Showing 1 words to 3000 words out of 184731 words
[22/10, 22:31] MRS. MU'UTASIM: *
🌟
AMEER DA AMEERA*
🌟
*Assalam alaikum barkanmu da wannan lokacin yan uwa ina fatan kuna lfy*
𝙨𝙩𝙤𝙧𝙮
𝙖𝙣𝙙
𝙬𝙧𝙞𝙩𝙞𝙣𝙜
𝙗𝙮
𝑴𝑨𝑴𝑨𝑵
𝑵𝑼𝑺𝑨𝑰𝑩𝑨
𝑪𝑬
✍
🏻
*1*
Gida ne babb
a wanda yake dauke da bangare uku ga yara nan suna wasa wata yarinya nagani an bigeta tana kuka yaran kowa yasoma guduwa suna shiga cikin gidan wanda ba yan gidan ba sun fita sunkoma gidan su
dayan yarinya ce ta tsaya akan mai kukan tana cewa yarinya
kadan ma kika gani indai nice dama nace miki duk uban daya hadani da yaya Safiyan ya dakeni saina rama kanshi ko ance miki namanta ne to ina sani nace dama sai munfito wasa na rama
yarinyar na kuka tace saina hadaki da mama na
wata mata ce ta fito
daga dayan bangaren tana fadin ke rashida wani dan iska ne ya tabaki agidan nan mu fidda reni nida uwarshi
wadda aka kira da rashida tana ganin mamanta tayo wajan ta tana cewa mama ba ameera bace ta ke dukana wai dan jiya munje gonar mlm bukar mun
ciro mango shine yabiyomu kuma itace tace muje mu ciro idan bamu ciroba zata mana wankan qaiqayi duk wanda baije ba
mama ta banka wa ameera harara wadda ita kuwa ko ajikin ta mama tace yanzu ameera bazaki dena halin azzalumai ba na daukar maganar da
kuke dauko mana kullin ana kawo mana karar ku musamman ma ke mai kunnen kashi
Ameera tace eh din baza adena ba kuma ai hadda diyarki muke zuwa wllh ko gobe tayimin gami da yaya safiyan saina jibgi banza ehee tana jijjiga jiki ita ala dole wai an bata m
ata rai sai masifa takeyi kamar ba gobe
Mama kuwa kama hannu Rashida tayi sukayi sashen mama ameer tana cigaba da masifa
Ameer kuwa nasashen innar ta ta nufa tana zuwa tayi sallama
sai wata tsohuwa ta amsa tana cewa ke kuwa kedaw
a naji kina daga murya tace nida rashida da mamanta" Inna tace to mai kika musu
ameera tace inna wallahi saina ci aban rashida wai jiyane munje gonar bukar shesuka shiga suna cire mango shine daya biyomu sukace wai ni na sakasu kuma ni ko gonar ma ban
shiga ba tana matso kwallar karya tace shine suka hadani da yaya safiyan yayi min duka da safe naje wajan umma gaisheta kawai yake dukana
Inna ta saka salati tana cewa shi dan banzan yaron nan shine ya dakeki to wllh bai bigi banza ba saina rama miki
dan iska mugu, ita kuwa ameera tana murmushi tace kuma bakiga yadda yake dukana ba kamar wata yarshi
Inna tace zaizo yasameni anan badai ke ya dakaba zonaga wajan ta matsa kusan inna tana cewa wllh jikina ciwo yake yi tana kukan karya, Inna kuwa sa
i zuba masifa takeyi kamar ta aro baki. (nace ashedai su ameera gado akayo)
mama na shiga gida da isa wajan wata mata tace sadiya kiduba kiga yadda ameera ta yiwa Rashida gaskiya abin nan ya isheni haka dan tafi karfinta saitake zaneta kullin
wadda aka kira da sadiya ta dago kai ta dubesu tace kiyi hakuri nana wllh kinsan ameera inna ce ke daure mata gindi agidan ko abbansu idan yayi magana inna ke rufeshi da fada nima kaina abun damuna yakeyi kullin addu'a nake mata Allah yashirye ta yarinya b
ata tsoron kowa kisan da cewa mutum daya take tsoro safiyan shima wani lokacin saita mishi mugunta
Maman rashida tace to shikenan amma kija mata kunne gaskiya tace to insha Allah, suka juya suka fita
Umma tayi tagumi tana tunani rashi ji irin na
ameera yarinya kamar aljana babu wanda take ragamawa ita batasan ya zatayi da yarinya nan ba kodayake ai lefin inna ne ita ce bata ganin lefinta
Tana nan abba yashigo da sallama amma yaji shuru ya sake wata nan ma shuru kawai saiya sayo kai ciki umma yag
ani zaune tayi tagumi da alama ta nisa cikin dogon tunani yazo yazauna akusa da ita duk batasan yazoba saida ya shafo fuskarta
Ta zabura da sauri yayi saurin riketa yana cewa haba sadiya menene yasaka kike wannan tunani ? Umma taja numfashi tace abba
n safiyan wllh lamarin yarinyar nan ne yayi yawa kaduba kaga yadda take dauko mana magana a garin nan amma inna bata gani duk wanda ma yazo sai dai suyita fada dashi
Abba yace kiyi hakuri umman yara mucigaba da mata addu'a insha Allah wata rana zata d
ena umma tace amin nan ta dauko mishi ruwa da abinci takawo mishi tace na hada maka ruwan wanka yana bayi
Abba yace to matata farin ciki na yana murmushi, Umma dinma murmushin tayi yazo ya rungumeta yamata kissing a kumatu tayi dariya tace oga ruwan
fa zai huce
Ya saketa yana dariya yace ki fiddo min kayan dazan saka tace ai tuni na fiddo maka yana kan gado
Ya fice bayi ita kuma ta zauna tana jiransa,
Safiyan ne yashigo gidan bangaren inna ya nufa yana shiga banka mishi harara tayi da
riya yayi zuciyar sa yace to inna gidan masifa kennan yau kuma komai nayi ake min wannan harara haka yana maganar zuci, yaji inna tace wato azzalumi ko uban me ameera tayimaka ka daketa inata magana ka wani ziramin ido kamar na uwarka da hanci kamar k
arass
dariya yayi dan ya saba da wannan ba'ar ta inna yace hajiya inna ikon Allah kaka ta ni kadai , Ameera na kan cinyarta tace tab wllh bazan yadda ba ta soma tirje tirje a kasa tana cewa itafa kakar tace ita kadai bada kowa ba
Inna tace butar
uwaka safiyanu nace tashi kabar min gida ai nan ba gidan ahmadu bane da sadiya to tafiyar ka nace kazo kasaka min yarinya kuka
Safiyan ya kama baki yace Allah yabaki hakuri masifatu, Inna kuwa ta dauko wani filo akusanta ta jefa miki tace fice tin
kafin na karya maka kafa
yace kai kaji karfin hali irin na inna ni har zaki iya karyani sabon jini ne nifa kekuwa duk kin tsufa
Inna tace uwarka sadiya ce ta tsufa baniba
Ameera tace inna kyaleshi ai yasan kinfi karfinshi, harara yamata ta koma
bayan inna tana boyewa fita yayi daga gidan yayi bangaren umma yashiga da sallama
Suka amsa ya karaso yana cewa umma abba sunun ku da gida atare suka amma da yauwa ,, Umma tace har kadawo daga makarantar yace eh umma na amma Hajara fa da Ibrahim
Umma tace basu zoba tukun nan daiko mai suka tsaya yi ne, Abba yace ai zasu dawo
aikuwa basu rufe bakiba sai gasu sun shigo Ibrahim ne agaba yana kuka hajara na rike da jakar makarantar su umma tace a a lafiya kukashigo Ibrahim yana kuka
hajara t
ace umma wllh kamal ne da Hanifa suka dakemu wai mufadama ubanda zai rama mana
Umma tace to kuyi hakuri kunji wata rana sai labari, Abba yace kuje kucire kayan naku kizo kukai wa inna abincin su tace to
umma
sukashige cikin daki suna fitowa saiga
ameera tashigo da sallama tana cewa abba sannu dazuwa
yace yauwa yar inna ya innar take tace lfy lau abinci mu nazo karba tana fada
Su ibrahim suka fito daga dakin nan yawo wajan ta yana cewa anty ameera yau aka dakemu nida hajara
Ameera ta
janyo shi jikinta tana bubbuga bayansa tace wai wani dan iska ne ya tabamin kune wllh ko waye babansa saina yi masa b'alle b'alle
Ibrahim yace kamal ne da haneefa
Ameera tace kai kai kai aikuwa basu daki banza ba dani suke zancen
Umma da abb
a da yaya safiyan sukayi kuri da ido suna kallon yadda ameera take masifa
Abba yace haba yar inna kiyi musu hakuri kila suma tsokanar su sukayi shiyasa suka dakesu
Ameera tace haba abba ya za'ayi a dakesu kuma kace wai na hakura gaskiya bazai
yiyuba saina rama musu
Umma tabige mata baki tace kiyima mutane shuru uwar neman rigima to karna ganki a hanyar gidansu ma
aikuwa ta saki kuka tana ihu waiyo Allah bakina inna umma ta kasheni
Abba yayi dariya yace kai wannan yarinya da neman
rigima kike. yace mamana kiyi shuru mana ki dauki abincin ki tafi
Ai kafin ya karasa inna tashigo tana cewa iyee lalle sadiya ai dama nasan kece zaki daketa ba kowa ba to Allah idan kika sake dukanta yanzu zanyi tsukiya muci danbe nidake dan baki isaba
kike dukarmin yarinya tafada tana huci
ita kuwa ameera tana ganin inna aikuwa ta kara sakin kuka tana rungume inna tace inna babu abinda na mata wai dan nace zan ramawa su Ibrahim dukansu da akayi shine ta dakeni
Inna tace wai sadiya nace uwar
ki ta haifeta ne kokuwa a kasuwa aka siyota ne da kullin saikin daketa to bari kiji duka dai saita rama musu dan basu isa ba suci bulus ta kama hannun ta suka fita
Washe gari tinda sassafe ameera ke shirin makaranta dan yau zata daukama kannanta fa
nsar dukan da aka musu
Inna tace ameera fito mana ameera tace ganinan inna dan kwali dan daura ta fito
Inna ta kama hab'a tace a a kinga kuwa yadda kikayi kyau
Aikuwa ameera ta washe hakora tana dariya taji an yabeta tace inna ta to na tafi
Inna tace nadawo lfy tana fitowa bangaren umma ta nufa nan suma su Ibrahim anshiryasu ta gaishe da umma da abba da yaya safiyan nan suma suka gaishe da ita, ta kama hannu su suka fita
Sauran yaran bangaren suma suka fito da shirin makaranta nan s
uka fita daga gidan yaran suka isa makarantar su
tukun Rashida da ameera da nafeesa suka isa nan malaminsu yazo suka gaishe shi nan aka fara koyarwa
Ameera ce taga wani yaro yana kallon ta yana dariya dankuwa tasha kwalliya kamar aljana kuma kowa
yasan halinta dan idan aka kama fada da ita bata barin bashi
aikuwa ta aika mishi harara mai nuni da zamu hadu anjima
Ana tashi ameera da kawarta khadija suna tafe suna hira
Ameera tace kawata ki rakani yau mu casa wasu yara
Khadij
a tace yauwa dama kwana biyu ban yi fada ba hannu na har kaikayi yakeyi mutafi amma suwaye
Ameera tace kamal da haneefa mana jiya suka kama min kannan suka zanesu nikuwa nace saina rama musu dan babu wanda ya isa ya dakar min yan uwa
Khadija t
ace aikuwa sun taba bala'i dan bazamu raga musu ba
can suka hangosu ita da kaninta sun tafiya aikuwa da sanda su ameera ke tafiya har suka zo wajan su
Carab sukaji an rikesu haneefa tace uban waye ameera tace ubankine nan suka bude musu idon aikuw
a sukayi arba da ameera
Haneefa da yake itama mafadaciya ce cikin fada tace lfy kuka taremu a hanya muna tafiyar. Ameera tace maiyasa kuka dukar min yan uwa
Haneefa tace su suka zagemu , aikuwa bata idar ba ameera ta bade mata ido da kasa nan
suka kama dukan ta kamar Allah ya aikota tana ihu tana cewa kiyi hakuri wllh bazan sake dukansu ba
Aikuwa ameera tace batasan hakuri ba saida suka nada musu duka sosai dan har an fasama haneefa baki da hanci kamal kuwa marin da khadija ta wanke ma
sa har hudu
Shine ya gigitasa ya rasa inda zai nufa ya rike yar uwarsa suka tafi suna kuka
wani dan saurayine ya karaso wajan su ameera yace to iyayen fada
Ameera tamai harara tace ina ruwanka sarkin iyayi
yace ke wllh yanzu zan za
neki , Ameera da khadija suka tafa suna dariya ameera tace kama isa saidai muzaneka wllh , khadija tace kai yanzu lado in banda abinka ina ruwanka damu banza jaki alade
Aikuwa lado ya shaka yace nine jakin ? tace eh din anfada jaki bata ida ba
ya wanke ta da mari
Aikuwa ameera ta dauko wani dutse tasamu bayansa ta buga mishi yasaki kara ya juya kan ameera
Itama khadija ta dauki dutsen ta buga mishi a kugunsa aikuwa yaji zafi cikin fushi yace wllh saina karya ku yanzu nan yafada yana hu
ci
Da gudu suka bar wajan yana binsu dayake dukkansu basuda jiki aikuwa sukamishi nisa
duk inda suka fuce suna ihu suna wai mahaukaci gashi nan zai kashemu taimako jama'a
aikuwa duk inda sukabi indai akwai mutane suma mutanen rufa musu
baya sukeyi kafin kace me tuni sun yaye mutanen layin kowa gudu yake yi nan suka yako kofar gidan mai gari
mutane ne a zaune ana hira a kofar mai gari ameera ta fara zuwa mai gari ya dauko lomar tuwo ameera tayo sufa ta tsallakeshi ta taka bayansh
i
Mai gari ya wanke fuskar shi da miyar kwanon tuwo ga akwai zafi tuwon
Mai gari yasaki ihu yana cewa annoba ce ta yo nan bai ida maganar ba khadija itama tazo a mugun gudu tabi takan kafarsa ji kake kass ta dira akan kafar ta kara karfin gudun
ta
mai gari yakara sakin kara yace man liman taimaka min ka kaini gida wannan wani iftila'i ne yashigo mana gari
Liman ya yunkura zai mike
kowa yayi zuru zuru yana kallon mai gari hallau shesu kalli hanya dasu ameera suka fice
Liman y
akusa mikewa lado yace ya angizashi kan mlm bukar
Sukayi gwaran kawuna kan mlm bukar ne ya bugu da gini aikuwa wajan ya fashe sai jini
Mlm bukar rike wajan yana fadin innalilahi wa'inna ilaihin raju'un munshiga uku wannan wani irin masifa c
e bai gama fadar sauran magana ba ya hango wasu mataliyar na maza sunyo kansu da mugun gudu
liman na ganinsu yace jama'a kutashi ga wasu bataliyar nan
Suna kokarin tashi suka iskesu aka ringa tabin kansu ana ficewa
Su ameera kuwa suna ta
gudu a hanya wata mata tana tafiya ashe mahaifyar su kamal ce aikuwa suka bangajeta sukayi gaba kafin ta tashi lado ma yazo yabi da kanta
Da sauri tayi ta maza ta mike tana komawa bakin hanya
Su ameera suna gudu suka samu wanu lungu anan s
uka boye lado yazo ya fice aguje sauran ma suka fice da gudu saida sukaga sunyi nisa sosai tukun suka fito sukayo gida
Acen kuwa kofar mai gari sai bayan sun tafi liman yayi karfin halin tashi ya tada mai gari da mlm bukar yana musu sannu duk da shi
ma yaji ciwo a hannu
Amma raunine yayi
mlm bukar yace wllh ko tambaya ba'a yi wannan yarinyar ce data addabi mutane itace ta tabo wani suke wannan tseren
Mai gari kuwa sai share ido yakeyi yana jan numfashi yace wllh saina mata hukunci aje
a kiramin inna tazo sai tabiya kudi an mana gyara
Dan aike aka tura kiran inna gidanta
Inna tana zaune saiga khadija da ameera sun shigo kamar wasu na Allah sukayi sallama inna ta amsa tana fara'a tace harkun dawo
Sukace eh inna suka
shige daki dan sungaji sosai gudun dasukayi ba kadan bane a kan gadon inna suka zube
Ameera tace khadija kisan kuwa ameer ya kusan zuwa hutu nan kauyen ? Khadija tace da gaskiya , eh wllh ta bata amsa suna haka shesukaji ana sallama da inna ameera
tace ke kin manta dazun muna gudu ta kan mai gari mukabi
khadija tace to sai me dan munbi ta kansa mu mukace yazauna a waje
Ameera tace shegiya kawata kina wuta suka tafa
Inna na fita waje akace mata ana kiranta a fadar mai gari , tace to ub
an shi mai garin zai banii da yake kurana ko wani akace yana bina bashi tana hararar dan aiken
Wanda aka aiko yace inna gaskiya ban saniba kawai kizo mutafi idankinje zakiji ko menene ma
Tace to jirani na fito
ya kalleta yace badai
guduwa zakiyi ba yana kallon ta
Inna tace kai ya naga kana kallona da fuska kamar an kona jarka to ba guduwa zanyi ba tashiga ta cewa su ameera wai ana kiran ta a kofar mai gari
Ameera ta zaro ido tace inna mai kikayi
Inna tace babu abinda
nayi yanzu zanje naji naga dan iskan dayakai karata ta fada tana fitowa tace dasu kufito mutafi , sukace to suka tafi zuwa gidan mai gari inna kuwa she surfa ruwan bala'i take ita ala dole an bata mata rai tana son taji wani yan banza ne yakaita
kara wajan mai gari....
𝙖𝙣𝙖𝙣
𝙯𝙖𝙣
𝙙𝙖𝙠𝙖𝙩𝙖
✍
🏻
[23/10, 00:40] MRS. MU'UTASIM: *
🌟
AMEER DA AMEERA
🌟
*
𝙨𝙩𝙤𝙧𝙮