Showing 285001 words to 288000 words out of 338813 words
karashen komai ya bayyana masu yarsu bayan shekaru dai dai har shekara ashirin da doriya.
Emotions din da aka barsu dashi ne dai har yanxu yaki barin su, kowa yana cikin wannan hali na shiga s
hocked.
Nanna na barin bangaren bahijja ta wuce main house, ita kadaice ke kokarin ganin ta basu courage gaba dayansu, anne kam saida aka sake komawa asibiti da ita don jikinta sake rikicewa yayi amma ko kwana daya batayi ba tasa aka dawo da ita, nannan
kuwa saida jininta ya dan hau.
Yallabai taj ko kullum yana zaryar part din nanna, saboda nannan da kanta ta kawo sabeeha da itama gaba daya har zuwa yanxu she’s down, itama kullum cikin kuka, kukanda ta rasa na menene, farin ciki ne ko akasin haka saidai
tafi dangantashi da na farin ciki, ammafa tanajin zafin cutarta da hadiza tayi, ta cuceta ta cuceta ta saboda ita kadai tasan irin rayuwar datayi, ta rabata da asalin iyayenta, ashe tanada gata haka? Gatan da bata taba tsammanin tana dashi ba a duniya ko
zata sameshi, ya allahu…
Ranar da majeed ya rungumeta da kwalla a idanunshi saida ta jita kamar yau aka kawota duniya, sai taji duniyarta ta sauya a daidai wannan lokacin, ta dunga ayyana aranta wannan mahaifinta ne? Mahaifinta na asali? Ashe tana da uba?
Allahu akbar.
It was a heartbreaking moment, tana hawaye yana hawaye, ta sanya hannayenta ta goge mashi hawayen dake fuskanshi ta kasa cewa komai, haka zalika shima.
Bahijja ko kasa hada idanun tayi da sabeeha tun daga ranar, da wani idon zata kalli diy
ar tata? Duk tafi bawa kowa tausayi don babu wanda yasan yanayin da take ciki sai ita kadai.
Nanna na shugowa sitting room ta tadda taj zaune ya shiga tunani, gaba daya shima ya shiga wani yanayi, duk sbaoda sabeeha da tun ranar ya kasa ganin, duk yanda
yaso ya ganta babu hanya, da zarar ya shugo part din nannan take guduwa bathroom bata yarda ma su hadu,
Har zuwa lokacin shima shock bai barshi ba, ta yanda fatima ta kasance jininshi ce? Yar uwarsa ce ta jini mafi kusa, ba tare da ya sani ba.
Yafi kowa
murna da hakan, yafi kowa murna, ashe bunciken da yake didn’t go to waste, ashe iyayenta ba asali ba tare da ita, kuma bawai abandoning dinta sukayi ba, rabata akayi da asalin iyayenta saboda mugunta kawai da rashin imani, duk wanda yaji abunnan saiyaga k
mar wasan kwaiwayo.
Yayi nisa sosai cikin tunanin da yake nanna ta dafashi sannan ya dawo cikin hayyacinsa, nanna ta zauna gefen sa tana dubansa,
Ya gaisheta a natse ta amsa sukayi shuru daga shi har ita kafin ya dubi anne yace “ya take?” Yana nufi
bahijja kenan?
Sai ganin hawaye kawai yayi akan fuskar nannan tace “tausayi take bani tajudeen, daman saitafi kowa jin zafi, haka zalika diyar tata ma, tausayi suke bani gaba dayansu, she’s shattered, mutane babu allah a ransu, all this while she was rais
ing maya unknowingly to her that her biological daughter was switched just because of hatred kuma she wasn’t treated properly, ta taso mara uba mara gata,kuma a wulaqance, ita datayi haka a tunaninta taci galaba akan ta batasan cewa kanta ta cuta ba,”
T
a danyi shuru na yan mintuna, kana ganinta kasan abun na mata zafi itama, ya dago yana son ya tambayi ya sabeehan take ita ma ya kasa, dakyar ya tattara courage din shi yace “how’s fatima? Is she okay”
“She will be fine Insha allah, bari na shiga na dubot
a” tana fadin haka ta wuce bedroom, tana shiga ta tadda sabeehar zaune ta hade jikinta waje guda, itama duk ta rame gaba daya kamar ba ita ba.
Nannan ta yi murmushi ganin ba kukan take ba ta karaso inda take a zaune a kasa ta kamo hannayenta ta maidota ka
n gado ta zauna nannan ma ta zauna tana kallonta tana murmushi.
“Allah ya maki albarka fatima, allah ya maki albarka fatima, allah yasan meya shirya shiyasa ya hadani dake batare da munsan juna ba, ina farin ciki da kika kasance yar bahijja kuma jininmu,
bamusan irin rayuwar da kikayi ba a baya ba don ke kadai ce zaki fadi irin rayuwar da kikayi amma ina godiya ga allah dayayi mana protecting dinki, ya kuma kareki ya maido mana ke wajenmu, alhamdulillah alhamdulillah…duk muna kaunarki, muna sonki sosai, ku
ma kinada gata, kinji ko”
Sabeeha na hawayen farin ciki tace “nagode nanna… kukan da nakeyi kukan farin ciki ne, ban taba tsammanin inada gata haka ba, na kasa yarda da hakan, idan na tuna irin rayuwar danayi a baya..”
Sai kawai tayi breaking hawayen dak
e fuskanta, ya soma saukowa sosai, nanna ta rungume ta sosai tace
“Ki mance da komai kinji, karki saka komai aranki kinji ko? Duk abunda ya faru mukaddari ne daga allah dama chan allah ya rubuta hakan ne zata kasance bazamu san ke jininmu bace sai bayan w
annnan shekarun masu tsayi,You have us all, kina cikin gata da soyayya, Ina fatan kuma zan ganki da mahaifiyarki..”
Saurin saukar dakai sabeeha tayi, jikinta yayi sanyi sosai wani sabon hawayen ya soma sauko mota.
Nanna ta lura da hakan tayi saurin jawot
a jikinta ta rungumeta, “tsakaninki da mahaufiyarki bahijja? Shin bakya farin ciki data kasance mahaifiyarki”
Nanna na gama magana kamar ta tsokalo mata wani abu kawai ta fashe da kuka, ta girgiza kanta, “meysa baza kije wajenta ba?”
“Bata sona!!!” Sabee
ha ta fada kai tsaye.
“Karki taba tunanin haka, wallahi babu wanda yakaita sonki duk soyayyar da muke nuna maki, bansan meya shiga tsakaninki da ita ba da har yasa kikayi wannan tunanin amma inaso ki sani duk avubda ya faru cikin rashin sani ne,ki bude zu
ciyarki fatima, wannan dama ce allah ya bamu harda ke, ki dauki abun kamar an sake haifarki cikin wata ni’imatacciyar sabuwar duniya kinji ko?”
Magangnun nanna ba karamin dadi sukayi ma sabeeha ba kuma suka sake kwantar kata da hankali,
……..
After
a week…
Cikin sati gudan nan abubuwa da dama sun faru ciki kuwa shine tabbatatuwar rayuwar sabeeha data chanza on a blink of an eye, tun bata amince da hakan ba tana ganin abun kamar wasa harta yarda, soyayya take samu da gata ta kowanne bangaren, har ta
soma sakin jikinta baiwar Allah, ganin abun take kamar a mafarki tana jin kamar za a ta tashi, dukda ta san kowa a gidan tunda sun kusa shekara da zuwan su gidan ita da hadiza jinsu take kamar yau ta fara sanin su, mutanene masu daraja da son jininsu fadi
n irin farin cikin da take ciki bata lokaci ne, a da kullum cikin kwanakin saidai taita kuka tana tuna irin rayuwar datayi a baya, amma kasancewar nanna da anne da anty fadila a gefenta uwa uba kuma mahaifinta, wanda har zuwa lokacin ta kasa yarda da ita s
abeeha wai tana da uba kuma tana da gata, soyayya suke nuna mata babu adadi, from left and right ta kowanne bangare, bangaren ya sameer ma da nashi iyalan suna farin ciki, musamman anty mubina, hamad ma ya samu damar yin magana da ita kuma yana mai farin c
ikin kasancewarta yar uwarsa ta jini, laila ko har zuwa lokacin ta kasa zuwa ta ga sabeehar saboda tunawa da irin abubuwan da suka mata ita da maya, yanxu ashe duk wannan lokutan maya ba asalin cousin dinsu bace yar matar da ta sauya masu cousin dinsu ce?
Kai ba lailan kadai ba duk wanda ya tuna da wannan abun sai yaji gaba daya baya son ganin mayar.
Yan uwan majeed ko tattaki sukayi tun daga Lebanon suka zo, iyayensa daman sun rasu, sai sisters dinshi, yanda kowa ya shiga shock haka suma suka shiga said
a suka zo sukaga sabeehar, it was an emotional moment for all of them abun dai ba a cewa komai.
Kamar dai yanda majeed yaji lokacin daya fara ganin sabeeha har yaga kamanninta da kakarsa haka suma yan uwansa suka dunga fada, ranar dai sabeeha taga soyayya
, haka suka dunga rungumeta suna sumbatarta a kumatu yanda suke a aladarsu suna murna harda masu hawaye itama dai hawayen farin cikin take.
Fadila kam ko maganar mayar ma bata son yi, akwai ranar da laila ta shiga part dinsu mayar donta dubota saboda ha
mad yace ta dunga zuwa tana dubata, yanda taga mayar hankalinta ya tashi sosai har kwalla saida ta mata saboda tsakani da allah tana sonta har cikin zuciyarta kuma ta kasa yarda da ba cousin dinta bace ta asali, shes a replacement of sabeeha, bayan wannan
yanda taga mayar ta koma ma saida ta tsorata, ranar sunsha kuka sosai maya na tambayarta shikenan yanxu ita ko kowan kowa bace kuma ba yar mummy da daddy bace yar mai aiki ce? Kuma yanxu shikenan tunda batada alaqa dasu za a koreta ko? Kuma duk sun daina s
onta ko? Laila dai nata tausasata tana nuna mata cewa bazasu tsaneta ba tunda itama yarsu ce kuma ba laifinta bane, itama haifarta akayi, batada laifi,
A haka dai suka rabu ta fito daga wajenta,
Tana koma part dinsu ta fada ma mami (fadila) yanayin data
tadda maya tana hawaye fadila ta daka mata tsawa sannan tace mata karta sake kawo mata maganar wata maya, gaba daya saitaji tsanar mayar daman tun farko tana doubting yarinyar kamar ba yar bahijja ba,ashe hunch dinta gaskia ne,
Bahijja ko har zuwa yanx
u ta kasa tattara courage din fuskantar yarta ta asali wato sabeeha, a cewarta bata chanchanci kasancewa mahaifiya a gareta ba saboda irin abunda tayi mata a baya, ta nuna tsana a gareta.
Nanna da fadila kullum nusar da ita suke illar kauracema sabeehar n
a qin fuskantarta da takeyi, kuma blaming din kanta da take bazai amfaneta da kkmai ba, ta kama yarta, ta jata jiki, abunda ya faru ya rigada ya faru bazqsu iya sauyawa ba, kuma rubutattacen al’amari ne, cuta dai hadiza ta cutar dasu cuta mafi tsanani wand
a allah kadai ne zai saka masu kuma zai sakama sabeeha.
Su hadiza ko kamar an shafe babin su, babu any track of them, dss ake magana fa
😂
tunda suka tattara su ko alamun motsinsu ko tarihin su ba a ji, ana chan ana shan azabar da sun gwammaci a kashesu ma,
musamman hadiza da basa sassauta mata.
Jamilu kuwa kwana daya biyu uku da baiji motsin jamila ba, ya kira wayoyinsu da hadiza shuru haka kawai jikin shi ya bashi akwai matsala wannan yasa ya tattara yayansa ya sayar da gidan da suke ciki ya tasa su sai k
auye.
Maya ko, bana jin zan iya fayyace maku a wani yanayi take ciki, ta shiga wata ukubar rayuwa, taga go no go, ta tabbatar da tabbas ita ba yar gidan bace, sabeehan dai datake wulaqantawa takema kallon wulakantacciyar itace asalin yar gidan, ita kuma
yar mai aiki ce, yar mai aikinda bama ta da asali ko tayi tunanin tana da uba, bata iya cin komai, bata iya chan komai, har wata yar natsuwa ce tazo mata, wato wargi ma waje ya samu, ko shaye shayen ma batabi ta kanshi ba, don ba kwaya ba ko roci ce bataj
in zata iya magance mata matsalar dake kanta, she cant bring her self to believing that ita yar hadiza ce kai ta cuceta data kawota duniya kuma mummy da daddy ba iyayenta bane na asali, innalillahi wa inna ialaihi rajiun, cikin kwana biyu ta rame ta kanjam
e, tayi la’asar, kullum tana daki bata fitowa, ay bata gama yarda da gaskiayra dake gabanta ba saidata yi kwanakin nan bahijja bata shugo dakinta ba yanda ta saba, matarda bata iya barci bataji motsinta ba, shikenan tata ta kare, yanxu idan komai ya lafa t
unda sun samu diyarsu korarta za ayi kenan? Kai tsanar datakema hadiza ko mutuwarta, tana jin inama za a tasheta ace mafarki take ko zataji sauqin abunda takeji.
Basira kullum saita kawo mata abunci, amma yanda ta kawoshi dakin nan haka zata daukeshi don
bata tabawa, kuma duk maganar da zata mata bazatace uppan ba, kullum tana daki futila a kashe,tana kuka.
Nanna ce kawai ke yawan dubata, sai kuma hamad da daddy (daddyn sabeeha
🥹
lol)dadyn nema yasa basira na kula da cinta bayan shiga dakin dayayi sau day
a don ya dubata, yaga yanda ta koma, da ya tuna abunda hadiza ta masu na sauya yarta datayi da tasu saiyaji gaba daya zuciyarsa ta tsinke, he cant help it, yanajin zafin abun sosai saidai kuma ya kasa yaji tsanar maya saboda ya rike ta a matsayin yarsa kum
a har zuwa lokacin yanajinta yarsa ce itama, kuma ba karamın tausayi take bashi ba don itama bata da laifi, laifin mahaifiyarta bazai shafeta ba.
Babban tashin hankalin da suka shiga a satin kuwa shine heart attack din da bahijja ta shiga, saboda damuwa
r data sama ranta, ranar gaba daya kowa ya shiga tashin hankali mara misaltuwa musamman majeed, da nanna da suka san abunda take ciki.
Saida likitoci wajen uku suka hadu akanta kafin a samu kanta da daidaituwar nunfashinta.
Idan ka ganta dole ta baka tau
sayi, lokacin da gaba daya ahalin sukaji cewa zuciyarta na cikin barazar bugawa sun shiga wani maquyacin hali.
Sabeeha ko tafi kowa shiga tashin hankali, duk kwanakin da suka dunga yi a asibitin tana gefen bahijja bata matsa ba, kuma basu hanata ba suka b
arta, anne cema tace su barta kusa da bahijjar saboda bahijjar tafi buqatarta a irin wannan lokacin.
Haka zata kwana tana salloli tana rokon ma mahaifiyarta lafiya, ko barcin kirki bata iya yi sosai, majeed ma yawanci a asibitin yake wuni, da daddare yake
komawa gida.
Duk sanda yazo yaga sabeehar kusa da bahijjar tana rike da hannunta sai yaji wani irin dadi a cikin zuciyarsa farin ciki mara misaltuwa ya lulubesa.
Kwanansu wajen uku a asibiti kafin bahijja ta farfardo, ranar data farfado wajen karfe shid
a na safe tana bude idanunta taji hannunta cikin na mutun, kwata kwata batayi tsammanin sabeeha ce a gefenta ba don tana bude idanunta komai ya dawo mata, ta fara kokarin tashi zaune har zuwa lokacin hannunta na jikin na sabeeha da barawon barci ya dan taf
i da ita tayi saurin farkawa.
Ashe tana kwance gefen ta ta dora kanta bisa gadon da bahijjar ke kwance, kafin barcin nan ya dauketa sallar asuba tayi ta dawo kusa da bahijjar ta zauna tana kuka tana kallon fuskarta, tana ayyana ma ranta cewa wannan mahaif
iyarta ce ta asali kuma itace ta tsugunna ta haifeta, tana jin yanda she’s blessed, don ba tun yanxu ba takejin tana son bahijhar sosai musamman yanda taga tana son maya sosai, tasha rokon allah dama ace itama tana samun irin wannan so da gatan
Tana ciki
n wannan emotional state din barci ya fusgeta, sai yanxu data soma jin motsi ta farka.
Bahijja na tabbatar da sabeehar ce a gefenta kawai saita fashe da kuka, tana hawaye sosai gwanin ban tausayi dayasa sabeehar itama ta soma kukan har zuwa lokacin hann
unta na cikin na bahijja idanunta yayi jaa sosai, samun kanta tayi da rungume bahijjar sosai kamar zata shige jikinta, hannunta na karkarwa, itama kanta bahijjar jikinta karkarwa yake ta kankame sabeehar sosai, suka rasa wa zai lallashi kowa.
Sun dade a c
ikin wannan yanayin basu san ma majeed ya shigo ba yana tsaye daga gefe tare da taj suna kallonsu.
Saida sukayi mai isarsu kafin bahijja ta iya bude bakinta ahankali dukda tana cikin wani yanayi na rashin kuzarin jiki tace “bansan da wani irin kalamai zan
nemi yafiyarki ba, I’m sorry my daughter I’m sorry for all that you have gone through I’m sorry for not being by your side when you grow up, my heart felt so so heavy a duk lokacin dana tuna ko rikeki ban samu nayi ba bayan na haifeki, i just had a glimps
e of you lokacin da aka ciroki daga jikina, when i was unconscious, i am so devastated for not recognizing you? How can i live with this kind of pain???? A tunanina inata rayuwar kwanciyar hankali kuma ban rasa komai ba, allah ya azurtani da komai ashe kin
a chan cikin wata rayuwar da bata kunshi komai ba sai kunci, hadiza ta cuce ni hadiza ta cuci, allah ne kawai zai min sakayya, ta cuceni….I’m very sorryyyyy my daughter.. ki yafeni, ki yafemin abunda na maki a baya, wace uwace zatayi ma diyarta abunda na m
aki…da wani ido zan kalleki, ki yafeni yata”
Ta karashe tana kuka mai karya zuciya, wallahi majeed dake tsaye saida kwalla ta zubo mashi, taj ko kasa tsayawa yayi ya futa daga dakin ya koma mota ya zauna.
Sabeeha na kuka harda majina tayi saurin tashi da
ga jikin bahijja ta tsugunna a gabanta kanta. Kasa tana hawaye ta soma magana “dan allah karki nemi yafiya a wajena, saukar hawayenki masifa ne a gareni, ni ce zan nemi yafi ya a wajenki…ma..ma!!!”
Wannan kalmar mama da sabeeha ta fada ba karamin shigar b
ahijja yayi ba, sai kawai taji wani sabon kuzari ya zo mata tama manta da canula dake hannunta ta sauko daga kan gadon ta tsugunna gaban sabeehar itama ta rungume sabeeha sosai, sai a lokacin majeed ya karaso cikin dakin yana murmushi bahijja na hangosa ta
dago sabeeha ya hadesu gaba dayansu ya rungumesu, sai ya kasance sabeeha na tsakiyansu sun rungumeta, a daidai wannan lokacin me zatayi banda godiya ga Allah, wani irin ni’ima ce ta lullubeta taji ko allah ya dauki ranta yanxu to zata kasance wadda tafi k
owa farin ciki a duniya, yau taji kuma tayi experiencing abunda ake kira soyayyar iyaye ga yayansu.
It was so genuine an emotional moment
🥺
ya allah.
Gyaran muryar da akayi ne yasa suka daqo daidai, fadila ce ta shugo gefenta laila da hamad sunzo dubiyar
bahijjar.
Fadila na dariya ta dubesu tace