Showing 207001 words to 210000 words out of 338813 words
kuma suka raba a tare.
Toh kodai dalilin dayasa ake namanta kenan, bazia manta irin maqudan kudaden da suk
a raba ba shida oga har fili saida ya saya a duten habuja duk jamila bata saji ba badan kudin sun kare da wuri bama ta hanyar chacha da yakeyi ay da har aure zai karo.
Sai kawai jamila taga yana murmushi a ranshi yace “harka ta samu kenan”
“Yanxu dai kin
san inda hadizar take ko?”
“Eh har gidan naje wallahi”
“Toh ay shikenan” ya fada tare da wucewa daki, ko minti biyu baiba ya kwado mata kira aranta tace jarababbe.
Tunda ya dawo gida bai sake futa ba sai wajen karfe biyar, yana futa sabeeha ta lallaba
ta wuce part din nashi, tayi abunda zata ta fuce.
Yana cikin workout cikin gym din daya fara zuwa wasu yammata sukazo inda yake tare da mashi sallama.
Irin classy abuja babes dinnan ne da sukagaji duniya sosai dan kowacce da yan kudadenta a jiki, ansh
a bbl duwawu tuku tuku kana gani kasan na natural bane ga attchment da sukaji akansu da suka daurama dankwali.
Sallamr da sukayi ne yasa ya aje abunda yake ya dago shi kwata kwata baima san dashi suke ba harya miqe zia bar wajen daya daga cikin babe din w
adda tayi dayar kyau tace “hey!!!, can i have a minute with you”
Fuskanshi babu yabo ba fallasa ya tsaya ya kalleta daga yanda take magana ya gane irin matan nan ne da suke flirting da mutane.
“If you don’t mind can i have your digit?handsome?”
Smirking
yayi kai tsaye yace “taken, excuse me please”
Yana fadin haka yabarau tsaye a wajen suka bishi da kallo, “teets daman na fada maki ba duka fararen nan ne masu son mata ba”
“Karya ne wallahi babu namijin da zai ganni baiji wnai abu ba”
“Okay then keep t
rying your luck”
“Kiji wai he’s taken?, ay wallahi ko mata goma ne akanshi teets saita sameshi,”
“Shegiyar gari” suka fashe da dariya harda tafawa.
Yana futowa daga wajen salim ya kirashi, ya shaida mashi yanda sukayi da agent din agency dinnan wanda
ya basu information din jamilu.
Yana aje wayar ya sauke ajiyar zuciya beneth his breath yace “where are you? FATIMA…..?”
…
“Mama..ana kiranki a waya” dan jamila ya kawo mata, kallon wayar tayi ganin yaron ya dauka kamar ta kwada mashi mari tace “taf
i dan ubanka bana hanaku daukan min waya ba”
Futa yaron yayi jamila ta kai wayar kunenta, dahiru yayi dariya yace “jamila kenan, tun jiya inata kira bakya dauka”
“Kai dahiru nifa matar aurece, kiran da kakemin bai dace ba karka sake kirana dan Allah”
“A
y baki isaba wallahi jamila, dole na kira ki dauka”
“Inkai ubana ne saika snai na dauka,kai wallahi jamilar daka sani a sa ba itace yanxu ba wallahi”
“Toh toh madallah, nace ba? Yar kawarki harta girma ashe? Ina nufin yarinyar da..”
“Dahiru…..!”
Ta kir
a sunanshi da karfi, “jamila kenan, kina tunanin zaku rufen baki ne? Kina tunanin na manta ne? Shekaru ashirin da doriya da suka wuce keda kawarki..”
“dakata haka ya isa, ay ban manta ba, bari zan kiraka anjima mijina ya dawo” ta kashe wayar kit…
Jamila
fa har zufa take sosai, ada tayi tunanin ta raina mashi hankali ashe yasan me yake, ya zatayi da wannan shegen?”
Kiran hadiza tayi a waya “hadiza akwai matsala…”
After 2 days…
Kwanan rabi biyu tana zazzabi, ayyukan daya shafi gyaran sama sabeeha ce ke
yi, ita ke dafa abunci da ake yima anne da nanna na karin lafiya.
Tundaga ranar ta kara tabbatar da yarinyar nada kazar kazar, sannan tana da amana, don sau wajen biyu anne na aje kudi intentionally ko zata dauka amma ko mataar dashi ba a yi kwata kwata,
gashu duk sanda zata gaishe da babba saita duqa har kasa saboda respect.
Lokaci guda anne taji yarinyar ta shiga ranta, nanna ko daman babu wanda zai yabi sabeeha kamarta.
Tana gama ayyukanta zata wuce dakinta ta zauna, kwata kwata bata yarda ta hada han
ya da yan gidan, allah ya taimaketa ma suna hutun makaranta.
Bangaren taj ko duk sanda zataje saita ambula hijabi ta rufe fuskarta kwata kwata bata yarda ta bari ya ganta ba, kuma allah ya taimaketa duk zuwan da take dakinsa tana gyara basa taba haduwa.
Akwai ranar da suka kusa yin clashing shida ita, ta futo daga part din anty fadila datasa azo a dauki lunch dinshi rabi tace taje ta karbo saboda su laila basa nan sun fita.
Haka ta zumbula hijab taje ta karbo abunci sannan ta dawo, tana gab da bude kofar
part din aka budo daga ciki, cikin sauri ta matsa tare da kauda fuskanta, kallo daya mata ya kauda kai ya wuce abunshi, ta sauke ajiyar zuciya tashiga ta aje sannan ta futo.
Kwata kwata bai taba kai attention dinshi gareta ba. Toh ta ina ma zai fara tuna
nin itace?
Cikin kwanakin nan taj yaje agency dinan yafi a kirga, da salim ya lura kamar raina masu hankali sukeyi suna karbar kudi dayaji haushi kawai yace ma taj babu kamshin gaskia atattare da mutanen, taj believed so aswell wannan yasa salim yayi t
hreatening dinsu indai basu kawo jamilu ba zasu saka hukuma a lamarin, don gaba daya basu da gaskia.
Abokin jamilu kuwa dayaji yayi saurin kiransa ta sabon layin daya chanza ya shaida masa komai, jamilu fa ido ya raina fata, idan aka gano komai zai iya sh
iga matsala, gwara tun kan akaiga hukuma ya fada masu gaskiar shi bashida alaqa da yarinyar kuma ya kaisu inda take kar ace za a kamashi.
Waehe gari da safe da kanshi ya tafi agency, oga ya nemi salim a waya don ya bada katin sa, ya shiada mashi jamilu
yazo, salim ya kira taj ya shaida mashi threat din da suka masu yayi aiki don jamilun ya bayyana kanshi, ko abunci kasa tsayawa taj yayi yaci ya futa.
Harya gane wajen don da kanshi yakai kanshi suka hade da salim.
Suna shiga jamilu yayi kuri kamar muna
fuki a zaune.
Oga ya kallesu yace “dan allah kuyi hakuri, kar kusa hukuma a ciki gashi nan wannan ne jamilu”
Salim ya dubi taj yace “this is jamilu,“
“Oga dan allah kuyi hkauri, dan darajar allah karku kamani”
Salim ya kalleshi yace “babu abunda zamu m
aka, tambaya daya biyu zamu maka”
“Kasan wannan yarinyar??”
Kallon hoton jamilu yayi yayi kamar bai ganeta ba
“Tayi wani laifin ne? Sata tayi ne? Kamata zakuyi?”
“Ah ah babu abunda tayi ka kwantar da hankalinka babu abunda zamu mata”
“Toh a gaskiya ni
dai ba marikinta bane,anguwwar mu daya nida mahaifiyarta wadda ta kasance kawar matata, toh shine daman ta nemi alfarmar a nema mata aikatau, saboda yarinyar bata da uba shine na rubuta nine marikinta”
Salim ne ya dubi taj ya mashi fassarar komai taj ya m
ashi magana da turanci shi ba wannan dogon bayanin yakeso ba, he wants to know inda take.
“Yanxu tana ina ita da mahaifiyar tata?”
“Sunbar anguwarmu kuma wallahi babu wanda yasan inda take”
“Ba kace mahaifiyarta kawar matarka bace”
“Eh…ay muma bamusan
inda suka tafi ba”
Salim na fassara mashi ya runtse idanunshi kafin ya bude jijiyoyin kanshi na firfitowa he’s so fed up, he wants to find her, he wants to see her.
Shifa salim kwata kwata irin mutanen nan ba abun yarda bane, basa gane kowanne yare saida
kudi, Ganin haka yasa salim cewa, “daga kan dubu dari biyar zuwa miliyan daya idan har kayi mana kokarin nemanta a duk inda take zamu baka abunda yafi haka ma”
Jamilu najin zunzurutun kudi haka ya bude idanu, kunenshi har motsi suke, salim na ganin haka
yasan cewa duk munafukai ne.
“Toh zanyi kokari.. zan tuntubi matata, tunda tasan babarta sosai”
Murmuahi salim yayi ya fada ma taj komai, ogan agencies din yace “toh oga gashi mun kawoshi…za a bamu namu kason ko?”
Aje masu few notes sukayi sukabar wajen
bayan sun bama jamilu card dinsu.
Jamilu bai taba sanin sanadiyar yarinyar nan zaiyi arziki ba auren da bai kara ba yanxu da kudaden nan zai kara saboda haka dole ya nemo masu yarinyar nan.
Washe gari yasa jamila a gaba, tun daren jiya yake mata sabab
i akan saita kaishi har inda hadiza take, tayi tayi ya fada mata dalili yaqi, karshe dai ya fada mata mutanen nan sunce zasu kawo hukuma idan har bai nemo masu inda yarinyar nan take ba.
Jamila najin hukuma hankalinta ya tashi, jamilu yace indai bata kais
hi inda hadiza take ba saidai aurensu ya kare a anan dole ta shirya suka tafi ya hanata kiran hadiza duk asunan wai kartaji abunda ke faruwa ta dauki yarta ta gudu.
Motar haya suka hau shida ita har maitama, suna isowa estate din jamila tace “bazasu barmu
mu shiga ba sai an kira daga ciki”
“Yanxu anan take? Hadizar da yar tata?”
“Eh”
“Toh me takeyi anan? Nadaisan duk danginsu babu masu arziki”
“Aikatau mana, aiki takeyi anan din”
“Toh shikenan muntafi kawai”
The next day..
Gaba daya ayau bai sam
u sun hadu da salim ba saboda asibiti daya kai anne treatment din da ake mata.
Basu dawo gida ba sai wajen yamma, har zuwa yanxu babu wanda yayi suspecting rashin lafiyar anne dagashi sai ita.
Kai tsaye ya wuce part dinshi ya dan kimtsa kafin ya futo ya
wuce main house.
Yana shugowa ya wuce sama direct bangaren oummi, bakinsa dauke da sallama ya bude kofar sitting room, kamshin turaren wuta nee mai dadi ya mashi sallama,da yasashi sauke ajiyar zuciya,knocking din kofar dakin nanna yayi daga ciki ta bada
izinin shugowa, kafin ya bude kofar, sabeeha dake tattara lunch din da nanna tasa azo a dauke tana jin sallamarshi gabanta ya wani fadi, allah yaso ta saka hijab dinnan saidai bata rufe fuskarta dashi ba, aiko wuff tayi saurin janyo shi wajen bakinta.
“H
ar kun dawo?” Nanna ta tambayeshi tana dubansa fuskanta dauke da murmushi, shima maida mata yayi da murmushin kafin ya amsa ta “eh”
“Hmm wannan futa da kukeyi daga kai sai anne cikin sirri ina fatan babu abunda kuke boye mana”
Ganin irin kallon da take
mashi bayan tayi tambayar ne yasashi kauda kanshi, don bayason su hada ido don bayajin zai iya mata karya.
“Laaa oumi, babu komai, munje factory ne kawai”
“Toh ay shikenan in tayi tsami maji,kayi luunche?”
Girgiza mata kai yayi yana jujuya wayan dake h
annunshi, yanda ta mashi tambayar nan yasan cewa ta gane suna boye wani abu shida anne.
“Fatima zuba mashi kafin a futa da sauran abuncin”
Tunda ya shugo baima lura da mutun a wajenba amma dayaji anne tace fatima sai kawai yaji yanason kai hankalishi zuw
a ga wajen.
Sunne kanta tayi kasa sosai yanda baza a hango fuskanta ba kwata kwata, gashi ta duqa tana arranging plates da warmers din kan tray zata futa dashi, shiko ya dage ya bita da ido sosai at the same time gabanshi na faduwa ya rasa dalili.
Kall
onshi nanna tayi ganin yana kallon inda sabeeha ke tsugunne, ga sabeehar itama bata dagoba kamar wadda ke tsoron za a kamata da wani abun”
“Fatima??…”
“Na’am” sabeeha ta amsa ta, ciki ciki “jeki kawai,”
Naam dinnan datace ne ya kara sashi kallon inda ta
ke don ya dauke idanunshi akanta,kamar wani mai nazari haka
Sabeeha ko nanna na ce mata ta tafi tayi saurin miqewa ta futa.
“Bari na zuba maka da kaina” nanna tayi magana don ganin yanda ya kalli sabeehar ya tabe baki kamar wanda ke kyan kyami ya
sa nanna tunanin ko ba kowa yakeson ya sa mashi abunci ba, itama don taga fatiman nada tsafta ne sosai yasa tace ta saka mashi, amma ganin irin kallon daya mata yasa tace fatiman kawai ta tafi.
Kallon dayama sabeeha ya gane itace take zuwa part dinshi tan
a gyarawa, shi gaba daya ya dauka she’s mute ashe tana magana, amma ko sau daya bata taba gaishesa ba kuma duk ma’aikatan gidan idan suka ganshi kamar su tsugunna mashi,
Sabeeha na fita daga dakin ta sauka kasa, itafa wannan abu ya fara damunta, kullum
tsoro da fargabar haduwa dashi take, shiyasa take kokarin ganin ta raba hanyar dazai sadata dashi gaba daya, Har Allah allah take su koma school.
Zaune take bakin gado ta dora kafa daya kan daya tana sanye da irin camisole dinnan dake kama jiki sosai,
hadiza na daga zaune bakin gado sai faman yaqe take yi.
“Hajiya karama dan Allah kiyi hkuri….”
Wani irin disgusting kallo maya ta mata tare da cewa “hkurin me kike bani?”
“Wai naga kwana biyu idan nazo gyara sai rabi tace kince karna sake zuwa bangarenk
i sainayi tunanin ko dan saboda abunda Fatima tayi ne”
“Meysa zan yarda dake? Yarki barauniya”
Murmushi hadiza tayi tace “laifin yata saiya shafeni?”
“Na tsaneku wallahi, dake da yarki, ko ganinku bana sonyi”
“Bakya son zamanta ne a gidan nan?”
Kai
tsaye tace
“Eh..”
“Toh saina maida ta inda muka futo indai zamanta anan yana damunki”
Kallon mamaki maya kema hadiza, “akan farin cikinki ay zan iya komai kuma zan iya sadaukar da komai”
“Harda yarki?”
“Eyy wallahibki yarda dani,”
“Kina tunanin zan
yarda dake ne?” Maya ta jefo mata tambaya, “hajiya karama kenan, nasan fa ba yarinyar nan ce ta dauki abunku ba ranar da kika shugo dakinmu aranar kika aje abunnan kuma na ganki da idona amma ban fadawa kowa ba saboda banason a bata maki ranki, yanxu zaki
iya yarda da maganata”
From the shock on her face zaka gane cewa mamaki ne karara akan fuskanta, kallon hadiza kawai take abubuwa na circulating aranta.
Sai kawai maya tayi murmushi don babu abunda yazo ranta sai tunanin duk yanda akayi sabeeha yar kishi
yar hadiza ce, uwarda ta haifeta dai bazatayi wannan abun ba amma ita meya dameta da wannan, she just wants to see the girl miserable don kawai akwai something off datake ji about yarinyar, wanda ke sata feeling anxious and scared kuma ta rasa dalili.
C
han bangaren jamila, dahiru fa baibar kiranta ba kuma taqi dagawa saida taga ya mata wani dogon text yasa tayi saurin kiranshi, yana dagawa tace “dahiru me kakeso?Ehh”
“Jamilaa..jamilaaaa ki daina qin daga wayata, wallahi kinsani babu kai, karkiga wai gir
ma yazo wallahi cikakken dan tasha nake”
“Toh me kake so? Ehh?”
“Kuna tunanin zaku yagi arziki ku barni ko? Toh wallahi baku isa ba,”
“Me kake nufi kenan?”
Dariya ya kyakyace dashi yace, “naji ance yarmu ta girma, madallah ashe dai da rayowar imani ara
nku keda kawar taki,“
“Me kake so dahiru, ka daina kirana tun kafin jamilu ya gane”
“Toh toh..saurareni, tunda kunci moriya nima sai a barni nasha romo ko?”
“Me kenan?”
“Kinga shekara nawa kenan tunda kika gujeni banyi aure ba, kuma da kumari na wallah
i, man power nake sha duk sati kuma abar tawa kullum bata kwanciya, shine nakeso ku bani yar tamu ko? Asirin namu yafi rufuwa dakyau ko ya kikace”
“Wai kana nufi hadiza ta baka yarta??”
“Ah ah ke kuwa yarta kuma? Kodai yar da kuka chanzo”
Dammm gaban ja
mila ya bada, wallahi karamin hauka ne dahiru bai sata ba, tashin hankali da ba a sa mashi rana.
“Kinga saimu rufawa juna asiri ko?” Ya karashe yana kyakyacewa da dariya.
Saurin danne abunda ke ranta tayi tunawa da babu abunda zai iyayi,“idan muka qi f
a? Me ka isa kayi? Meka sani dahiru? Bakasan komai ba, barazanarka ta banza ce wallahi dahiru,mteww dan wahala”
Tana fadin haka ta kashe wayar, ta soma kiran hadiza, hadiza na dauka ta labarta mata komai wayar da sukayi da dahiru, hadiza tayi shiru tana w
ani nazari.
“Dake shi tsinannne wai tunanin yayi min barazana zaiyi, bayan babu abunda zai iya, kowa idan talauci ya gama bugunshi sai kuma hauka, kinyi shiru bakice komi ba?”
“Jamila…anya wannan ba shawara ce mai kyau ba eh? Zamanta anan yana kawo min
matsala, na kasa jan yata a jiki, kuma farin cikinta shine damuwa ta ayanxu,”
“Yanxu me kika yanke kenan”
Dariya hadiza tayi tace “dahirun ne daman daidai da ita, ay namayi kokari rikon danayi mata shekara nawa?ki kirashi ki shaida mashi na bashi ita wa
llahi, zansan yanda zanyi da hajiya”
“Kice kawai dangin ubanta ne sukace lokaci yayi kuma an mata miji, ina wannan matsolon kanin dalha, ki bashi yan chanji kawai ki rufe bakin sa”
“Hakan ma za ayi, kinga kuma kwa huta da masu nemanta, inama zan bari tay
i associating da masu kudi, kamar yanda kikace ne kila wani ya ganta yakeso shine yake bibiyarta ay bazan taba bari a sauya mata rayuwarta ba wallahi,ina ribar tawa kenan?”
“Oh hadiza kishiyarki ta shiga uku…”
“Ay kishiya daya gareni a duniya, ba a taba
abunda hadiza ta kwallafa rai akai a zauna lafiya, wallahi zan iyayin komai jamilaa…”
“Haba waa dama chan kinyi sanyi ne hadiza yanxu nasan asalin hadiza ke magana, kinfi shaidan” suka kyakyace da dariya….
….
The next day..
Yau ta kasance Saturday’,
da sassafe ya futa gym don ya saba da hakan yana dawowa gida lokacin wajen karfe tara saura, wayarshi ya dauka ya soma kiran salim, yana dagawa ya tambayeshi any update akan jamilu, ya shaida mahsi gar zuwa yanxu bai nemesa ba, taj yace anya kuwa ba guduwa
yayi ba? Salim ya shaida mashi ay irin waennan mutanen idan har sukaji maganar kudi babu abunda baza su iyayi ba, haka nan sukayi sallama gaba daya ya kasa samun natsuwa, a matse yake da yasan inda take, shin ko tana cikin koshin lafiya? Wace rayuwa take
yanxu? Tunawa da sanda ta bashi labarin ita marainiyace yayi, da kuka abubuwan datayi mashi, He wants to pay back for everything taht she did for him, she stood by him alokacin dayafi kowa buqata, ta kula dashi dukda tasan rayuwarta na cikin hadari.
Ta wa