Showing 42001 words to 45000 words out of 338813 words

Chapter 15 - MATAR TAJ COMPLETE

tabbatr da anan part din tayi barci kenan.

Sabeeha na fitowa ta fuskanshi qibla ta tada sallah tana idarwa ta hade jikinta waje guda tana tunanin ray

uwar datayi a gidan bataji karar futowarsgi daga bedroom dinba harya karaso inda take, inuwarsa ta fara gani kafin ta dago idanunta, suna hada ido hudu tayi saurin gyara zama

tana zazzare idanu, kirjinta na dukan uku uku haka ta dake,kanta a kasa tace “goo

d morning”

Ba wannan ne ya kawoshi wajenta ba don haka ya samu waje ya zauna yana fuskantarta, “whats your name” yanda ya furta calmly yas ata dago da sauri suka hada ido, tana kallon yanda idanunshi ke kyalli, saurib dauke nata tayi muryanta kasa kasa t

ace “fatima!” Kallon bakinta yayi, sai a lokacin ya lura da yanayin hakoranta datayi magana, kauda kanshi yayi ya sake jefo mata wata tambayar, “so ke yar aiki ce?”

Tana jin haka gabanta ya bada wani dammm,

“Waya kawo ki? Who are you exactly? What was

your agenda for coming into my life?”Yanxu da ya sake magana sai taji yanayin muryarshi ya sauya, “khaal?”ya sake jefo mata tambaya,

Tana jin haka tayi saurin dagowa ta kalleshi, wani irin kallo yake mata mai kama dana tsana, don haka kawai zata iya f

asaara kallon,bai tsaya ma ya amsa tambayoyin da yayi mata ba shurun da tayi ya bashi amsa don haka ya miqe har zaibar parlor ya dan dakata,“you’re just a maid, my maid, keep that in mind and don’t have any stupid thoughts on your head, da zarar na gano ab

unda nakeson na gane zan sallameki,”

Yana barin wajen ta bishi da kallo, maganganunshi na karshe sun mata zafi sosai kamar zatayi hawaye, tama rasa wani irin tunani zatayi, he was calm at first then kuma lokaci guda ya sauya, tambayoyin da ya mata ne su

ka dawo kanta, waya kawota? What was her agenda? Duk yanda akayi hidaya ta fada mashi wani abun kenan? Daman ammu ta fada haka zata faru, gashi kuwata ta tabbata, innalillahi, yanxu wani irin kallo yake mata? Bazata iya tantancewa hakan ba, kuka bazatayi k

asa a gwiwa ba,bai nuna mata alamun ya ganeta ba kwata kwata.

Ta dade tana nazari har barci barawo ya saceta a zaune ba tare sa saninta ba.

Shi ko baima koma barcin ba yanata fama da waya yana aiki ya dade sosai har wajen karfe bakwai ya fito, ko kallo

n inda take baiyi ba ya fuce daga part din.

Bata farka ba sai wuraren karfe tara haka,yar wayar da jamid ya taba bata na gefenta, daman yawanci wayar amfanin da take mata duba time ne kawai, ba wani abun take da wayar ba, tana ganin lokaci tayi saurin m

iqewa zaune, tana nazarin me zatayi da zaisa ya tuna ta, na farko dai routine dinta data saba shi zata fara yi, maganganun ammu na kara karfafa mata gwiwa ta miqe ta wuce bedroom din, tasan a daidai wannan lokacin ya futa don haka ta fara kokarin gyaran be

droom din nashi.

Hidaya dasu fadwa basu san cewa sabeeha tana dakin taj dinba, sonata kuwa data ganta a part din nashi batayi tunanin anan ta kwana ba,sannan kudirinta har zuwa yanxu bata chanza shi ba.

***

Wajen karfe goma na safe ya shugo gidan, d

a fadwa yaci karo a kasa tana kokarin fitowa daga part dinta cikin shiri da alamu fita zatayi, tubda ya shigo take binshi da idanu, yana sanye da kayan gym yau ko sauyawa baiyiba, don yana gama workout ta nufi gida, daga sama har kasa take

binshi da idanu

tana hango gumin da ya danyi daga workout din kwance a jikinshi dukda daga ac ya fito,

he’s so attractive yet so calm and hard at the same time,kammaninshi gaba daya ya fita daban daga nasu, donshi kanar ruwa biyu yayo, the arab side of him a fuska ne th

e physique side of him kuma irin na manyan maza, yawanci fararen mazan saudi zaka gansu kamar solobiyo shidai ya fita daban, tama rasa yanda zatayi describing dinshi, the inner him is like a black American every womans dream,

Ta shagala sosai wajen kall

onshi harya wuce ta gabanta yayi kamar dutse ya gani a wajen, “hey baby brother”

Ay kamar da iska take magana, ya wuce sama ba tareda yace mata ci kanki ba, murmushi kawai ta danyi tana tuna wasu abubuwa,da yanda hidaya ke underestimating dinshi, akaha da

i zata bisu da ido dashi da hidayar taga wazai cimma wani,haka ta fuce tana murmushi ita kadai.

Tana shiga motarta tayi dialing wata number ana dagawa ta soma magana “any update!”

“Yes boss,”

“Doctor fah? Have you handle him? You need to be meticulous b

ana son any kinds of problem,”

“Yes boss”

Ana fadin haka ta kashe wayar tana murmushi kawai,dadin yanda take taimaka wa hidaya takeji ba kadan ba.



Bangaren taj yana haura wa sama ya wuce daki, gaba daya yama manta da wata sabeeha, ajiye jakarsh

i yayi kafin ya soma cire rigar jikinshi, yana cirewa ya ajiyeta a wajen ya rage daga shi sai short tight, kai tsaye ya wuce bathroom yana bude kofar yasa kai cikin bathroom din cikin saurin ta juyo hankali a tashe, suna ido hudu jikinta ya soma rawa shi k

uwa ganinta daga ita sai towel take memory din lokacin da suke cikin bathroom yazo kanshi,

burkicewar da tayi yasa juya mashi baya ta fara

Kokarin zura hijab dinta allah yaso ta shugo dashi, taba kokarin sakawa ma ya shugo, innalillahi wa inna ialihi

rajiun kawai take aranta,

Allah ya taimaka ma ta daura towel a jikinta da yake akwai towels da yawa a bathroom din ta

allah ya taimaka saida ta saka ya shugo bathroom din, shi baiyi expecting din kowa ba don haka ya shigo kai tsaye, tunda ya kafeta

da kallo harta saka hijab dinnan bai cire idanunshi a kanta ba , take kawai fuskanshi ta koma jaa sosai,sabon memory na mashi flashing, ranar da ya shigo bathroom zaiyi futsari ya kasa cire zagiyar wando, sai kuma memoryn ya sake confusing dinshi gata nan

ta tsungunna gabanshi zata zare mashi zariyar wandon shi sai lokacin daya shugo bathroom lokacin ta gama wanka harya fara kokarin taba kirjinta a bathroom din sai abun ya mashi kamar itace take kokarin sakashin yin haka, gashi ga ta a bathroom din a lokaci

n, mekenan hakan ke nufi? Kusancinsu har yakaiga shigansu bathroom a tare ko me? Wannan yar yarinyar? A maid? Har tana zare mashi zaryar wando? Yama kasa tuna what next happens after that, “What the f**k!!!”

Ya fada yana mata wani mugun kallo, jijiyoyi

nshi sun fito rado rado, tana jin saukar muryarshi tayi hanzarin juyowa ta nufi hanyar futa daga bathroom din, kamar zatayi tuntube haka ta karaso tsakiyar dakin tana haki,shiko ya kasa wrapping mind dinshi, yama rasa dalilin bacin ranshi, me sukayi da yar

inyarnan? Abunda hidaya ta fada gaskia ne? Yana ganin ta kamar karamar yarinya,did she take advantage of him da lalurar daya tsinci kanshi Koko yaya? Don ya kasa gane dalilin da yasa ya nemi taba wannan yarinyar.

Sabeeha kuwa kasa tsayuwa tayi a dakin t

a fuce bedroom din ta nufi hanyar kofa daidai nan sonata ta shugo, ko kallon inda take sabeeha batayi ba ta fuce daga dakin.

Sonata kuwa suman tsaye tayi don jarabar mamaki, cikin abund abai wuce second biyar ba ta kalli sabeehar harta gano cewa daga bath

room take donga digon ruwa nan akan fusknta, hankali a tashe sonata ta shige cikin bedroom dinshi, tana jin saukar ruwa cikin ta ya duri ruwa itama, ta dauka wajen 20mins tana zarya tsakanin dakin yanda kasan ta dauka 2hrs haka takeji, allah allah kawai ta

ke ya fito taji meya kawo sabewha da sassafe dakinsa, badai kwana tayi anan ba?“Haa it can’t be possible” tana gama fadin haka saigashi ya fito daga bathroom, yana ganin sonata ya sake hade rai, daman ranshi a bace yake, wankan ma cikin bacin rai yayi yana

kallon gabanshi, dake shedan shugaban yan zuga ne haka ya dunga raya mashi banzan abubuwa akanshi, yanxu haka yarinyar nan taga jikinshi? She take advantage of lalurarshi, sai yaji gaba daya ya tsaneta, ko kallonta baya son yi.

Sonata na ganinshi gaba

daya abunda ke kanta ya warware tama mance da haushin da takeji,nufoshi tayi ganin yana neman karasawa wajen walk in closet, “babe good morning”

Ko kallon inda take baiyi ba yace “excuse me” yana fadin haka ya wuce bathroom, tasan me hakan da ya fada yake

nufi, ta futa zai shirya kenan, harta juya jiki a mace zata futa ganin yanda ya mata magana ta dakata, wani irin smirking flirty murmushi tayi kafin ta tunkari walk in closet din, tana shiga ta karo kofar wajen yana kokarin shafa body sprays dinshi,

“Ar

e you deaf” ya fada in a harsh to, ay ko sauraron sa batayi ba ta tunkari inda yake tun kafin ta karaso ta dakatar da ita, “dont you dare take a single step” tana jin haka ta tsaya kyam,

Take ranta ya baci ta soma magana , “why are you pushing me away ba

be? Why? Don’t tell me it because of that maid?”

Da mamaki ya dago yake kallonta, kishi ya rufe mata idanu sosai, “yes, is it because of that ugly maid? Did you sleep with her? Huh?”

Yanda take magana kamar zata tashi sama, ranshi idan yayi dubu ya baci

sosai, comparing dinshi da wannan yarinyar kadai da takeyi ba karamin bata mashi rai yake ba, take ya daka mata tsawa

“Get d hell out!!!!, this should be the first and d last time da zaki kara shugo min part dina, idan na kwana da ita whats your problem

with that? Isn’t She my wife!!!!!!”

Ay kamar ya buga mata guduma aka, kuma yaga hakan a fuskanta, daman ya fadi hakan ne donya baqanta mata rai sosai,batayi wata wata ba ta fuce daga dakin rai a bace kamar zata amayar da kayan hanjinta don masifa.

Afiy

a na kwance a daki tana barcin asara sonata ta shugo, tana karasowa inda afiya take ta soma tashinta “babe babe”

Sama sama afiya ta soma jinta, harta bude idnaunta ahankali, ganin sonata na kuka yasa afiya ta zauna tana kallonta tace “yadai?, kuka fa kike

yi? Ko haryanxu kin kasa samunshi? Wai whats so special about him, that thing da kike nema a jikinshi akwai thounsands da suke dashi kuma kina samu, what so special about him”

Sonata najin abunda ta fada ta soma dunqule hannunta tana furzar da huci taka

ici tace “If i can’t have him then no one should,”

Da mamii afiya ta kalleta don bata gane inda ta dosa ba, “what do you mean”

“Babe i need your help,yarinyar nan jiya a part dinshi ta kwana, qila ma tare suka kwana ,what if he slept with her? What if sh

e got pregnant bfr i do? Plan dina will be ruined i need your help”

Shuru afiya tayi tana sauraronta itafa wannan batada hankali, kallonta kawai afiya keyi, batasan cewa addinin mu bai amince da cikin da babu aure ba, duk plan dinta was ta knock him off a

nd have him sannan ta samu ciki dashi wannan zaisa bazai barta ba, batasan cewa intimacy bfr marriage is prohibited kuma shi zaiza ma bazai taba auren nata ba bayan wannan ma auren baturiya? kafira kuma yar bariki ma? That’s impossible.

“Babe are you even

listening to me” sonata ta tamabyi afiya

“Yes come again?”

“Yarinyar nan a dakinshi ta kwana, lets do something bfr its too late”

Afiya najin haka tace “trust me ans just calm down okay”

5pm…

Kusan a tare duk sukayi parking motocinsu, motar hiday

a ce ta fara shugowa kafin ta fadwa, gaba dayansu kana ganinsu kasan da bala’i suka dawo gidan, tunda sukaji batun kwanan sabeeha a dakin taj, afiya ce ta kirasu ta shaida masu hakan conference call ma sukayi. kowannensu da abunda ke cikin zuciyarsa.

Su

na shugowa cikin gidan hidaya tasa head maid ta kira mata sabeeha, daidai nan taj ya sauko daga sama daman hidyaa ta kirashi a waya.

Duk kusan a tare duk suka karaso, yana zuwa ya zauna kan kujera ya daura kafa daya kan daya, hidaya dai tana mamakin yanda

ya dan fara sauyawa, gaba daya attitude da bai taba yi ba take ganin yanayi yanxu,bama wannan ba tukunna, maganar yarinyar nan da afiya ta tsorata su ne a gabansu inda tace masu ay a dakinsa ta kwana, kuma barinta around him is vwry risky, he could easily

trust her once again tunda itace wadda ta kula dashi lokacin da baya cikin hayyacinsa.

Sabeeha na futowa tundaga nesa ta hango cirko cirko, ga sonata ga afiya ga fadwa a zaune hidyaa ma a zaune sai taj shima yana daga zaune, tareeq ne dai baya nan.

Tun

da ta karaso gabanta ke dukan uku uku,

Hidaya na kallon taj din babu wasa kan fuskanta ta turo mashi divorce paper tace “sigh this up”

Daukan paper yayi ya soma karantawa, takarda ce ta yanda akeyin saki irin nasu achan kasar, yanda addini ya tanadar,

aaida ya karance paper tass kafin ya dago ya kalli hidayar, “dis what i should have done already,we wouldn’t know whats she might come up with, tunda wanda ya kawota baya raye, i don’t trust her, yanda yayi kokarin cutar dakai itama zata iya yin haka”

Sab

eeha najin haka gabanta ya bada wani dam, tunda hidaya ta soma magana take kallonshi, shi baika san tana wajen ba kwatakwata,

Idanunshi na kan paper,

“Maybe ma harda ita akayi planning kidnap din,” fadwa ta karashe tana mata wani mugun kallo,

ta ajiy

e mashi pen agabanshi, daman kamar jira take tamafi kowa kosawa tunda afiya tace mata idan har sukayi wasa wani abu zai iya shiga atsakaninshi da yarinyar.

Gaba daya binshi suka dunga yi da idanu ganin yaqi motsawa,sabeeha kuwa a daidai wannan lokacin b

abu abunda take sai hawaye, wato abunda suka kulla kenan, su maida abun zuwa khaal, sun kulla mashi duk sharrinsu akanshi, yanxu sa sukaga taj din zai iya ganowa shine suka maida kan khaal kenan, ita kuma da khaal ya aura mashi ita dole za ayi zargin bakin

su daya da khaal tunda ya bata property din taj, bayan wannan ma tasan hidaya ta gano cewa khaal ne ya kawo ta gidan ba tare da saninsu ba, so they want to use that against her, “innalillahi wa inna ialiahi rajiun” ta furta ahankali, kunnsshi ne kadai ya j

iyo mashi furucinta,sai yaji presense dinta a jikinshi,allah allah take ya dago ya kalleta amma yaqi, baiyi wata wata kawai ya dauka pen din ya sanya hannunshi kan paper din, yana kokarin rubuta saki kawai sukajiyo muryar ammu data futo, barci takeyi amma

wani ikon allah haka kawai ta farka a daidai wannan lokacin gabanta na faduwa, wannan yasa ta fito kuma taji gaba daya abubuwan da sukace, tsayarwa datayi tana hangosu jiran decision din taj din kawai take.

“Karka sake ka rubuta komai kan paper nan”

Gaba

daya dagowa sukayi suna kallonta,fadwa ce tayi saurin miqewa tsaye tace “why? Saboda me ammu?”

Ko kallon inda take batayi ba ammu ta karaso inda sabeeha take tace “bazata bar gidannan ba, she can never, ko kun raba aurensu abunda ke tsakaninsu zai maido

su”

Da mamaki duk suka juyo suna kallonta, hidaya data kagara da zancen ranta idan yayi dubu ya baci da maganganun da ammu keyi, tace “i have said it all, yarinyar nan yau zatabar gidannan, dama chan we have never accepted her she can never be part of thi

s family”

“Well yanxu dole kuyi accepting dunta tunda she’s PREGNANT!!!!!!”

Gaba daya dakin ya dauke wuta kamar mutuwa ta gifta, fadwa afiya hidaya sunji maganar ammu kamar saukar aradu,

“She’s pregnant for him”

Suka ne kawai sonata batayi ba don baq

in ciki, hidaya kuwa idanunta yayi jaa sosai, shi mai gayya mai aikin gaba daya ji yayi kamar an toshe mashi kunne sai kawai ya saki pen din, idanunshi yayi jaa sosai ya dago suka hada idanu da sabeeha, take yaji kamar an zuba mashi ruwan dalma a zuciyarsh

i tsabar bacin rai, sabeeha kuwa baiwar allah kamar ta kurma ihu tsabar furgici, tama kasa karantar yanayinshi gaba daya mai wuyar fasaara, da kyar ta dauke idanunta akanshi ta maida kan ammu, saurin runtse mata idanu ammu tayi alamun tayi trusting dinta,

hannunta ammu ta kama ta rike dake ta faman karkarwa, me ammi take nufi da abunda ta fada yanxu? Dauke idanunta tayi daga kan ammi ta maida kan mutanen dake parlorn sai suka dunga mata wani irin gizo, tana hango bala’i cikin idanun kowannensu…..itama ammu

karfin hali ne yasa ta fadi hakan…….



💋

BOSS LADIES WRITERS

💋



MATAR TAJ (destined with you

🩵🤍

)

Written by

Queenmarh





Book2

PAID

Chapter 66

Update!!

Unedited!

Fadwa ce tayi saurin miqewa taba kallon sabeehar sa ammu tace

“no thats not possible, karya ne”

“Daman ana karya da ciki?” Ammu ta jefo mata tambaya kafin ta maida dubanta ga taj din dake zaune tace, “yanxu saikayi deciding, zaka koreta ne da cikinka a jikinta?”

“Ammu…..ya za ayi mu yarda nashi ne? What if ba nash

i bane?” Fadwa ta sake jefo ma ammu tambaya, gaba daya kamar tama fi kowa rikicewa tsavar bacin rai,

“Ay gashi nan a gabanku, shi yasani idan ma nashi koma ba nashi bane, decision ya rage nashi to decide on that, saidai inason ka sani, all this while yar

inyar nan tana tare dakai, kuma tare kuke kwana duk kun san da wannan,”

Tunda suka soma magana hidaya tayi shuru tama kasa cewa komai, she


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login