Showing 174001 words to 177000 words out of 338813 words
bama househelp Dinku ta karashe”
Girgiza kai kawai laila tayi taja plate din ta soma ci, “leftover din zakici?”
“Toh menene a ciki?”
“Nace ki kaima house help dinku ta cinye sauran”
Girgizq kai kawai laila tayi, tana mamakin halin lail
a na kyamatar yan aiki, babu abun kaskanci a wajenta kamar masu aiki, shiyas atake tausayin sabeeha sosai, bata taking chances wajen bullying dinta da disgracing dinta a ko ina,
Washe gari da safe gaba daya gidan kowa yaji batun rashin lafiyar nanna
da kwantar da ita da akayi a asibiti, duk sai kowa ya damu sosai harma da yan aikin gida,musamman sabeeha, don macece mai kamala da faran faran da kowa ga kyauta ga mutunci sosai sai fatan samun lafiya kawai suke mata.
Tun wajen karfe bakwai hamad ya tash
i ya wuce part dun anne.
Rabi dake kula da bangaren nata yasa ta dauko mashi duk wani abun amfani da zasu buqata sannan suka bishi dasu mota ya shiga.
Around 7:30 ya iso asibitin ko jiran mamanshi baiyi ba, ya fito cikin natsuwa ya nufi asibitin.
Yana s
hugowa daidai wajen dakin nata ya hango taj daya dafe kanshi shi daya zaune, ko kallon inda yake hamad baiba tubda ya dauke idanunshi harya shiga cikin dakin da sallama.
Anne ya hango kan abun sallah, bata tashi ba tunda tayi sallah ta dan nemi runtsawa a
wajen.
“Anne…good morning ya mai jiki” ya fada ahankali gudun kar mara lafiya ta tashi.
“Morning dear, ya kuke kowa da kowa?”
“Duk suna lafiya” daidai nan ya karaso inda take ya zquna kan couch.
“Zuwan safiya haka hamad? Baka huta ba”
“Bazan iya huta
wa ba ay tunanin halin da ku ke ciki bazqi barni ba, i missed you”
Shiyasa cikin jikokinta take bala’in son hamad ba kadan ba don ya fita daban.
“Toh ay gashi ka ganni saika zo ka tafi ko”
“Please anne karkice na tafi I won’t”
“Toh shikenan ay, wake s
on zaman asibiti allah na tuba inba dole ba.
Murmusawa yayi tare da aje mata bag din daya shugo dashi.
Anne tayi saurin kallonshi tace:
“Kaga tajudeen kuwa, tunda ya tafi sallah bai dawo ba”
Shuru hamad ya danyi kamar bazaiyi magana ba chan yace “na ga
nshi zqune a reception kafin na shugo”
“Jeka ce mashi ya shago mana, ko rintsawa yaronnan baiyi ba wallahi”
Kamar bazai tashi ba haka ya miqe tsaye ya nufi wajen kofar sannan ya futa.
Yanda yabar taj din haka ya taddashi a zaune ya dafe kanshi.
Rasa me
zaice mashi hamad yayi, sai kawai yace
“Barka da safiya”
Dagowa taj yayi ya kalleshi kafin ya sauke idanunshi ya gyara zamanshi ya amsa shi babu yabo ba fallasa.
“Bismillah!!”
Ya mashi nuni da kofa, sannan ya juya ya barshi zaune.
Miqewa yayi shima a
natse yabi bayan hamad din jiki a mace, koda ya shugo ita din ya fara kai idanunshi gareta, ganin yanda take barci peacefully yasa shi sauke ajiyar zuciya.
Tashi anne tayi ta dubeshi tace: “zan wuce gida akwai magunguna na daya kamata na sha, ka zauna da
ita okay”
“Ya za a barshi shi kadai da…”
Dakatar hamad anne tayi tace “wuce ka kaini gida”
Tana fadin haka ko kofar magana bata bashi Damar yiba suka fice.
Suna fita anne ta dubi hamad tace “babu wanda ya kamata ya zauna da ita kamarshi, yafi kowa k
usanci da ita saboda mahaifiyarsa ce”
Kalmar mahaifiyarsa saida hamad ya sake nanata ta zuciyarshi, shifa bai taba jin anyi maganar nanna tana da da ba,yadai san cewa ta taba aure sau daya kuma bata sakeyin wani ba bayanshi.He’s so curious da son jin wann
an zance .
Bayan tafiyarsu ya zauna kan couch bini bini yake dagowa ya kalleta ya kasa samun natsuwa, ga tausayinta ya dameshi, tunowa dq ta dalilinshi take kwance ayanxu.
Kasa hakura yayi ya karaso inda take,kamar anne tasan he needs time with her, ya z
auna kujerar dake gwfen gadon mara lafiya, samun kanshi yayi da kamo hannunta kamar wanda kejin tsoron tabata, ya riko hannun gam yana jin dumin mahaifiyarsa, wallahi irin wannan yanayin daban ne bazai misaltu ba.
Ya sumbaci hannunta ahankali ya soma maga
na yandq bazai tashe ba “aftaqiduk kthyran ya oummi, nayi kewarki sosai, i was blinded into thinking my life was complete without you, it was never, saima juyawa da tayi into miserable life, i had a traumatic days and night without you oummi, bansan dadin
uwa ba,bansan yanda zan kalli cikin idanunki ba, i wish i could take out your pains that i caused you ya oummi, duk da an samin tunanin kinyi abandoning dina bana iya barcin kirki bana iya cin abuncin kirki ba tare da tunanin ki ba, shin a wani hali kike?
Meke damunki? Meysa kika barni Baki waiwayeni ba? I was selfish all this time banyi tunanin ni wani hali na jefaki ba, ki yafeni ya oummi” yana magana amma baisan sanda ya soma jin lema lema ba akan fuskanshi, kuka da wuya ya sauka akan idanunshi amma akan
mahaifiyarshi ya kasa controlling kanshi don she’s his weakness
Duk maganganun nan nashi a kunneta don tunda ya riko hannunta ta farka daga barci amma taqi nuna alamun haka, ka dumin hawayenshi na sauka kan hannunta daya rike she can feel how yanda yake
trembling, ya Allah, zuciyarta na mata wani irin zafi ta kasa hana kanta hawayen dake sauko mata dukda bai lura ba. Abu kamar a mafarki haka takejin komai
Misalin wajen karfe goma da rabi sai gasu sun dawo asibitin,hamad, anty fadila, ya sameer.
Da sal
lama suka shigo dakin, yana zaune kan couch ya dafe kanshi da hannu daya,ya amsa sallamarsu sannan ya tashi zaune a natse duk suka juyo suka kalleshi,
Ya sameer ne yayi gyaran murya ya karaso inda yake ya miqa mashi hannu suka gaisa, anty fadila ta bishi
fa kallo sosai, sai a yanxu ta kara tabbatar wa da dan nanna ne, don ga kamanninsu sosai ba kadan ba, da yanayin yanda yake magana da komai, dagowa yayi sukayi ido hudu dashi,ya gaisheta a natse ta amsa cikin mutuntawa kafin ta karasa wajen nanna.
Hamad d
ai na tsaye daga gefe ya nade hannayenshi a kirjinshi.
“Sannu Nanna…ya jikin? Allah yasa kaffara ne”
Bude idanunta kenan jin sallamarsu, Kallonta nannata tayi da idanunta da suka rine sosai suka fada tace “ku kira doctor ya sallameni”
Hamad ya futa do
n kiran doctor sai gashi ya dawo.
Ya sameer ya bar taj tsaye ya nufi nanna shima don yayi mata sannu. Shidai sunne kanshi kawai yayi kasa bai karasa ba gudun bacin ranta a natse ya futa daga dakin.
Dudubata doctor yayi don tabbatarta lafiyanta kafin ya
kalli sameer “za a iya sallamarta yanxu, amma gaskia dole a kula da lafiyarta, kar a dunga bari tana shiga duk wata damuwa dazai janyo mata shiga shock irin wannan,“
“Thank you doc” Sameer ya fada yana miqa ma doctor hannu.
Ko kallonsu nanna batayi ba,
gaba daya yanayin ta ya sauya kamar ba nanna ba, tayi wani irin fayau abun tausayi, kokarin tashi ta soma yi , jiri na dibanta,kayan da aka zo da ita dasu sune a jikinta,ganin yanayin da take ciki yasa anty fadila tayi saurin kama hannunta da babu canula a
jiki ta taimaka mata.
Sameer da hamad suma suka mara masu baya.
Daidai nan ya fito daga office din doctorn daya bata sallama, da prescriptions din magungunan da zata buqata na qarin jini.
Nanna ta mashi kallo daya ta dauke idanunta suka fita daga cik
in asibitin ita da fadila da hamad, uncle sameer kuma ya dan dakata.
Magana suka danyi da taj kafin ya futo shima suka shiga Motar da suka zo dashi gaba daya, suka wuce.
Suna barin asibitin anne ta kira sameer, yana dauka ya shiada mata an sallami nanna
suna kan hanya ma,hamdala tayi kafin suyi sallama.
Babu wanda yayi magana tunda suka shiga cikin motar har suka iso gida, suna isowa suka wuce main house direct gaba dayansu banda hamad daya sake futa da motar.
Anne na zaune a sitting room sukayi salla
ma,take farin cikin fuskarta ya bayyana tayi saurin miqewa tsaye suka karaso inda take.
“Alhamdulillah!!! Sannunku da dawo ya jikin naki?”
Anne ta tambayi nanna tana kama hannunta suka zauna,murmushin yaqe kawai nanna ta mata batace komai ba sai ya samee
r ne yace “ga magungunan da doctor yayi prescribing, sannan ya umarci a gujema duk wani abu dazai daga mata hankali”
Maganar da sameer yayi yasa anne ta dubi su shida fadila.
“Allah yasa kaffara ne, nasa ayi maku breakfast, Ina tajudeen din?”
Shuru duk
sukayi gaba daya wannan yasa anne cewa , “barin shi kukayi achan?meysa?“
Bata gama rufe bakinta ba nanna ta miqe ta wuce sama don ko maganarshi bata son ayi.
Binta sukayi da kallo harta hau sama, wallahi duk ta zama wata iriya gaba daya kamar ba nanna
ba.
Tana barin wajen anty fadila tayi saurin matsowa inda anne take zaune uncle sameer yayi gyaran murya yace “anne kun barmu cikin duhu, me….”
Saurin dakatar dashi tayi batama bari ya karasa magana ba tace “Zamuyi maganar daga baya, this is not the r
ight time, jafaru ya kira maganar marayun da za ayi sponsoring karatunsu, ayi budgeting abunda ya kamata sai a sanar dani ”
Gaba daya suka hada baki wajen cewa “Allah ya ja da kwana ya kara arziki mai albarka su kuma allah yasa karatun ya amfanar dasu” t
a amsa da ameen sannan ta miqe ta bi bayan yar uwarta rabi na biye da ita da warmers cike da abuncin, tuwo na musamman anne tasa a mata da miyar ganye saboda karin jini, da sallama ta shiga part din nanna, a zaune ta taddata bakin gado ta dafe kanta da han
nayenta.
Koba’a fada mata ba tasan kuka take yi,nuni tayima da rabi ta aje warmers din ta futa, nanna najin sallamar anne kuwa tayi saurin goge hawayen dake fuskarta ta dago ta kalli anne.
Murmushi anne tayi mata sannan ta karaso inda take zaune ta dafa
ta tace “hajara,”
Dagowa nanna tayi ta kalleta sai ga hawaye, ganin haka yasa anne saurin kokarin kwantar mata da hankali.
“Dan Allah kibar wannan hawayen, karya jawo maki wata matsalar, allah kadai yasan yanda kikeji aranki, amma ina rokonki da ki kwant
ar da hankalinki, ga abunci nan an kawo, freshen up saiki samu ki danci wani abun okay?”
Rabi dake zaune a sitting room din nanna tayi saurin shugowa bedroom din jin kiran da anne ta mata, tana shugowa ta wucewa bathroom kafin ta futo, “bismillah hajiya
an kammala”
“Sannu rabi” nanna tayi magana dakyar.
Miqewa anne tayi ta futa “bari na barki zan dawo anjima”
“Toh anne” Nannata amsata
Tun bayan futar anne takai wajen minti talatin kafin ta miqe ta shiga bathroom ta watsa ruwa.
Bayan tafiyarsu
jiki a mace ya shiga cikin motarshi, yafi kusan 30mins a zaune bai motsa ba, ya runtse idanunshi saboda wani irin ciwon kai dake damunshi tsakanin daren jiya da yau, kirjinshi ko har yanxu nauyi yake mashi.
Jiki a mace ya tada motar yayi reverse yabar har
abar asibitin.
In less than 15min ya iso transcorp, ko iya parling baiba ya aje masu motar a wajen ya wuce sama.
Koda ya shigo dakinsa zama kawai yayi bakin gado ya dafe kanshi, wani irin zazzabin mai zafin gaske na neman dibanshi, kota cikinshi bayaji d
on rabonda ya sama cikinshi abunci ko ruwa tun dinner din da sukayi a gidan.
Zaman nan dayayi saiya zamana kamar bazai iya tashi ba saboda zazzabin gadan gadan ya taho mashi dole ya kwanta yaja duvet ya rufe jikinshi.
Anne na zaune kan couch ta jawo wa
yarta ta soma dialing number shi gar sau uku ba a dauka ba,gaba daya abunne babu dadi, tasan yanxu haka shima yana chan cikin wani hali, tund aga mahaifiyar tasa itama.
Yanda rabi ta aje abuncin nan haka ta dawo ta daukeshi don kwata kwata bata taba shi
ba, saima kwanciya datayi anne ta shugo dakin saitayi tunanin ko barci tayi wannan yasa ta barta tadan huta.
Anne na fita nanna ta ta jawo hoton dake aje kasan pillow dinta, kurama hoton ido tayi sosai ta kasa daukewa sai hawaye…
40 years back….
Shek
arar nanna goma chif a saudi, acikin wannan shekaru abubuwa da dama sun faru da ita, masu dadi da mara sa dadi.
Ranar da allah ya hadata da abdallah shine ranar data fara zuwa makka domin yin umra, don a madina take karatu.
Shigarta kenan ka’aba ta fu
skanceta taji wani irin sanyi na dibanta, ranar ta kasance rana mafi sanyi ga wata ni’imatacciyar iska dake kadawa
ko’ina kamar za ayi ruwa, gashi lokacin babu irin mutane sosai dinnan don babu cunkoso kwata kwata, take wani hawaye mai sanyi ya sauka kan f
uskanta ayayin datayi ido hudu da dakin Allah ta fara dawafi, daidai wajen hajarul aswad ta tsaya tare da shafa wajen ta rufe idanunta, takai wajen minti biyu a haka kunnuwanta suka soma jiyo mata muryoyin dake gefenta saidai muryar mutun daya ce tafi zama
a kunnanta inda yaketa yin addu’oi da larabci, saitaji gaba daya kamar ita yakema adduar, tana dena jin muryar tasa ta bude idanunta tare da kallon gefenta inda allah ya bata ikon ganin irin jakar maniyyata da suke sakawa, cikin hanzari ta dago ta dauka j
akar tare da juyawa don ganin mai ita.
Saboda yanda kowa ke sanye da ihram yasa ta kasa gane kona wanene wannan yasa kawai ta rike ta cigaba da ibadarta.
Tana gamawa tayi safa da marwa ta sauke umra sannan ta wuce wajen da ake kai abubuwa idan sun bata.
Tana zuwa ta masu bayanin inda ta tsinta abun, wani dan paper form suka bata tayi signing ta saka information dinta don haka akeyi idan har mutun ya tsinci abu saboda gudun kar wani abu ya bata daga ciki, tana cikin rubutawa abdallah ya iso wajen.
Dake t
ana daga chan gefe wannan yasa batama lura dasu ba.
Tana gama rubutawa ta karaso wajen macen security din dake wajen ta bata paper din, matar ta soma zazzage jakar don shigarda abubuwan dake ciki, kusan kullum sai an samu irin jakar don duk maniyyata irin
ta suke amfani da saidai banbancin color.
Hajara dai na tsaye har matar ta gama shigarwa tana gamawa dake counter daya ne sai dai babu cudanya wajen mata da maza kowanne da bangarensa ta miqa bangaren maza, abdallah dake tsaye ya tabbatar da nashi ne aka
duba id din dake ciki sannan yasa hannun tabbatar da babu abunda aka dauka a ciki, kafin aka bama hajara itama tayi signing.
Magana abdallah yayi da security din yayi mashi nuni da counter din mata adaidai lokacin ta dago bayan ta gama rubutun idanunshi y
a shuga cikin nata, suka sallameta ta juya, shima ya karba jakar ya fita.
wannan ne mafarin haduwar taheel da nanna.
Duk wani abu da allah ya rubuta ko allah ya kaddara indai alkahiri ne saiya faru cikin kankanin lokaci, daga wannan ganin dayayi mata
allah yasa mashi qaunarta a zuciyarshi, abunda bai taba ji ba,encounter dinsu na biyu shine ranar da aka gudanar da wani babban taro a makanrantarsu,cikin ikon allah kuma ya sake hadasu ta wata hanya daban, ita bata ganeshi ba don saida yayi mata bayani t
a gane, baizo mata a matsayinshi ba, da matsayin da yake dashi a kasar yayi mata godiya sosai.
Daga wannan lokaci soyayya ta kullu tsakanin taheel da hajara, hajara itace mace ta farko da abdallah ya fara so, tsaftaccen so yake mata haka zalika itama ta
ke mashi,su a nasu aladar babu wani jan lokaci wannan yasa ya nuna mata aurenta yakeson yi, sannan ya buqaci ganin iyayenta.
Da farko nanna ta tsorata don babu wanda yasan dashi a gida sai anne, tsoranta na biyu shine aqidar babansu santuraki, idan mace t
a gama karatu shike zaba masu mijin aure, kamar anne data gama karatunta already ya bada ita ga dan business partner dinshi.
With the support and courage din da anne ta bata kuma ta shige mata gaba suka sanarda mahaifinsu santuraki, daga nan mafarin tanga
rda ta shigo don santuraki bai amince ba, don itama ya mata miji, tana gama karatu.
It was a very hard moment for nanna don tana masifar son taheel,rashin amincewar iyayenta bazaisa ta aureshi ba, dole ta hakura da abdallah.
Ta shiga damuwa sosai ba kada
n don anne ce kawai tasan wannan,karatunta ma duk yayi baya tayi wani irin rashin lpy sosai.
Tsakanin yan uwa sai Allah, halin da nanna ke ciki anne ma ta shiga amma dole ta hkura da zabinta tabi na mahaifinta amma bazataso yar uwarta ta shiga irin halin
data shiga ba a baya wannan yasa ta sake tada maganar tare da rokon mahaifinsu, alhaji santuraki nada dogon buri da future akan yayanshi, but hajara failed him dalilin halin da anne ta shiada mashi take ciki wannan yasa ya yanke wani tsatsauran hukunci, in
da ya yarda saidai ya shaida mata idan tayi regretting decision dinta she has to forget tanada uba.
Anne bata yarda ta fada mata wannan last furucin mahaifin nasu ba akayi auren abdallah da nanna.
Bayan aurensu da shekara guda allah ya azirtasu da d’a na
miji inda yaci sunansa (Tajudeen abdullah taheel)abdallah yayi murna yyai murna mara iyaka ba kadan ba, adduar da ya dade yanayi allah ya amsa ta, ya samu magajinsa.
Bangaren nanna babu wanda ya kaita farin ciki itama,koda ta shaida ma anne itama tayi far
in ciki sosai ba kadan ba, saidai a lokacin ne nanna ta fuskanshi har zuwa lokacin akwai matsala tsakaninta da mahaifinta, don har zuwa lokacin bai amince kuma ya karbi taheel a matsayin mijinta ba wannan kadai yasa ta kasa komowa gida don batasan da wani
ido zata kalli mahaifin nata ba saboda bijire masa