Showing 60001 words to 63000 words out of 338813 words

Chapter 21 - MATAR TAJ COMPLETE

akan fuskarta kamar wadda ke mafarki ga bakinta na motsawa ahankali sai kuma dan karkarwa datayi, dan duko da kanshi yayi daidai bakinta don jin abunsa take fada, “didi…didi..bazasu yi maka komai ba..i will always protect you..din allah karka tafi ka bar

ni didi..”

Dukda a rarrabe take fada hakan baisa ya hade maganganun nata ba, yana mamakin mafarkin me takeyi, jin sunan dayaga tana kiranshi dashi yasa ya gane mafarkin hardashi takeyi kenan, amma meysa take kuka tambayar daya dunga na kanshi kenan, why w

ould she cry out while calling his name, “didi….” Abunda ya sake ji kenan saidai baiji karahen zancen ba, hannunshi daya ya daga ya dorashi kan fuskarta, yanajin temperature dinta yayi saurin daga hannun nashi ya miqe ya shige bathroom, kafin ya gitk da bo

wl a hannunhsi da handtowel ya zauna gefen gadon, ya rasa dalilin dayasa yakejin zafin da takeji, kamar an dauka ciwonta an saka mashi haka yake ji,ya rasa meysa yake jin haka game da ita, itace mace ta farko daya taba yima haka, and yana tunanin saboda ci

kin shi dake jikinta ne,saurin kauda komai yayi daga tanshi ya saka towel din a cikin bowl din yana matsewa ya dagoshi zai saka akan fuskarta memory din lokacin da bashida lafiya ta zauja tare dashi yazo mashi, gaba daya kamar an tunkudo memoriws din haka

suka zo mashi batch by batch, take ya fuskanshi dalilin dayasa yakejin abunda yakeji game da ita, which he can define it as utmost respect he has for her, aduk lokacin da zai tsinci kanshi cikin kunci zai ganshi da ita suna hawaye,she has become part of hi

m acahn baya, ya samu soyayyar da kulawar kusanci da bai taba samu ba a wajen kowa, zai iya fasaara hakan da soyayyar da uwa kema danta uncontrollably fond, tund aya saka towel din akan fuskanta yake kallonta sosai, zuciyarshi ta gaka aminta da ita, koda

kuwa yayi denying to yayi ma kanshi karya.

Ya dade a gefenta har saida zazzabin ya sauka sauka daga jjikinta wajen karfe daya kafin ya koma gefen gadon ta dayan barin ya zauna, anan zaune barcin ya tafi dashi….



💋

BOSS LADIES WRITERS

💋



MATAR

TAJ (destined with you

🩵🤍

)

Written by

Queenmarh





Book2

PAID

Chapter 69

Ahankali ta soma bude rinannun idanunta da sukayi mata nauyi, kokarin tashi ta somayi harta miqe zaune,kwata kwata bata lura dashi ba saidata fara kokarin sauka d

aga kan gado taji kamar an rike hannunta gam,da mamaki ta juyo, take ta sauke idanunta akanshi, yana daga zaune ya jingina da bed board din gadon ya rufe idanunshi sleeping soundly, ga hannunshi daya hade da nata ya rike gam kamar wadda za a kwace mashi it

a,tundaga yatsunshi tabi da kallo har zuwa calm face dinshi da gashin baki ya zagaye ta, tayi mamaki sosai ganinta kwance akan gadonshi gashi kuka a gefenta ya rike mata hannu gam, jiya gaba daya bata cikin hayyacinta lokacin daya shugo dakin, sai yanxu ta

ke tuna yanda ya dauketa jiyan hankalinshi a tashe, saurin runtse idanunta tayi ta budesu akanshi, ganinta kwance kan gadon nashi ya tabbatar mata bai gano cewa bata da ciki ba kenan.

Hannun nata ta fara kokarin zamewa daga nashi ta kasa, saima dagowa dat

ayi kawai taga ya bude idanunshi tarr akanta, tun lokacin data farka

ya tashi shima amma bai bude idanunshi ba, yanajin yanda take kallonshi,harta fara kokarin zame hannunta daya rike.

Lumshe idanunshi yayi ya sake bude su akanta, fuskan nan babu yabo ba

fallasa yanda take koda yaushe, sai kwarjini da cika idanu.

Daburcewa taso yi ganin yanda yake kallonta yasa tayi saurin cewa “dan allah kayi hakuri bansan yanda akayi na…”

Zare hannunshi dayayi ya miqe tsaye yasa ta dakata, bedroom slippers dinshi ya sa

ka sannan ya zagayowa ya wuce hanyar bathroom, tunda ya wuce ta bishi da idanu har saida ya shige bathroom din ta sauke ajiyar zuciya ta doka tagumi, bai wani dade ba ya futo daga bathroom din ya tunkari inda take, cikin hanzari ta kauda idanunta lokacin d

a suka hada idanu, a daidai gaban gadon ya tsaya yana kallonta na yan sakanni kafin ya soma magan acikin kamala “how are you feeling now? Akwai abunda ke maki ciwo”

Cikin sanyi yayi maganar kamar bashi ba, sai taji wani irin sanyi aranta ganin ya sauya lo

kaci guda, gira daya ya daga mata ganin ta kafeshi sa idanu, saida yayi cliking fingera dinshi ta dawo daga tunanin data shiga, tayi saurin kauda idanunta wani irin siririn murmushi ya kubce mata tace “Alhamdulillah i’m feeling better”

Yana jin haka ya sa

ke magana “zaki iya tashi?”

Da mamaki ta dago for the second time ta kalleshi don tabbatar da daga bakinshi maganar ta futo,bata gama tunanin ba again kawai taga ya miqo mata hannu, tana ganin haka ta gane me yake nufi, kanta a kasa ta daura dan hannunt

a kan nashi ta miqe tsaye, dake yana gabanta saita zama yar smally a gabanshi saboda ya fita tsayi sosai,da taimakonsa ta shiga bathroom ya bude mata kofa, kafin ya futo ba tare da yace mata komai ba.

Yana futa ta sauke wani irin murmushi, a gurguje tayi

hot bath sosai yanda jikinta zaiyi mata dadi sosai kafin tayi wankan tsarki tana gamawa ta dauro alwala ta nado jikinta da towel, saida ta gama ne ta fara tunanin yanda zata futa don bata shugo da hijab dinta ba, gashi tana jin kunyar haka, fatarta sai has

ke da sheqi takeyi tsakanin kwanakin nan, kallon kanta ta dunga yi a jikin mirror din toilet din, gaba daya ta sauya kamar ba ita ba, wannan dafewar data yi lokacin da take wahala a gida duk ta baje, wani sa’in inta kalli kanta har mamaki take, yanda kasan

an sauya ta gaba dayanta, inta koma gida ba kowa ne zai ganeta ba sabod asauyawar tayi yawa dama wahala ce da talauci ta dankwafar da ita ta lalatata.

Sauie ajiyar zuciya tayi ta janyo wani towel din ta nadoshi wajen kirjinta dake cike kamar suna neman y

i mata yawa, harta nufi wajen kofar futa taji knocking daga ciki, cikin hanzari nufi kofar ta bude, yana nan a tsaye, daman sallah yayi yana idarwa yaji shuru babu motsi a bathroom shine yayi knocking don ya tabbatar ba passing out tayi ba don jiya Ya tsor

ata sosai da lamarin ta.

Ganin she’s perfectly fine yasa shi kauda ido ya matsa ta futo shi kuma ya shige daga ciki.

Yana shiga ta nufi closet da hanzari ta fiddo daya daga cikin rigunan da ammu ta saya mata ta saka sannan ta shafa mayukan data bata da

turare mai sanyin kamshi kafin ta futo da hujab a hannunta.

Sallar itama tayi don kusan karfe takwas ta gifta, harta isar da sallah bai futo ba harta miqe zata zare hijab din datayi sallar dashi sai gashi ya futo daga bathroom din, direct dakin shiryawa

ya nufa ya saka kaya marasa nauyi kafin ya futo, sai faman kamshi yakeyi mai dadi,kafafunshi na cikin bedroom sandals ya futo, harta gyara dakin fess fess hatta wajen

beddings saida ta sauya sabo, yana kokarin daukan wayarshi da incoming call ke shugowa ta

shugo dakin hannunta rike da mug a hannunta, tunda ya daga wayar yayi shuru baice komai ba saima kallon bayanta daya tsayayi lokacin taba kokarin rufe kofa data shugo, tana juyowa ya kalleta daga sama har kasa, kayan jikinta sunyi mata kyau, pink din dogu

war riga daidia jikinta, wajen kanta kuma ta daura veil din kayan ya danyi baya gashin baby hair dinta ya futo,zama yayi bakin gadon har zuwa lokacin wayar na kunenshi yana magana kadan kadan cikin harshen turanci, karasowa tayi har inda yake ta dan jinkir

ta tana tunanin yanda zatayi ta bashi, bata gama tunanin ba ya mika mata hannu alamu ta bashi, kallonshi tayi harta tsinci shika kallon nata yake, murmushi tayi mashi tare da miqa mashi mug din, yana karba yakai bakinshi direct har zuwa lokacin bai sauke w

ayar dake kunnenshi ba, tana daga tsaye yasha kusan rabi, bata gajiya da kallonshi a tsaye harya gama sha shi baima san ya gama ba saima miqa mata mug din da yayi ta karba fuskanta wasai ta futa daga daki ya rakata da idanu.

Tana shiga kitchen tabi mug di

n dayasha tea din da kallo, yau shine yasha avun hannunta willingly? Saitaji dadi aranta sosai.

Noodles ta dafama kanta taci ta koshi anan kitchen din don rabonta da abunci tun jiya da yamma data kasa cin komai.

Saida ta tsaftace ko’ina kafin ta fito zu

wa bedroom din, a tunanin by that time ya futa already don tasan kullum saiya futa da safe, tana shugowa taga akasin haka saima ganinshi da tayi a zaune kan gado har zuwa lokacin yana waya, bata jin mai yake fada saboda accent din da yake using british ne,

wannan yasa ta kasa gane me yake fada.

Futowa ta sakeyi zuwa sitting room donta ta bashi waje zamanta keda wuya ammu ta shugi donta dubata, bayan sun gaisa ta tambayi ya jikinta nan ta shaida bata babu ciwon bayan ma da kafa duk ya tafi, nan ammu ta mata

bayanin abunda ya faru jiyan sannan ta shaida mata ta bar shan maganin.

Sun dade sosai suna hira har sabeehar ta fada mata yanda yau ta hada mashi coffee kuma ya shanye duka, daga yanda take fada ma ammu ta gane taji dadin sauyawar da yayi,

“Ay jiya ba

kiga yanda hankalinshi ya tashi ba, ya dauka ko wani abu ne daya danganci cikin”

Shuru sabeeha tayi jin abunda ammu tace, saitaji wani iri aranta,ganin haka yasa ammu ta kama hannunta tace “karki damu kinji, just keep focus,komai zaizo mana cikin sauki

Insha allah”

Sun dade suna dan tattaunawa cikin maganar da sukayi kwata kwata basu kawo karyar da sukayi na cikin ba saboda sabeeha ta fada mata bai fita ba yana nan bayan wannan ma kar wani ya jisu wannan yasa suka daina maganar cikin.

Saida ammu zata f

ita tasata dole ta koma bedroom din.

Da sallama a bakinta ta shugo dakin, shi kuka ya fito daga closet, maganinta daya saka a jikin jacket din daya fita dashi da sukaje asibiti ya dauko, gaba daya yama manta dashi sai yanxu,ajiye yayi gefen bedside kafin

ya kalleta yace “your medication” ya karashe yana mata nuni da ledar, cikin natsuwa ta amsa shi da “tohm”

Baice komai ba ya nufi hanyar futa daga dakin maganar datayi ya dan dakatar dashi, “thank you”

“For?” Ya jefo mata tambaya ba zato ba tsammani, “uh

m…for helping me yesterday”

Yana jin haka ya juyo ya kalleta “don’t think highly of your self, i did that only bacause..”

Ya kalli cikinta kafin ya maida dubanshi gareta, “don’t thank me for taking my responsibility”

Yana kaiwa nan ya fuce.

Bayan futar

shi Jiki a mace ta nufi wajen bedside ta dauka maganin ta balla tasha.

Yana futa ya wuce sitting room din sama, hidaya na daga zaune ta hakimce kan kujer tana jiran zuwanshi, yana ganinta ya karaso ya zauna, “sabahal khair” ya gaisheta kai tsaye, abunda

ke cinta tayi saurin dannewa ta amsa gaisuwar tashi kafin tace “ya jikin nata??”

Yayi mamakin tanbayar tata sosai ba kadan ba saidai bai nuna ba a zahiri, “hamdullah!!”

Ya amsata a garaje, shuru tayi tana son tambayarshi abu amma tanajin shakjar yin hak

a yanxu ta rasa dalilin dayasa take dan shakkarshi , kodan ya sauya ne cikin kwanakin nan sauyawar tashi ma tayi yawa sosai, don yanxu ko gaisheta zaiyi baya mata yanda yakeyi ada.

“So yanxu ka yarda da wannan pregnancy din naka ne kenan?”

Yana jin abund

a ta fada ya kalleta, kai tsaye ya amsa ta “eh…”

Yana fadin haka ta sauke wani irin makirin murmushi chan kasan maqoshi kafij tace

“Okay then,tunda kayi accepting banida ja akan maganar,”

Jinjina mata kai kawai yayi kafin ta miqe ta fuce daga parlorn.

……

Tun fitar dayayi dazu nan bata sake ganinshi ba har wajen karfe tara na dare, tunda tayi sallah tasha magani takeji wani irin azababban barci yana fuzgarta haka ta hana kanta barci nan ta zauna jiran dawowarsa.

Misalij wajen karfe goma kuwa sai gas

hi ya dawo gidan da shopping bag daya a hannunshi, yana shugowa yaci karo da barad daya futo daga dakin ammu, taj na hangoshi ya sauke mashi murmushi,yaron shima yana hango taj din yayi saurin karasowa inda yake ganin babu kowa a kasan, daman tsoronshi kaf

hidaya ta ganshi da taj din.

“Uncle taj”

“How are you?” Taj ya tanbayeshi yana mai shafa kanshi, “im fine uncle, where anty fatima?”

Shuru taj yayi yama rasa me zaice masa, ya dai lura wannan yarinyar yake nufi, “whos anty fatima?”

“Your best friend m

ana… opss sorry i mean bibi”

Taj najij haka ya dan duqa a gaban yarin yace “is that her name?”

“Yes uncle…ka manta ne? Kaika saka mata sunan fa?“

“Bi..bi” taj furta ahankali, kafin ya kalli barad din ya sake jefo amshi tambaya “is she nice?”

“Yes uncl

e shes very nice and calm, itace ma ta..…”

Shuru yaron yayi tunawa da gargadin mamanshi, ganin yayi shuru yasa taj shima baice mashi komai ba ya bude shopping din daya shugo dashi ya deba chocolates da yawa ya zubama barad a aljihunsa kafin yace “ka boye

su”

Girgiza mashi kai yaron yayi ya haura sama, yana son tambayarshi ya jikin babansa amma ya kasa.

Saman shima ya haura ya wuce part dinsu direct, kofar bedroom ya bude ya shugo bakinshi dauke da sallama dukda muryarshi bata futo ba yanda za aji sosa

i kamshin nan ya amsa mashi direct zuwa hancinsa, tundaga nesa ya hangota kwance gefen gadon a kasa ta saka kanta kan katifar gadon, tana sanye sa wasu kayan daban bana dazu ba a jikinta.

Takowa yayi daidai bakin gadon inda take kwance ya tsaya yana kallo

nta kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ajiye ledar daya shugo da ita sannan ya wuce bathroom, ya dan dade sosai a ciki kafij ya futo ya shurya zuwa kayan barci .

Harya futa tana nan kwance abunda sai faman sauke ajiyar zuciya take, kokarin tashinta ya somayi

ta hanyar dan taba in da kanta ke wajen amma ko gizau, kamarma tayi nisa sosai a barci, gashi baya jin zai barta ta kwanta a kasa saboda zazzabi, duqawa yayi a gabanta ya fara taba kafadarta ganin still farkawa kawai ya sungumeta gaba dayanta kamar yar ba

by ya miqe tsaye,gaba daya batada wani nauyi amma a ido zaka dauka tana da nauyi saboda dirin da take dashi,ahankali ya zame slippers din kafarshi ya rankwafo zuwa gadon ya kwantar da ita kafin ya miqe tsaye ya zagayo gefen gadon ya zauna.

After 2weeks

Cikin satin biyun nan abubuwa da dama sun faru tsakaninta dashi, yanxu ta gama karantarshi tsaf, tasan abunda ke saurin pisaing dinshi off wanda take gudarma hakan sannan, halayyanshi ne da mood dinshi ta kasa karanta dan yau saika ganshi sanyi sanyi gobe

kuwa gaba daya saiya sauya, bata fasa kyautata mashi ba kullum ba tare da ta nuna gajiyawarta ba, kullum da safe kafin ya fita zata dafa mashi coffee ta bashi, kafin ya futo daga wanka kuwa zata fidda mashi kayan da zaisa, ranar daya saka wanda ta fidda m

ashi ba karamin dadi taji ba sosai, yanxu ya fara dan sake mata kadan, don idan ta dafa abunci ma anan part dinsu yana ci sometimes, kuma kamar yanda ammu ta fada mata da zarar yana daki ta dunga kasancewa a tare dashi don ta janyo kusanci taakaninsu yanxu

abunda ta dage dayi kenan, ta dan rage tsoron yi mashi magana saboda yana amsa ta sama sama idan ta mashi, abunda yafi yi mata dadi arai shine yanda koda yaushe yake tambayar if she’s okay, kwata kwata baya nuna mata ya damu da cikin amma actions dinshi k

e bayyana mata hakan.

Yanxu ya hanata kwanciyar kasa ma, a kan gadon shi take kwanciya, da yake saitayi barci yake kwanciya wannan yasa bata gane inda yake kwana ba, kota farka bata ganinshi a dakin.

Bangaren su afiya babban shiri sukayi na ganin sun zub

da cikin nan amma kudirinsu bai cimma ruwa ba, saboda gaba daya sabeehar ma basa ganinta, ba ita kadaiba harma taj din,don basa saukowa yin breakfast, daman wannan damar suke nema kuma bata samu ba, dole suka hakura harsai sun samu chance, bangaren fadwa g

aba daya zaman gidan ma ta kaurace mashi, idan ta fita tun safe bata dawowa sai yamma, saboda idan har ta zauna a gida tana tuna cewa akwai wata dake dauke da cikin taj din a gidan zata iya komai, zata iya komai akanshi,

Bangaren hidaya ko gaba daya yanxu

ta maida ahankalinta wajen kamfani, product din datake developing yana neman failing,risk din failure din product din yafi samun da za ayi a cikin kamfanin, ita bata ma hango risk din da kamfanin ke ciki, duk wani illlegal ways shi take amafani don ganin

kamfanin ya tsaya, wannan investment din data dakatar ba karamin taimakon kamfanin yakeba, taqi accepting haka, a ganinta indai ta cigaba da karbar wannan investment din da zarar aka gano wanda ke bayarwa shikenan tata ta kare.

Ta wajen taj duk abunda k

e faruwa a kamfanin yana sane dashi,saidai baiyi yunkure yinkomai ba haka zalika bai nemi ainahin sanin dalilin dayasa hidaya ta cire investment din da yake bayarwa ba cikin airei, kuma tun

data nuna batasan komai ba game da identity dinshi shima shuru yay

i baice komai ba saima maida hankalinshi dayayi ga abubuwan dake gabanshi.

Mutalib ko bai fasa shigema taj dinba, daman dalilin shigarshi wajen gym dinnan kenan, har saida ya dan samu taj din na kulashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login