Showing 288001 words to 291000 words out of 338813 words

Chapter 97 - MATAR TAJ COMPLETE

“what a happy family.. kodai mu koma ne mu barku ku cigaba da moment dinku”

Dariya duka sukayi gaba dayansu, kowa yana kallonsu, bakin sabeeha ya kasa rufuwa, data kalli bahijja saita kalli majeed.

Gaggaisawa s

ukayi gaba dayansu, aka sha hira bahijja tace itafa a sallameta su koma gida taji sauqi, fadila nata mata tsiya, hardasu cewa wai ay sabeeha tafi kama da dangin ubanta, saboda launin fatarta.

Laila ko tana samun dama ta kamo sabeeha ta rungumeta sannan ta

ce “welcome to the family fatima, im so glad we’re cousins”

Murmushi sabeeha ta mata suka dan taba hira, hamad ma ya shiga cikinsu aka sha hira.

Bahijja dai yau tasan tayi breakfast na kirki rabonta da abunci tun ranar da taji cewa sabeeha yarta ce ta as

ali wadda hadiza ta mata replacing da diyarta wato maya…sai a yanxu ta tuna da maya.

Sallamar taj ce tasa duk suka maida hankalinsu zuwa ga kofar, yana shugowa idanunshi ya shiga cikin na sabeeha, samun kanta tayi itama da kallonshi.

“Ah ah ashe kana t

afe kaima” fadila tayi magana,

Dan murmusawa yayi, majeed yace “ay tun dazu yazo, kusan ma a tare muka iso asibitin”

“Good morning..ya mai jiki” taj yayi magana

Bahijja ta amsa, fadila ma ta amsa, laila ta gaishesa haka zalika hamad, sabeeha ma ta dago

ta mashi kallo daya tace “good morning..”

Jiki a mace ya amsa har yana tambayar how shes doing, ta amsa da shes fine..sannan ya samu waje ya zauna yana facing dinta, tana daga zaunen nan tana jin idanunshi akanta.

Bahijja ma ta kasa duake idanunta kan s

abewhar, data kalleta saita yi murmushi, shea the happiest mother on earth, wani irin so take ma sabeeha mara misaltuwa, yanda takeji game da ita daban ne, she will do anything to protect her and love her unconditionally……

After a month!!!!

Alhamdulill

ah alhamudulillah…

Sallamar da akayi ne yasa ta juyo wa da sauri tare da aje duvet din dake hannunta, nima dana rako hamad da paper bags bansan sanda na sakesu ba tsabar mamakin dana shiga, shi kanshi kasa duake idanunshi yayi akanta, tayi wani azababba

n kyau, wato kwanciyar hankali ma wani abu ne mai mahimmaci ga rayuwar dan adam, wallahi in kunga sabeeha bazku taba cewa itace ba duk kyan datayi a saudi bai kai kyan datayi ba yanxu cikin wata guda, don wannan ya qunshi kwanciyar hankali, farin ciki da k

uma natsuwa, ga uwa uba gata ta ko’ina, tayi bul bul abunta fuskanta sai annuri take, sutura ko yanxu saidai sabeeha ta bama sutura baya, mayukan da take amfani dasu so hmm ba a magana, dady ya saya mata dankareriyar wayar da ake yayi, fadila ko ranar daya

ta kashe ta shiga shopping mall tayi mata sayyayyar budurwa, lokaci guda suka chanzata, bahijja ko cewa take arzikinta bashida amfani idan har sabeeha bata amfanu dashi ba, duk wani properties dinta ya koma karkashin sunan sabeeha.

Dakinta ko da aka ware

mata abubuwan da aka saka mata a ciki ba a cewa komai, anan main house ma aka fidda mata part dinta don anne da nannan sunce wajensu zata zauna hakan fa baisa bahijja taqi organizing mata part dinta ba anan bangaren su kusa dana maya.

Dakin nan an zuba d

ukiya kamar me, ko quarter shi maya bata samu ba, duk gatan da sukayi ma maya bai kai ko 10% na wanda akema sabeeha ba don komai suna yinshi ne extra yanda bazatayi lacking komai ba a rayuwa, zasu maye mata gurbin abunda data rasa a baya.

Talking of may

a, bayan dawowar bahijja daga asibiti aka zauna akayi magana, tsakanin majeed da bahijja dasu anne, manya dai kawai suka zauna sukayi magana akanta.

Da aka zauna maganar mayar fadila na maganar a nemi chan dangin maya na chan kauyensu a miqata wajensu,sum

a su san da zamanta tunda bata da uba kuma shegiyar uwar tata tana chan a kulle, sai kuma bahijja tace bazata taba yarda a rabata da mayar ba tunda itama yarta ce, koda kuwa bata haifeta ba koda kuwa sanadiyarta suka rasa yarsu suka reneta a matsayin tasu

she’s still their child, kuma zasu riketa kamar tasu itama.

Fadila dai bataji dadin wannan zance ba don gudun abunda zaije ya biyo baya, jinin hadiza ce fa? Barinta cikinsu abu ne mafi hadari,kuma she expect duk abunda hadiza ta masu bazasu yarda su rike

yarta ba a matsayin tasu.

Duk wani abu daya danganceta ma abun kyama ne kuma abun gudu ne, saidai kawai allah ya rufa asiri.

Amma kuma duba ga yanda mayar tayi sanyi, ta koma wata saliha saliha sai duk kowa ya soma jin tausayinta anne ma tace a bunne mag

anar kawai yanda take tunda babu wanda yasan da cewa ba yarsu bace in banda hadizar da mutanen gidan gaba daya, duniya bata san da zancen ba don haka ya tsaya a haka kawai saidai abun gudu shine idan har aka tashi aurar da mayar, idan anzo buncike.

Amma

kuma duk wani abu da ake mata baza a fasa yinshi ba, kama daga kan karatunta, gatan da ake mata da komai babu abunda zai sauya, laifin uwarta bazai shafeta ba, sun rugada sun karbi kaddarar abunda ya faru, kuma babu wanda zai iya sauya komai tunda ya wuce

.

Shugowar hamad da sallamarsa yasa ta juyo tana kallonsa, fuskanta dauke da murmuahi da kullum cikin yinshi take, tana sanye cikin wani dankararrwn lace, zata iya cewa wannan ce sutura mafi tsada data taba sanyawa a jikinta, tayi bulbul, yarinya ciki

n wata guda ta sauya gaba dayanta, tsabar kwanciyar hankali, da farin ciki da take ciki.

“Ya hamad!!!” Ta kira sunansa firgigi ya dawo hayyacinsa, ya sauke mata wani murmushi mai kyau.

“Ina kwana ya hamad?”

“Lafiya lau my beautiful cousin” baima san ya

fada ba, ta sauke fuskanta tana blushing, wannan ne first time daya fadi hakan, shima baisan yayi subutar baki ba saida ya gama fada.

Paper bags din daya shugo dasu ya aje mata a gefe sannan yace “mami tace a kawo maki,”

Ahankali ta danyi blushing sannan

tace “mami bata gajiya, ace mata na gode allah ya kara arziki mai albarka”

Ya amsa da ameen, “hmm kije mata godiyan da kanki, daman tace kwana biyu baki shigo ba kinyi breakfast??”

“Ah ah” ta amsa shi tana murmusawa

“Let me wait for you ki gama sai Muj

e muyi a kasa” ya fada kai tsaye, ta danyi shuru, sannan ta cigaba da gyaran gadon shi kuma ya zamu waje ya zauna kan wani dan pink couch da akeyi decorating dakin dashi, samanshi irin furr blankies ne a jiki, komai fess fess, ga dakin sai kamshin bakhoor

yake.

Tana gamawa ta tattara paper bags din ta aje su closet sannan ta futo, ya miqe tsaye, hannunshi ya zuwa cikin aljihunsa ya zaro abu daga ciki sannan ya dubeta yace “can i see you palm”

Dan murmushi tayi surprisingly sannan ta bude mashi palm dinta

ya sauke mata wata yar sarka mi kyan gaske jikin pendant din sarkar akwai letter F a jiki fatima kenan, sannan ga wani dan diamond stone pink a tsakiya.

Tana ganin sarkar ta bude baki zatayi magana yace “don’t thank me, its a gift from me”

Shuru ta dany

i wani irin dadi na dabaibayeta, tun safe kowa ke gifting dinta da abubuwa ta rasa dalili, koda tajw gaida anne da safe haka ta bata wani zobe har tana bata tarihinshi, tun tana budurwa babanta ya saya mata shi, irin customize unique gemstone ne made of em

erald and sapphire akayi zobe dashi, wane diamond wane gold, value dinshi ba karami bane don arziki ne mai zaman kanshi.

Daman bata samu wanda ya chancahnci yayi inheriting dinshi ba tun daga kan yayanta sai yanxu, zuciyarta ta aminta da babu wanda is mor

e valuable da zaiyi inheriting sai sabeehar.

Haka nanna ma ta gwangwajeta da gifts da batama bude wasu ba, don basa gajiya da saya mata abubuwa, set of abayas ne, gadget ne, kai komai ma babu abunda ta nema ta rasa, wasu yan zobunan gold nanna ta saka m

ata a hannunta da kunenta, wai tana mace ya kamata ace tana gayu karta zauna hannunta babu zobe.

Oh wai hannun sabeeha ma kanshi dauke yake abubuwa masu daraja, haka yan chukwi chukwin hannayenta suka fito fess fess cikin zobunan.

Saukowa sukayi ita da

hamad, tana gaba yana biye da ita a baya yana cracking jokes da ita, gaba daya ta gama sakewa da kowa, ta zama wata yar gayu sosai kamar ba ita ba.

Suna karasowa dining din idanunta ya suaka kan na taj, yayi kamar bai gansu ba, tunda suka kusa karasowa y

a kafeta da idanu, haka kawai yaji he’s not confortable yanda ya ganta da hamad tunda ba muharraminta bane, kuma har zuwa lokacin akwai aurenshi akanta.

“Kin sauko yarinyar kirki” nannan tayi magana tana murmushi, dan murmusawa sabeeha tayi tace “eh nanna

n”

Kujera hanad yaja mata zata zauna kenan taj ya dago da idanunshi ya nata wani kallo daya dayasa cikinta rudawa, ta kasa fassara irin kallon gaba dayanshi, don gaba daya yanayinshi ya sauya tunda suka karaso.

Saurin kauda idanunta tayi tana hana kanta

sake hada ido dashi, ta zauna a natse, daidai nan laila tayi sallama hannunta rike da warmers mai aikinsu na biye da ita.

“Good morning nanna..good morning uncle taj..”

“Good morning dear” nannan ta amsa ta taj ko ko dagowa baiba ya wani hade hannayenshi

a kirjinshi, “mami tace a kawoma uncle taj da sabeeha breakfast”

“Ah lallai mami naji dasu fa, wannan exquisite breakfast haka” nanna tayi magana,

Kamshin turaren da sukaji yasa duk suka dago, anne ce ta karaso da yar sandar ta dake taimaka mata wajen

takawa saboda kafa, doctor yace ta dunga yawan saukowa kasa karta lamunci zama a sama tana breakfast, wannan yasa yabxu take saukowa ayi da ita ba kamar da ba da rabi ke kai mata sama.

Rabi dake shige da fuce daa warmers da sabbin yan aiki da aka kawo su

biyu tana karasowa ta fara kwasar gaisuwa sabeeha tayi saurin minkewa zata tayasu rabi tace “ah ah kiyi zamanki hajiya karama…”

“Anty rabi ki daina kirana da hajiya karamar nan ki kirani da sunana pls” ta fada adan shagwabe, duk sauta bawa kowa sha’awa so

cute har wani lumshe ido take tana tabe baki, hamad ya kasa daina kallonta taj ko idanunshi na kan sa, anne ta murmusa tace “toh kin daiji ko rabi? Karki maida min jika tsohuwa, koda yake hajiya tace, ki jira taje ta sauke farali tukunna saiki kirata da h

ajiya da hujja”

Duk aka kyalkyale da dariya, rabi ta soma serving abunci cikin jin dadin yanda ake mata a gidan kamar ba yar aiki ba, kowa sonta yake sosai basa kyamatarta.

kai rabi tayi ma sabeeha murna sosai, tayi murna ba kadan ba, daman fa tun farko

tana ganin yarinyar tasan jinin masu arziki ce, don akwaita da kyau.

Cikin natsuwa kowa keyin breKfast, babu abunda kake ji sai sautin faranti da chokula, suna gamawa rabi ta futo zasu kwashe sabeeha da laila suka tayasu, su anne kuma suka koma sitting ro

om ita da da nanna da taj.

Laila da sabeeha na futowa suka nufi sitting room, suna karasowa sukaga babu kowa a kasan, daidai lokacin hamad yayi ma laila flashing a wayanta tana ganin call din ta dubi sabeeha sannan tace “muje garden”

Sabeeha dai binta ka

wai take suka futo tare, suna karyo corner wajen garden daga nesa kawai sabeeha taga an kawata wajen, suna shiga kuwa gaba daya yan kananun yaran gidan suka soma ihu harma da iyayen, “happy birthday!!!”

Wani irin shock sabeeha ta shiga ta bi kowa da kallo

daya bayan daya, su anne na daga tsaye da nanna a gefenta ga bahijja da majeed suma a tsaye rike da flower bouquet ga hamad a gefensu da fadila, anty mubina ma da ya sameer na daga tsaye anty laila ce kawai bata wajen, su abla na rike da bubbles da ballon

s, taj kuma na daga tsaye shima daga chan gefe ya saka hannayenshi cikin aljihun sa, har zuwa lokacin yanayinsa bai dawo daidai ba.

Laila ce ta jawo hannunta zuwa gabansu ta tsaya tabi ko’ina da kallo yanda aka kawata wajen ga wani decor da akayi daga gef

w an rubuta Happy 23rd birthday Fatima.

Tana kallonsu batasan sanda hawaye ya sauko mata ba, all this while bata san asalin date of birth dinta ba da cikakkun shekarunta don da an tambayeta saidai tace 20.

She can’t express yanda taji a daidai wannan lok

acin saidai hawayen farin cikin kawai.

Bahijja ta tako inda take ta rungumeta sannan ta soma goge mata hawayen fuskanta kafin tace “yau kin cika shekara ashirin da uku a duniya, allah ya yi maki albarka ya kare daga duk wani sharri”

Tana gama fada ta gig

e hawayen datake kokarin boyewa, tunda sabeehar ta karaso wajen taji wani abu ya daketa, dakyar take dannewa kawai.

Bouquet din ta miqa sabeeha ta karba, “don’t cry okay??” Girgiza mata kai sabewha tayi alamun bazatayi ba, kafin ahankali tace “thank you M

aamah na”

“Love you always and forever” bahijja ta fada tana pecking khmatunta,

Majeed ya karaso shima ya rungumeta sosai yana farin ciki yace “happy birthday my princess…”

“Thank you dada” sabeeha ta amsa tana murmushi, haka suka bita daya bayan daya

suna rungumeta, she felt their unconditional love har cikin zuciyarta.

Bahijja ta fidda wata dankararriyar set din sarkar gold da tasha wani mahaukacin package, ta fiddota waje sannan ta saka mata a wuyanta, tana gama saka mata tace “toh muje muga gift di

n daddy ko”

Duk suka dunguma zuwa compound din gidan, suna fitowa maaikatan da sukayi delivering package din suka soma budewa, wani katon kwali ne mai girman gaske suka soma dagawa har sukayi nasarar cireshi gaba daya ballons masu shegen yawa suka zubo, t

ake wata dankareriyar mota ta bayyana, fara tarr irin Porsche dinnan ta mata, shock din data shiga ita kanta ji take kamar ba a dubiyar take ba, daddy ya danqa mata keys din porshe din mai kyan gaske, “this is from daddy, but….saikin gama school zaki fara

tuqawa okay???”

Bai gama magana ba sabeeha ta duqa har kasa ta rasa da wnai baki zata masu magana, she’s speechless,

“Oupps anne fa tace kujerar hajji na jiranki next year insha allah” fadila tayi magana tana murmushi, sabeeha najin tayi sujjada ta godem

a Allah tana kuka, jikinta da bakinta na rawa tace “bansan ta yanda zan gode maku ba, allah yasa da alkairi, ban taba tsammanin zan samu irin wannan gatan ba maamah, dada,.. im bery grateful allah ya saka maku da mafificin alkahiri yaza kufi haka ya daukka

ku ya tsareku,” tana gama fada ta dubi ta dubi sauran dake tsaye sannan ta cigaba “anne..nanna…mami,(fadila) ya hamad dady abla (uncle sameer) anty mubina, cous (laila) sunan da take kiranta yanxu kenan, ya hamad..daidai wajen taj ta dan dakata tana kallo

nshi cikin ido sannan tace “uncle taj… i will like to thank each and every one.. bansan da me zan saka maku ba,“

Yanda take magana saida ta basu tausayi, magana take jikinta na rawa tsabar murna.

“Mami ku bari na daukemu pictures” laila tayi magana aka

tsa tsaya ana picture, kowa har rushing suke wajen daukan picture din da ita, laila ta dubi ya hamad tace “ya hamad ka shiga a maku”

Dan matsawa yayi gefen sabeeha rike da bouquet aka dauke su a hoto, ganin sun danyi nesa da juna yasa laila cewa “ya hama

d ka matsa sosai mana baiyi kyau ba ka tsaya kamar soja”

Tana fadin haka ta dan matsar dashi kusa da sabeehar sosai, anne da nanna suka murmusa, anty fadila ma murmushin tayi kawai.

Ana gamawa laila ta dubi taj dake tsaye ya hade rai shidai bazaka taba

tantance yanayin da yake ciki ba koda yaushe mood dinshi daban ne.

“Uncle taj picturesss”

Kamar bazai motsa ba chan kuka kawai sai ya matso, shi baima tsaya ya bama laila damar cew baiyi kusa da sabeehar ba don baima bada wani gap ba jikinsu na gogan ju

na,

Laila ta soma daukan pictures din, kai wallahi ba karamin matching sukayi ba abunda, sai wanda ya hango hadewarsu.

Ba a gama daukan hoton ba sabeeha ta zaro idanu gabanta na faduwa jin hannunshi a ta wajen ass dinta, cikin sauri ta dubi su bahijja g

anin hankalinsu baya garesu yana ga motar da dady ya saya mata suna dubawa ita kanta lailar bata lura ba don ta baya ya dora hannunshi a wajen, daya tashi ma palm dinshi biyar ya bude yayi ya dora a wajen kamar wanda zaiyi spanking ass dinta.

Juyowan data

yi ta dubeshi in so much shock yasa shima ya kalleta fuskar nan babu annuri kwata kwata, jikinta ya soma rawa cikin sauri ta matsa daga kusa dashi kamshinsa ya biyota.

Gaba daya aka tattara aka koma cikin gida.

Maya dake labe wajen entrance din apartmanı

dinsu duk abunda ya faru akan idanunta, tun bayan futar bahijja daga dakinta don tana tashi da safe bahijja ta shugo dakin ta don taji ya jikinta, don kwana tayi da ciwon kai, gaba daya ta daina sakewa sosai kullum tana daki, har abun ya soma damun bahijj

a,ta nuna mata ta cire komai aranta ta mance da komai amma taqi, tana shigowa dakin as usual yanda ta saba duk zagayowar shekara she will be the first da zatayi wishing mayar tare da mata adduar shekaru masu albarka don bazata taba mancewa da ranar haihuwa

rta ba musamman yanzu da komai ya sauya.

Haka ta shigo mata da gift sannan tayi wishing dinta, gidan yan boko kenan

😂

Maya na kuka ta karba gift din tare da rungume mummyn, atleast yanxu ta kara tabbatar da suna sonta kuma yace a wajensu dukda basu suka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login