Showing 225001 words to 228000 words out of 338813 words

Chapter 76 - MATAR TAJ COMPLETE

ranar datazo yi kata gyaran daki tace mata tana tsami shine ta bata hadadden turare ta dunga fesawa, wannn abu kam ya mata dadi daman gata da kwadayin abun duniya na kyale kyale.

Tana futowa kitchen ta nufa inda rabi da basira keta faman gyar

e gyare,batayi niyar yi masu magana ba ko sallama saidia tayi tsammanin ganinsu a kitchen din don tana suke fita kofar baya, kallonta sukayi gaba dayansu ta wani ci jan baki radau, itama ta bisu da kallon sama sama, basira da bakinta baya shuru tace “zaki

futa ne”

“Eee,”

“Aiko kinyi kyau wallahi,” ta fada tana dariya kasa kasa, bata amsa ta ba ta fuce.

Rabi ta maida hankalinta ga abunda take tana girgiza kai, “ikon Allah, allah mun gode maka daka bamu iyaye na gari” rabi ta fada aranta

“Anty rabi matar

nan fa ko dubo yarta batayi ba fa amma tasa kafa ta fuce harda su jam baki wallahi ko kyau batayi ba”

“Ke basira kin fiye gulma wallahi kinsan ba mutunci ne da ita ba intajiki ke da ita don munafurci amma kika ce tayi kyau da zata futa”

“Toh ay wai na fa

sa mata kai don jinta take kamar wata budurwa, ga fadin rai, itadai yarta babu ruwanta allah bai saka mata dagawa ba, inda allah bai kaika ba kace saika kai kanka”

Shuru rabi tayi itadai tunanin abunda takeyi kawai shine aranta.

Ta backyard hadiza ta f

uto, irin kallon da rabi ke mata yasa tace “munafuka, lokaci na nan zuwa wallahi ni da kaina zan sallameki mteww” ta dola tsaki, bata gama rufe bakinta ba ta hango taj dake futowa daga motarshi a compound din kunneshi maqale da waya, da alamu daga gym ya d

awo, kwata kwata bai lura da itaba don ba hanyar su daya ba, harya wuce zuwa part dinshi.

Aranta tace “yau nayi gamo, badai wannan ne balaraben ba dan nanna? Chap” maido da dubanta tayi ga motar daya futo daga ciki.

“Lafiyayyan namiji kamar wannan? Daga

gani kuma mai arziki don ko ba a fada ba kana ganinshi kaga arziki, kai ko kyawunshi zaisa mutun ya soshi ko ba kudi, ballema duk tsatson daya futo daga wannan ahalin arziki na biye dashi kamar jela, wani irin murmuahi tayi wanda ita kadai tasan ma’anar sh

i, yanxu ta ajiye buri biyu wanda in anyi duniya dan manzan allah saita cikasu ko ana ha maza ha mata, koda kuwa zatayi yawo tsirara ne.

Yana shiga part dinshi yanda ya futa ya barshi haka ya dawo ya taddashi, ko dinner din jiya ba a kwashe ba, ganin ha

ka ya tabbatar mashi bata shugo ba.

Sama ya wuce zuwa bedroom dinshi shima yana nan yanda yake dan ya hargitsashi ya watsa papers da yake review din ayyukansa da laptop dinshi, he was never a dirty person kuma yanason ko’ina ya zama organize amma saboda y

anason ya kasan ce da ita tunda ya lura idan tazo abunda ya kawota kawai takeyi ta futa wannan yasashi yin haka don ta dunga dadewa yanajin motsinta a kusa.

Bathroom ya wuce shima dai kana ganinshi kasan ba a gyara ba kwata kwata, hakan ya sashi dan jin d

adi don yana expecting zatazo tayi gyaran, yamayi tunanin ko tazo ta tafi har allah allah yake ya dawo daga futar dayayi don baiyi niyar futa bama dande kawai yanason ya miqar da muscles dinshi data nannade mashi jiya, ya zama weak lokaci guda saboda kawai

yayi kissing dinta.

Haryayi wanka ya sauya kaya ya zauna yana duban laptop dinshi babu ita babu labarinta babu breakfast kuma.

Yakai wajen awa guda shuru, daman saida wata zuciyarshi ta ayyana mashi bazata zo ba, gudun hakan ne ma yasa tun farko ya biye

mata data nuna bata sanshi ba, don idanda yayi insisting zata dunga distancing kanta dashi ne.

Samun kanshi yaui da aje laptop din ya miqe tare da sanya bathroom sleepers dinshi ya futa.

Kasa ya sauko daidai nan aka kwankwasa kofar ya kafe wajen kofar d

a idanunshi don son ganin ko waye zai shugo, basira da allah allah take ta shugo don yaune ta taba shugowa bangaren tana bude kofar tayi saurin dagowa tare da washe baki, tuni tray din hannunta ya nemi subucewa, jikinta ya fara rawa, bata taba ganinshi so

close ba sai yau, saidai ta ganshi daga nesa ko taji bilki na maganar sa.

“Wayyo allah” ta fada kamar wata zararriya saitaji kamar zatayi futsari ga wani gumi daya tsatsafo mata tsabar kyawunshi daya kidimata.

Take ya hade ranshi sosai kamar bai taba dar

iya ba, ranshi ya wani irin mugun baci ya dubi tray din hannunta da gumin fuskanta ke neman duga akai.

“Who d hell are you?” Yayi magana kamar da tsawa tsawa, basira aka sake kidimewa kamar ta ajiye tray din ta ruga a guje, “where’s the other maid??” D

a turanci yake magana basira ko turancin babu sai kadan kadan shima don ta taba yin aiki a lagos ne, wannan yasa takeji amma mayarwa ke bata wahala sai dan pigin”

“Good moni sir, me i go wash and clean here today!”

Saurin kauda idanunshi yayi ganin haka

yasa basira tunkarar wajen dining jikinta na tsuma zata aje yayi saurin dakatar da ita, not looking at her site cause he feel disgusted yace “take it back, and call the other maid” ya sake magana cikin husky voice dinshi da bai cika fiddata ba sai idan ran

shi ya dan baci, wani irin kwarjini yake dashi dakesa hankalin mutun ya tashi lokaci guda.

Tuni tayi saurin juyawa tana janyo dankwalinta dqke neman faduwa don ko hijabi bata saka ba ta taho, gaban rigar duk a jiqe don bata dade da gama yin wanke wanke ba

rabi tace mata tazo taje takai breakfast dinsa sanna ta gyara part din nashi tunda sabeehar jikin babu dadi.

Kamar wadda ake ingizowa haka ta dawo main house ta kitchen ta biyo tana shugowa ta aje tray din tana nishi kamar wadda tayi tsere, dakin rabi ta

nufa tana faman susar kai tana shugowa rabi ta kalleta a burkice.

“Ke ya haka kamar wadda aka wullo daga sama”

“Anty rabi…anty rabi..”

“Ke nutsu mana, kin gama gyaran ne”

“Billahillazi bazan kara shiga bangaren nan ba,”

“Meysa?”

“Ni wallahi tsoro m

a yake bani na rantse da Allah, kin ganshi kamar ba mutun ba, allah mai halitta yanda yaso, koroni yayi yace wai fatima taje”

“Baki fada mashi bata da lafiya ba?”

“Yoh ina zan iya anty rabi? Ko idanunshi kasa kalla nayi, wallahi ko taku biyu banba yace n

a futa”

Shuru rabi tayi tana nazarin yanda za ayi, ba huruminta bane shiga bangarenshi don ita ke kula danan, kuka tunda fatika ta fara gyaran part din bai taba cewa ta futa ba dukda ba utace ta fara aiki a part din ba wannan yasa ta gane ya aminta da gya

ran fatiman don gaskia tafi basira tsafta sosai kuma daga yanda anne tayi bayanin yanda za adunga kula da bangarensa ta gane shi mai son tsafta ne sosai,

Kallon basira tayi ganin yanda gaba dayanta sai a slow, kana ganinta kaga zubin kauye kwata kwata bat

a wayewa, gashi dai suna samun ci mai kyau da sha mai kyau don harda turare ma ana basu kayan wanka kuwa sabulu mai kyau ake basu amma gata nan dai saika rantse bata wanka ko dan baka ce, fatarta bata gogewa kwata kwata.

“Mtew kema jibeki dan allah kamar

wata jaka, matsa dan allah” ta fada tana miqewa ta nufi dakinsu basira inda sabeeha ke kwance.

Da sallama suka shiga dakin basira na biye da rabi, daidai nan ta budo kofar bathroom, rigar dazu ne a jikinta bata sauya ta ba, wato kwanciyar datayi ta dade k

afin barci ya dauketa, bayan ya dauketa kuma bata wani dade ba ta farka jin kamar abu na fita daga kasanta wannan ya tabbatar mata baqon watanta ne yazo mata,allah yaso ma bata ciwon mara sai ciwon kafa datake yi duk wata idan zaizo mata, shika bawai ya za

ma mai tsanani bane, gaba daya tayi wani irin fayau lokaci guda har tayi wata yar rama.

Kallonta rabi tayi tace “sannu ya jikin? Zazzabin ya sauka?”

Dan murmushin wahala tayi kadan tace “eh”

“Masha allah maganin daman yana da kyau sosai hajiya ce ta ban

i zazzabin dana dunga yi kwanaki inasha zqzzabin ke tafiya,”

Zama tayi bakin gado suka bita da idanu, rabi ta zauna gefen ta, so take ta tabbatar zazzabin ya sauka kafin ta mata maganar gyaran part din.

“Anty rabi kinyi shuru.. ki fada mata”

Basira tayi

magana tana duban rabi, “kinga wai basira na tura ta gyara chan bangaren tunda bakyajin dadi toh shine yace a turo wadda ke gyara wa da alamu dai gyaranki yafi so”

Kauda kai sabeeha tayi ko maganarshi bata so ayi kwata kwata, “in bazaki iyaba bari naje d

a kaina,”

“Wallahi kina zuwa zai koroki kema na rantse da allah” basira tayi magana tana wuce bandaki da sauri karka rabi tace mata ta koma

Tashi tsaye sabeeha tayi muryanta a dishashe tace “ah ah bari naje nayi zan iya”

Rabi najin haka tayi saurin cewa

“yawwa shiknn ma allah ya kara sauqi” ta fada tana miqewa ta futa daga dakin don itama dai tsoron nashi take ji harga allah ranar daya tsare sabeeha a kitchen saida cikinta ya kada, kyawunshi mai rikitarwa ne gashi da kwarjini.

Jiki a mace sabeeha ta miq

e, wajen kayanta ta nufa ta rasa me zata saka hijabanta daman biyu ne dayan jiya maya ta farkeshi dayan kuma yau tayi amai a jikinshi duk ya baci dole ta jawo wani kayafij doguwar riga da baida wani girman kirki ta dora kan rigar jikinta da basira ta bata

ta saka.

Irin cotton rigunan nan ne na zaman gida wanda ake rarraba masu idan sunzo yawanci irinsu basira da ake kawowa daga kauye zaka gansu ko kayan kirki babu haka suke zuwa.

Futa tayi ta nufi hanyar kitchen ta baya ta futo ta nufi part din, slippers

ne kawai a kafarta daya bayyana yan kananun toes dinta farare tass jijiyoyin kafar nata sun fito dake farar kaface, tunda ta fito wata iriyar iska ke kadata tana shiga sassan jikinta, duk ni’imar dake lulube da iskar baisa taji saukin abunda takeji aranta

ba, da ason ranta ne wallahi bazata taka zuwa inda yake ba da kafafunta saidai kash babu yanda ta iya.

Tana zuwa daidai kofar gabanta ya soma tsananta bugu sosai, kwata kwata tunaninta ya rarrabu kashi kashi, wanda hakan yasa batama san a wani yanayi take

ciki ba physically.

Knocking tayi ahankali kafin ta sanya hannunta dake karkarwa wajen handle din tana kokarin budewa aka budo daga ciki, kamar allah allah yake ta shugo yana jin an taba kofar ya karaso wajen, din daman bai tashi daga inda yake ba tun ba

yan futar dayar maid din.

Jira kawai yake ta shigo ya sanya ta a idanunshi ko zai ji sauqi aranshi, tsakanin jiya da yau ya kasa gane yanayinshi ya kasa gane tunaninshi, ya kasa gane kanshi gaba daya ma, zuciyanshi ne kawai ke controlling dinshi, kuma ya

kasa hanata yin hakan.

Maybe kodan ya dade yana son ganinta, jikinshi na begenta, daman ance action speaks louder than words bazai iya expressing komai ba a baki amma gangar jikinsa da zuciyarta taki yarda ya yaudari kanshi.

Har mamakin kanshi yake kamar

wanda is obsessed with her, actaully he is din baisan hakan ba sai yanxu.

Kallo daya ta mashi gabanta ya wani irin fadi don saida jikinta ya amsa don a gaskia yau sai taji tana jin kwarjinin sa sosai, abunda ya faru dasu a bakin kofar ya dawo mata sabo f

ill, yanda ta dunga jin nunfashinsa a kan fusknta,yanda bakinsa ya dunga yawo cikin nata ,yanda ya dunga kissing dinta deep kamar his life depends on it.

Cikin sauri ta dauke idanunta akanshi tana kokarin hana kanta wannan tunani mara amfani, shiko tunda

ya zuba mata idanu ya kasa daukewa, a fuska dai bazaka tantance meke yawo aranshi ba, don fuskanshi bai chanza ba, kallonta kawai yake kamar wani sabon kamu tundaga tsakiyan kanta da iska ke kada mayafin, gashin edges din daya kusa cike gefe gefen fuskanta

ya bayyana baki wuluk, idanunta yabi da kallo datake jujuyashi, tanada irin hazel brown greenish idanu da saika kureta da kallo sosai zaka gani, shidai bazaice ya taba mata irin wannan kallon kurillan ba duk zamanshi da ita, cause this look is kinda diffe

rent don akwai affection da attention cikinshi, maida dubanshi yayi ga hancinta daya danyi pointing daidai fusknta daya karama fuskan nata kyau, he find it so attractive, maido da dubanshi yayi ga dan bakinta daya dunga kissing jiya, yanda ta saki lebban n

ata da suka dan bushe amma they look moist yana hango yan kananun hakoranta, sai guda biyun nan na gaba da aka gyara mata saima ya kara mata kyau.

Gaba daya ya shagala da kallon nata itako sai a lokacin tayi takaicin futowa haka, sanin ita ba ma’abociyar

saka bra ba.

Hade rai tayi sosai tana jan mayafin nata don ta rufe sosai, ba tare da ta kalleshi ba tace “good morning sir, if you excuse me i will like to do my job”

Kallonta yake sosai kamar baisan tanayi ba yana mamaki kafiya irin nata, she’s still ac

ting as if yesterday doesn’t happened, kamar yau ta fara ganinshi, baisan cewa the most peaceful people are the ones that are very hard to deal with.

Kamar ba fatiman daya sani ba, yarinyar dayake mamakin yanda take da hakuri sosai.

Baice mata komai ba y

a matsa gefe ta shugo ciki ya rufe kofar.

Kitchen din part din ta nufa yana daga tsaye ya saka hannunshi cikin alji’un shi harta fito hannunta rike da vacuum cleaner, pillows din parlorn ta fara tattarawa sannan tayi connecting ta fara goge gogen parlor,

yi tayi kamar babu existence dinshi a wajen kamar he’s invisible to her, shiko kallon ta kawai yakeyi duk inda ta gifta akan idanunshi.

Tana gamawa ta kinkimi vacuum din ta wuce sama dashi, aranta tana fatan allah yasa karyace zai biyota don a taorace tak

e sosai dashi gabanta na mugun faduwa soaai allah allah kawai take ta gama ta futa.

Fatanta bai karbu ba don tana shugowa taga yanda gaba daya bedroom din yake a hargitse tasan zata dan jima kafin ta gama, kuma da gayya yayi hakan, haka nan ta fara kokari

yaye duvet din gadon tana cikin nadewa kamshinsa data barshi dashi a kasa tajishi a kusa da ita sosai, take gabanta ya sake faduwa ta danne zuciyarta ta cigaba da abunda take,

“Fatima!!!“

Ya kira sunanta ahankali, saida jikinta ya amsa amma tayi kamar

batasan yanayi ba.

“Fatima i’m sorry….”

Itace kalma ta biyu dayayi using wajen yi mata magana, chak ta tsaya da zare duvet din da takeyi, hawaye takesonyi amma ta hana kanta, “I’m sorry for not trusting you bibi, I’m sorry for…”

Da sauri ta juyo hannunt

a na karkarwa tace “sorry????”

Takowa ya somayi tayi saurin cewa “sir please…i don’t know who you’re mistaken me for, i don’t know what you’re talking about, i don’t know why you’re doing this to me, this is so unfair, you touch my body unwillingly to me

, why are you doing this to me?”

Ta karashe tana neman fashewa da kuka yayi saurin takowa inda take, tayi baya sosai kiris ya rage bata fada jikin gadon ba.

“Fatima please..this is enough, i know that i have no right to be face you after all you’ve gone

through because of me, i have wronged you for not trusting you, for everything..please fatima”

Saurin toshe kunenta tayi kamar zatayi hauka tace “please stop…stop…” jikinta ya soma tsuma, zafin jikinta ya zurfafa ta bude jajayen idanunta tace “I don’t kno

w who this fatima you’re talking about but please ka kyaleni ka rabu dani, why is it so hard for you to just leave me alone? I’m just a mare house-help nothing else, why are you trying to force me while i dont even know what you’re talking about”

Runtse i

danunshi yayi ya bude su ya kalleta yace “khaal..khaal is alive”

Karatun bakinta daban na fuskanta daban,don yana hango yanda ta shiga wani shock, “khaal bai mutu ba yana raye, kuma na gane komai, na gane irin rayuwar danakeyi da yan uwana yanda suke fat

an ganin bana raye, up until not im hating and regretting not trusting you, for everything youve done for me, for trying to make me understand,..”

karasowa yayi dab da ita soaai saidai akwai yar tazara a tsakaninsu sosai, “na gane komai, kuma up untill t

he last minute they didn’t hesitate to kill me, fatima you made me who i am today,without you i would have been history fatima, I’m hating my self for letting go of you please….

“Na shiga uku” ta wani fashe da kuka mai tauma zuciya jikinta na mazari, take

hankalinshi ya tashi ya wani irin rugumeta sosai tuni ta saki jikinta kamar an zare duk wani energy dinta, turashi takesonyi amma ta kasa ya kamo waist dinta sosai ya sata jikinshi ya rufeta sosai, duk kamshin dake tashi a jikinsa baisa tayi calming kanta

ba, ta dunga fizgewa tana kuka sosai.

Shiko babu abunda yake sai dabbing bayanta yanajin zafi soaai, baisan cewa yayi hurting dinta sosai ba sai yanxu, kuma har yanxu yana tuna last kalamn datayi masa daya koreta, maysa bazai bude idanunshi yaga gaskiyar

dake gabanshi ba,har sai lokaci ya kure, idan lokaci ya kure he will regret it gashi kuwa yanxu he is regretting it more than anyone else.

Har cikin zuciyarshi yakejin zafin hawayenta da kukanta dake futa ahankli ahankali data gaji da tureshin ta hakura,

saida ta natsu ya soma jin zafin jikinta na shigarshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login