Showing 15001 words to 18000 words out of 338813 words

Chapter 6 - MATAR TAJ COMPLETE

daidai ba, kunenshi ya gama toshe wa gaba daya memory dinshi ya dawo mashi yana flashing akanshi,ya runtse

idanunshi hannunshi na kan kunnenshi ya toshe, baima son lokacin da

aka fito dashi daga cikin motar ba, yana bude idanunshi hasken rana ya buge shi sai kawai ya sume daidai nan motar ambulance din da ka akira suka karaso tare da motar policey,cikin hanzari aka sakasu cikin motar, abun mamaki an fidda taj da sabeeha sai ak

a rasa matuqin motar kuma, haka aka dungumesu sai asibiti……

***

Tunda ta fara sharara gudu kan titi babu abunda ke yawo a zuciyarta sai tsoro da fargaba, idan har bata dakatar dasu daga zuwa asibiti ba wannan zai iya jawo mata babbar matsala, bama ita

kadai ba saboda kowa yasan hadatin kwayar nan sannan ana neman masu ta’ammali da ita, kuma tasan definitely za ayi kwakwaran buncike, gashi ta yanda ta samu kwayar ma illegally tanan za a fara gano wa.

Bayan wannan ma plans dinta zai ruguje, dalilin bashi

maganin badan komai bane sai don ta kaishi gidan mahaukata, ya kare rayuwarshi achan.

Wayarta ce ta katse mata tunani tana ganin wanda ke kira tayi saurin dagawa takai kunneta, abunda ya fada mata ne yasa ta rikide fara masifa

“You are fucking stup

id, how can you loose him how?”

Hidaya ta daka mashi tsawa a cikin wayar, “i’m sorry ma’am, it happens lokaci guda, bayan na dakatar da motarsu he manage to escape”

“Su kuma fa?” Ta sakw jefo masa tambaya

“I’m sorry ma’am”

Kamar zata zauce tace “what

do you mean by that?”

“An wuce dasu asibiti…..”

Wani irin cursing word ta rarumo ta afka mashi, “im going to kill you idan ka bari wannan ya ruguza min plans dina, idan nasan bazaka yimin aiki yanda ya kamata ba dana bari an kasheka a banza, didn’t you

hear me correctly dazu? Nace maka duk yanda za ayi karka bari suje asibiti now what!!!!! Now whattttt answer me you bloody fool”

“And you better make sure that you come clean on this, don wallahi idan ka jawomin matsala i will Be the one to finish you m

y self, sannan na baka nan da yan awanni duk inda yake ka nemoshi, you had me right?”

“Yes maam” ya amsa ta da gaggawa

Gudun motarta ta kara kamar zata tashi sama,fadwa da kyar ta cin mata, har suka karaso asibiti, already an shigarda su sabeeha emergenc

y room.

A chan gida kuwa tareeq na karasowa gida ya tadda zuwan ammu, “kanwar babansu hidaya”

Wadda ke aure a kasar waje, tun bayan zuwan datayi bayan mutuwar khaal hankalinta ya kasa kwanciya da lamarin gidan bayan tabar gidan, daman saboda mijinta ne t

a koma, rana daya kuma allah ya dauki ransa, gashi batada yaya dashi zamanta a kasarshi babu amfani don haka ta dawo kawai ko sati ba ayi da mutuwarsa ba.

Acahn asibiti kuwa ba karamin shick sabeeha ta shiga ba dakyar aka samu ta farfado, koda ta farka

babu sunan data dunga kira sai didi didi, akaita wajenshi,tana son ganinsa, tamaqi yarda ayi dressing hannunta da karfen motar ya buga wanda yayi sanadiyar dislocating da yayi harya kumbura, ganin hankalinta yaqi kwanciya yasa likitocin suka kaita inda taj

din yake.

Room 2, ana kaita ta ganshi lokacin yana kwance an mashi allura ana jiran ya farfado saida ta tabbatar hes fine kafin ta bisu aka gyara mata hannun nata aka mata sedation daya sa barci ya dauke ta saboda radadij da hannunta keyi.

Hidaya na s

hugowa asibitin fadwa ma ta karaso, kusan a tare suka shiga wajen emergency ward, Hidayan dake gaba ce ta nemi ganin doctorn da yayi treating mutane biyun da aka kawo emergency for accident yanxu, nurses din dake wajen ne suka jagorancesu inda yake, gabata

r da kanta ta farayi kafin ta nemi sanin condition din da yake ciki, ganin hankalinta a tashe yake yasa doctor ya soma mata bayanin, “he’s in shock for now, bai samu wani ciwo ba sannan mun bashi sedation zuwa anjima zai farfardo, idan ya farfado zamuyi ma

shi general test da scan don mu tabbatar idan akwai wani condition din.”

Tana jin haka ta sauke nauyayyi ajiyar zuciya sannan ta nemi akaita inda yake aranta ta kudirci bazama ta bari ya farfado ba zata nemi a mashi transfer ko kuma tasa suyi discharging

dinshi.

Sai a lokacin fadwa ta fuskanci avunda ke faruwa, bayan an kaisu dakin da taj din ke kwance.

Kallonshi suka dungayi gaba dayansu, fadwa ce tayi saurin cewa “how i wish this will be his ending, i just canto stand him”

Dagowa hidaya tayi ta mata w

ani irin kallo kafin tace “if you cant stand him zaki iya futa”

“Wai ukty ban gane maki ba? Isn’t that what we all want?…na lura yanxu kina kokarin boye min wasu abubuwa, waye wanda tareeq ke magana akai? Sannan wani file suke magana akai”

“You dont owe

me an explation, just get out!”

“Wallahi bazan fita ba saikin fada min ukty, what are you hiding? Meysa kike kokarin outing dina waje? “

Ganin yanda fadwa keyin ihu yasa hidaya taja hannunta suka fuce daga dakin ta jata har wajen motarta.

Suna fita nur

se ta shigo dakin daidai nan ya soma bude idanunshi ahankali harya budesu gaba daya tarrr yana kallon ceiling, kanshi wani irin nauyi yake mashi har zuwa lokacin, nurse din na lura da shi tayi saurin futa daga dakin ta wuce wajen doctor lokacin yana tare d

a sabeeha itama ta farfado,

“Sir the other patient ya farka yanxu”

Sabeeha najin haka ta tashi zaune, sai kawai taji gabanta na faduwa, doctor na ganin haka yace mata “maam you need to rest”

“Dan allah ku barbi naje na ganshi,dan allah, i need to see hi

m please”

Ganin yanda ta damu sosai yasa doctor ya yarda suka fito harda ita suka nufi dakin taj din, har zuwa lokacin gabanta baibar bugu ba sosai, doctor ne ya shiga kafin ta sanya kafarta cikin dakin, a zaune yake ya hade hannayeshi a kirjinsa, budo k

ofar da akayi yasa shi maida dubansa ga kofar, har idanunsa ya sauka kan doctor, sabeeha data hangoshi zaune cikin sauri ta karaso insa yaoe batayi wata wata ba kawai ta rungumeshi tsam a jikinta, bugun kirjinta na sauyawa “didi, didi are you okay? Meke da

munka ? Hope bakaji ciwo ba, im so worried about you,?” Ta karashe tana fitowa daga jiki shi ta kama kafadarshi tana dubawa, kafin ta maida hannayenta kan fuskanshi tace, “talk to me didi? Talk to me please meke maka ciwo”

Yanda yake kallonta haka take ka

llonshi, gaba daya ya zama so confuse, WHOS THIS? Abunda yake tambayr kanshi kenan, how did i end up here? Yadai tuna suna cikin mota har sukayi accident dalilin yowa kansu da truck

dinnan tayi daga nan he can’t remember ya akayi ya shiga motarma, sai yabx

u daya bude idanunshi yaganshi anan.

Hannunta data dauka akan fuskanshi ya kama duka da hannenshi ya cire daga kan fuskanshi, fuskanshi a hade kamar bai taba dariya ba babu wasa ya dubeta daga sama har kasa ya bude bakinsa cikin isa da aji yace “Who are

you????, what give you the audacity to touch me?”

Dam gaban sabeeha ya bayar, yanda yake magana da yanda yake kallonta gaba daya ya sauya, his tone was very harsh and hard at the same time, sai kawai ta sandare tsabar mamaki, yau didi ne ke tambayar wacec

e ita? daidai nan aka turo ko hidaya ta shugo,

“I said who the hell are you?” Ya daka mata tsawa wanda yasa jikinta ya soma tsuma, ba sabeeha ba hatta hidaya data shugo gabanta ba karamin faduwa yayi ba jin yanda yayi magana,

Jikin sabeeha na bari gash

i ya kama dan hannunta sosai ya rike gam, take taji wani irin tsoronsa ya durar mata,batama san lokacin datace “didi nice fah ni ce bibin ka? Why are you like this”

Yana kallon hawaye na sauka akan idanunta amma bai saki hannunba saima danqewa daya sakeyi

yace “can someone explain whats going on here, why I’m i here, who’s this??”

Tuni jikin hidaya ya soma tsuma, dagowar da zaiyi kuwa ya hangota daga bakin kofa, baima san lokacin daya saki hannun sabeeha ba yace “first love…”

Yanda ya fada saida gabanta

ya bada wani dammm, muryar shi Nayin amo, at that moment jikin hidaya ne kawai ke dawainiya da ita badai hankalin ta ba don hankalinta ya gama barin jikinta gaba daya, ko ba a fada mata ba she can tell ya dawo hayyacinsa, he has regain his memory…….



💋

BOSS LADIES WRITERS

💋



MATAR TAJ (destined with you

🩵🤍

)

Written by

Queenmarh





Book2

PAID

Chapter 60

Update!!

Yanda ya fada saida gabanta ya bada wani dammm, muryar shi Nayin amo, at that moment jikin hidaya ne kawai ke d

awainiya da ita badai hankalin ta ba don hankalinta ya gama barin jikinta gaba daya, ko ba a fada mata ba she can tell ya dawo hayyacinsa, he has regain his memory…

Gaba daya daga sabeehar har doctors din dake tsaye da nurse duk mamaki sukeyi, doctor ne y

a karaso inda yake zaune yace, “calm down sir,”

“Why should i calm down? I fucking need an explanation, and who’s this? Wace wannan”

Yayi nuni da sabeeha, tunda ya fara magana jikin sabeeha ya soma tsuma,

first love!” Ya sake kiran hidaya datayi tsaye

gaba daya hankalinta ya gushe saida ya sake kiran sunanta kafin ta farfado, ta ma kasa yunkurawa saboda yanda kafafunta suka sage, meke shirin faruwa kenan? Badai abunda take tsoro bane ke shirin faruwa? Hankalinshi ya dawo?”Tambayar da take ma zuciyarta k

enan aranta, da yake a bude tabar kofar lokacin data shugo

cikin dakin wannan ya bama fadwa data biyo bayanta damar jin duk abubuwan dake faruwa kuma tabbas muryar taj din taji, don haka itama ta shugo tayi sake tana sauraron yanda yake magana.

Dakyar

hidaya ta tako zuwa inda yake kafafunta na janta, don ta tabbatar da zargin da take, tana karasowa ta kama hannunshi cikin nata dake ta faman karkarwa yanda yake kallonta haka take kallonshi, gaba daya ya zama confuse ganin yanda suke kallonshi kamar yau s

uka fara ganinshi, ga sabbin fuskokin da bai taba gani ba a gabanshi, banda hidayar daya gani a tsaye don ko lura da fadwa baiyi ba.

Tana riqe da hannunshi ta soma magana,”big baby!”

“Yes first love,” ya amsa ta

“I can’t believe this, ka tuna komai yanx

u? You remember everything?”

Da mamaki yake kallonta ganin yanda take magana surprisingly, “did something happen to me? Meysa kuke kallo na haka? How did i end up here?” Yanda ya karashe zaka gane hankalinshi a tashe yake, yayi wani irin jaa lokaci guda

,gaba daya a cikin duhu yake babu abund ayake nema sai karin haske, ganin yanda hankalinshi ya tashi yasa doctor ya soma magana, “sir you had an accident few hours ago, you were rushed to the hospital kaida wann…”

Saurin dakatar da doctor hidaya tayi tace

“Alhamdulillah alhamdulillah!!!!! You’re awake finally” tana karashewa ta rungumeshi tsam a jikinta, “oh my god! Big baby, youre back, this is unbelievable”

sabeeha sakqe tayi tana kallon sabon drama da take shinfida tana kallon ikon allah, fadwa kuwa j

uyawa tayi kafafunta na karkarwa ta fuce daga dakin, she can’t believe abunda kunnuwanta ke juyo mata, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, tama rasa wa zata kira a waya a daidai wannan lokacin, afiya ce ta fado mata arai tayi saurin dialing number ta, sai

da ta kirata kusan sau uku kafin ta dauka, kamar ma daga barci ta tasheta cikin fada tace “why are you calling da safiyar allah nan dan allah, its 6am here in dubai”

“Afiyaaa!! Listen to me, shikenan komai ya lalace”

“Me kike nufi?”

Jikin fadwa har ts

uma yake wajen furta,

“ Hankalinshi ya dawo, he has regain his memory”

Zumbur afiya ta miqe zaune, babu wani kayan arziki a jikinta tace

“What do you?,”

“Are you stupid ne? Bakiji me nace bane? Hankalinshi ya dawo he has regain his memory,”

“Na sh

iga uku” afiya ta fada hankali a tashe kafin ta tari nunfashin fadwa ta cigaba “shikenan… daman ni nasan za ayi haka saida na fada maku lets end him once and for all kuka tsaya, kuna wani kwana kwana, now what if he remembers everything? How we treated him

, shikenan…shikenan, we have lost all, wallahi we can’t compete with him,”

Wani irin dogon tsaki fadwa tayi tare da kashe wayarma gaba daya, afiya is not helping d matter kwata kwata

Wayar na tsinkewa afiya ta miqe hankalinta a tashe ta wuce dakin sonata

, ta soma banging kofarta,…

Komawa cikin asibitin da fadwa bata sake ba kenan ta shige motarta tabar wajen.

Chan cikin asibiti kuwa, taj na daga zaune yayi saqe yana sauraron hidaya, ganin tana kame kame yasa shi maida dubansa ga calender dake gefen ga

don da yake zaune “wait what?? 2023?? Yaushe muka kai 2023? Was i in coma or what?”

Doctor ne ya tari nunfashi sa wajen cewa “sir please you have to calm down first, lets observe you firs, zaka iya tuna last activity da kayi?, i mean inda kaje ko somet

hing that you’ve been up to?”

Shuru taj yayi yana kokari tunawa chan kuma ya kama kanshi dake sara mashi yace “i just got into my car, was driving then…then”

Ya dan dakata ya kasa karashewa saboda wani irin Dummm da yaji kunenshi yana mashi, take wani me

mory din yayi mashi flashing,daya faru lokacin daya masu amnesia,hankalinshi lokaci guda ya sake tashi don kwata kwata he can’t recall sanda hakan ta faru dashi, abu yanda kasan a mafarki haka yake ganin komai, ganin haka yasa hidaya saurin cewa, “hey look

at me don’t over think your self, karkayi tunanin komai, ka kwantar da hankalinka i will explain komai idan muka je gida, banason wani abu ya sameka okay?”

Shi Kwata kwata baya jin abunda take fada ma saboda wani hajijiya daya dunga ji, yanda kanshi ke

mashi wani dumm, dan dole ya koma ya kwanta kan gadon, yana mai dafe kanshi.

Duban doctor hidaya tayi tace “za a iya sallamarshi yanxu?”

“No ma’am we can’t do that, akwai necessary test da ya kamata ayi mashi,musamman yanxu dana lura kamar he can’t re

call yanda akayi yazo nan, and it looks like kamar ya mance da wasu abubuwan it can be a result of shock due to the accident ko yanada wani issue ko lalura kafin ya samu accident?”

“I don’t need any fucking test, Bakaji me tace bane? Dişcharge me right no

w!”

Ya daka ma doctor tsawa, yanda yake magana daga gani yanada temper, hidaya najin haka ta tabbatar kwarai hankalinshi ya dawo jikinshi he’s back,take taji wani irin sanyi a ranta dukda fargabar da take ciki, agabanshi bata magana daya a musa mata,tha

ts the level of respect he has for her,for now burinta daya kawai ta fiddashi daga asibitin karsu gano wani abun, idan har suka gano to tabbas shima likitoci zasu fayyace mashi komai, wanda hakab zai zame mata babar matsala, don he will suspect her, and he

will be disappointed, wanda bazata taba barin hakan ya faru ba, tunda ya dawo yanxu dole tsarin plan dinta ya sauya, she can’t lose to him never…don haka ta tattara duk wani kuzarin daya rage mata ta dubi doctor tace“Can we talk privately about this?”



Yes” doctor ya amsa ta kafin ya dubi nurse yace “prepare for QR test immediately”

“Yes sir” ta amsa shi kafin su fice gaba dayansu, sabeeha na daga tsaye kamar gunki, tayi saqe kamar wanda aka kwashewa ruwan jikinta, kanta a kasa ta kaasa dagowa ta kalles

hi,sai hawaye dake tsiyaya akan fuskanta,har suka fice bata motsa ba daga inda take.

Gaba daya jikinta yayi sanyi kalau,dakyar ta iya dago fuskanta ta kalleshi, ganin ya runtse idanunshi sannan ya dafe kanshi yasa ta sauke kanta kasa, tana tuna yanda ya

yi mata dazu,babu abunda take sai nazarin komai abunda ya faru ayanxu, yanda yake magana tabbas haka ya tabbatar

mata ya dawo hayyacinshi, allahu akbar, yau adduar ta amsu, ya dawo hayyacinshi, kullum fatan allah yasa ya dawo hayyacinshi, abun yazo mata a

bazata lokacin da bata taba tsammanin haka ba , ta wani bangaren cikin zuciyarta kuwa fargaba take sosai, sai tsoro daya cika mata zuciya, kamarma bai ganeta ba? Yanda yake kallonta dazu tana hango tsananin furgici akan fuskarci, yana mata kallon wadda bai

taba sani ba kamarma ya mantata gaba daya, “innalillahi wa inna ialaihi rajiun” ta soma ta soma furtawa yanayin bugun zuciyarta na sauyawa.

Taj dake kwance ya dafe kanshi babu abunda ke running a mind dinshi sai memories din dake zuwan mashi da bai san

yaushe akayi hakan ba.

Hidaya na futowa tare da doctor suka wuce office dinsa, suna zama,ta soma mashi bayanin rashin lpy da taj yayi, sannan ta dora mashi da ya samu amnesia shekara daya da ta wuce around 2022 kuma yanzu tana kyautata tsammanin ya daw

o hayyacinshi ne,kuma tana zargin ya warke, saida ta fayyace mashi komai daya danganci health record dinsa kafin ta buqaci a sallameshi da gaggawa, tayi hakan ne don hana doctor yayi wani dogon buncike.

“Inason a sallameshi kawai,akwai consultants dinshi

da yake kula da progress dinshi they will take it from here”

“We will do that ma’am amma sai mun tabbatar bai samu wani injury ba daya danganci accident din da sukayi cause he’s our responsibility now”

Ganin doctor na neman jayyaya akan sai yayi buncik

en health dinshi yasa tace “he doesn’t need any of that, idan ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login