Showing 24001 words to 27000 words out of 295116 words
dinsa suka tafi gida.
Da dare Yana zaune a inda suke Hira yaga motar Alhaji Dauda ta tsaya a kofar gidansu da sauri ya tashi ya n
ufi inda yayi parking sai yaga harda bakon Alhajin Zakariyya suke tare, sun gaisa sosai kafin Alhaji Daudan ya fada Masa Amininsa Kuma Dan uwansa ne yaga Amina Yana so shine nace yazo muji da zafi -zafi akan bugi karfe.
Jafar yaji Dadi sosai zaifi kowa mur
na idan hakan ta kasance Dan ya yaba sosai da hankalinsa sosai.
Cikin gidan Jafar ya shiga ba jimawa ya fito Yana musu iso ciki sun gaisa da Nanna Alhaji Dauda ne yayiwa Nanna bayanin koma itama irin amsar Jafar ta fada idan tana so ba matsala ba inda aure
baya Kai mace Nasarawa batayi nisa ba.
Cikin ikon Allah kuwa Amina taji Alhaji Zakariyya ya kwanta mata a rai Kuma zata iya aurensa duk da fada Mata Yana da Mata harda Yara biyu.
A cikin wata biyu akayi bikin Amina da Alhaji zakariyyan, Jafar yayi Mata ko
mai da uba yake aka kaita can Nasarawa state cikin garin Akwanga.
Wannan kenan.
Haka Jafar yaci gaba da karatunsa har ya Gama ya dawo gida Yana jiran shiga camp.
Lokacin da saki post na tafiya service sunan Jafar ya Fado a cikin masu zuwa Jos yayi murna s
osai ko banza Yana jiyo kamshin gida tunda suna makotan jahohi.
Bayan gama zaman camp wata makarantar 'yan Mata jeka ka dawo aka Kai Jafar, Baiyi wata biyu ba Allah ya hada shi da wata yarinya Rabi'a yaji yarinyar ta kwanta Masa tana Kuma da irin Qualities
din da yake fatan Samu a gurin matarsa.
Zuwa lokacin gama service dinsu har magana tayi karfi inda iyaye suka shiga.
Wani gida Jafar ya saya kusa da gidansu ya gyara' ba'a dauki lokaci ba akayi bikinsa da Rabi'a suka tare a gidansu. Duk wata kulawarsa da
soyayya ya tattara ya baiwa Rabi'a ba abinda ta nema ta rasa sai abinda baza'a rasa ba. Rabi'a irin matan Nan ne masu kissa kafin wani lokaci ta kanainaye zuciyar Nanna.
Kwanci tashi ba wahala a gurin Allah aurensu ya shekara Amma kalubaken da suka Fara fu
skanta na Rashn zaman ciki a jikin Rabi'a kusan barinta uku. Ana haka Jafar ya samu aiki da ma'aikatar gona ta jihar Bauchi BARDA.
Cikin kankanin lokaci kofofin wadata suka budewa Jafar kafin shekara biyu ya gina gida Mai kyau sunje makka shida Nanna.
Nan
da Nan likafa tayi gaba Amma dai matsalar su na Nan ta rashin haihuwa.
Yayin da abin ma ya Fara damun Nanna har ta gaji tayi Masa magana akan ko maganin hausa za'a fata nemawa Rabi'a ne.
Amma sai ya nuna Mata ayi hakuri tunda tana ganin consultant na Gynic
ology a gani idan ba wani cigaba sai ayi na hausan.
A Kuma ciki shekarar ne Alhaji Jafar ya koma Abuja da aiki inda arzikinsa ya Kara bunkasa gashi Allah yayi shi Mai sakakken hannu bashi da rowa ko kadan, in dai Yana gari to kofar gidansa Cike take da jam
a'a, sai Suma mutane suna tausaya Masa akan rashin haihuwa ga dukiyar dai Kama hankadota ake Amma ba magaji.
Ana haka Allah ya kawo ibtila'in ambaliyar ruwa a Adamawa state yankin MUBI.
Lokacin da gwamnati tarayya zata tura masu zuwa jaje sai sunan Alhaji
Jafar ya shigo cikin tawagar vice president.
Sun jajje guraren da b'arnar ta afku anyi rubuce rubuce sosai da Alkawarin ka na gwamnatin tarayya sanan an bada kayan agaji ga wadanda iftila'in ya shafa a hanyarsu ta komawa ne Alhaji Jafar suna tattaunawa da
Ardon filanin Yana Karayi Masa bayanin abinda ya faru.
Suka jiyo maganar mace daga bayansu lokacin ayarin sun danyi nisa dasu, da sauri Ardon ya juya Yama fadin "ho! 'yar nema Saida Kika biyoni Nan ko ma'u?"
Dariya tayi tana kare fuskarta da wani littafin
Mai Dan fadi dake hannunta cikin shiga take ta Kamala Riga da siket na lace brown sai takalman ta da jaka da mayafinta farare.
Har kasa ta tsuguna tana gaishe da Baffan nata kafin ta Dan kalli gurin da Alhaji Jafar yake ta gaishe shi.
Baffan nata ta mikaw
a littafin hannunta tana fadar "Baffa ga project din nawa komai ya kammala".
Baki sake Alhaji Jafar ke kallonsu wannan 'yar yarinyar har ta Gama karatu ake nufi ko me"
💋
❤
💋
❤
️️
AUREN HUCE HAUSHIN
💋
❤
️
💋
❤
️
🔷
PEGE TEN
🔷
Story
&
Written
By
MAMAN FATIMAH
******Jujjuya littafin project din Ardo yayi, sai Kuma ya mikawa Alhaji Jafar Yana fadin "Duba ka gani Yallabai ni tunda ba ganewa zanyi ba,naji Dadi da Allah yasa aka Gama wannan karatun ba domin na saka auduga na toshe kunnuwa naba
da ba'ayi karatun Nan ba, tunda Wanda yaso auren nata yace in dai zatayi karatun Nan shi ya fasa, shi Kuma Dan uwanta na wajen kanena yace karatu Babu gashi tunda tana ganewa Kuma tana so, kaga yanzu duk gurin nan namu ita me yiwa mutane Allura".
Kallont
a Alhaji Jafar ya karayi,sannan ya kalli Ardon Yana fadin.
"Yaushe ta Fara karatun ne na ganta karama amma har ta hada diploma?"
Gyara tsayuwa Ardon yayi Yana fadin "wallahi am tun tana aji hudu na furamare Dan uwanta ta kaita aji daya na sakandire tunda y
ayi wani zuwa suka zauna da kannen nasa yaga tana da kokari shine yace Mata idan ta Gama makarantar tana son taci gaba da karatu, shine tace Masa tana son ta Zama malamar asibiti, to tunda sukayi haka ya kudurci aniyar tsayawa akan karatunta shi yasa da ak
ayi Mata chaaaa akan maganar aure yace Bai Hana ayi maganar aure ba. Amma ya Dora sharadin saidai idan mijin ze barta tayi karatu abinda ya gagara kenan aka fasa Amma duk yan uwanta anyi musu".
"Masha Allah. Allah ya Sanya Albarka, haka ake so a rinka bari
n Yara Mata suna karatu barin ma na bangaren lafiyar da malaman makaranta, yanzu ba cewa kayi ita ke yiwa mutane allura ba da sauran abubuwa? To da batayi karatun ba da basai an tafi wai gurin an nema ba? Ba komai in Sha Allah zatayi auren ta Kamar kowa".
Ardo ya amsa da "Allahumma Amin".
Ma'un Alhajin ya kalla "Asma'u kin amince na tafi da project din naki na duba a hankali in yasa said dawo Miki dashi".
Kai ta gyada alamar Eh.
Sunyi sallama da Ardo tawagarsu suka wuce zuwa Yola inda zasu bi jirgi zuwa Ab
uja.
Wannan shine silar haduwar Alhaji Jafar da Ammah, ya koma maida project da Kuma kafa gwanatinsa cikin ikon Allah suka yarjewa juna.
Lokacin da magana tayi karfi Rabi'a taso tada hankalinta saida Nanna ta taushe ta da kalamai masu kwantar da hankali.
C
ikin kankanin lokaci akayi bikinsu. Amarya ta tare cikin ikon Allah zaman Rabi'a da Asma'u ya kasance Zama Mai tsabta.
Wata uku da auren Asma'u ciki ya bullo duk masoyin Alhaji Jafar ya Taya shi murna sosai a lokacin ne Alhaji Jafar ya biyawa Rabi'a makka
kusan abinda ya kwantar Mata da hankali kenan Dan ya fada Mata idan take tayi addu'a sosai akan matsalar ta.
A haka rayuwa ta dunga gurguwa har cikin ya Isa haihuwa Ardo dasu Inna maimuna sun so Ma'un to koma gida zaman haihuwa Amma Nanna ta Hana tace meye
amfanin ta ita in dai sai Asma'u ta koma gida.
Cikin ikon Allah a wani dare nakuda ta tasowa Asma'u lokacin Alhajin Yana nan, Nan da Nan suka nufi asibiti wurin karfe biyu da rabi Amma kafin hudu Allah ya dauketa lafiya ta haifi takwaye mace da namiji.
Mu
rna gurin wannan iyalin ba magana ranar suna yaran aka bar musu sunan su sai dai su Hassan da Hasana aka daka musu.
Kullum yaran suna tsakanin Rabi'a da Asma'u suka rainon 'ya'yansu. Lokacin da aka yayesu a lokacin Allah ya baiwa Rabi'a ciki itama ba'ayi w
ata biyu ba Asma'u ma ta Fara laulayi, cikin ikon Allah cikin Rabi'a ya zauna kusan lokaci daya suka haihu Rabi'a haifi Hamza yayin da Asma'u ta haifi Abdul Hakeem.
Bayan haihwar Hamza Rabi'a Bata Kara haihuwa ba Saida Asma'u tayi maza biyu sanan Rabi'a ta
haifi mace Murjanatu, bayan Murjanatu Rabi'a ta Kara haihuwar Salma sai auta Hameeda ita Kuma Asma'u ta haifi Sulaiman sai auta Musaddiq, zuwa lokacin sunansu ya bace yayin da ake gadawa Hajiya Rabi'a Mama wasu na waje suce Hajiya Mama, Hajiya Asma'u Kuma
Ammah.
WACECE FATIMAH ZAHRA?
'ya daya tilo ga kanin Ammah shaqiqi Muhammad Sani. Mahaifiyar Zahra Najwa Balarabiyar Jordan ce sun hadu da Muhammad Sani ne lokacin da yaje karatu kasar da farko mutunci suke da Najwa sai daga baya ya juye ya Zama soyayya
har Allah ya nufesu da aure da taimakon wani malaminsu Dan kano Dan kusan ta bagarensa su Ardo wanda suke Kira Baffa ya Sani ya Kuma amince da Malam Muhammad Kabir ya Zama waliyyin Muhammad Sani a can.
Lokacin da Muhammad Sani ya Gama karatu ya zauna a ca
n yayi aiki kusan shekara biyu daga baya ya tattaro nasu ya nasu suka dawo Nigeria, lokacin Najwa nada cikin Zahra wata bakwai a lokacin Kuma Ammah na goyon Sulaiman Mama na goyon Hameeda.
A Jimeta Muhammad Sani ya sayi gida saidai suje Mubi kawai suga i
yayensa,ba dadewa Najwa ta haifi 'yarta Zahra wadda taci sunan mutum biyu mahaifiyar Najwa da Mahaifiyar su Ammah.
Haihuwar Zahra ba dadewa Muhammad sani ya Sami aiki a Abuja karkashi minstary of internal affairs da taimakon Alhaji Jafar.
Zahra nada wata b
iyar wani cikin ya bullo a jikin Najwa Mai wata irin masifar laulayi, Wanda ya tilasta Ammah ta dauke Zahra daga bakin nono.
Lokacin da komai da dai dai ta a gurin aikin nasa ya dauki Najwa suka koma Abuja.
Saida watan haihuwarta ya Kama ya kaita Mubi shi
Kuma ya koma Abuja.
Lokacin data haihuwa iyayenta sunzo Nigeria da kanwarta Nawwara a Karon na biyu Mahaifiyar ta taso tafiya da Zahra Ammah ta dunga magiyar abar Mata ita harda kukanta.
Lokacin da suka Gama wanka Muhammad sani yazo ya tafi dasu tafiyar d
a har abada Basu dawo ba a hanya sukayi hadari sun bar Jos Basu karasa Abuja ba.
Yan uwa da iyaye sun shiga cikin tashin hankali marar misaltuwa Ammah tayi Kika Kamar ba gobe,ta rasa Dan uwanta shakiki, ba karamin Kai ruwa Rana akayi ba kafin Ummee kakar Z
ahra ta hakura ta barwa Ammah Zahrar.
Tunda daga lokacin Ammah ke baiwa Zahra wata irin kulawa ta musamman sai Kuma shima Mai gidan ya kwallafa ransa akan soyayyar yarinyar abinda ya haddasa tsana Mai tsanani tsakanin Mama da zahra inda ita mamar ke ganin
Kamar nema ne yasa Alhaji ke kaunar Zahra, tana ganin idan Dan tana 'ya mace ne karama ai itama tana da nata kananan 'ya'yan mata Amma baya nuna kulawa akasu Kamar Zahra ko Dan tafisu kyaune tunda Babu inda ta baro uwarta.
Wannan kenan.
Ranar da za'ayi j
arabawar share fagen shiga karamar secondary ta gwamnatin tarayya tun sassafe zu Zahra suka shirya ita da Sulaiman da Hameeda da Salma duk da Salma ta girmesu Amma yawan yi Mata repeating yasa suka taddo ta.
Har sun shiga mota Bala direba na niyyar shiga Z
ahra ta bude ta fito da sauri ta nufi cikin gida Sulaiman Yana kiranta tayi banza dashi ta shige da gudu ta karasa dakin Ammah tana fadin "Ammah na manta kayana da Ya Hassan ya kawo min har zamu tafi na tuna".
Daga toilet Ammar ta fito ta nufi bedside loc
ker ta janyo ta mikowa Zahra ledar tare da fadar "Maza kada ku makara mana".
Kai Zahra ta gyada kafin tace "Ammah ki kara yi Mana addu'a Dan Allah Ina son naci jarabawar saboda Abbana yace idan naci makarantar zemin kyautar wani Abu"
"To naji maza Allah ya
bada sa'a"
A kofa suka hadu da Sulaiman ya biyo ta tana fadin "Na rantsa da Allah zamu tafi mu barki ba Dan Abba ya fito ba da wallahi sai dai ki fito kiga bama gidan".
Kafin ya saki labulen ya juya Zahra ta Kai kofar da zata kaika compound din gidan.
Ma
sha Allah anyi jarabawa an Gama sai jiran sakamako.
A haka sukaci Baga da zuwa makaranta har suka Zama common enterence a matakin jaha.
Lokacin da suka dawo zaman gida lokacin ne Alhaji Jafar da kansa ya yiwa Zahra passport da visa Saida ya Gama komai sann
an ya fadawa su Ammah da Mama. Godiya Ammah ta shiga jerawa Mai gidan nasu,yayin da Mama tayi shiru Kamar bazatayi magana ba sai Kuma tace "yanzu Yallabai da kanka zaka rakata ai da Koda Hasana ko Hassan ka hadasu zasu kaita ko Kuma a fadawa cen kakannint
a su turo a tafi da ita ai cacar kudin Kamar yayi yawa".
Daga Ammah har Alhaji Jafar din kallon Mamar suke ita dai Ammah shiru tayi yayin da Alhajin yace.
Saboda ban San darajar 'ya'ya ba zan hada Yara a tafiyar uwa duniya daga Nan har Jordan na kwanta a
gida hanakli kwance ko?"
Kai ta gaigice tare da fadin "gani makudan kudi za'a kashe".
Wani kallo yayi Mata "kada ki kawo b'araka Rabi'a duk yaran dake gabana daya na daukesu yada zan yiwa abinda na Haifa haka zan yiwa marainiyar Allah. Da Kuma kike maganar
cacar kudi idan zan jera shekara Ina Kai zahra Jordan kullum ba abinda ze girgaiza a cikin abinda na mallaka".
Ku tashi kuje.
Lokacin da zasu tafi anyi Mata tsara sosai Dan Nanna ma kilishi tasa aka yi Mai yawa na tsaraba.
Har kano su Ammah da yara sukayi
musu rakiya.
Lokacin da sukaje Jordan din ba karamar murna kakanninta zukayi ba Dan Babu zato suka gansu, sun Kuma Kara yabawa da cika Alkawarin Alhaji Jafar Dan da kansa yayi musu Alkawarin ze kawo musu Zahra Dan ko a waya Bai fada musu zuwansu ba,sai ad
dress dai daya taba tambaya can wani lokaci.
A ranar Zahra taga zallar soyayya a gurin dangin Najwa Dan gidan cika yayi da 'yan uwa aka dasa sabon kukan rashin Najwar da kyar Abbie da Abbanta suka dinga Basu hakuri Dan ma Alhaji Jafar ba larabcin yakeji so
sai ba saidai Wanda suke Jin turanci suka ringa magana dasu.
Lokacin da Alhaji Jafar din ze tafi masukin daya Kama a hotel Abbie hanawa yayi duk yanda yaso zillewa kin yarda yayi dole ya amince aka sauke shi a wani part dake kusa da nasa Ummee din, Dan ba
karya dukiya dai Kam akwaita Dan shi kanshi Alhajin yayi mamakin yanda ya riskesu Bai taba kawo haka suke ba lallai yasan hadin Allah ne kawai da suka bawa Muhammad sani auren 'yarsu Dan tazarar Mai nisa ce a tsakanin su.
Kwanan Alhaji Jafar bakwai ya wuce
Umara yayin da Ummee tayi Masa Alkawarin zasu hadu a Saudiyyar tunda zata kawo Zahrar Nan gurin iyayenta da 'yan uwa su ganta a cikin garin Madinatul Munawwara.
Satinsa daya da zuwa Suma su Zahrar sukazo Saudiyyar ita da Ummeen da Aunty Nawwara.
A Nan ma
Saudiyyar Zahra taga gata iya gata Dan kowa Nan Nan yake da ita, Dan kanwar Ummee Hanifa sosai ta kafe sai dai a bar Mata Zahra ta tafi da ita Istanbul inda take aure Wai Bata yarda da zaman Nigeria ba.
Ankai ruwa Rana da ita kafin ta hakura Dan da gaske A
lhaji Jafar ya bude Mata aiki Dan cewa yayi idan irin haka za'a ringa yi bazai Kara bawo musu ita ba saidai duk Mai son ganinta taje ya ganota Kamar yanda Ummee keyi, hakuri aka ringa bashi.
Saida aka Kai Zahra makka suyi kayi umara sannan suka fara Shirin
baro kasar.l Sayyaya dai Zahra ta shata Dan wasu kayan sai a awon cargo akayo musu su.
Sarkar gwal da warwaro zobe kuwa kirar Saudiyya da Dubai zuwa kirar Bahrain sun Kai kala goma duk dai dai size din ta sai na Ammah biyu na Hasana ma biyu shi kanshi Al
hajin anyone mass goma Sha Tara ta Arziki.
Ranar da zasu dawo Zahra Tasha kuka haka kakarta Ummee,har jidda sukayo musu rakiya Basu suka tafi ba sai da jirgin su Zahra ya tashi a sararin subahanahu wata'ala.
Saukar safe sukayi anan suka samu Bala direban A
lhaji Dan Bai fadawa kowa sun taho ba sai Balan kawai, sau da yawa idan ya fada gashi Nan a hanya hankalin Nanna baya kwanciya har sai ya iso.
Lokacin da suka shigo harabar gidan suna tsayawa Zahra to garzaya cikin gida tana fadin "Ammah!!! mun dawo".
Da g
udu Hameeda ta fito daga part dinsu, rungume juna sukayi suna ta tsallen murna Sai jikin zahra Hameedar ke shafawa gani take kamar canza Mata Zahrar akayi.
Da sauri Ammah ta fito tana "fadin wa nake gani ne haka Kamar bakin saudiyya zuwa ba notice?"
Alhaji
n ne ya Bata amsa.
"Surprised din ki mukayi ko Zahra na?.
Kai ta gyada masa.
Kayansu ne su Bala da Mai gadi suka Fara shigowa dasu kafin Alhajin ya nufi part dinsa na cikin gidan yayin da Ammah ta rufa Masa baya.
Har yayi wanka ya shirya Mama Bata shigo b
a, har ya tambayar Ammah yayi Ina Rabi'a ? Tace Masa tana ciki watakila ko barci take.
Kusan kwana su Zahra sukayi tana baiwa Hameeda labarin abinda ta gani da inda sukaje a Jordan da saudiyya, wurin karfe biyu Ammah ta tashi zatayi nafila ta jiyo su suna
Hira a dayan bed room dinta lokacin wuri biyu da rabi na dare, leko tace su kwanta basu san dare yayi sosai ba.
Washe gari an baje tsarabar Zahra an baiwa kowa dai dai gwargwado.
Amman tsarabar Hameeda daban take Dan har sarka Saida ta