Showing 297001 words to 300000 words out of 338813 words
tundaga nesa ya hangita tana hade fuska, ganin ta ganshi tayi mashi wani irin izgilin kallo ta kauda ido yasa shima ya kauda nashi don inda sabo ya saba,tun sanin da yayi mata daman yasan ta iya wannan, har zqi wuce ta gabanta ya dan dakata, baiyi niy
ar mata magana ba karta kawo mashi raini amma kuma ya danne yace “are you okay?” Ya fada cikin sanyi.
Kamar jira take a harziqe ta dubeshi, “do i look like I’m not?”
Ta kafeshi da idanunta da suka soma jaa, full of hatred, ganin haka yasa ya kauda nashi
zai wuce abunshi ta dakatar dashi.
“Wajen wannan munafukar kaima zakaje ko?”
Chak ya dakata tare da waigowa ya kalleta da mamakin who shes referring to as munafuka.
“Dama chan nasan ba kowa ke sona ba a gidan nan,babu wanda ya taba damuwa da rashin lafi
ya na, amma da yake munafukar nan ce….” Ta cije lebe ta kasa karasawa, magana take cikin bacin rai da futsara idanunta ya rufe, shiko sai yanxu ya dauko inda ta dosa, ya zama vwry speechless, baiga dalilin da zaisa ta fara wannan magnagnun ba, amma ya mata
uzuri tunda it will be very hard for her to move on.
Matsowa yayi har inda take ya fuskanceta sannan yace “babu wanda ya tsaneki a baya haka zalika babu wanda zai tsaneki a yanxu, sannan babu abunda ya sauya, be mindful maya and this should be the last t
ime zakiyi pointing dinta as munafuka,”
Yana kaiwa nan ya wuce zuwa main house ya barta tsaye, tana jin wani abu a maqoshinta, tunda gaskiyar ko ita wacece ya bayyana babu wanda ya kasance stands by her kamarshi, kullum saiyazo part din ya dubata, sannan
ya bata baki akan karta saka damuwa aranta, koda kuwa zaizo sau goma bazata ce mashi tak ba saidai taita hawaye, da aka kwantar da ita asibiti ma lokacin data suma data gane hadiza ce uwarta shike zuwa koda yaushe harta farfado, yanxu kuwa data ganshi rike
da abubuwa a hannunahi zai shiga part din tasan shima wajen sabeehar zaije, gashi yanda ya maida mata magana akan kawai ta cema sabeeha munafuka ya nuna alamun ta fita mahimmanci yanxu, kowa ta sabeeha yake saboda itace yarsu ta asali,
Arantaa tanajin ya
nda ta tsani gaba dayansu kowa ma, aikin sharrin shaidan kenan, babu abunda bata saqawa a ranta na rashin alkairi wanda shike tunzurata.
Jan kafafunta ta soma yi zuwaga part din mutuniyarta wato anty laila, dake su suna daga chan kasa kasa apartment dinsu
, tunda daman tasan anty laila ce tafi kowa sonta amma tayi mamakin da tunda abun nan ya faru bata nemata ba, yawanci idan bata leka gidanta ba kwana biyu ita ke kiranta a waya, don duk wani hirar nan cikin main house maya ke kai mata.
Tana knocking mai a
ikin gidan ta bude kofar, sannan ta dubeta sama da kasa, abunka da maganar cikin gidan kowa yasan da zanjen cewa ita ba yar gidan bace yar mai aiki ce hadiza, daman yawanci a junansu suma yan aikin suna yan gulmammakin nan, basa kaunarta kwata kwata saboda
bata da mutunci ko kadan, ga wulaqanci ga tozarta na kasa da ita, sau nawa basira zata kawo masu labarin yanda takema sabeehar data kasance ashe itace asalin yar masu gida.
“Kallonna na uban ke kikeyi? Munafuka” maya ta fada rai a bace
Kauda idanu yar a
ikin tayi sannan ta tabe baki tace “bari a fada ma hajiya tukunna saiko shugo”
Ran maya idan yayi dubu ya gama baci, yau itace za ace sai an shiga an tambaya kafin ta shugo, lallai saita koyama yar iskar yarinyar nan hankalo.
Mardiya na kokarin rufo kofa
maya ta bangajeta zata shiga daga ciki mardiya ta tsare gabanta tace “cewa nayi ki tsaya na tambayo hajiya tukunna kafin ki shugo”
Maya batayi wata wata ba ta daga hannu ta kwasheta da mari, mardiya ta dago rai a bace tace “kutmar ubanchan, ni kika mara?
???”
“An marekin, shegiya yar matsiyata, ke kina yar aiki har kin isa kice na jira a kofa ki shiga ki tambayo izinin shugowata, kamar baki san koni wacece ba??”
Mardiya ta daga hannu kenan zata rama anty laila dake zaune parlor tace
“Mardiya waye ne?”
“Wannan mayar ce”
Maya ji tayi kamar ta sake watsa mata mari, yar aikin nan ce ke mata haka?
Wani irin kallo mardiya ta mata kafin ta yi kwafa ta barta tsaye, ta kara gaba abunta.
Duk sanda maya zata shigo bata taba mata haka ba sai yanxu hasalima yan
a shugowa suke rufe kofar ko amsa gaisuwar su bata yi, yau ko mutunci gaisuwar ma bata samu ba kowa a wuya yake da ita.
Rai a bace ta tako zuwa parlorn tana huci takaici babu ko sallama ta karaso anty laila na zaune kan kujera ta dora kafarta datasha lall
e kan kujerar.
Kamar dai yanda ta saba idan ta shigo ta tadda anty laila kan kujera zama take gefenta haka wannan karan ma ba tare da wani tunani ba ta nemi zama anty laila ta dakatar da ita.
“Ke baki iya sallama ba? Sannan kuma saboda rashin kunya kin s
hugo min parlor kai tsaye zaki zauna kan kujera? Waya baki izinin yin haka?”
Mamaki baisa maya ta karasa zama ba tunda ta dan duka zata zauna din, nuni anty laila ta mata da carpet tace “zauna nan bana son rawar kai,ki tsaya a matsayinki, ki fadi abunda y
a kawoki”
Maya was in total shock, shock din face impression dinta ya gaza boyuwa.
“Kin tsaya kin kafeni da idanu?”
Cikin tsiwa maya tace “nafi karfin na zauna akan carpet wallahi”
“Toh sannu yar masu gida, futsararriya”
Mamakin da maya ke ciki bazai
misaltu ba, kallon anty lailan kawai take da mamaki,
“Anty laila nice fa? Maya?” Maya ta fada jiki a mace kamar zatayi kuka dan takaici.
“Wannan wani irin maganan banza ne? Bansan ke din bace? Rashin kunya zakimin?Idan bakisan matsayinki ba yanxu ki sani
, karki sake shugo min part babu sallama ko kuma kai tsaye haka sannan kiyi tunanin zama inda kikaga dama,”
Tana kaiwa nan ta dubi hanyar kitchen ta kwalama mardiya kira tana zuwa tace “inta futa maza ki rufen kofa” tana kaiwa nan ta tashi ta wuce sama.
Maya batasan sanda wani siririn hawaye ya soma sauko mata ba don takaici, lallai yau to her face taga wani abu da ake kira sa wulaqanci karara, wato matsayinta baikai ta zauna kan kunera ba saboda yanxu ita ba yar gidan bace, saita tuna yanda anty laila ke
mata a baya, har tana fatan dama itace maminta yanda take barinta tayi abunda taga dama, yanxu kuwa saboda ba itace asalin yar masu gidan ba sabeeha ce shi kenan yanxu ta fara ganin wulaqanci, “sabeehaa sabeehaa sabeehaaa kai ta tsani sabeeha tsana mafi t
sanani.
Mardiya ta kalleta irin kallon wulaqancin nan tace “malama zan rufe kofa,”
Wani irin kallo maya ta mata wanda yasa mardiyya cewa “karki sake min kallon banza wallahi, bawai kinfi karfina bane ko kin fini daraja a gidan nan, duk tushe daya ne mtew
w” tana kaiwa nan tayi slamming kofar akan fuskar mayar da shock bai barta ba, yau yar aiki ta zageta, sannan ta nuna mata cewa duk daya suke tunda itama yar aiki ce, duk wannan abun baisa tayi nadama ba ko kuka tayi learning lesson dinta na wulaqanta sabe
eha datayi, babu cin fuska da gori da batayi mata ba, yan aikin gidan kuwa babu wanda bata zaga ba ta uwa ta uba, ashe ashe itama dai ba asalin kirki ne da ita ba, dole ta nema ma kanta mafita dole ne wannan.
MATAR TAJ (destined with you)
Writte
n by
Queenmarh
Book2
PAID
Chapter 111
Kamar ana jan kafarta tana goge hawayen fuskarta hannunta na rawa tsabar bacin rai haka ta nufi part din taj, da wani kuduri aranta, as’usual part din na bude ta samu shiga kai tsaye ta wuce si
tting room sannan ta haura sama, babu wani darr aranta.
Tana hawa saman tayi knocking daya biyu daga ciki ya amsa da come in don a tunaninshi ko me gyaran part dince.
Kai tsaye ta bude babu ko sallama, ya gama shirinshi kenan zai futa ya zauna bakin gado
yana kokarin saka wrist watch dinshi akayi knocking din, bayan ya bada izinin shigowa baima dago yaga ko wayene ba yaji muryar maya.
“Inason magana dakai…
Ahankali ya dago da mamaki ya ganta tsaye idanunta sunyi jaa sosai, jikinta har wani rawa rawa yak
e,
maida hankalinshi yayi ga abunda yakeyi yayi kamar baisan da ruwan mutun a wajen ba, ganin haka yasa ta soma takowa “stop right there”
Ya dakatar da ita, “fadin abunda ke tafe dake daga nan”
Wani abu taji ya tokare mata a maqogaro, shima zai nuna ma
ta iyakarta kenan? A harzuka ta soma takowa tana danne abunda ke taso mata ta hana kanta hawaye a daidai lokacin shi kuma ya miqe tsaye, ya mata wani irin kallo dayasa tasha jinin jikinta.
Abunda taso yi ta kasa kawai ta sauke idanunta kasa hawaye ya som
a sauko mata, yanajin tana sheshekar kuka nan yabita da kallo da mamaki.
“Dan allah karka gujeni, idan duk kowa ya nuna baya sona karka qi ni, wallahi ina sonka uncle taj, inasonka sosai fiye da raina, ka taimakeni ka aureni,”
Ta karashe tana kallonshi,
shima kallon nata yake sai yaji wani dan tausayinta ya ratsa shi, da ranshi harya soma baci sai kuma data fara kuka yaji bacin ran ya tafi, bayason ganin mace na kuka ko kadan, a sanyaye ya kauda idanunshi sannan yace “stop…crying, clean those”
Ya fada ya
na mata nuni da fuskanta, wani irin sanyi taji aranta, plan dinta is working,
“meke damunki? Who hate you?” Ya tambayeta a natse.
Daga yanda yake magana ta gane cewa ya danji wani abu game da kuka nata, so shes going to play a victim game, don ya tausaya
mata.
Matsar kwalla ta sakeyi tare da sunkuyar da kanta, sannan tace
“Kowa, duk basa sona sunfi son wannan munafukar, ta rabani da kowa, sanadiyarta kowa baya sona”
Tunda ta soma maganar sabeeha yaji bacin ran nashi ya dawo sabo haryama wanda ya fara j
i data shugo mashi daki babu sallama, babu gaisuwa kai tsaye.
Wato daga yanda take magana ya hango jealousy, da bakin ciki a cikin magan ganun nata, harma da rashin kunya a ciki, don harda anne ta sako a maganar tana fadi mashi yanda dama chan ba sonta ta
ke ba, banda rashin hankali irin nata bai kamata tace sabeeha ruined her life ba ta rabata da kowa hasalima sanadiyar chanzasu da akayi ne yasa sabeehar ta shiga rayuwa mai kunci, rayuwarta ta gaza inganta saboda rabata da akayi da asalin iyayenta ita kuma
akayi replacing dinta a matsayin sabeehar.
Kwata kwata bata dago taga yanayin da yake ciki ba take ta zuba, trying to make him pity her, nanko ta tabo inda bai kamata taje wajen ba.
“Youre ungrateful” ya fada rai a bace sai a
Lokacin tayi saurin dagowa
ta kalleshi saida gabanta ya fadi kuwa, ranshi a bace ya cigaba “are you trying to blame her for what your biological mother did? Did fatima hate you for being on her seat this whole time, did you even know what she had to go thru????” Ya sake jefo mata t
ambaya trying to add sense to her brain don yaga yarinta ma yana daya daga cikin abunda ke damunta bayan she’s being brutally selfish.
“Instead of you to be grateful?”
Bakinta ta soma motsawa tana hawaye, “yess because saboda ita na rasa komai, kowa fati
ma fatima fatimaa…i hate her, i wish ta dade da mutuwaaaa…”
nuni ya mata da kofa, baice komai ba tsabar bacin rai amma tasan abunda yake nufi, jikinta na rawa ta kalleshi tana tattara courage din yi mashi magana a wannan yanayin “whys everyone siding on h
er?? Meysa ka tsaneni Uncle taj?”
Bai sake kallonta ba ya nufi hanyar futa tayi saurin shan gabansa, without any second thought ta soma kokarin zare veil din dake kanta sannan ta soma kwance igiyar rigarta, a tsorace take dashi amma wani confidence takeji
kawai nayin abunda yazo ranta.
“Wallahi zan iya baka komai, har kaina zan iya sallama maka,…” ta karashe tana kokarin sauke rigar tata kasa taji saukan mari tasss akan kuncinta ranshi a mugun mugun bace, babu abunda ya tsana kamar yaga loose mace, musam
man wannan yarinya qanqanuwa.
Ay baisan futsararriya bace ta karashe sai yanxu, bai iya dukan mace ba ammada da akwai belt a jikinshi babu abunda zai hanashi zaneta, a very young girl like her har tana iya yin tunanin sakin jikinta to a man? For the fac
t yana matsayin uncle dinta, ranshi inyayi dubu ya baci sosai ba kadan ba hannunshi har karkarwa yake ya mata nuni da yatsa “before i count to 3, if i dare see any sights of you here, you’ll regret it”
Ay ko marin daya mata yasata gama shiga hayyacinta, t
ayi saurin maida rigar jikinta a furgice ta futa tana kuka.
He feel so disgusted, ranshi yayi mugun mugun baci, irin yara kamar wannnan abun tsoro ne musamman a cikin ahali babba kamar haka, she can go to any extent don ta samu abunda takeso, kuma ko kuny
ar idanunsa bataji ba, bayason yayi making abun as an issue but zai iya zaneta sosai akan wannan don ya ladab tata.
A furgice ta futo ta wuce part dinsu, tana shigowa as usual ta tadda basira na goge goge, tabi takan ruwan mopping din ya bare rai a bace t
a wuce sama, basira ta kalleta ta bita da harara “mai baqin hali, mteww dama ance abunda ka shuka shi zaka girba, waye zai taba tunanin kece yar hadiza, kai allah ya wadai, itako sabeeha babu ruwanta halinsu daya da hajiya ashe shiyasa ma babu ruwanta sabo
da itace yarta ta asali bake ba yar masu da fadin rqi da izgilanci,mtewww”
Haka nan ta dingi kwashe ruwan don harya jiqa carpt din walkway din wajen.
Maya na shiga daki ta soma fashe fashen data saba tana hawaye, gana daya turartukanta dake kan dresser s
aida ta fashesu duka har hannunta na fidda jini, kamar wadda ta haukace haka ta miqe ta soma watso kayan wardrobe dinta hartayi nasarar daukan wani box irin na jewelry box haka dake boye a wajen, ta bude shi, take kwayoyintabda kayan mayenta suka bayyana a
ciki, ba tare da wani tunani ba ta fiddosu ta aje bakin gado, ta fara ambulawa cikinta, kan kace me kawai tayi over dosing kanta sosai, muyagun kwayoyi ne da shansu keda hadari sosai don har mental asylum yana iya kai mutun idan ya zama addictive kuma ya
fara taba kwakwal.
Tana layi ta zaro wata allura ta dura a cikin syringe sannan ta chaka ma kanta tana gamaqa ta soma sauke ajiyar zuciya ahankali hankali chan kuma ta bange dipp.
Acahn wajen taj kuwa bayan futarta haka ya futo ranshi a bace zuwa main
house yana shiga ya wuce part din nanna, suka gaisa, ta tambayi jikinsa yace mata da sauki, ya futo ya wuce part din anne don achan zai karya, yana shiga ya zauna, fadila ma na part din annen suka gaisa dashi tasa laila karama tayi serving dinshi abunci ya
ci anan parlor.
Yanaci suna hira, shida anne sama sama,har ta tambayehsi jikinsa don nannna tace shima zazzabi ya hanashi zuwa yin breakfast yace mata da sauki, fadila tayi murmushi tace “abun naku kamar hadin baki kaida fatima, itama haka ta tashi da zaz
Abi saida aka hada mata allurai ma allah dai ya kra sauqi”
Yayi shiru baice komai ba, yana tuna abunda ya faru dasu jiya da daddare, ya gama deciding situation dinsu shida ita, daman shima bawai so yake asan da aure a taakaninau ba don idan nanna tasan ir
in rayuwar dayayi a baya she will be heart broken, bama ita kadai ba.
And har yanxu yana jin guilt din abunda yayi ma sabeehar da yanda ya qulaqantata a chan saudiyar aftwr all he has done for her.
Yana cikin wannan tunanin anne tace “ inka gama ga shiga
ka dubata, nasan ta farka yanxu ko?”
Fadila ta dubi laila tace “yanxu kika fito daga dakinta ta farka kuwa?”
“Ah ah mami tana tare da mummy ma sanda na fito amma bari na sake dubawa”ta amsa sannan ta futa daga dakin.
Bayan ya gama cin abunci ya fito d
aga part din anne har zai sauka kasa kuma ya dakata, yana mai duban bangaren sabeehar, samun kanshi yayi da shiga part din da sallama, sabeeha da farkawanta kenan laila na zaune gefenta while bahijja ta koma part dinta don ta mata corn chicken soup da zata
dan sha.
Tana jin sallamanshi gabanta ya wani irin fadi dam, saiga kamshinsa ya biyo baya wanda laila tunda ya shugo dazu taji kamar kamshin sa taji a dakin sabeeha,ba ita kadai bama hatta bahijjar saida taji wannan kamshin.
“Bismillah uncle taj” laila
ta fada ahankali, sabewha kuma ta kauda kanta zuwa gefe,
Zama yayi wajen cute resting chair setting din da akayi a gefe yana fuskantarsu.
Gaba daya wajen saiya zama awkward, laila ta dubi sabeeha data hade ranta tayi kamar batasan da zuwanshi ba kasa ka
sa tace “madam yadai? Yazo dubaki”
Yi tayi kamar batajita ba wanda duk hakan akan idanunshi akayi, ya dubi laila da itama a lokacin ta dago karaf suka hada idanu, wani irin signaling yayi mata da ita kanta batasan yanda akayi ta gane me yake nufi ba wanda
yasa ta tashi ta zura flats dinta sannan ta futa, sabeeha har zata mata magana sai kuma tayi shuru kawai wajen ya dauki silence.
Sun dauka wajen minti biyar a haka baice qala ba haka zalika bata