Showing 126001 words to 129000 words out of 338813 words

Chapter 43 - MATAR TAJ COMPLETE

baima tsaya ya sake kallonta ba ya wucewarshi, ta miqe ta wuce sama.

Da sall

ama tayi knocking kofar bayan an bata izini ta shugo, anne na zaunw kan babban carpt din parlornta gabanta shaqe da warmers na abinci data gama ci, sai cup din tea da take sipping.

Zama maya tayi a kasa kusa da ita tace “barka da dare anne na, you called

for me”

“Yes i did”

“Inaso ki tattaro kayanki gaba daya daga part din sameer ki dawo nan,”

Hankali a tashe ta kalleta, harga allah batason dawowa nan wallahi, part din anty laila tafi sakewa sosai achan, babu takura babu tsangwama, idan zata futa sau da

ri babu wanda zai tsaya questioning dinta, shes just living her best lif.

“Anne, I’m comfortable achan, and ina taya anty laila yan gyare gyare”

“Wani gyare gyren zaki tayata tanada helpers har guda uku?”

“Anne….”

“That’s final…and secondly karki sake

treating helpers din gidan nan yanda kikayi treating yarinyar nan daxu, suma mutane ne kamar kowa and sunada gata, treat each and everyone one of them with respect understood?”

“Yes anne”

“As from today Hamad zai dunga kaiku school and shi zai dauko ku,

jeki saida safe”

Miqewa maya tayi, ko iya amsa mata saida safe batayi ba ta futa rai a bace kamar ta kumbura ta face.

Tana saukowa ta soma dialing number mummy ta.

Cikin shesheka ta soma magana “Mummy na gaji, na gaji, I don’t want to stay here anymore

please its been 2yrs now mummy”

“Meya faru baby? Whats wrong talk to me?”

Aka amsata daga chan, “nidai kawai na gaji, i hate the environment here, i missed you i missed daddy dan Allah kumin booking flight na dawo”

“Haba baby na, yanxu fa zaki shiga fin

al year, i promise you zamuzo nida dady, aiki ne sun mana yawa kinji, i missed you more than life its self my dear,dont cry okay,”

Rai a bace maya ta kashe wayar, daman tasan bazasu yarda ba, ita ta gaji da garin nan, ta gaji, she missed everything, her l

ifestyle, rayuwanta achan england her friends komai ba, gashi yanxu an fara saka mata strictness tun ranar da nanna ta ganta a hotel”

Samun waje tayi nan bakin compound ta wajen backyard ta zauna tana hawayen takaici.

“Zaki bata kyakyawar fuskarki da haw

aye,”

Dagowa tayi taga hadiza tsaye, hannunta rike da smoothie data lura da shi sukafi sha ita da laila.

“Waya bata maki rai kike kuka?“

Wani irin banzan kallo maya ta mata, “kiyi hkuri idan tambayar danayi ta bata maki rai, amma duk wanda ya bata maki

rai allah bazai barshi ba, kuma an dau hakkin ki da daddaren nan an sakaki kuka”

Wani irin sanyi maya taji aranta, saitaji kanta na wani irin girma sosai, “ga smoothie, indo tace kinason shansa da sanyinsa ko”

Kallon smoothie din tayi sannan ta amsa, kur

a mata idanu hadiza tayi har saida ta saka straw din a bakinta tasha kusan rabi, murmushi hadiza tayi ganin tayi kamu babba.

“In zauna a kasa in jira ki gama” batajira amsarta bama ta zauna a kasa tana kallonta jefi jefi,wayarta ne tayi ringing ta amsa,

“haba babe sai yanxu zaka kirani?”

Chan akayi magana wadda daga maya sai wanda ke maganar sukeji, “dan allah kayi hkuri,zamu hadu, im in a tight position rn”

Tana gama magana sai kuma tayi wani makirij murmushi hadiza na kallonta harta gama wayar ta miq

a mata sauran smoothie din harta tashi hadiza ta miqe tace “toh saida safe”

Ko kallonta bata sake ba ta wuce part din anty laila ta shaida mata abunda anne ta fada, ran anty laila ya baci sosai don ta rasa meysa anne

kejin haushin duk wanda yazo kusa da i

ta, me akema mayar da suke tunani? Inba suna tunanin wani abun take mata ba mey zaisa tace ta koma part din, kai abunnan ya bata mata rai sosai.

Washe gari ta kama sunday, duk wani preparation da anne tasa a mata anyi komai, kama daga registration da sa

uransu, harkar masu kudi, duk wani abu daya kamata a nema anne tayi providing wanda bai samu bama tace za a kawo daga baya.

Wajen karfe bakwai da rabi na dare anne tasa aka kira hadiza da sabeeha, saman suka hau har inda take sabeeha sai kallon saman take

ya burgeta sosai don gaskia masu arziki ne sosai nesa ba kusa ba, saidai ba komai ke dadata ba don taga abubuwa sosai na morewar rayuwar a saudi, nan dinma dai ba banza ba.

Tunda hadiza taji anne na nemansu sama gaba daya ta rasa natsuwarta, ta kira ja

mila yakai sau goma bata dauka ba, sabeeha ko ta tambayeta yafi sau ashirin shin ko tayi wani laifi ne, don har kusan marinta saida tayi, duk a tunaninta ko tayi wani abun da ya jawo za a koresu, hakanan ta wuce saman sabeeha na biye da ita a baya.

Suna s

hugowa parlor ba kowa sai kamshin turaren wuta mai dadin gaske dake tashi.

Shugowar ta kamar shugowar wata basarakiya, she’s a definition of strong woman, bata daukan nonsense sannan bata yarda kwata kwata a taba mata ahalinta, the santuraki name has be

en going for over decades.

Zama tayi hadiza ta dan duka daga zaune wani irin maqoqon baqin ciki na bullo mata a zuciyarta, wallahi bata kaunar matar nan kwata kwata ko kadan.

“Hajiya ina wuni ya kafa”

Kai tsaye anne ta amsa ta “lafiya, ya baqunta”

“H

ajiya ay babu baqunta, gida ne nan din ay”

“Masha allahu”

Muryarta a sanyaye tace “Ina yini”

“Lafiya lau”

Shuru ne ya dan biyo baya, kafin anne tayi gyaran murya tace “gobe ki shirya zaki bi su laila makaranta, duk wani abunda zaki buqata yana wajen ha

mad”

Da mamaki hadiza ta dago, don bata gane kan zancen ba “hajiya ay bata zuwa makaranta”

“”Gobe zata fara”

Shuru hadiza tayi tama rasa me zata ce, “duk abunda kike buqata ki fada”

Sunkuyar dakai sabeeha tayi, wallahi taji dadi sosai aranta ba kadan b

a, bata tabsa tsammanin tana da wani rabo na karatu ba tun bayan dan wanda tayi a saudi,”allah ya saka da alkahiri allah ya kara budi ya kara arziki mai albarka”

Murmushi anne tayi tace ameen”

Sai a lokacin hadiza ta dawo daga tunanin data shiga, ta dan

murmusa harda sunkwi dakai tace “allah ya albarkaci zuria, ya kara arziki mai albarka mun gode sosai hajiya kun gama mana komai”

Girgiza kai kawai anne tayi ta sallamesu suka sauka kasa, tun daga corridor suka raba hanya hadiza tayi waje sabeeha ta shiga

daga ciki tayi shimfida ta kwanta.

The next morning ta kasance monday morning, the first week of new session kenan, cikin shiri laila ta futo ta nufi part din anne dukda akwai dan tazara tsakanin nasu, tana shugowa ta wuce sama other side part inda maya

ke ciki, koda ta shiga barcinta take hankali kwance ba takura,dakin yayi kyau sosai wallahi ba kadan ba.

Jan bargonta laila tayi tace “wakeup 9 ya kusa ki tashi haka nan”

Yaudai ta tashi other side of the bed, don tunda maya ta tasheta take masifa, aha

ka dai tayi wanka ta soma shiri, shafa chan goga chan haka ta dunga yi, laila ko tunda ta fita daga dakin kasa ta sauko, hamad ya shugo, indo yasa ta kira sabeeha, aikuwa sai gata ta fito sanye da kayan laila da aka bata sai kuma hijab data zabga akai.

Mu

rmushi laila tayi tana matsowa kusa da hamad tace “yaya whats her name”

“Ask her your self” ya bata amsa

“Kai amma tana kama da..”

karasowar sabeeha da gaishesu datayi yasa laila dakatawa tace “good morning to you too, finally na samu course mate”

Mur

mushi sabeeha ta danyi mata hamad ya kauda kanshi.

Kamshin turarenta ya tabbatar masu ta iso fa, hamad yayi gaba abunshi bashida time dinta, tana saukowa ko kallon inda laila ke tsaye da sabeeha batayi ba tace “muje”

Gaba tayi laila tabi bayanta sabeeha

followed them too har gaban range rover dake parke,

“Ya hamad wazai zauna a gaba”

Sai a lokacin maya ta dago taga sabeeha, take yanayinta ya sauya, “ina wannan din zataje?”

“School” kai tsaye laila

Ta amsata

“Wani school din?”

“School dinmu mana,”

“Wtf, house maid din ce zata bimu school? Kula damu zatayi achan din kokuwa”

Ran hamad ya baci ya futo ya budema sabewha kofar gaba yace “get in”

Jiki a mace sabeeha ta shige,maya ta kama kugu, “wai meye haka ne?”

“Ki shugo dan allah zamuyi latti fa”

A

fusace ta bude bayan ta shiga ta zauna, tana mai hararan kujerun gaba, ta rasa me kawo yar aiki yake nufi? Nannying dinsu zatayi ko menen?

“She’s schooling with us, jiya anne ta fada ma ya hamad nima wajenshi naji”

Message din da laila ta tura mata

ne yasa ta doka wani zagi, “kam bala’i, wallahi bazai yuwu ba”

Kasa kasa laila ta soma mata magana “anne fa tace dole ta dunga binmu school, why are you untop of your voice? Zaki hanata zuwa ne”

“But this is so unfair, ya za ayi a hadamu da yar aiki? Dis

gusting people? Ay abun kunya ne ma idan aka gane, sannan kuma a hadamu a mota daya?”

“Not a single word from your uncontrollable mouth, idan kika sake magana cikin motar nan you will get out”

Bakinta fa baya shuru, batasan naga da ita ba “that will be b

een better”

Bai kulata ba ya cigaba da tuki, sabeeha dai tayi shiru kuma duk taji abunda ta fada don daga murya take sosai, aranta sai takejin wani irin zafi,

Har cikin school ya shiga dasu, afusace maya ta futa afiya tabi bayanta ya rage daga sabeeha sa

ishi a motar.

Wani envelope ya bata dake kunshe Entry card da wasu document haka harda timetable din course din da take.

Hannu buyu tasa ta karba taki yarda su hada ido dashi, tun ranar,

“Your Entry card and other accessories da zaki buqata, zan baki nu

mber na take it down, idan wani abu ya taso just give me a call”

Godiya ta mashi sannan tace “banida sim a wayar”

“Okay” kawai yace mata sannan ya fito itama ta fito ya jagoranceta zuwa cikin makarantar, dake

Shima anan ya gama karatu so yasan wurare so

sai haka ya dunga zagaye da ita ya nuna mata wurare sosai sannan ya hadata da lecturer da zai engaging dinta in some activities din da ba lallai ta iyasu ba ko ta sansu karya zamana ita ce aka bari a baya.

Koda ta shiga first lecture she was so uncomforta

ble, dukda kowa na harkarshi, haka ta samu chan kuryar class ta zauna, kuma tunda aka fara karatun tana dauka dake kanta na jaa sosai.

A second class suka hadu da laila, she was so nice to her wallahi, harta saya mata lunch ta kawo mata auditorium dinsu.

Lokacin tashi nayi hamad yazo ya daukesu, maya dai sai faman gunguni take, rai a bace har suka iso, su auka fara fita sannan ya bama sabeeha sabon sik card tayi mashi godiya ta wuce cikin gida.

Da sallama ta shugo dakinsu ta tadda hadiza na cin abunci,

ko kallonta batayi ba saika sabeeha ce ta mata sannu da hutawa.

“Keda wa kuka tafi makarantar?” Itace first question datayi mata.

“Nida su biyun nan bansan sunayen su ba sai yayansu”

Girgiza kai hadiza tayi aranta tace “samun waje”

Da daddare sabeeha

ta cire sim din da mutallib ya bata a samsung din ta saka sabon, tunda ya bata wayar bata taba kunnata ba sai yanxu, tana saka sim din number shi kawai ta fara gani yayi saving da ya hamad, saita samu kanta da dan murmusawa, don yanada kirki sosai bashida

fada kamar dayar kanwar tasa jarababbiyar, ita dayar kuma babu ruwanta very nice.

Saudii..

Yau kwananshi biyu a hotel, and so far that’s what make him relax and revive abubuwa da dama, rabonshi da mutallib tun ranar and he regret yanda suka kare not i

n a good terms, he didn’t listen to him yanda ya roki hakan, abunda yasa yayi reflecting har yayi dana sanin rashin jin daga gareshi shine tunawa da yayi da sabeeha, haka ta dunga rokonshi akan ya saurareta yaqi, ya amince da ita yaqi, ya fuskanceta yaqi,

al’amarinta ya mashi katutu azuciya, he feel guilty of his action, the way he treat her the way ya dunga wulaqantata its pains him.

Abun na biyu kuma maganar detective da yayi, he has come to conclusions of yanda zaiyi, he wants to be center minded, leavi

ng all emotions behind, dole ya gano komai.

Knocking da akayi mashi ne yasa yace “yes come in” Aka shugo, wannan baturen ne yaronshi ya shugo fuskanshi wasai, “morning sir”

“Morning merk”

“Your suit and the cards are all ready” baturen ya fada

“Thank

you merk”

Fita merk din yayi shi kuma ya miqe zaune kugunshi na daure da towel ya sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ya tako gaban dresser yana kallab

attractive muscles dinshi, “i have to do this” ya fada beneath his breath.

A gaggauce ya shirya ciki

n suit din da suka amshesa sosai ya saka rolex dinshi sannan ya zauna ya saka sock da givench covers ya miqe tsaye, kokarin bottoning wandonshi ya soma sabeeha ta mashi flashing sanda bashida lafiya, tana saka mashi button din riga, saurin runtae idanunshi

yayi yana hango yanda take mashi smiling.

kauda tunanin yayi hanzarin yi kafin jikinshi ya mutu ya saka tie ya feshe jikinshi da turare, kai masha allah la kuwwata illa billah, he looks damn richyyy cute and handsome, irin mafia boss dinnan, curly hashin

nan sai kyalli suke, fuskar nan sajen dake wajen ya kwanta baki lub, ya cika namiji cikakke ingarma lols

Wata gucci bag ya dauka dake dauke da surface a ciki da wasu important abubuwa sannan ya fito gabanshi na faduwa, addua yayi take yaji duk wani abu

ya kau mashi ya shiga lift ya sauko kasan.

Yana fitowa baturen nan ya bude mashi seat din baya har da dan sukwi dakai, hannu kawia ya daga mashi ya shiga bayan ya zaune shi kuma ya zagaya dayan side din ya zaune shima driver ya jasu.

Motar ba motar daya

zo da ita bace, wata zabgegiyar ford ce, bayanta an kafa T-ford a jiki, the only car he designed for him self, guda uku ce kawai kaf duniya.

Tafiyace mai dan tsayi sukayi babu abunda yake sai kallon window da yanda ciyayi ke yawo, “everything is set sir



Juyawa taj yayi ya dubeshi, ya dan maida idanunshi kan screen din gaban shi ya kalla shima kafin yace “good job merk”

Daidai taheel company motar ta tsaya, kai zo kaga idanuwa kowa ya juyo yana son ganin wazai futo, bai wani ja masu rai ba ya futo, mai

estically kai kuzo kuga kallo, baki a sake mutane ke kallon shi, surprisingly unsurprising, waenda suka san lafiyarshi lau basuyi mamaki ba don toshiyar baki aka masu, tafiya yake kamar bahubali ana matsa mashi ana sunkuyawa to show utmost respects to him,

kwarjini da haibarsa kadai bazaisa ka tunkareshi bama.

Kai tsaye ya shigo reception nanma suka bishi da ido, kowa na tsoron tunkararsa karma mutun ya rasa aikinsa.

Merk na gefenshi suka shiga lift basuyi landing ko’ina ba sai office dinta.

Nanma secrwt

ary dinshi na ganinsa harzai tafi ciki ya dakatar dashi, dole ya tsaya merk ya bude mashi kofa ya shugo daga ciki.

Unexpectedly kawai ta ganshi ya shugo dagowan da zatayi, saida gabanta ya dan fadi, kai tsaya yaja kujerar baki ya zauna ya daura kafa daya

kan daya, yau ko tukarar inda takema baiba.

“Good morning mrs hidaya”

Kambuuu, hidaya nitsewa ne kawai batayi ba ta zuba mashi ido, is he insane?

“Ba tare sa wani bata lokaci ba i have a deal to make”

Mikewa tayi ta zagayo gaban table ta hade hannu a

kirjinta tace “taj taj taj…yaushe ka girma haka har kana take dokokina, har kanada audacity din tsayawa gabana trying to make deal with me? Ka fara shaye shaye ne? Ni kake fadama wannan magana”

“Mrs hidaya this is an office, not here to argue”

Nade hanna

yenshi yayi yace “i have 2

Options, give me a position or i take what is rightfully mine”

Damm taji gabanta ya sake badwa saidai bata nuna mashi komai ba saima wani irin kallo da take mashi mai wuyar fasaara, yana hango tsantsar tsana, irin muguwar tsana

r nan don shi kadai ne shimfide kan fuskarta har saida ya dauke idanunshi akanta don he couldn’t believe it, so this is it? Wannan ne kadai zai bashi answers to his questions and he will truly see whats been hidden for over the year, THE TAHEEL COMPANY!!!

Ga mamakinshi sai yaga ta fashe da wata muguwar dariya irin sosai dinnan fa, saida tayi mai isarta ta ta tsagaita ta kalleshi “tajudeen lallai ka girma, you want a title right? An office? Okay go ahead”

Kallon cikin idanunta yayi, yana kara mamaki ba kad

an ba, “is this who really she is, did he think of her other way? What really is she?

Miqewa yayi tsaye ya juya zaibar office din, “be careful you might trip over, and don’t think of playing games with me”

Hidaya fa ? Hidaya ce ke mashi wanna. Magana

kamar wata enemy dinshi? Bai tsaya ya kara sauraronta ba ya fuce.

Gulma ta gama karade office ko’ina, babu abunda ake fadi sai the coming back of the heir”

Reporters kuwa duk sun gama cike campanu, waiting for opportunity amma babu.

Office aka bashi

as the ED, office ne mai kyau don yana gaba da coo, da GED rank wato group executive director rank din hidaya kenan.

Tunda ya zauna babu abunda yake sai nazari, hes so lost in his thoughts about


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login