Showing 162001 words to 165000 words out of 338813 words
kiyi kokari kina gujema stress din”
“Insha Allah.. ya kafan ki?”
“Kufa kuke wani damuwa da kafa, wallahi garau nakejinta yanxu, abun kunya ni ban samu hawan jini ba da shekaruna gashi ke saboda tunani zaki jefa kanki a halaka”
Girgiza kai kawai nanna t
ayi don yayar tata tasanta ciki dabai, duk falewar da zatayi bazata taba yarda ba don ta san duk wani condition da take ciki.
“Toh anne za a rage tunanin,”
Mumrushi tayi mata sannan sukayi sallama anne ta fita.
Wata nayyayyiyar ajiyar zuciya nanna ta sa
uke,idanunta sunyi jaa sosai take taji kirjinta na mata wani irin nauyi, tayi hanzarin daukan pills dinta ta sha sannan ta kwanta.
Daki anne ta koma ana mata tausa hamad ya shugo suka gaisa, wuraren past 7 don anan idar da sallah ya shugo, hira suka danyi
jefi jefi ya danci tuwon da aka kawo ma anne sannan ya mata sallama kan zai dawo anjima.
Yana sauka kasan yaga yan aikin gidan nata faman shirya dinner a dining duk bai buqata saiyaje ya diba.
Sai a lokacin sabeeha ta fado mashi yasan by this time an da
ukota, amma rashin ganinta da baiyi ba dazu sai yaji babu dadi gaba daya, gashi bazai iya sqwa a kirata ba, toh akirata yace mata mene? Saboda mene? A wani dalili kenan? Saurin watsar da zancen yayi ya wuce gida.
Yana parking a part dinsu ya shiga daga ci
ki.
Kai masha allah, gaskia anty fadila badai gayu ba, itama gidanta mansion ne mai zaman kanshi baikai nasu anne ba don shine family house dinsu amma shima badai girma ba gari guda.
Ko’ina yasha adon gold and off white, parlor ga wani katin frame na hot
on su su hudu, laila hamad then babansu sai mamansu.
Daidai zai shugo yaci karo da laila data debo abunci zata wuce sama, hartasa yar aikinsu ta kawo mata tanajin sallamarshi ta karbe karyayi mata fada, irin waennan kananun abubuwan kamar irinsu gyaran ga
donta da gyaran wardrops dinta ita keyi, ba’ayarda yar aiki tayi ba saidai wanke toilets da shara, saboda kar shagwabewar tayi yawa, sometimes ma itake girki a gidan, dakin mamansu kuwa itake gyarashi tass.
Gaskia an basu tarbiyya kam mai kyau, babu raina
na gaba musamman na kasa dasu.
“Hello ya hamad!”
“The next time kika kara cemin hello saina mareki, baki iya gaisuwa bane”
“Sorry ina wuni how was your day”
“Alhamdulillah ya amsa ta” ta turo baki tare na bin hanyar stairs ya dakatar da ita.
“Kinje t
a koya maki?” Ya jefa mata tambaya daman yanason yaji ko yaushe sabeehan ta dawo.
Damn gabanta ya bada, tsakani da allah dazun nan ciwon mara ya riketa sosai tunda ta kwanta take barci bata tashi ba sai yanxu shaf ta mance da batun driver daya kamata ta f
ada ma anne.
Ganin yanda tayi tsuru tsuru yasan bata da gaskia, “are you dumb?”
“Innalillahi wallahil azeem yaya ciwon mara nake dazu sai yanxu na iya tashi”
“Is that the question that i asked you?”
Ganin ta sunkuyar dakai yasa shi zaro ido don sai yan
xu ya fuskanci inda ta dosa, “what!!!!!! Bakida hankali???? “
“Yaya wallahi mantawa nayi”
Ko sauraron baiba don kamar ya kwada mata mari haka ykeji ya fuce daga gidan a fusace kamar zai tashi, yayi hanzarin shiga motarshi ya juya akalar motar.
Gudu yake
sosai gabanshi na faduwa, yanajin kamar yayima laila dan banzan duka, ya za’aui ta manta and ya bata strict instructions akan ta fadama anne asa cikin drivers available one yaje ya daukota, gaba daya saiya fara jin wani irin rashin dadi da tausayi sabeeha
r yanxu haka shes stranded batasan ya zatayi ba innalillahi wa inna ilaihi rajiun.
Yana isowa school din ya wuce direct wajen department dinsu hankali a tashe, duban duniya yayi mata bai ganta ba, gashi duk securities daya tambaya sai suce basu ganta ba d
on ana yi shifting na rana sun tafi.
Haka nan ya zagaye school dinnan gaba daya da securities ana nemanta, har akayi sallar isha’i, cikin ikon allah wani tunani yazo masa ya nufi masallacin mata, bai shiga ba yasa daya daga cikin securities mata suka shig
a ko za a ganta.
Tana shiga saigata kuw sun fito tare, tana daga kwance chan sakon masallaci ta jigata sosai ga gajiya ga yunwa, sallah kawai takeyi ta koma kwance.
Tana ganin hamad ta sunkuyar da kanta feeling so sad, wallahi yarinyar nan ba karamin kas
he mashi jiki take ba haka kawai yake jin tausayinta bayason ganin ta cikin kunci ko kdan, yana hango tsananin damuwa da rashin farin ciki cikin idanunta, kamar someone that is lonely and longing for something.
“Dauko littafanki”
Komawa tayi jiki a mace
ta dauko ta fito suka wuce taba biye dashi a baya har suka iso mota ya bude mata seat din baya ta shiga ta zauna ya rufe
Kunna motar yayi ya saka ac kadan sannan yayi reversing ya futa daga school din.
Shi shuru ita shuru aka rasa wanda zaiyi magana.
S
hi wani irin rashin dadi yakeji, how can he be so careless, dayayi tunanin kiranta yayi confirming kota dawo da duk haka bata kasance ba.
“Kayi hakuri ya hamad, ka dawo saboda ni, wallahi ba laifina bane, bansan kazo da wuri ba dazun da bazan bata maka l
okaci ba,”ta fada cikin sanyi, zuciyar sa kam ta karaya dajin furucinta sannan ga abunda ya biyo baya da bai fuskanta ba.
“Why are you sorry? Daman ba extra lectures kika tsaya yi ba?”
Nanata abun tayi a ranta batason cewa komai yanxu data fuskanci kamar
akwai dan misunderstanding.
Ganin taqi cewa komai yasashi cewa
“Now tell me meysa kika bata min lokacin”
“Daman class rep dinmu ne yace min lecturer dinmu na nemana shine naje, bayan naje kuma yace min ba nemana yake ba saidai ko wani lecturer ne bash
i ba,“
“And sai kuma akayi yaya? Ya nemi karin bayani.
“Shine na sauko kasan don banga rep dinmu ba kamar ya tafi, anan ne naji wajen wani security cewa kazo kun jirani harkun tafi, kayi hkuri hakan bazata kara faruwa ba”
Shru yayi bayan ya gama sauraro
nta tass, a cikin maganganun nata ya fuskanci abubuwa biyu, na daya babu wani extra class datace ma laila da maya zasuyi, secondly kuma batasan cewa shima kanshi da wannan wrong info din yabi ba.
“Bakiyi laifi ba, but next time ki dunga kirana idan abu ya
faru dake, kamar yanxu this is very wrong for a lady ki zauna, and im sorry bansan
cewa driver bai biyo sahunki ba yazo daukanki i should have called you naji ko an maidoki”
“Insha allah”
Suna karasowa gida yayi parking ta wuce bayan sunyi sallama sanna
n ya wuce part dinsu.
Yana parking ya wuce ciki dirwct zuwa dakin laila yana shiga yayi knocking tana zaune tayi zuru avun tausayi don tasan yau zai sauke mata, kuma harga allah bata kyauta how can she forget this.
Yana shugow ata moqe tsaye kamar zatayi
kuka “yaya don girman allah kayi hkuri wallahil azeem banqi fada ba da gangan”
Tass ya kwashe ta da mari, “meysa kikamin karyan extra class da kikace zasuyi?”
“Answer me” ya daka mata tsawa ganin tayi shuru, ta fara daburdabur, “wallahi ban maka karya b
a, meysa zan maka karya yaya, tare mukayi statistics class da ita kuma a gabana lecturer yace zaiyi extra class”
“Ita da bakinki tace maki zata tsaya yi?”
“Ah ah,”
“Then how did you conclude zatayi?”
“To ay naji maya tace zatayi extra class ne sainayi
tunanin class din zatayi”
Saida ta fadi hakan ya gane inda gaba daya akayi misleading dinsu, wannan kafurar yarinyar futsararriyar ce, kuma saiya koya mata hankali.
“The next time kika kara bani wrong information saina tattakaki”
Hamad nada sauqin kai s
osai amma in aka taboshi bashida sauqi.
Yana kaiwa nan ya fuce ya barta da kama kunci, anty fadila data fito daga part dinsu ita da oga don su ne a sama da maya kasan is for hamad tana ganin yanda ya futa tasan sunyi rikici kenan da qanwar tasa.
Bedroom
din laila ta shiga ta taddata tana kuka shabe shabe.
“Menene kuma me kika masa? Nasan kece mara gaskia”
Cikin shesheka tace “mami wallahi ba laifina bane, kinga maya ce tace wai sabeeha zatayi extra class shine nayi tunanin class din zatayi ashe bashi za
tayi ba shine shine muka tafi muka barta a school, toh dazun daya dawo damu yace na fada ma anne asa driver yakaita ni kuma bayan nasha maganin ciwon mara yasa ni barci na manta gabadaya shine yazo yanxu..”
Tun kafin takai aya fadila tace “innalillahi wa
inna ilaihi rajiun karkice kin yarinyar nan kuka vari a makaranta tun da yamma har zuwa yanxu, amma bakida hanklai, are you mad?what sorr of nonsense is this? Eh”
Haka ta dunga balbaleta itama hankalinta ya tashi, abun babu dadi.
Sabeeha na shiga part
dinsu ta tadda dakin kacha kacha, daman ita ke gyara wa duk sanda ta dawo daga school to yau ko zanin gado hadiza bata daga ba.
Wata iriyar yunwa takeji wannan yasa ta fuce zuwa kitchen ko zata samu wani abun da zata kaima cikinta.
Tana shugowa taci karo
dasu rabi da hadiza a kitchen din anata faman gyare gyaren kwanuka na dinner da akayi.
Gaishesu sabeeha tayi sai a lokacin hadiza ta tuna da ita, batace mata komai ba sai binta take da ido tana girgiza kai.
Ganin irin kallon da hadiza ke mata na tuhuma
yasa taji yunwar ma ta tafi gaba daya ta juya zata cire kayan jikinta dan tazo ayi aikin da ita daidai nan sukayi karo da maya data sauko kamar zata tashi sama, a kufule saboda yanda hamad yazo saura kiris ya mareta akan wannan yar wanke wanken.
Wani irin
turata baya maya tayi kamar zata fadi ta daidaita tsayuwarta, “wallahil azeem da ya hamad ya mareni saboda ke wulaqantacciya yau da sainaga jini a bakinki, haka kawai saboda kin tafi yawanki na iskanci sai yazo ya balbaleni? Banza barauniya, asarraru, yar
wanke wanke, gaba dayanku wahalace ta maku yawa tsabar Samun wajen har kin isa kisa yazo kamar zai dukeni? Ke a wa? Who’s your father? Ke yar uban wacece? Wataqila ma wajenshi kika gado sata”
Rabi dataga abun yayi yawa ne yasa tace “haba maya, me ta ma
ki? Ya zaki mata kazafin sata?”
Hadiza na daga tsaye tana wanke wankenta ko tak bata ce ba ranta in yayi dubu yayi mugun baci sosai, saida taji anyi batun sata ne yasa ta juyo ta kalli sabeeha, maya dataga haka tace, “ki daina yi mata wani kallo, inta s
ato ke zata kawowa ay ba wani ba mteww rubbish”
Tana fadin haka ta juya tabar wajen hadiza ta fizgi hannun sabeeha zuwa backyard, ta kama hannunta sosai kamar zata ballata tace “dan abu kaza kaza…..”ta kundumo mata ashariya tace “koda na tura ki chan wata
kasa daman sata kika koyo??? Eh????”
Tana shekar kuka tace “wallahi mama ban taba yi ba, wallahi da gaske nake”
“Zata maki karya ne???? Wallahi bazaki Jawo min magana ba, gwraa na tattaraki gaba daya ki koma chan wajen dangin ubanki lafia”
Tana kaiwa n
an ta bar wajen kamar zata tashi sama.
Tana barin wajen sabeeha ta duka anan dakalin wajen ta saka kanta tsakanin cinyoyinta sai hawaye, kuka take sosai bakajin sautin ma sosai sai kadan kadan.
Jin alamun an dafata ne yasa tayi saurin dagowa ta miqe tsay
e, nanna ta kalleta ganin tana saurin goge hawayen dake fuskarta kar a gani.
Saukowanta kenan kasa, daman tana zama ne a balcony dinta dake sama saiya kasance yana daga wajen backyard din, kaf conversation dinsu taji, wannan yasa ta sauko.
“Ina wuni Haji
ya akwai abunda kike buqata”
Kallon fuskanta nanna tayi hawayen sun kasa tsayawa, ba karamin tausayinta taji ba ga muryanta ya soma dishewa, irin wannan ba tuhumar mutun akeba zama ake dashi a tambayesa akan komai bawai a yanke mar hukunci ba,
Hannu nan
na tasa ta share mata hawayen a maimakon ta daina sai kawai ta fashe da hawayen sosai, nanna batasan lokacin data rungumeta ba ta soma padding bayanta, “shiii, ya isa haka”
Tana fadin haka ta zarota daga jikinta sannan tace “share hawayen”
Ta gogesu tass
sannan tace “now tell me
Meya faru?meysa akace kinyi sata?
Kujerun dake wajen nanna taja masu suka zauna tana fuskantar sabeeha.
“Wallahi hajiya banyi ba, sharri ne,”
“Zan yarda dake idan kika fada min meya faru”
Ajiyar zuciya sabeeha ta sauke tana
jin wani irin sanyi aranta tace”Daman dazu ne a school muna zaune ana lectures sai kawai maya tace anyi mata sata, tayi reporting to lecturer din saiyace duk wanda ya dauka ya futo dashi ko yasa a shigarda report, duk sai naga suna kallona bansan meya faru
ba wallahi, sai wata daga cikin students tace wai a duba jakana,im the suspect,nace masu ni banida jaka ma don littafaina ma a hannu nake rikesu,sai lecturer yace na fito zuwa stage zaiyi questioning dina, wallahi hajiya ina tashi bansan ta inda agogo yaf
ito ba sai kawai suka
fara ihu wai gashi nan nice na dauka, shine aka kira securities, sukazo za akaini disciplinary, sai wata sabuwar student ta dakatar dasu ta fidda same watch din tace ay wanda ya fito a jikina ita ta bani na aje mata ga nasu nan a waje
nta lokacin data shugo class ta tsinta, toh kinji yanda akayi”
“Toh ita din da gaske ta baki ki ake mata?”
“Wallahi ah ah, banka santa ba wallahi ranar na fara ganinta a class din”
“She saved you?
Da mamaki sabeeha ke kallonta “yes she saved you, duk
yanda akayi na hannunta shine nata na asali wanchan dayan kuma its possible ko wani ne yaso yayi maki sharri, you should be thankful to her”
Sabeeha tayi mamakin maganar nanna sosai don sai yanxu ta fuskanci hakan, “sunanki fatima ko?”
Ta girgiza mata ka
i alamun eh, “na yarda bake kika dauka ba kinji, sannan next time ki dunga lura da mutanen dake kusa dake, wanda ke kusa dakai shike da damar cutar dakai”
“Tohm hajiya nagode sosai”
“Karki sake yin kuka kinji ko? Tunda bakiyi ba me zaisa kiyi kuka, now g
ive me a big smile”
Take kuwa ta sauke mata murmuhshin ta mai kyan gaske, nanna ta dunga kallon idanunta tana tunanin ina ta taba ganin ta ko me kama da ita.
Kallonta da nanna keyi yasa itama ta kura mata idanu tana tunanin ina ta taba ganin ta, sai kawa
i tayi zumbur ta miqe tsaye “laa hajiya kece wallhi kece, kece wadda kika taba bani kudi da yawa dana baki jakarki da kika yadda a masallaci”
Tunani nanna ta farayi yaushe event haka ya faru, “hajiya wallahi kece, wajen masallacin gidan man salbas dake ka
n Hanyar wajen gari? Shekara biyu da suka wuce? Kika mance purse dinki a masallaci harna biyoki da jakar lokacin zaki wuce”
Kama baki nanna tayi set of hakoranta suka fito rass tace “allahu akbar kece wannan yarinyar? Yar amana? Kece mai robar kwai ko?”
“Eh nice hajiya ni ce wallahi”
“Allah sarki, wani ikon allah kenan?”
Dariya sabeeha tayi ashe har hannunta ta kama tsabar excitement, don har yau batajin zata taba manta nanna, saboda matar lokaci guda ta shiga ranta,
“Wallahi Har kika yadda wani dan ho
tonki ina dashi ma na ajiye shi cikin kayana kafin na tafi saudi”
“Saudi? Meya kaiki saudi?”
Shuru sabeeha tayi ta dan dakata batason tuna abunda ya faru a baya kwata kwata,
“Aikatau naje yi achan”
For few seconds babu wanda ya sake magana, yanayin nan
na ya sauya gaba daya, “allah sarki yanxu na kara yarda bazaki taba yima kowa sata ba saboda kinada amana, dare yayi yanxu jeki kwanta”
“Nagode sosai hajiya saida safe”
Sukayi sallama nanna ta bita da kallo.
Hilton….
Misalin karfe tara da rabi daid
aiya shigo, dakin bayan sunyi sallama da salim daya saukeshi, workers din wajen suka biyoshi da shopping dayayi ma kanshi na abubuwan da zai buqata na zamn da zaiyi.
Fuskanshi na kalla, ya shanza hair cut kuma ya amshe sa sosai don yayi kyauba kadan ba, g
a gashin bakinsa daketa fama kyalli yasha gyara.
Agogon hannunshi ya zame a je gefe sannan ya shiga ya watsa ruwa mai zafin gaske sannan yayi ordern brunch na dare aka kawo mashi yaci kadan saboda tashin zuciya dayakeji sama sama.
Nan yasa akazo aka kwas
hi abunci don bai wani ci na kirki ba.
Yana zaune laptop dinshi nakan cinyanshi yana aiki da yan dube dube call ya shugo mashi, kallon screen dinshi nayi to my surprise kawai naga wani hoton sabiha da fuskatan yayi zooming sosai, tayi murmushi, skin dinta
kamar madara ga dan v lips dinta yayi wani irin jaa gashi idanunta sun fito zara zara, ya dade yana kallon wayar bawai mai kiran yake kallo ba sai fuskarta daya kasa dalilin saka hotonta da yayi akan screen dinshi, ya dade sosai har call din ya katse kafi
n wani ya shugo ya dauka yasa speaker.
“Hello sir!!”
“Yes saalem?”
“How are you feeling now sir? Ko nazo muje asibiti?”
“No its just minor headache, will feel much better by tomorrow”
“Okay sir please let me know idan kana buqatar wani abun at anytime
”
“Thank saalem” taj ya amsa shi don haka yake kiranshi.
Yana kashe wayar ya shiga messages din da merk ya tura mashi, yana dubawa, reports ne ya turura mashi na avubuwan da suka faru tsakanin jiya da yau.
Dayaga labaran dake circulating akan hidaya s
ai yaji zuciyar na karaya, wallahi wholeheartedly ya dauketa a matsayin daya bata kafin tayi watsi dashi tayi disappointing dinshi, kuma yana tausayin barad da jamid, albarkacinsu ne kawai zaisa bazai saka hannunshi ba cikin almarin don idan yayi haka she
will be behind bars forever, yanxu ana trail ne