Showing 111001 words to 114000 words out of 338813 words
hannu,madam na ganin suna neman disappointing dinta, badan tayi training dinsu ba a daidai wannan lokacin data koresu wallahi, tanason idan za ayimata aiki a dunga yi
da zafi zafi, musamman idan taji aikin masu hannu da shuri ne musamman wannan gidan da zasuje suyi aiki, millions zata samu wallahi tunda auren farko ne da za ayi a cikin familyn, so dole za a kashe kudi ayi abu mai kyau sosai, kallon sabeeha madam tayi s
annan tace “ke ma zaki bisu, tunda kin zama staff”
Hadiza najin haka wani dadi ya lulubeta, batayi tsammanin madam zata dauki sabeehar ba wannan zai bata damar daukan shawarar jamila, tabar aikin anan itama ta dan fara ko a cikin gida ne don tasan custome
rs din madam din kuma tana da numbers dinsu, zasu iya kiranta tazo har gida ma ta masu.
“Gobe da safe zaku zo cikin shirin around 5,akwai duk wani abunda za a buqata achan, sannan zan shirya menu, daga gobe saturday zuwa monday za ayi abinci da safe da
rana da kuma dare, both continentaland traditional, duk wadda tasan zata kawo min matsala gwara tayi magana tun wuri, zan hadaku da maza biyu saboda su taimaka sai masu serving uku,”
“Tohm madam bazaki samu matsala ta wajen mu ba Insha allah”
Sauke aji
yar zuciya tayi sannan tace “5am sharp.. za a zo daukan ku by 7, dot, aikinku zai fara da lunch ne banda breakfast gobe”
“Okay ma’am” duk suka amsata cikin ladabi.
Wani irin dadi hadiza takeji yau, dukda ba wannan ne aikinta na farko ba na zuwa gidan m
utane, last one da sukaje sun samu kyaututka sosai, harda su soveignair aka basu, fankar dakinta ma souvenir dinne na wani bikin da gomna da akayi anan abuja, bayan wanna an masu tara ta arziki don harda ragowar kayan abunci aka basu.
Washe gari da safe
misalin wajen karfe hudu sabeeha ta tashi tayi wanka ta gyara dakinsu sannan ta dafa ruwan shayi ta shirya kayanta guda biyu sannan tasa abaya cikin abaya’s din data dawo dashi ta dira hijab din da hadiza ta bata akai.
Wajen karfe biyar saura yan mintu
na kadan suka fito, tsakar gidan babu kowa sai kiraye kirayen sallah dake tashi.
Ataqaice dai biyar daidai ta masu a gargajiya plug, madam anan ta kwana ma tsabar bata son wani mistake, duk wani abunda zasu buqata an shirya shi harda menu din spcial abunc
in su, sauranma haka suka iso suma suka zauna, misalin karfe bakwai daidai motar da zata daukesu ta karaso, koya ya dau kayanshi, sabeeha na rike da nata dana hadiza suka fito compound din nan suka tadda madam tsaye sai fama washe baki take, “acema hajiya
waennan sune professionals dinmu, kartajo damuwa indai wajen aiki ne,”
Tunda suka tukaro motar hadiza ta tabbatar gidan manya zasuje ba kananu ba din ba a taba kaisu a irin luxury car haka ba, wani sain ma tura su akeyi cikin motar gargajiya plug din.
Ci
ki suka shishiga sabeeha sai baya baya take har motar yayi occupying kowa ya tage gaba ne babu mutane, wannan yasa ta shiga gaban ta zauna suka fuce daga wajen.
Tafiyace mai dan tsayi kusan kinti talatin, hadiza har gyagyadawa saida tayi anji sanyi ac,
bama ita kadaiba harda sauran na bayan, so basu san har an iso ba.
Tunda suka karyo layi sabeeha kebin anguwar da kallo, wallahi saitaji kamar tana saudi, anguwar is so organize, peaceful and elegant, babu tarkacen gidaje sai tairarru da suka gaji da kyau
, ga uban securities a anguwar kamar villa lol.
Daidai gaban wani katafaren gida driver ya tsaya yayi horn, securities masu uniform suka leko, ganin motar yasa suka bude gate din ya kutsa kai cikin gidan, sakin baki sosai sabeeha ta dunga yi tana kallon g
irma gidan da apartment har guda hudu a wajen, gari guda.
Kashe motar Driver yayi ya bude motar gaba daya suka fufito, hadiza ma bin gidan ta dunga yi da kallo kamar ba gidan biki ba babu hayani ba komai sai tarin motoci burjik kamar kamfani.
Driver ne
ya masu jagora ta bayan babban apartment din dake tsakiya suka zagaya, sunsha zagaye kuwa kafin ya tsaya daidai inda ya kamata ya dakata sannan ya kira a sanarda isowar masu abunci.
Wata ce ta fito ta masu jagora zuwa bq da aka tanadar masu, wallahi shim
a apartment ne mai zaman kanshi babu abunda babu a ciki, ga dakuna har uku a ciki yanda zasu sake harda parlor, babu abunda babu a ciki.
Ajiye kayayyyakinsu sukayi, yanmatan suka karbi daki daya sabeeha da dayar yarinyar sukuma sauran suka karba sauran da
kunan, mazan kuma aka basu dayan part din.
Wannan matar ce dai ta sake zuwa ta masu nuni da inda zasuyi girkin da komai da aka tanadar masu sannan tace hajiya tace duk abunda suke buqata da babu su fada sukace tohm.
Nan suka fara prepping abuncin rana
na baki, babu zama haka suka dunga dorawa suna saukewa, ana lodawa sabeeha kayan wanke wanke.
Sai wajen azahar suka samu gamawa, kuma lahamdulillahi everything looks perfect.
Bq suka koma sukayi wanka sukayi sallah sannan suka ci abunci, daman serving ba
nasu bane don akwai waenda zasuyi serving.
Sabeeha tunda ta zauna ta kasa tashi, wani irin ciwon baya ne ya riketa, tasa. Ba period zatayi ba amma abun yayi yawa daurewa kawai takeyi.
Koda dayar budurwar mai suna habiba ta ga yanda ta kasa tashi ta ta
mbayeta menene nan take shaida mata abunda ke mata ciwo, ta tausaya mata sosai don duk yawan uban wanke wanken nan haka hadiza tace tayisu duka don zasu buqaci kayan anjima idan an tashi yin dinner.
Dakyar ta samu tayi wanka sannan tayi sallah ta kwanta
ko abuncin bata samu taci ba.
Chan cikin gida babu abunda ke tashi sai guda riiiiriii…a daidai lokacin da aka shugo da amadya cikin gidan, wato ana sallar azahar gidan ya hade da mutane sosai, yan uwa da abokan arziki, dangin amarya dana ango, ango dan
gata, babban jika ga hajiya anne ikon Allah, Sufyan Sameer Santuraki da amaryarsa leedarh Yusuf.
Jiya jum’a aka daura aurensu a yola, don yar yola ce, yau saturday kuma za a fara hidimar biki gobe budan kai da yini.
Bikin babu wani hayaniya don ango bay
a kasar ma ana daurawa amaryar zata bishi chan england, don achan yake da zama tunda ya gama karatu ya samu aiki, haka zalika yan gidan basu fiye son wani kide kide da rawe rawe ba ko gayyar su dinner dasu mother party daddys party da sauransu, saidai a ci
kin gida zasuyi duk wani hidima, aci mai kyau asha mai kyau ayi ruwan kudi aji dadi rayuwa between familys.
A babban parlor aka zauna dayasha ado, kai kudi yayi allah ka mana arziki mai albarka, kowacce ka ganta zaune babu abunda take aai walwalin,su an
ty fadila an fito, tasha lace mai masifar kyau da tsada, fuskanta ta danyi makeup mara hayaniya, su nanna da anne na zaune suma dai ba’acewa komai, bakiin anna yaqi rufuwa yau auren babban jika, anty mubina ma na zaune da mubin dinta a kan cinyanta, she ca
n’t believe dansu ne yayi aure yanxu lallai sun manyanta, dangin amarya ma ba a barsu a baya ba don gaba daya sunsha gayu sosai don suma sunada arziki sosai, tarba ta mutunci aka masu sosai sannan aka shigar da amarya bayan ta gaisheda kakanni.
Su laila
karama ana daga sama, sai faman tashin maya take taqi tashi, wani irin barci take kamar matacciya tun safe ko wanka batayi ba.
Anty laila kuwa uwar ango tana daga chan bangarenta kamar zata fashe, yan uwanta sun zagayeta gaba daya, masu zigata da masu
nuna mata fushinta bashida amfani, don abunda takema fushin bashida amfani.
Tunda ta zauna babu abunda take sai hade haden rai, maysa a matsayinta na mahaifiyar sufyan baza a fara zuwa wajenta ba,? Ita gaba daya auren nan shes not in support of it, sufyan
is just 27, dandai ya dage ne yanaso kuma bata isa ta hana ba.
A taqaice dai sai wajen dare aka dungumi amarya bayan an shiryata aka kaita wajen maman ango, taje ta gaisheta, ganin yanda dangin amaryar suma suke jin kansu yasa laila ta sauke nata kasa.
Da yamma sunci wani kwakwa, don aiki suke nonestop, daurewa kaqai sabeeha take, itace dauko kaza jeki kai kaza ajiye kaza bar kaza miko kaza.
Sai dare wajen karfe tara ta samu sarari, tayi wanka tayi sallah ta kwanta jiki duk wajala duk tsami.
W
ashe gari da asuba suka sake tashi suka fara aiki don yau harda breakfast, za ayi.
Saida aka gama komai suka tuna ba ayi egg sauce ba, tuni hankali su ya tashi, gashi babu kwai balle a fara sarrafawa don ya kare, dole daya daga cikin zawaran tasa sabeeha
tabi inda matarnnan ke zuwa dubasu ta sanar da ita, don ba hurumin su bane shiga cikin gidan dandai ya zama dole ne, hadiza batasan da haka ba donta zagaya bayan gidan.
Jiki a mace sabeeha ta bi hanyar da matar nan ke bi ta shiga cikin gidan, lokaci guda
kanta ya rabu gida biyu ta rasa ina zatabi, corridors ne har kusan guda uku a wajen, har wani jiri jiri takeji wallahi tsabar gajiya, dauriya kawai take, inda ta soma jin hayani na dan tashi ta nufa a natse tana fatan taga matar, adaidai lokacin maya ta ka
ryo kwana babu zato ba tsammani kawai sukayi gware gwab, smoothie din dake hannun maya ya fadi kasa bottle din ya fashi, rai a bace ta dago batayi wata wata ba kawai ta sauke mata mari a fuska, cikin saurin sabeeha ta dafe kuncinta tana mai dubanta “are yo
u mad? Bakida ido ne? Wacece ke?”
Hamad dake tsaye don yanxu suka gama musayar yawu shida maya din ranshi ya baci batama san ya biyota ba yana jiyo muryarta ya karaso wajen, kallonta yayi sannan ya dubi sabeeha dake rike da kunshinta ta sunkui dakai,
Qaurin dataji sabeeha nayi ne ya tabbatar mata da yar aiki ce wannan yasa ta cewa “kina tafiya kamar wata dabba, bakida ido ne?”
“Maya!!!!” Hamad ya daka mata tsawa yace “how dare you call someone da dabba?”
“Na kirata din kaina kira? Karka shiga gonata
, ka fita harkana”
“Well alamun sun nuna kece mai halin dabbobi,wadda batasan darajar mutane ba”
“Fuck off…” ta karashe tana galla mashi harara sannan ta bangaje sabeeha hartanayin baya kamar zata fadi ta kara gaba.
Kallon sabeeha yayi yace “i’m sorry f
or her behavior,”
Dagowa sabeehar tayi ta danyi murmushin takaici tace “bakomai”
Tunda ta dago hamad ya kalleta ya kasa dauke idanunshi a kanta, yanda yake kallonta haka take kallonshi garta tsargu tayi saurin duqawa zata kwashe glass din ya hanata nan y
a tambayeta ina zata je? Kuma wa take nema.
Anan yasa ta tsaya ya kira indo mai aikin gidan gaba daya tazo sannan ya umarci ta kwashe gwalbar, sabeeha na fada mata abunda ya kawota ta futa.
Tunda hamad ya juya babu abunda yake sai tunani, she looks s
o familiar amma ya rasa a ina ya taba ganinta.
Sabeeha na komawa hadiza ta kalleta tace “daga ina kike?”
“Cewa akayi naje na fada masu babu kwai”
“Shine kika dade haka, uban me kika tsaya yi? Shishigi kome?”
“Banganta bane saida wani ya kirawota”
“U
ban waye yace kije? Shin ba ance iyakacin mu nan ba?
Matar data aiketa ce tace “Haba hadiza, kwai kawai nace taje ta fada masu babu saboda ba ayi egg sauce ba”
Acahn parlor maya na shigowa daki laila na ganinta ta gane ranta ne ya baci, “ke kuma dawa
?”
“Useless workers dinnan mana, mutane na tafiya kamar wasu blind monsters”
Tabe baki laila tayi don tasan halinta da masifa yanxu haka ka bibiya fault dinta ne.
Biki yayi biki fa, tun wajen karfe biyu aka fara hidima, an jera kujeru anyi decorating
wani shashe daga compound, mutane an taru dagin ta ko’ina, amarya ta fito fess fess sai walwali take anyi budan kai anyi hotuna an watsa kudi sosai ba kadan ba sannan an rarraba sovereign na futar hankali, kawayen amarya harda zobunan gold aka basu Masha a
llah.
Maman ango tayi ma amarya kyautar gold, anne da nanna suka bata sarkar diamond mai kyan gaske, masha allah,lefen amarya ko da aka bude don ba a kaisu yola ba dozin biyar akayi mata, kaya dai hmm ba a cewa komai masha allah saidai ace allah ya sanya
alkahiri ya kawo kazantar daki amarya dai yar gata ce yanda ango yake dan gata.
Yan matan amarya da kannen ango sunsha kyau, maya da laila anci makeup an masu kaya iri daya, samarin gidan ma su abal da hamad suma sunyi kyau harda sauran kannun kai wanga
family gwanin ban sha’awa.
Bayan an gama abunci an fita dashi masu serving sun shirya, chan bangare su hadiza sun shiga bangaren da aka basu sunyi wanka sun dan huta hadiza data faki fuskar sauran ma’aikatan tayi wuf ta fice daga dakin, daman tanata ne
man yanda zatayi ta shiga cikin gidan ta samo wa kanta customers, don zata dunga bin manyan mutanen nan tana fada masu su sukayi girki idan suna buqata ta basu number ta, its her own method of startingher own business.
Tunda ta shigo babu abunda take sai
famn girgiza kai, gida fa ya hadu ya gama haduwa, “anty duk suna waje”
Wata yar yarinya ta fada ma hadiza dake shirin bin wata hanyar daban kamar shes lost, washe baki tayi aranta tace ashe nima na saje da masu kudin nan.
Inda yarinyar ta nuna mata ta nu
fa sai gata kuwa a compund din gidan dake cike da mutane sosai, masu gidan kalangu da gidan kwarya anata yi son taya murna.
Daddaga kai hadiza ta soma yi ganin yanda akwta watsa kudi oo abundai sai Allah, masu kudi dai basajin zafin kudi ta fada aranta.
Kamar ance ta juyo karaf idanunta ya sauka kan anne, wani irin dammmm taji gabanta yayi, saurin mutsike idanunta tayi ta bude, ta karajin wani damm damm, juyawa da zatayi kuwa ta hango nanna da fadila a tsaye sunama amarya barin kudin, wani irin jiri ta
somaji tayi saurin yin baya ta fita daga wajen, tafiya take amma batasan ina kafarta ke wullata ba har saida ta jiyo muryoyin wasu mutane na cewa , “kai wallahi amaryar nan yar gata ce, aure a gidan Alhaji santuraki ay kamar an tsomaka cikin daula ne.”
Ba
ta tsaya sauraronsu ba ta shige cikin daki ta kullo kofa, allah yaso babu kowa ciki ta fara safa da marwa gaba daya ta gurkice ta zama kamar mai tabi ko wadda taga dodo, babu abunda take sai innalillahi wa inna ialihi rajiun, gaba daya komai na dawo wa kan
ta, kunci da zafi da rashin datayi duk ya gama dabaibayeta,komai ya dawo mata sabo kamar jiya akayi, the hatred that pain komai ma.
Wayarta ta soma kiciniyar nemowa tama manta cikin jakarta datake ajewa, saida ta burkice kayanta gaba daya ta samo wayar sa
nnan ta fara dialing number jamila, kira daya biyu tana dauka ta soma magana “jamila na shiga uku..jamilaa……”
Yanda take magana yasa jamila gane cewa akwai matsala kenan.
“Kimin bayani menen? Meya faru?”
“Jamila gidansu na dauko kafata na kawo kaina..in
nalillahi jamila zuciyata na zafi,”
Doka salati talati tayi yanda hadiza zataji daga chan kuma bangarenta sai ta sauke wani murmushi kafin tace “toh se me? Malama ki kwantar da hankalinki, akwai wanda ya ganki ne cikinsu?”
“Ah ah babu inda muke zaune dab
an”
“Shine kiketa faman tada hankali? Yoh zama su iya tuna koke wacece? Zasu wani tuna da rayuwarki ne hadiza?”
“Ya zanyi jamila? Eh,in suka ganmu fa nida sabeeha karsu..”
“Kinga natsu, ki cigaba da harkarki ko sun gankin sai me? Zama ne akayi ba zaman
dadi ba aanoda haka ba komai bace ke a wajensu haka zalika kema babu wnai abu tsakaninki dasu”
“Toh shiknan, amma kina ganin ba komai?”
“Eh ki kwantar da hankalinki”
“Toh.. zan kuraki anjima”
Tana kashe wayar ta wuce dakin da sabeeha ke ciki tana kwa
nce ta raqube, kallo daya hadiza ta mata ta dauke kanta, ta futo zuwa daki tasamu guri ta zauna sai hawaye, “laifinka ne, laifinka ne”
Abunda take fada kenan.
Abuncin daren data kasa concentrating kenan dole ta futo akayi da ita idanunta nakan sabeeha, d
ataga tana faman riqe baya wannan yasa tace taje ta kwanta ta huta.
Dake kowa yaga yanda yarinyar ta wahala babu wanda yace takk.
Kwanan ranar hadiza ido a bude tayishi, ta kasa zaune ta kasa tsaye, babu abunda take sai hawaye data tuna baya, saiyanxu
hankalinta ya fara zuwa ga yarta.
Washe gari da safe akayi breakfast aka gama, daman daga breakfast sai lunch da za ayi kawai don ranar za akai Amarya airport kowa zai watse.
Hadiza fa kasa sukuni tayi saida ta kira jamila, ta dan tausasa ta kafin ta
kashe wayar.
Sunyi abuncin rana sun gama suna jirane kawai a sallamesu sannan akaisu chan gargajiya plug, kowa ta hada kayanta jiran driver kawai suke, har sun fito indo ta jagorancesu cikin gida, tunda hadiza taga sun shiga ciki gabanta yake fadiwa ta k
asa dannewa tace “ina zamuje kuma na dauka mota zamu wuce kawai?”
“Hajiya zata sallameku tukunna”
“Ah ah madam ay za a bama koma menen mu wucewa zamuyi”
Wani irin harara sauran matan suka watsa mata tana neman yi masu baqin ciki indo dai batace masu kom
ai ba.
Sabeeha na bayan uwarta kanta a kasa hadiza kamar karta bisu haka taji.
Basu tsaya ko’ina ba sai main parlor inda babban hoton marigayi santuraki ya mata iso tun daga nesa, cikin hanzari ta dauke fuskanta suna daga baya baya, indo ta masu nuni da
waje suka zauna.
Kusan a tare anne da nanna suka sauko, zama sukayi