saura
n yaran suna bukatarki kusa dasu ko badan Babansu ba ki duba girman Hajiya Inna har Yamai Saida tasa aka kaita ko a jirgine dai ai tanayi dake ne amma Kika kasheta da dadin Baki akan kina tafe kikayi zaman ki karshe ma kikayo hijira daga can, duk laifin Ha
jja ne wlh ita an taba Mata dan 'yar so ba zaman lfy, gobe nace aje Abuja a daukeki tunda ba jirgin sokoto direct, kije kiyi ta yi masa addu'a bakin uwa Mai Albarka ne akan 'ya'yan ta muma muna tayaki nasan fushi yayi idan ya huce ze nemi gida".
Har ranta
bataso wannan hukuncin ba Amma yata iya da Yaya ishaq uba ne sak tun bayan rasuwar mahaifinsu bai barsu da kukan maraici ba, duk rintsi baya Bari su koka uwa uba yanda ya janyo gudan jininta ya nuna Masa hanyar nema tun a kananun shekaru duk abinda yaront
a ya zama shine sila gashi Zuwa yanzu Allah yayi Masa karfin daya fi na Yayan. Hira sukaci gaba har Aunty Badi'a ta fito itama kamar me Zuwa gasar sarauniyar kyau ita Fara ce tas buzuwa kallonta Yaya ishaq din yayi "wato ta wata fuskar naji dadin zuwanki Z
ainab ko banza mutuniyar ta koyi gayu irin naki da dai sai a hankali".
"Kai Yaya wlh bani na koya Mata gayu ba Daman Aunty na me class ce ko Aunty?".
"Fada Masa dai,kawai nasan dai na koyi amfani da perfumes designers dani kowa ne ma saye nake Amma yanzu t
unda ta bani naji dadinsu nake amfani dasu". Dariya yayin Yana fadin .
"Ba cinya ba Wai 'yan magana sukace kafar baya, Wai yanzu Ina da kikace min zakuje? Bana son yawo har an Fara min sallama idan ta Gama idda".
Ido Aunty Badi'a ta kwalalo "sallama Kuma?.
"Wlh kuwa shi yasa nace ta tattara tayi hakuri zanyi Mata booking ta tafi kawai muci gaba da addu'ar Allah ya bayyana shi duk inda yake".
"Gaskiya kam shi yasa kenan ranar da mukaje gidan sarki kingmakers sun fito daga meeting da Mai martaba Naga ana nuna
ta har wani dogari Yana kokarin Zuwa gurin mu muka tafi".
"Kinsan kuwa sakon daga fada yake".
Baki Ammi ta rike "tab gara nasan inda dare yayi min kafin wannan labarin ya Isa kunnen general".
Ta fada suna nufar kofar fita daga falon.
"Da dai kin yiwa k
anki gata"
Yaya Ishaq ya fada.
*********
Tun safe su Mahmud suka fita da Sameer su shiga can su fita can duk da Sameer Kusan Dan kallo ne an Kai ruwa Rana kafin a samu ganawa da Wanda alhakin matsalar ke hannunsa Basu suka dawo ba sai dare a gajiye s
uka dawo Jin dadinsu daya ba a hotel suka sauka ba gida ne. Sameer yayii musu order din abincin Africa. Saida sukayi wanka sannan sukaci abincin inda Allah ya taimaka sunyi sallah a wani masallaci a hanya. Bayan Mahmud ya shiga daki wayarsa ya Ciro ya shi
ga ciki gurin da akayi Masa connecting da CCTV nan ya lalace gurin kallon Zahra yanda yake more kallonta yasan da ace tasan da CCTV a dakin bazata Bata sakewa haka ba tana sabgoginta. Amma ganin ita kadai a dakin take zuba yanda takeso, amma yanda ya fuska
nceta kamar wani Abu Yana damunta ya Raina yanda take walwalarta, ya rasa aikin me suke ita da Mai Taya ta zama Dan gani yayi ita Mai tayata zaman ta fita waje da alama wani Abu ta sawo Dan can baya yaga ta hada wuta da gawayi akan wani Abu ta Dora tukunya
Mai Dan girma, so yake yaga wace wainar zasu toya.
Dayar wayar ya dauko Yana kokarin kiranta sai kuma Kiran Mr Lee ya shigo akan Yana fada Masa kome yake ya fito bakin da zasuzo daga Thailand sun karaso shi kadai ake jira, tashi yayi Yana Kiran Sameer aka
n ya zama ready zasu fita.
**
ZAHRA.
Tun bayan data gama break Basu zauna ba aiki Zahra ta dauko dambun Nama take son yi yau akwai Naman da yawa sai kuma abinci shima Mai Dan yawa haka Nan taji tana son kaiwa Abban ta da Baba Malam abincin juma'a zila
i ce tace a sawo kufat ayi suyar dambun a Kai tunda da yawa za'ayi ta Bata kudin aka sawo ta Dora, Basu suka Gama aikn ba sai bayan azzahar zilai ita ta mikawa zayyan bayan ta wuce ne ya bude abincin yaga irin garar da aka kawo Masa yayi ta mamakin yanda m
atar oga ta iya girkin hausa haka Mai shegen Dadi gashi ita Kuma ba bahaushiya bace ko Ina ya samo wannan da Kuma dalilinsa na zabar wannan rayuwar shifa ko a mafarki baiyi tunanin ogan nasa ze iya sakewa har ya Mike kafa yayi zamansa a irin wannan muhalli
n ba da iyalinsa, haka yayi ta sakawa Yana kwancewa.
Sai da su Zahra suka Gama Zuba komai a mazuban da suka Dace sannan Zahra ta wuce ta Kira magaji a waya akan yazo tana nemansa sannan ta shige wanka sai bayan la'asar magajin yazo lokacin ita kadaice a fa
lon tana tulawar alqur'ani, Saida ya cika cikinsa Yana zuba Santi sannan ta bashi yace ta fito Masa na Baba Malam Dana gurinsu Ammah har ya Kai kofar fita daga parlour ya juyo Yana fadin "inyeeh su Adda Zahra an girma har an Fara aikin neman ladar tsaffi
da fatan dai kin fadawa mijin naki kada garin neman lada a kwaso zunubi". Ya karasa fada Yana dariya.
"Allah ya shiryeka magaji Kai Kullum baka girma ko?"
"A'a zancen gaskiya ne Dan bawan Allahn nan baki San yanda yayi ya Nemo kudin sayen kayan nan ba Amm
a kin tashi kin zuba irin wannan garar Dan kawai Kinga baya gari ko?"
Harararsa tayi "To nayi kayan nan dai nawa ne mijina ya aje min Bai Kuma yi min iyaka ba duk abinda nakeso zanyi dasu idan bazaka Kai ba dawo ka aje min sai Aunty zilai ta Kai ko naje
da kaina". Ta taso ta nufo inda yake da sauri yayi gaba Yana fadin.
"Allah ya huci zuciyar uwar gidan Mahmud tuba nake".
"Dan rainin hankali shi dai gurinsa ya saka mutane magana".
Aunty zilai ce ta Bata amsa Sam Bata lura da fitowarta ba.
"Kema uwar dakin
a Kamar kin manta halin Mai sunan Alhaji ai shi burinsa Ke nan yayi jan magana".
"Ai sai yayi tayi tunda halinsa ne"
Abincin zilai ta kawowa Zahra Nan cikin parlour some times Bata fiye son zaman dining ba, kitchen zilai tayi niyyar komawa Zahra ta Hana "
ki zauna a nan muyi lunch din Ina Zaki kuma koni bafulatana bana irin wannan d'abi'ar".
Sun Fara cin abincin kenan door bell din tayi k'ara zilai ce ta tashi taje ta bude Mujiba ce tare da wata yarinya Sa'ada 'yar makotansu.
"Kai! Kai!! Kai!!! Tab amma dai
batan hanya kikayi Mujiba, yanzu Alkawari da amana sunce haka? Yaushe rabonki da gidan Nan?"
Dariya mujibar tayi tana fadar "eh lallai da sauranki irin wannan Baki zai- zai, Kuma shike Nan daga kawoki saina dunga sunturi a gidanki ai Mai gidan saiya saka
Mai gadi ya hanani shigowa tinda Zan zamar masa matsala, Wai ke tsaya waye a gate din gidan nan daya tsaremu da dogon turancin daga Ina zuwa Ina me mukazoyi ke tambayoyi dai gasu nan kamar zanga Mrs president".
Ta fada Tana Zama a kujerar dake kusa da zahr
ar Sa'ada ma ta zauna.
Spoon din hannunta Zahra ta aje "Bari kawai Muji wlh Nima haka na ganshi haka Nan Rana tsaka ya canzawa Mai gadin gurin aiki ya mayar dashi makarantar gidan Baba Malam ya ringa share share ya kirawo wannan bansan ko daga Ina ba yanda
aka wayi gari da Mahmud shima haka aka ganshi nifa lamarin yafi karfin tunani na kawai na saka ido ne Naga karshen film din".
Ta fada tana Dan tab'e Baki.
"Amman wlh Baki da kirki auren naki kike cewa film dan bawan Allah ya biya sadaki ya daukoki daga gi
dan ku ya killace ki guri daya ya Baki ci da Sha amma ki Kira Masa aure Shirin film humm zakiyi bayanin film da alama komai normal yake tafiyar Miki ko Aunty zilai?"
Dariya tayi "A'a babu ni a cikin wannan maganar kunga tafiya ta".
Ta wuce kitchen da plate
din abincin ta.
" Kinga Sauko kiyi serving din ku, ni ban iya abinda Kika iya ba ku Kenan bakinku ba kintsi ku dunga sakin magana irin haka Ina Dadi Kinga kin Kori Aunty zilai daga wurin".
Tasowa tayi ta sauko kusa da zahrar tana fadin "lallai kina Jin Da
di irin wannan garar haka sauko sa'ada Wai Ina Mai gidan na Dan kwana biyu ban ganshi ba?"
Plate din ta ture gefe ta dauko tissue tana goge bakinta.
"Yayi tafiya jiya baya Nan".
Tsayawa mujiba tayi da cin abincin. "Bayanan Kamar ya?"
"Kamar yanda na fad'a
Miki yaje taron gamayyar Qungiyoyin da suke taimakawa ilimin makarantun government Dana allo a Nigeria da wasu kasashen Africa, to a Nan zone din namu na north east shine aka dauka a Bauchi state, a jigawa da Kano ma duk suna da nasu wakilan tunda state u
ku suka dauka".
"Masha Allah kice wata Rana ku sai turai tunda Mai gida ya Fara irin wannan babbar harka ai ku hannu sama chololo lallai mutuniyar kinzo da goshi".
Tsaki tayi wlh ki raba kanki da camfi Wai nazo da goshi to tun kafin nazo yake aikinsa Kuma
tafiyar ma dagawa sukayi tun ba labarina a rayuwarsa zasuyi abarsu Nima da abinsa na same shi sai yanzu ne dai ta Kara tasowa.
Haka suka dunga Hira har Kusan magariba sannan suka tafi Zahra ta Basu kilishi da biscuits masu yawa.
Saida magaji ya Fara Kai
sakon Baba Malam sannan ya karasa gida, yauma aikin Ammah ne lokacin daya shiga parlourn ta ba kowa sai Alawiyya tana saka turaren wuta da freshner tambayarta yayi Ina Ammah? Tace Masa taji dakin Abbansu can ya nufa da basket din da ledar knocking tare da
sallama a kofar falon Mamace ta amsa Masa ya bude ya shiga da alama wani Abu suke tattaunawa.
Gaishe da Abban yayi sannan ya gaishe dasu Ammah Yana aje basket din da ledar Naman da aka kunshe cikin poil paper.
"Abba gashi inji Adda Zahra tace a kawo maka"
.
Mama ce ta taso tana fadin"Kai Masha Allah lallai wannan 'yar tana ji da Abbanta". warmers din ta Fara cirowa tana bude miyar falon ya cika da kamshi Curry da spices.
"Abban ne yace "magaji sannunka Kaima lallai uwata ta haifu Allah ya yiwa wanna aure Al
barka ya tsane idon makiya wlh naji Dadi kwarai da gaske a Miko min nan Naga abinda uwata ta kawo min".
Ya fada Yana mik'awa magaji bugun Abuja biyar zuwet.
"Na gode Abba, Kuma ta bada an kaiwa Baba Malam ma ya fada Yana nufar kofa.
"Masha Allah nasan uwat
a zatayi abinda yafi haka".
Cikin rawar jiki mama ta kinkimi basket din ta Kai gurin da Abban yake zaune ta dora akan coffee table, sannan ta dauko ledar, ledar yace ta bude lafiyyayan dambun naman rago ne yasha kayan Hadi ya sayu jawur dashi sai Kamshi k
e tashi, Dina yayi yakai Bakinsa ya tauna Yana fadin "Masha Allah uwata ta Gama min komai wlh har Raina Ina son yarinyar Nan bilhaqqi uba ta daukeni sak duba ki gani Rabi'a ga Asma'u a zaune amma Ni ta yowa wannan garar Kai madallah, Yau abincin ki sai dai
yayi hakuri na uwata zanci".
Ya fada yana kallon Ammah. 'yar dariya tayi Ammah tana fadin "Ana ta sabon d'a wa yake ta tsohon da inji barmani choge".
"Gaskiya kam, ai Babu Mai shafewa Zahra Zane a gurin Abba"
Mama ta fada.
"Ki Fadi ki Kara Zahra yarinya c
e mai tsananin yi min biyayya ki duba yanda lamarin auren Nan ya kasance Amma tunda tayi 'yan koke-kokenta ta hakura ba Wanda ya Kara Jin kanta, duk da mijin nata Mai Karamin karfi ne akan wadanda suka nemi aurenta Allah be nufa ba da Kuna duba da inda ta
fito da Kuma uwa uba dangin mahaifiyar ta Amma tayi zaman ta Ni kuwa ba abinda bazan yi Mata ba matukar baifi karfin arzikina ba".
"Wannan gaskiya ne duba da yanda ta waye tayi karatu Mai zurfi ai ba wata ce bijirewa zatayi ayi ta Kai ruwa Rana"
Mama ta fa
da.
Yar dariya kawai Ammah tayi duk Dadi ya cikata Bata taba tunanin Zahra nada wayo haka ba tasan dai abun duniya Bai rufe Mata ido ba.
✨✨✨
✨✨✨
AUREN HUCE HAUSHI
✨✨✨
✨✨✨
Maman Fateemah.
Page 32
______
_Qaran alarm din daya saita ne ya tashe Shi sallar Asuba, duk da bai kwanta da wuri ba Dan sai Kusan karfe biyu na dare suka shigo gidan, meeting din nasu sun jima suna tattaunawa akan sabon kafanin da zasu bude a jihar kebbi na shinkafa, masallacin da suk
e sallah da gidansu akwai tazara sosai shiyasa ya saita kafin sallar Asuba da kamar hour daya, sai da yayi yaqi da Shaidan sannan ya samu ya sauko daga gado Bai jima a toilet ba ya fito sanye da bathrobe Fara tas Mai jikin towel. Jallabiya ya saka yayi ra
ka'atanul fajri sannan yayi waje a Yana niyyar yiwa Sameer knocking ya bude ya fito.
"Barka da Asuba" Sameer ya fada yana mikiwa Mahmud hannu sukayi musabaha,
"Ashe ka tashi ai nayi tunanin saina shafa maka ruwa sannan ka mitsa".
'yar dariya Sameer yayi Ya
na fadin "irinku da kuka San inda kuka dosa Kuna dagewa da mujahada to mu ta Yaya zamuyi kwance muna barcin asara ai sai lalacewa tayi yawan".
"Kayya Kai dai Allah ya datar damu kawai"
"Allahumma Amin"
Sameer ya fada lokacin da suka jero suna Kara tattauna
wa akan harkokin yau da Kullum, Sameer ne yaja musu motar suka fice daga gidan, bayan sunyi sallar zama sukayi akayi karatu Kusan masallacin mahadar 'yan Africa ne mazauna can Kusan duk Wanda yake a kukkuken gurin Baya Bari khamsu salawat ta wuce shi, s
ai da gari ya waye sannan suka nufo gida.
A hanyar ne Sameer ke fadawa Mahmud sunyi waya da Habib jiya a kan training din da za'ayi na matasa maza da Mata na koyon sana'a.
Har suka zo gida suna zancen, yaso yayi barci amma ya fasa, so yake ya Kira Nigeria
baze iya mazewa ba Kamar yanda yayi niyya Bai gane shi Mai rauni bane sai akan yarinyar nan,sai da yayi Mata nisa ya gane shayi ruwa ne, duk da Bata shigo rayuwarsa da Wasa ba kafin ya hadu da ita shi jarimi ne sannan shi baima fa San yanda kake kwana da
Abu ka Kuma tashi dashi, shifa idan ya tunata har wani ji yake zuciyarsa ta harba, yaso ya dan Bata iska, so yake ya fahimci shin ta karbeshi da zuciyarta da gangar jikinta ko Kuma har yanzu tana zaune dashi ne by force na iyayenta, amma idan ya kalli kwa
yar idanunta Yana hango wani Abu na daban a cikinsu Kuma uwa uba yanda sukayi rayuwa a Dan zaman da sukayi da ita.
Bayan sun shiga gida kowa nasa gurin ya dosa Dan shi dai Sameer barcin ya kama, shi kuma daya shiga wanka ya sake, shifa idan ze wuni Yana z
ubawa jiki ruwa bashi da damuwa. Sai da ya gama komai ya Haye gado daga shi sai singilet Fara sol da boxer short.
Wayar ya dauko dauko cikin ikon Allah yaga Zahra online ji yayi wani Dadi yaji ya rufe shi, vedio call ya Kira daya wayar Kuma ya bude connect
ion din CCTV.
Tana cikin charting da Aunty Nawwara kawai kiran nasa ya shigo Yana kallon yanda ta kwalalo Ido waje abin har yaso bashi dariya, hijabin da tayi sallah ta dauko ta rufa kirjinta sannan ta daga Kiran suna hada Ido taji gabanta ya Fadi ji tayi
abun Nan na da ya dawo Mata.
Sallama yayi mata da husky voice dinsa wanda ya saukar Mata da wata muguwar kasala, a hankali ta daga idonta ta kalleshi cikin murya Mai rauni da rashin karsashi ya amsa Masa sallamar, kuri yayi da idon Yana kallonta yanda tayi
Masa wani irin kyau