Showing 183001 words to 186000 words out of 338813 words
home school teacher dake kula dashi ta shaida yana zaune a visiting area, don tun safe ake zuwa daukan student, on a blink
of eye aka nemeshi aka rasa, jamid kamar zaiyi hauka, school gaba daya ta rikici aka fara duban cctv, abunda suk
a gani ne ya sake tadama jamid hankali, don footage din ya nuna wani mutumi ne ya shugarda barad din cikin wata baqar mota, home school teacher data gane ko wanene ta shaida masu ay driver din dake zuwa daukansa ne lokacin da yake zuwa day kafin a maidashi
prep border…
Jamid was so confused don a lokacin yana kwance baisan meke faruwa ba, baima san wanenene driver ba, tsoronshi daya karya kasance driver nada sa hannu da fadwa…
Waya mutallib ya dauka yayi typing message kafin ya aje wayar ya maida duba
nshi ga barad dake zaune, yaron yayi shuru baice qala ba,har suka isa hideout suna isowa mutallib ya bude mashi kofa ya futo.
Dauko yaron baiyi ma mutallib wuya ba saboda yaron ya sanshi, ciki suka shiga yana fatan kar yaron ya tsorata idan yaga khaal don
yanada wayo.
Cikin ikon allah Koda yaron yaga khaal bai nuna yaji tsoron ganin shi ba, saima tambayar khaal din yayi how is he alive? Mamanshi tace ya mutu bazai dawo ba, gashi kuma yanxu yana raye that means mamanshi karya ta mashi kenan? khaal ya rasa
wani answer zai bashi…
Kallon khaal yaron ya sakeyi Sai kawai ya fara kuka sosai yana tambayar khaal da gaske an kama mamanshi? Friends dinshi sunce mamanshi is a kidnapper an nunota a tv, har bullying dinshi aka fara yi.
Tausayin yaron ya gama babaiba
yeshi,idan ya taso yaji abubuwan da mahaifiyarsa tayi a baya abun zaiyi affecting dinshi sosai…
Call din taj yasa mutallib futa daga inda suke don ya amsa, gaisawa sukayi kafin mutallib ya soma magana.
“Na kawoshi yana tare da khaal yanxu.”
Shuru akay
i daga chan mutallib na jin yanda ya sauke ajiyar zuciya, “please take care of him”
Da mamaki mutallib ya soma magana, “duk abunda mamanshi tayi maka baisa kayi abandoning dinshi ba? Why?”
Daga chan taj ya bashi amsa kamar haka, “saboda he’s innocent,“
Murmushi kawai mutallib yayi yace “kamar yanda kayi hasashe, an saka kamfanin a kasuwa, next week za ayi bidding akan, kuma darajarshi ta sauka akwai possibility kamfanin B&B ne sukeson su saya saboda su kadaine tayi partning dasu kafin wannan scandal din,
”
Shuru taj din yayi yana wani dogon nazari akai, saida mutallib ya sake magana kafin yace “i will call you back” ya kashe wayar ya soma dilaing number merk, yana daukan wayan ya soma mashi proper bayanin yanda abubuwan ke wakana a kamfanin, already yasan
fadwa has take over tunda daman itace next to hidaya, at first ya dauka agenda dinsu daya da Hidayar tunda duk wasu abubuwa da sukeyi akan karya gaji kamfanin mahaifin nasu ne, kuma zasu iyayin komai akanshi sai yanxu ya fuskanshi ba hakan bane, nata plan
s din dabanne, daman he never trusted her tunda har ta iya cin amanar yar uwar tata, dubaga lokacin da aka kama hidayar ta futo ta nuna cewa kwata kwata basusan komai gameda abunda yar uwarsu keyi ba, kuma dalilin dayasa ta hanasu su kansu yan uwanta su sh
iga harkar business, ta juya komai akan hidayar, yanda dai sukayi ma khaal, lokacin da aka ce yana amfani da kamfanin wajen yin illegal abubuwa, ashe ita sayarda kamfanin ma takesonyi, kuma ga competitors dinsu.
Jamid na barin school fadwa ta karaso i
tama, tana zuwa neman barad din aka shaida mata ay driver yazo ya daukeshi, tana barin wajen ta shiga mota taja da mugun speed, tayi mugun sake da bata daukeshi ba tuntuni tun kafin ma tayi threatening hidaya dashi, dole hidaya will not sit still zatayi ko
mai akan danta, musamman yanzu data gano komai tasan wacece asalin fadwar, hidaya has so much influence da zata iya yin hakan,ko zaman sati biyun nan datayi a detention center dinnan fadwa ce tasan yanda tayi duk wani lawyer yaqi daukan case din hidayar, d
ole hidaya ta zauna a ciki don tasan sirrinsu ita da mahaifinta, kuma idan har ta fito zata iya zame masu barazana shiyas ayanxu tayi deciding daukan barad don tasan shine weakness din hidayar shi zaisa taqi making any moves.
Nigeria…
Baze university a
buja…
Suna gama debate presentation kowa ya futo daga class, excitedly, musamman haya da sabeeha sai wasu maza biyu da suka kasance a group dinsu suke.
Sune overall best a cikin group dinsu kuma sabeeha ta kasance leader dinsu don itace jagaban, beauty a
nd brains.
Tunda suka fito daga auditorium din class mates dinsu da waenda suka zauna akayi presentation din dasu babu abunda suke ce mata sai “nice presentation,”
Lokaci guda saita zama kamar wata celeb, babu abunda yafi burge kowa sai yanda ta dunga de
bating lecturers din da aka ajiye for questioning.
Tunda suka fito hamad yake kallonta, gaba daya ya shagala da murmushin da takeyi, duk wanda ya ganta yasan she’s so excited.
Gefenta ya kalla yaga samarin da suke tafe tare dasu sai kawai ya hade rai ya
kauda kai.
Dan tureta haya tayi ta dago ta kalleta chan kasa kasa tace “ga admirer dinki chan”
Cikin saurin ta dago kanta idanunta ya sauka kan nashi, tayi saurin dauke idanunta ta dubi haya tace “ki bari dan Allah”
Dariya haya tayi ta tsaida samarin da
suka fito tare dasu ita kuma sabeeha tayi saurin karasawa inda yake ya wani hade hannayenshi a kirjinshi.
“Ya hamad! Ina wuni, kazo da wuri yau”
Bai amsa ta ba yace “how was the presentation?”
“Alhamdulillah”
“Good” ya bata amsa kai tsaye sukayi shuru
gaba dayan su aka rasa wazai magana, “su waye waenchan? “ ya sake tambayanta yana kallon wajensu haya.
“That’s haya, my friend,”
“I know!”
Ya bata amsa kai tsaye and still looking into her eyes yana jiran amsar da yake nema.
Wani iri taji ganin irin k
allon da yake mata saita samun kanta da cewa “group members dinmu ne sauran”
Dan tabe baki kawai yayi kamar bazaiyi magana ba yace “are they also your friends?”
“No ya hamad, kawai munyi presentation ne tare”
“Okay!!” Ya fada kai tsaye, daidai nan su ma
ya suka tunkaro inda suke tsaye, ko kallon inda take batayi ba ta shiga mota, laila tayi mata murmushi ta shiga itama.
Ganin haka yasa sabeeha kallonshi don yana tsaye har zuwa lokacin, ganin yanayinsa har zuwa lokacin yana nan yanda ta taddashi yasa ta b
ude baki zatayi magana kenan ya juya ya shiga motar.
Bude motar tayi itama ta zauna yaja motar suka bar harabar school din bayan ta tura ma haya message din cewa ta tafi.
Around wajen 3:30pm suka iso gida, maya ce ta fara fita kafin laila, ya rage dagash
i sai ita, tana kokarin futa daga motar ya tsaidata.
“Male friends are prohibited islamically, don’t make one”
Tana jin haka tasan me yake nufi wannan yasa babu gaddama tace mashi “Insha Allah”
Laptop dinshi daya bata aro ta aje mashi “thank you” ta fad
a kafin ta futa daga motar.
Ya sauke ajiyar zuciya kafin ya wuce airport da motar.
Cikin gida gaba daya sai hada hada akeyi, a sauke wannan a dora wannan, gaba daya ma’aikatan nata aiki.
Dakinsu ta fara zuwa ta aje littafanta sannan ta dauro alwala tayi
sallah kafin ta futo kitchen din.
Da sallama ta shugo rabi ta dubeta tace “har kun dawo da wuri haka?”
“Eh anty rabi, sannunku da aiki”
“Yan mata dake wajen suka amsa da yauwa sabeeha.
Gefen inda hadiza ke tsaye ta nufa tace “ina wuni mama”
Ganin i
do yasa hadiza cewa lafiya ta tsake hannunta daga veggies da suke gyarawa ta fita daga kitchen din.
“Zauna ki taya su yankawa” rabi tayi magana sabeeha ta zauna ta soma yankan veggies din.
Yanda aketa fidda sabun warmers yasa sabeeha tunanin kodai baqi z
a ayi ne bata gama tunanin ba cikin yan matan dake yankan veggies sahura da bintu suka soma magana kasa kasa.
“Ay naji ance manyan baqi za ayi,”
“Harkar masu kudi zakaga abu allah ka mana arziki, aure a cikin gidan nan ay daula ce”
Dariya sukayi kasa ka
sa sabeeha batace masu tak ba don bata yawan shiga cikinsu saboda irin gulma da tsegumin nan da basa rabo dashi, shiyasa suke ce mata wani sa’in tanada girman kai, uwarta kuwa batada mutunci, ji take kamar a gidan aka haifeta.
Misalin karfe takwas daidai
hamad yayi packing motarsa daidai main house, daga baya aka budo kofar, wata kyakyawa mata ce ta futo da dan cikinta daya futo, farace tass Masha allah, zagayowa sufyan yayi hamad ya bude booth suka kwaso kayansu.
“Sannu maman baby” hamad yayi magana yana
mai dubanta.
Murmushi ta danyi cikin kunya tace “yauwa!”
Kallonsa sufyan yayi yace “bari na aje kayanmu a part din mummy ka shiga da ita part din anne.
“Ah ah kuje ciki bari nakai maku kayan chan”
“Thank buddy” sufyan ya fada yana mumrushi suka shiga
main house shi kuma ya wuce part din anty laila da kayansu.
Da sallama suka shugo antu fadila dake saukowa daga part din anne tana hangosu ta fara murmushi.
“What a surprise…ango ango…masha allah saukan yaushe”
Dariya yayi ya kalleta yace “yanxu fa mami
, ina wuni”
Cikin sauri ta karaso kasan ta rungume matar sufyan din tace “bari na fara gaisawa da sirilata tukunna, how are you my dear? Masha Allah,allah ya raba lafiya”
Tsabar kunya taqi dagowa ta kalleta ta sunkuyar dakai tace “mami ina wuni mun samek
u lafiya?”
“Lafiya lau alhamdulillah”
Laila dake saukowa daga dakin maya ta biyo mami tana jin muryar ya sufyan tayi saurin saukowa, “ya sufyan…”
“Princess…” tayi saurin saukowa jikinta har tsuma yake batama lura da matarshi ba tace “yanxu kuka iso? Ina
wuni”
“Lpy lau princess how are you?”
“Im fine yaya” tana fadin haka ta dubi matarshi tace “ina wuni”
“Lafiya ta amsata anty fadila tace “ kuje anne na sama, gashi ana kiran salla saiku huta”
Suka wuce saman itama suka wuce part dinsu.
8pm
Nanna n
a zaune kan sallaya bayan ta idar da sallah ta nade abun salla kenan akayi knocking kofa daga waje.
“Yes come in”
Ta amsa don duk a tunaninta sabeeha ce, rabonta da ita yau tun safe data tafi school ko lekowa batayi ba da yamma.
Nanna na kokarin juyowa
wadda ta bude kofar tayi saurin cewa “nannna!!!!”
Tana jin muryar bahijja tayi saurin dagowa da mamaki karara akan fuskarta, “bahijja, is that you?”
“Ni ce dai bahijjan ki nanna!”
Cikin hanzari bahijja ta karaso cikin dakin ta rungume nanna, nanna ta ka
sa magana tace” saukan yaushe? Shine baki fada min ba ko jiya da mukayi waya”
“I was so excited nazo nayi surprising dinki,”
“Oh my god, what a surprise…kuma babu wandaya fada min”
“Ay babu wanda yasan da zuwan nawa ma, Happy 60th birthday nanna,”
Mu
rmushi nanna tayi don ta manta gaba daya banda yanxu da bahijjar ta fada.
“Oh kudai baku mantuwa, ni nama manta da wani abu wai shi birthday,no wonder business partners dina keta kirana yau, i wanted to take a rest for the day naki dauka”
Dariya bahijja
tayi tace “yanxu dai ki shirya mu fita, please don’t ask me ina zamuje its a surprise”
Dariya kawai nanna tayi tace “toh”
Kusan a tare suka fito ita da nanna, nanna ta saka wani lace na alfarma mai kyau peach color sai mayafi kusan same color da lace d
in, ta zuba dankunne masu kyan gaske sai Yalqi suke kamar diamond, tunda ta sauko from the look of yanda gidan yayi shuru tasan cewa babu kowa, duk sun fita kenan, koda suka karaso mota hamad na tsaye na jiransu.
Yana ganin nanna yayi saurin rungumeta dak
e yanada tsayi saida ya dan rankwafo sosai yace “happy birthday nanna”
Dabbing bayanshi tayi fararen haqoranta suka fito rass tace “thank you hamadudu, yaushe ka kara tsayi ne haka”
Dariya sukayi gaba dayansu ya bude masu kofa suka zauna ya shiga mazauni
n driver ya tuqa motar.
Bahijja ta kalli nanna, wani irin farın ciki ne gaba daya ya gama lullubeta, yau zatayi testifying wannan rana kamar ta yau, abunda ta dade tana addua akai.
“Ina majeed din? Na ganki ke daya”
“Yana chan nanna, ni kadai nazo, ay d
ole ma nazo saboda rana irin ta yau”
Nanna bata gane me take nufi ba kawai dai ta murmusa har suka iso wajen, hamad na parking ya futo ya bude ma nanna anty bahijja ta futo ta kama hannunta.
Wani dan kyalle ta karba hannun hamad abu kamar abun yara fa su
ka rufe mata fuska, abunka da yan boko masu wayewa saita tafi da abun nasu suka shiga wajen din.
Suna isowa wajen hamad ya fara shiga daga ciki bahijja zare mata abun fuskan nata aka kunna haske bauu ko’ina.
Kananun yaran suka fara ihu…
“Surprise!!!!!!
!!!”
Saida nanna ta kifta ido ta sake bude kafin ta fara ganin mutanen dake tsaye a wajen, anyi decorating wajen yanda kasan za ayi dan mini event, an kawata wajen da decorations na zamani, ga banners din hotonta a kafa an rubuta happy 60ths birthday, fam
ily and friends kowa ya halarta, kai waje dai masha allah duk wanda ke wajen is close to her harda business partners dinta.
Gaba daya wajen ya dauka da “Happy birthday to you..”
wani irin breath taking murmushi takeyi, kamar zatayi kwalla tsabar farin c
iki, ga iyalansu kowa ya hallara, sameer ne da nashi iyalan duka, harda yan makaranta abal dake karatu a dubai, ga sufyan da matarshi, kowa dai ya hallara.
Babu abunda take fada sai “Alhamdulillah alhamdulillah, thank you so much thank you thank you, when
did you plan all if this?”
Tayi tambayar bakinta ya kasa rufuwa, kowa nata kokarin hugging dinta, aka bama anne waje ta nufi inda take ta rungumeta itama tace “Allah ya karo shekaru masu albarka”
“Ameen ya Allah yaya”
Gaba daya hankalinsu bai kaiga a
nty bahijja ba don tana daga bayan nanna saida fadila ta hangota tukunna tace “bahijjaaaa,kamar bahijja nake gani”-
“Anne tace ba kama bane itace,”
Kyakyacewa da dariya anty fadila tayi ta rungumeta tace “wai daman zaki dawo nija yau shine baki fada min
ba?”
“Wanted to Surprise everyone shiyasa nace anne karta fadama kowa, ya sameer ne kawai da nanna suka san zanzo”
Kallon ya sameer fadila tayi tace “kofa dazu saida mukayi mganarki dashi baice min komai ba akan zuwanki”
Dariya akayi gaba daya, aka fara
gaggaisawa,
Maya dake zaune chan wajen da aka zazzauna kwata kwata bata tasoba tunda hamad ya shugo ya shaida masu isowar nanna, tanajin muryar mummynta kamar a mafarki tayi saurin mikewa ta tunkaro wajen,
Tana karasowa wajen sai hawaye ta taho a guje
ta rungume mummyta “mummyyyyyyyyy!!!!!!”
Bahijja na jinta a jikinta tace “babyyyyyy!”
“Mummy yaushe kika dawo? Meysa baki fada min zakizo ba,”
“Daman zanyi surprising dinki ne babyn mummy, how are you?”
“Im fine mummy ina dady?”
“Daddy yana chan baiz
oba”
Gyaran murya anne tayi wanda yasa hankalin kowa ya koma gareta tace “lets have dinner ko”
Aka zazzauna gaba daya, masu serving suka soma zagaye da casserole shaqe da abunci kala kala, aka ajiya, wani abunma saika rantse ba cikar yan kasar bane.
Tun
da suka zauna table din family gaba daya babu abunda ake sai hira, bini bini anne zata kalli nanna daketa faman murmushi tana kallon kowa dake wajen, kana ganinta kasan tana cikin farin ciki, its been long rabonda ta ganta cikin farin ciki haka.
Kananun j
ikoki nata yawo a waje gwanin ban sha’awa, fadila da bahijja ko nata faman hira don seat daya suka zauna, gefenta kuwa maya ce ta wani maqale mata kai kace zata sha mama, yar shagwaba kenan, laila ko me zatayi banda yi mata dariya.
Hamad da sufyan sunata
hira gwanin birgewa, amaryar sufyan ko tana gefen anty mubina don akwai yar kunya tsakaninta da anty laila wato maman sufyan kenan sirikarta.
Sameer ko sai faman magana yake da mutane da aka gayyata family friends.
Ana tsaka da cin abunci ana hirarrakin
yaushe gamo anne ta miqe tsaye tayi gyaran murya.
Duk kowa ya maida attention dinsu gareta, bude taron tayi da sunan Allah sannan ta fara godiya ga waenda suka halarta, sannan tayi godiya ga allah daya azurtasu da arziki mai albarka da iyalai.
Sannan ta
dora da tana son tayi introducing addition to their family wanda ba kowane yasanshi ba.
Maganarta ta karshe yayi daidai da budewar kofar wajen da securities din wajen sukayi, ya sanyo kafarshi cikin wajen kowa ya juyo don ganin ko wanene, kwata kwata bais
an da yawan jama’a a wajen, yana sanye da jallab fara khaal yayi nadin kundura akanshi, sai ya zamo kamar wani tauraro daya haske wajen aka bishi da kallo.
Nanna na ganinshi sai kawai murmushin dake fuskarta ya kara tsananta, anne na ganin fuskarta tayi h
amdala aranta don wannan na tabbatar mata da hajara ta hakura da komai kenan.
Dakawata anne tayi da magana ta dubi anne sannan tace “bismillah hajara, bani ya kamata nayi introducing dinshi ga kowa ba face ke”
Wasu hawaye ne masu zafi suka sauko mata aka
n fuskarta na farin ciki tayi saurin sharesu ta miqe tsaye ta nufi inda taj yake gabanshi na dukan uku uku ya kasa dagowa ya kalli oummi dinshi.
Tana karasowa ta kama hannunshi da babu jakar daya riko a ciki yayi saurin dagowa ya kalleta ta sauke mashi mu
rmushi ta juyo tana duban kowa dake wajen kafin ta soma magana.
“This is my one and only son Tajudeen Abdullah Taheel allah has unite us after we got separated for more than 40years Alhamdulillah”
Tana fadin haka ta maida dubanta ga taj tace “Meet my co
workers and your cousins, your family”
Murmushin da