Showing 159001 words to 162000 words out of 338813 words
mahaifinki shine yaci amanar mahaifiyarku ko? Toh ita mahaifiyarku itace taci amanar shi,“
Wannan tsoron da tashin hankalin da fadwa ke son gani akan fuskar hidaya shine ya bayyana,
don ni har kamar hawaye hawaye nake gani kan fuskarta, ta umarci driver ya juya akalar motarshi zuwa island dinta.
Gudu suke sosai har suka iso tama manta da wani barad tana isowa ta shiga yatch dinta.
Suna isowa tayi hanzarin shiga motar da zata karasa
da ita, har zuwa lokacin wayarta na hannunta tana kallon hotunan fadwa da basit sannan da documents din nan daya tura mata da asuba.
Wayar na hannunta messages suka dinga shugowa rutu rutu kamar yaqi, notifications daban daban daga social media, saiga cal
ls na biyo baya, wannan na kastewa wannan na shugowa, messages din ta fara dubawa bata fuskanci komai ba yoh ta ina ma zata fuskanci abunda ke faruwa, hankalinta a tashe da abunda taji kuma ta gani, wanda take fatan ba haka bane.
Driver na tsayawa ta tunk
ari cikin uncompleted building din, su black basu san da zuwanta ba don bata zuwa a wannan lokacin kwata kwata.
Ciki kawai ta shiga suna kwakwance sun shawu sosai basu farfado ba ta fada dakin da abdallah ke rufe.
Tana shiga ta kunna haske ya bade daki
n gaba daya sannan ta tako har inda yake kwance,”abdallah!!!!”
Shine abunda ta furta kawai, yanajin itace ya tashi zaune gaba daya yayi busu busu da gashi yau shekara kusan nawa ta kamashi, yana mai fuskantarta, yanayinta ya gane cewa ranar dayake jira ta
bayyana kenan.
Yau shekara kusan uku ne, ta kulleshi akan mahaifiyarta, akan ya fadi sirrin mahaifiyarta da babu wanda ya sani sai shi kadai.
“Kin dawo ne na sake maimaita maki ko kuma har yanxu baki yarda ba?”
“Karya kake yi karya ne, mahaifiyara baza
ta tana cin amanar abbu ba, zan iya sawa a kasheka yanxu idan baka karyata kalamanka ba”
“Karki yaudari kanki, idan kinsa an kasheni bazai chanza gaskiyar almari ba, mahaifiyarki itace butulu, itace taci amanar mahaifinki, da
kaskantacce, kuma wulaqantacc
e, wanda mahaifinki ya taimaka wa alokacin da yafi kowa buqata, saboda san ransu suka ci amanarshi,”
“Karya kake!!!! Karya ne bazai taba yuwu ba…mahaifiyata ta kasance mai amana, abbu yaci amanarta, shine yaci amanarta”
“Alamu sun nuna gaskia dake boye S
hekara da shekaru sun bayyana a gareki, kuma kin kasa amincewa da hakan?, toh ki bude kunenki dakyau, ko ki yarda ko karki yarda wannan ita ce gaskia daya…”
“Mahaifinki ya kasance mutun mai mutunci mai taimakon na kasa dashi, mai adalci, ya daukeni nida b
asit ya rufa mana asiri amma hakan baisa mahaifiyarki da basit sun ci amanarshi ba, babu wanda yasan da abunda ke tsakaninsu shekara da shekaru sai ni kadai, don ko su kansu basu sani ba, nayi dakon wannan cin amanar akan idanuna na shekaru, banida damar b
ayyanawa, haihuwar yar uwarku shine symbol na cin amanar taheel da mahaifiyarku tayi…..yar uwarki Fadwa yace ga abdul-basit.”
Sharrrr saiga hawaye kan fuskar hidaya kamar fanfo, sosai fa ba kadan ba tayi taga taga zata fadi kasa ta zube a wajen.
Babu a
bunda take sai jujuya kanta, maganar shi ta karshe na yawo akanta..”yar uwarki fadwa yace ga abdul-basit”
Takai wajen minti goma a haka ta kasa motsawa, abubuwa da dama na yawo akanta, lokacin da mahaifinsu ya kawo taj gidan, da irin yanayin da mahaifiyar
su ta shiga, da yanda suka dunga treating mahaifinsu saboda ita, wallahi baqin cikin su ne na yanda suka daina kusantarshi gaba daya yasa zuciyarshi ta buga, sun nuna mashi tsana mafi tsanani musamman ita.
Abdalla dai na zaune yana kallonta bai sake cewa
komai ba, tana daga nan zaune aka banko kofar, warrant na arrest dinta aka bada amma zuwa wajen nan da akayi suka tadda yaran black dakeda illegal makami bindigu yasa dole a kama duk wanda ke ciki.
Ba kowa ne kuma ya bada tip din inda take ba sai black.
Yaranshi gaba daya aka kamasu.
“You’re under arrest mrs hidaya abdallah, for……..”
Haka suka dunga jero mata crimes da charges iri iri kanta ma yayi wani irin dumm batajin abunda suke fada kwata kwata.
Aka fidda abdallah aka sashi a mota zuwa asibiti don
bashi taimakon gaggawa.
Few minutes ego..
Lokacin da take zaune a mota bayan investigator ya tura mata hoton fadwa da basit, wannan mesages din da suka dunga shigo mata bana komai bane saina abubuwan da aka tashi dashi a safiyar, an fidda evidence dum
u dumu na illegal business datake a karkashin kamfanin, bayan ta iso island lokacin data wuce su black, batasan baya tare da yaransa dake sheme sun shawu ba, kuma yaga isowarta, yayi mamaki sosai wannan yasashi sauraron conversation dinsu ta hanyar recorde
r daya saka a dakin, bayan ya gama jin duk maganar tasu yaci karo da news din dake yaduwa wannan yasa yayi gaggawar tura sako da jiran a bashi umarni, ana bashi kuwa ya fita daga island yabar yaranshi sannan ya samu waya ya kira ya shiada ma police inda ta
ke sannan akwai wanda tasa akayi kidnapping idan anje za a ganta a wajen.
Daman already anyi tracking line dinta don anje gidan da warranty din questioning dinta ba a ganta ba, ana tracking location dinta kuwa yayi daidai da inda aka turo report, wannan y
a basu damar zuwa don ayi arresting dinta….
Wayyo rayuwa kenan….
😭
✊
💋
BOSS LADIES WRITERS
💋
✊
MATAR TAJ (destined with you
🩵🤍
)
Written by
Queenmarh
✍
️
Book2
PAID
Chapter 91
Abuja nigeriaa…
Tun daga nesa ya hango su biyu,ko
wacce na rike da jaka a hannu sai faman yanga akeyi, maya kam tafi kowa yauqi kamar bazata taka kasa ba.
Duban agogon hannunshi yayi ganin 4 daidai, da yasan yauqi zasu fara da yayi sallar sa kafin ma ya karaso school din, ganin babu sabeeha a tare dasu y
ayi mamaki sosai, don yawanci ma da zarar sun futo take yin gaba tabarsu, itadai badai sauqin kaiba, ya lura kwata kwata batason a bata mashi lokaci.
Gashi dagashi har ita ba ma’abotan son magana ba amma yanxu sun dan saba sama sama, he’s picking interest
on her, yanda take da kamewa da sanin darajar dan adam wannan yafi burgeshi game da ita sosai ga biyayya.
“Hello ya hamad..”laila tayi magana suna karasowa inda yake.
Bai kalleta don suna isowa ya kauda idanunshi akansu, da mamaki yaji muryar maya tace
“Hi”
Bai amsa masu ba don sallama yayi expecting daga garesu kamar yanda sabeeha ke mashi da zarar ta ganshi sannan ta gaishesa.
“Wa’alaikum salam, tunda baku iya sallama ba, “sorry ya hamad assalamu alaikum”
Banza yayi da ita maya ko ta wani irin tabe
baki suka bude kofar baya.
Ya tsaya bai motsa ba yana jiran isowar sabeeha, maya tayi winding glass din tace “mu tafi mana tana da extra class yau sai anjima zata dawo”
Ko kallon inda take baiba saida laila tace “ya hamad da gaske, dazu munyi class din s
tatistics da ita lecturer yace duk wanda is left behind baiyi catching up da lectures din yau ba ya tsaya za ayi extra classes, probably ta tsaya ne for the class”
“Ke maisa bazaki tsaya ba?”
“Ya hamad bazan iyaba marana yana min ciwo, sabeeha will help
me out”
Girgiza kai kawai yayi ya zagaya mazaunin driver ya kunna matar tare da barin wajen.
Yana saukesu gida yasa laila ta fada ma anne asa daya daga cikin driver suje su dauko ta zuwa anjima don zai koma office bazai samu dawowa ba sai dare.
Ko
minti biyar basuyi ba da barin wajen ba ta fito cikin sauri ganin 4:15 saboda tasan hamad by 4 yake isowa gashi batason bata mashi lokaci kwata kwata, gaba daya tayi wani iri, fitowanta kenan daga office din lecturer da akace yana kiranta koda taje office
din nashi ya shaida mata bai nemeta maybe wani lecturer din ake nufi ba shi.
Hakanan ta fito jiki a mace, gashi class rep din ya tafi shine daman yace ana kiranta.
Haka nan ta tsaya wajen minti talatin babu ya hamad wajen inda yake parking, tayi mamaki
sosai ba kadan ba wata dabara tazo mata ta wuce inda tasan su laila na zama ko zata gansu, koda tace nanma babu su, haka nan ta juya zuwa masallaci tayi sallah sannan ta fito ta zauna wajen inda yake parking gudun kar yazo suna nemanta don bata neman abun
magana.
Tana nan zaune abubuwan da suka faru dazu suka dunga mata flashing a kwakwalwa, hankalinta ya tashi sosqi ba kadan ba, abu daya za ayi mata dake tayar mata da hankali shine qazafi, tana jin zafin abun sosai, dukda anyi clearing komai hakan baisa
taji wani iri ba don har toilet ta shiga tasha kukanta ta godema allah yanda maya ta tsaya kyam tana kallon cikin idanunta tana attacking dinta da sata, batajiba bata ganiba, daa allah yaso class din basuda yawa sosai don da irin general class ne idan aka
ji wannan wani ba lallai ya yarda ba itace tayi satar ba.
A zuciyarta ta soma magana “banajin inada rabon jin dadi a duniya ne shiyasa”
Hawaye mai dumi ya sauko akan fuskarata tayi saurin gogewa tare da dago kanta jin alamun mutun a wajen.
Irin patrol s
ecurities dinnan ne dake assisting wajen parking.
“Baki tafi ba?”
“Ina wuni” tayi saurin gaishesa ganin babba ne.
“Lpy lau, inace kece ake zuwa daukan ku a wata katuwar bakar mota keda yan uwanki? Ay sun tafi tun dazu? Ya akayi baki bisu ba?”
“Wallahi
ban sani ba, qila sun jirani ne ban fito ba da wuri” ta bashi amsa.
“Toh ki kirasu a waya,”
“Tohm nagode”ta amsashi ya kara gaba.
Wayar ta zaro tana kallonta, tama rasa me zatayi, what if da gaske sun jirata bata fitoba suka tafi? Ita a wacece zasu zaun
a jiranta ita da ba kowan kowa ba?” Da wannan tunanin ta aje wayar kawai ta kasa kira, nan ta fara tunanin ya zatayi, yoh ta ina ma zatayi kiran babu kati a wayar.
Jikinta yayi sanyi sosai kalau ta zama stranded gaba daya.
Acahn gida suna isowa kowacce
tayi hanyar part dinsu, fadila ta wuce nasu while maya ta wuce na anne, zansu dabarar da takeyi duk welends take kwana wajen anty laila donta samu damar fita son ranta.
Kuma anne bata hana ba don ya sameer yayima anne magana akan ta dunga barinta tunda t
ana taya laila hira don batada yar budurwa kamar laila.
Anne batayi jayyayya dashi ba don babu wani abun kawai dai daman so take ana sa ido akanta tunda nanna ta ganta a hotel.
Shi ko ya sameer anty laila ce ta sashi gaba da mita da qananun maganganun ya
nda ta saba ay ba’a sonta a gidan da anty mubina ce baza ace maya ta bar part dinta ba dayake ita aka tsana itace yar agola wadda keda bakin jini shiyasa ake kyamatarta, wannan qananun maganganun nata yasashi zuwa wajen anne ya roki abarta tana zuwa tayata
hira tunda duk an zama daya.
Lokacin data shugo part din anne babu kowa a kasan sai hadiza da sukayi kicibus hannunta rike da iced squeeze orange, kamar ta daidaici lokacin dawowarta kuwa.
“Sannu da dawowa hajiya”
Ko kallonta maya batayi ba ta wuce sam
a, hadiza tabi bayanta.
Tana gab da shiga bedroom dinta hadiza ta cimmata “in shugo?”
Dan dakatawa maya tayi sai kuma tace “shugo”
Rufo kofar hafiza tayi tana duban mayar data watsar da takalmanta da handbag dinta a kasa ta yaye yalolom gyalen data rike
shi a hannu sannan ta fada gadonta tana sauke ajiyar zuciya.
“Sannu kin gaji ko? Ga juice nan mai sanyi yanxun nan akayi juicing dinshi”
Hannu maya ta miqa mata ta karba sannan ta zauna tasha juice din kadan ta miqa ma hadiza, a tunanin fita zata yi saiy
aga akasin haka, “in hada maki ruwan wanka?”
“Hada” ta amsata da gadara.
Jiki na tsuma hadiza ta shiga bathroom ta hada mata ruwa mai zafi sosai a jacuzzi ta watsa mata liquid bath soap dake wajen masu kamshi sannan ta fito.
Miqewa maya tayi ta wuce han
yar bathroom tana rage kayan jikinta ta watsar anan kasan.
Haka hadiza tabi kayan tana tattaresu ta saka a laudry basket sannan ta futo ta gyara mata gadon fess fess kamar ba a haushi ba sannan ta tsaya don jiran fitowarta.
Takai wajen 30mins cikin bathr
oom bata futo ba hadiza dai na tsaye ta fito.
Da mamaki maya ke kallonta, cikin rashin iya magana tace “ke kuma zaman me kikemin a daki? Ko dan hannu za amin ne ban sani ba?like mother like daughter?”
“Yo hakuri hajiya maya, daman na tsaya ne naji ko kin
a buqatar wani abun? Ko zakici abunci? Ko kinason a dafa maki wani abun da kikeso”
Wajen dresser maya ta nufa tana daukan man ta zata shafa tace “kije ki kawo min pepper soup din kaza, amma thighs din kawai nakeso, karki cika yaci sosai”
Murmushi hadiza
tayi tsabar jin dadi tace “toh sai me kuma kikeso, fada kin duk abunda kikeso zan maki”
“Shiknen, idan kin gama kizo ki wanken undies dina sai bathroom dina ba a wankeshi da kyau ba”
“An gama hajiya maya, ay babu abunda baza a yi maki ba gimbiyar gidan n
an”
Maya ji tayi kanta kamar zai fashe sosai ba kadan ba, hadiza na fita tayi smirking “lallai wannan anyi bagidajiya,”
Fitar hadiza daga saman taci karo da rabi data futo daga part din anne da sauran yan matan dake hauro mata da abunci sama.
Rabin ce
ke assigning dinsu inda zasu dinga aiki kuma tayi mamakin ganin hadiza a sama don aikace aikacen ta bai shafi sama ba wannan yasa tabi hadiza da kallo suna saukowa kasa tayi kicibus da ita a kitchen tana kokarin daura abunci.
“Hadiza meya kaiki sama inac
e aikin ki a kasa kawai yake.”
Rai a bace hadiza tace “banida ikon yin aikin daya wuce na kasa ne? Ke kinsan matsayina kuwa a gidan nan?”
“Menene matsayin naki? Inace aiki kikazo yi ana biyanki? Kinada wani matsayin ne bayan wannan bamu sani ba? Ki fada
min dalilinki na zuwa sama inva haka ba na sanarwa da hajiya, babu amsu zuwa saman sai wanda aka yarje masu kuma bana jin kina cikin waenda akace su dunga hidima a sama”
Hadizq tajji zafin maganar rabi amma haka ta hadiye ta danne tace “ba komai ne ya kai
ni dama ba, jikar hajiya ce ta buqaci a kawo mata juice da parpesun kaji shine na hau saman”
“Ba aikinki bane idan tana buqatar wani abu zata nema wajen masu girki ko ta kirani”
“Ke kuma asuwa?? “
Suka jiyo muryar maya daga bakin kitchen din, juyowa
rabi tayi ta kalleta, tana daure da towel a kirjinta ko me tazo dauka a kitchen din allah kadai ya sani,
“Daga yau duk abunda ya shafeni ita ce zatayi min, karki sake questionining dinta, banason iyayin banza da wofi, kema ba yar aikin bace ba har kinada
ikon fadin yanda za ayi da abunda baza ayi ba”
Sunkuyar dakai rabi tayi, gaba dayansu zasu haifi uku ta wallahi amma yanda take magana kwata kwata babu respect a ciki.
“Mteww…ke yama sunanki?”
Ta nuna hadiza da hannu, binta da ido hadiza tayi, sai kawa
i wani murmushi ya kufce mata ta kasa magana saida mayan ta kara cewa “baki..”
Cikin sauri hadiza ta katse ta “hadiza..sunana hadiza”
“Inason smoothie yanxu kafin ki gama pepper soup din”
“Tohm an gama yanxun nan kuwa za ayi maki sai kuma me kikeso? Ki
fada kin ayi maki yanxun nan”
Dan tabe baki maya tayi tana jin wani irin dadi aranta amma ta basar tace “ya isa”
Ta futa rabi ta girgiza kai aranta tace “futsararriyar yarinya”
Hadiza kuwa ta bi rabi da kallo tayi kwafa sannan ta fara kokarin yi mata sm
oothie data buqata.
Ahankali akayi knocking kofar kafin a shugo da sallama, nanne ce zaune akan gado cikin irin maroocan gowns dinnan mai hula, tana ganin anne tayi saurin sauke kafafunta daga kan gado ta aje takardun dake gabanta da glass din dake hann
unta.
“Wa alaikum salam! Anne!! Lafiya dai dakin bari nazo ay keda kike fama da kafa” nanna tayi magana tana kallon yayar tata.
Takowa anne tayi ta zauna gefen gado inda nanna ke zaune tace “nazo dubaki ne, ya zazzabin?”
“Alhamdulillah anne doctor yazo
dazu ay dan zazzabine fa, alhamdulillah ya sauka ma, ina wuni ya fama da iyali”
“Toh alhamdulillahi,”
Shuru ne ya dan biyo baya kafin anne tace “hajara!”
Nanna najin yanda ta kira sunanta tasan akwai magana.
“Na’am yaya”
“Nayi magana da doctor dazu, b
a zazzabi kadai ke damunki ba harda hawan jini kuma nasan damuwa ce tasa maki shi, Hajara ina ganin lokaci yayi daya kamata ki waiwayo rayuwarki ta baya….”
Murmushi nanna tayi ta kalli anne tace “wallahi babu abunda ke damuna babu wata damuwa anne, kawai
stress din aiki ne ba wani abu ba, ina gab da retire nima na huta abarma yara suyi”
“Hajara kinsan abunda nake nufi, bazanyi forcing dinki ba tunda kin nuna bakyason ayi maganar, bazan iya sanin abunda kike ji aranki ba amma inaso ki sani ni yar uwarki ce
hajara bakida kamarni, nice uwa a gareki kuma nice uba, bana fatan rasaki hajara don ayanxu ne nafi kowa buqatarki, babu wanda yasan gobe da abunda ke cikinta, kiyi hkuri hajara, bazan fasa baki hkurin nan ba kinji, ki aje komai a gefe ki nemi…”
Hawaye n
e suka fara neman ambaliya akan fuskarta tace “Anne please..dan allah dan allah badan halina ba mubar zancen nan,”
Shuru anne tayi sannan ta kama hannunta tace “shikenan hajara na bari, allah ya rufa asiri allah ya sawaqe, tunda kince ba damuwa bane, amma