Showing 108001 words to 111000 words out of 338813 words
take magana kamar tana
magana ne da wani makiyinta ko kuma someone that she’s scared of
Futa sukayi gaba dayansu zuwa wajen press conference dake cikin kamfanin, suna shugowa aka fara kyaskyasta masu hotuna, yan labarai sun cika wajen, charaf ta k kama hannunshi ta rike cikin
nata tana wani irin makirin murmushi kamar ba ita ya gani ba yanxu a office dinta, haka ta dunga janshi har suka zo wajen zamansu suna facing reporters dake ta faman daukansu hotuna.
Suna zama tayi gyaran murya ta soma magana gwanin ban tausayi.
“We are
here to clear the air and the rumors going around, kamar dai yanda kuka sani wannan qanina ne kuma jinina abun alfahari na banida kamarshi” ta karashe tana sumbatar hannunshi harda hawayenta, “some few months ago ya samu amnesia which cause alot of proble
m and emotional damage to all if us…his relative,”
Ta dan dakata tana matsar kwalla, abunfa kamar drama taj yayi saqe.
Wani reporter ne ya jefi mata tambaya “shin ya samu sauki ne? Kuma zaki bashi makaminshi na shugabancin wannan kamfanin”
Da sauri ta d
ago idanunta harda kwalla ta daga hannu secretary dinta ya shugo da wasu takkardu harda wani professional likita da aka sanshi sosai a kasar suka shugo tare suka tsaya daga bayanta doc din ya gabatar da kanshi kafin ta bama mutumin answer.
“Wannan shine d
r james, shine ke handling case din tajudeen, kuma har yanxu shike kula da lafiyarsa har muna fatan allah yasa ya dawo hayyacinshi, my brother is not just mentally ill, he’s also suffering from brain tumor, he only needs you prayers rn”
Tunda ta soma maga
na yake kallonta da mamaki? Hidaya ke karya agaban idanunshi kuma akan lafiyarshi saboda kamfani, duk girmanta da yake gani
saida ya runtse idanu ayau don tayi mugun bashi mamaki? Daman dukiya da power zaisa mutun yayi haka?”meysa zatayi haka? Why lie?
“But madam ayanda muke ganinshi a haka he doesn’t look like someone that…”
Saurin katseshi doctor yayi yana mashi bayanin ay haka yake, za a ganshi kamar lafiyayye saidai kuma baya cikin hayyacinsa baisan me yake ba kuma yana da cutar mantuwa, kai wata k
aryar da aka lafto kan rashin lafiyar nan ba karamin mamaki ya bama wasu reporters dinba saidai basuda jaa da maganar doctor din tunda official statement ne.
“Ma’am akwai hirar da kikayi watannin baya da suka wuce and kin shaida mana baida wani amfani
don kwakwalwarshi ta tabu gaba daya, shin akwai wani hope din samun lafiyarshi,?”
Kamar jira take ya kai karshe tayi saurin cewa “babu wani hope..babu he will forever stay like this,”
“Ma’am bakya fatan ya samu sauqin ne?”
Sai a lokacin ta lura da tabar
ar data so yi nan danan ta sauya fuska kamar ba itava abun tausayi ta sumbashi kumatun taj ta shafa kanshi kamar wani dan yaro tace “sai nafi kowa farin ciki idan naga qanina ya dawo hayyacinshi ya samu lafiya, he’s my life, my everything he only has me in
this world cause ni kadai ce gatansa kuma farin cikin sa”
Chapp wannan Kalamai nata na karshe sun kara rikita mashi lissafi, ashe irin wannan words din dake futowa daga bakinta are something that are easily comprehended? Sai ya fara contemplating shin da
man duk soyayyar da take nuna mashi throughout his life are just like a comprehensive words?
Wallahi gaba daya he’s lost in his thoughts, baima san har ta jawo hannunshi sun futo daga wajen ba, sai binta yake kamar raqumi da akala, suna isowa office dint
a ta dubi fadwa tace “take him home”
“Kai kuma babu inda zakaje, you will stay back, and i forbid you from any activity da zaisa ka shiga public, gym da kake zuwa, malls da duk wani encounter din da kake,”
“Why????” Shine kalma ta farko data futo daga
bakinshi, har gabanshi ta iso tana mai kallon cikin idanunshi yana kallon nata tace “because i said so, i will never allow you ka ruguza min duk wani tanadi danayi shekara da shekaru, you’re nothing and you can never be anything da zaisa…”
Sai kuma tayi s
huru kawai ta dubi fadwa tace “take him home, and makesure that babu any reporter da yayi noticing da motarshi yazo, zansa amaida motonshi gida.”
Taj fa is speechless, ya rasa tunanin da zaiyi, he’s so disappointed, wallahi inya cigaba da kallonta sauran
respect din da yake mata zai iya zubewa kasa, baya kaunar karya, balle yayi participacing a cikinta, ta sashi cikin wani state daya kasa gane what is right and wrong, she manipulated him into thinking duk yanda akayi she has her reason for what she did amm
a he’s giving her benefit of doubt wannan yasa bai musa ba yabi bayan fadwa, saidai abubuwa da dama na mashi yawo a kwakwalwa musamman maganar sabeeha, inda take ce mashi meysa bazai bude idanunshi ba? Waenda ke sanshi su yake nisantarwa waenda basa qaunar
ganin shi sune yake saka wa as his top priority.
Yana cikin wannan tunanin fadwa ta bude motarta ya shiga itama ta zaga wajen driver ta shiga, tasaka belt, sannan ta fara kokarin saka mashi ya kalleta tace “akwai reporters anan you need to behave”
Tana
fadin haka ta fara janyo belt din kamar tana shafa kirjinshi harta saka mashi ta sauke wani makirin murmushi, tana hango yanda he’s lost in his thought gaba daya, badan hidaya ba bazai taba shiga motarta ba lallai dole ta nemi amincewarshi da yardasa, ta h
aka ne kawai zata maidoshi tafin hannunta.
Suna cikin tafiya ta soma magana da siyaya.
“Why are you so shocked kamar bakasan how obsessed she is akan power ba da kamfanin nan? She wants it all to her self, there no way zata bari komai yayi slipping a h
annunta ba so easily, abubuwan da tayi akan kamfanin nan yafi karfin tunanin ka so i will advice kayi stooping so low karka sa ta fusata ka koma gidan jiya tunda gashi nan ka dawo normal ”
Yana jinta yayi banza da ita saidai gaba daya maganganunta yayi br
eaking dinsu into his head, trying to understand inda maganrta ta nufa.
Chan gefe ta gangara da motarta tayi parking ta dubeshi, “you need to trust me taj, nasan we are not in a good terms amma inason ka sani bazan taba cutar dakai ba, ina sonka ina qauna
rka”
Wani irin banzan kallo ya mata ranshi a mugun bace har zai bude bayan motar tace “kanaso ka kira ma kanka masifa kenan? Bakaji me tace bane? Karka sake kayi abunda zaisa ayi tunanin lafiyarla kalau, kalla!!”
Ta nuna mashi mirror, waenchan da kake ga
ni reporters ne, kuma kana futa zasuyi capturing and i promise me you will be shattered”
“What do you mean?” Ya tambayeta a zafafe, “when the time comes you’ll understand, hidaya bata kaunar bata son ganinka..youre a threat to
her”
Wata irin tsawa ya da
ka mata dayasa ta zuba mashi ido a furgice, “don’t you dare..dont ever say that to my face, kina tunanin zan taba yarda da maganar ki?karya kike i will never, now step on this car kafin”
“Calm dowm mr T ford”
Surprisingly yake kallonta jin kiranshi da ta
yi da sunan, mumushi kawai tayi ta kunna motar suka bar wajen.
Yana dawowa gida sama ya wuce rai a bace,sai yanxu yake ganin all his life he’s being controlled, zama yayi yana kara kallon press din da sukayi daxu, daya kalla ranshi ke kara baci, magnagn
unta sun bashi mamaki sosai, harya fara tunanin anya hidaya ce wannan? The hidaya that he knows will Never do this, koshi banza ne wannan kadai daya gani bawai an fada mashi ba ya zashi kokonto akan rayuwarsgi gaba daya, wallahi bai taba son shiga cikin fa
mily business dinsu ba he’s never interested kwata kwata, why are people around him like this? Haka khaal shima yyi kuma yayi mamakin labarin dayaji yanxu kuma hidaya? Noo noo? Thats impossible, dole she has her reasons maybe kamfanin yana cikin matsala, s
hiyasa take kokarin ganin ta rike kamfanin a wajen, deep down wata zuciyar tashi na ce mashi are you blinded? Open your eyes and face the reality of your life, saidai kuma tsabar how manipulated he is yasa yaqi bude zuciyarshi da zancen, saidai tambayr kan
shi daya soma yi? what’s going on in his life? What has he missed?
Hidaya ko takanshi batabi ba, cause batajin he needs any explanation from her, lokaci guda maganar taj ta rufe ruff kamar ba a taba yinshi ba, kuma shawarar fadwa ce data kawo mata last
minutes lokacin da ta rasa yanda zata shawo kan matsalar da take ciki.
Da daddare daidai lokacin da take yawan shiga study room dinta yaje don ya sameta kuma ya shaida mata cewa bashida interest alan family business din, koda ya karasa yana gabda yin kn
cking ya soma jin magnaganu daga ciki, maganganun are not very clear kuma bawai yayi eavesdropping bane kawai yaji last sentence din nata ne a kunnenshi kamar wake up call, “i was silent and low for a reason not because na barshi ne donya ruguza min plans
dina,…i have come this far babu wanda ya isa yayi crashing dina, nor him not even khaal daya shiga gonata ban barshi ba.. kina tunanin turashi da nayi karatu chan england is not for a reason? No!!!“
Magana fadwa ta maida mata saidai ita ba ajin muryarta
kwata kwata, dan dakatawa yayi yana nazari maganar me suke? Mey ya kawo khaal a zancen nasu har take cewa shima bata barshi ba? What is the beginning of the discussion,sannan turashi karatu England datayi is for a reason? What was the reason?”
Gaba daya
ya kasa puzzling maganganun nata, shigan da baiyi ba kenan ya juya yana nanata magnganun nata akanshi,fadwa ta fito daga ciki, tana ganinshi ta tabbatar yazo wajen hidaya ne, hiw she wish he came earlier dayaji magnagnun dasukayi da hidaya.
Saidai hakan
ma bata baci ba its a chance to her wannan yasa tayi wani murmushi, cikin sauri sauri tazo wucewa ta gefenshi tayi saurin watsa papers din data fito dasu a gabanshi intentionally, karaf idanunshi suka sauka kan headline din kan paper don da harufa manya
aka rubuta, transfer of inheritance da shares ne
A kasan baiga sunan waye a jiki ba don rubutun sunyi kananu.
Kauda kanshi kawai yayi ya wuce ba tare da ya waiwayeta ba, yanata saqe saqe maganganunsu aranshi.
Fadwa ko tana tattare papers din ta miqe
tabishi da kallo harya shige daki tayi smirking ita kadai tasan abund ake ranta.
Tunda ya dawo dakin babu abunda yake sai safa sa marwa,tunanin maganganunsu ya gama addabarshi.
Yana cikin wannan tunanin call ya shugo mashi, unknow number ne wannan y
asa yaqi dagawa, tana katsewa wani call din ya shugo rai a bace ya daga wayar yakai kunneshi, to his fullest surprise muryar fadwa yaji, har zai katse wayar ta dakatar dashi da sauri tace “zan fada maka abu daya ko ka yarda ko karka yar wannan choice dinka
ne,”
Kitt ya kashe wayar yaqi sauraron abunda ta fada sannan ya danna mata blocking.
Fadwa tunda ta tashi take nazarin yanda zatayi ta shiga tsakanin taj da hidaya, duk wani trick tayi amfani dashi amma alamun sun nuna basa tasiri akanshi, kwata kwata
, tsakanin jiya da yau ta kira wayanshi sau ashiri da different numbers baya shiga saboda yayi restricting wayan.
Wata dabara ce tazo mata wadda take tunanin zata iya amfani da wannan don ganin ta cimma burinta.
Achan nigeria yau kwanan sabeeha bakwai
cirr, kuma tayi shi ne cikin kunshi da rashin walwala, wallahi harta soma baki, sauro ya gama cicinye ta gashi ta saba da hutu, chan saudi babu sauro sai ac nanko sai
azababben zafi, ko arzikin fanka bata samu ba a parlor iya daki ne kawai akwai fanka, ski
n dinta yayi rudu rudu yayi jaa sosai abun tausayi, tsakaninta da Hadiza kuwa tsangwama ne da masifa, ko gaisheta tayi saita balbale ta da masifa, wallahi ko qaunar ganinta batayi, yanxu haka suna tare da jamila datazo gidan suna kuskus.
“Kinga wannan y
arinyar ko wallahi wallahi kadara ce a wajen ki hadiza, ki jata aiki gidan abuncin nan da kike zuwa, ko allah zaisa wani tsoho ya ganta anan wajen ki aura mashi ita.”
Shuru hadiza tayi tana nazari kafin tace, “jamila kinsan abunda kike fada kuwa? In fid
data duniya fa kike cewa?“
“Toh ajiyeta zakiyi? Dole wata rana zaki aurar da ita, bayan wannan ma yanda rayuwar nan ta sauya mai kudi ma yana jin jiki balle talaka? Na rantse da allay idan rusau dinnan da akeyi yayo kanku shikennan kun shiga uku”
Hadiza
ta mata mugun kallo tace “dole kice na shiga uku ay tunda kunyi nakanku ke bakida damuwa”
Jamila tace “to ay na baki shawara kinqi dauka, ana takai wake ta kaya? ki sata gaba kawai ko wanke wanke ke tanayi a wajen mene amfaninta in bata nemo ba? Ke zaki n
emo mata taci ko kuwa?”
Sun dade suna tattaunawa don da safe ne kafin jamila ta wuce gida, hadiza na shirin fita sabeeha ta shugo, har kasa ta duka ta gaisheta ko arzikin amsawa bata samu ba, wannan kudin da mutallib ya bata su ta zaro ta ajema hadiza
a gefe, kafin ta soma magana a natse cikin kamewa, “mama, ga wannan ko za a saya abuncin gida dashi”
Kallon kudin hadiza tayi kafin ta dubeta tace “fita ki jira ni waje”
Tana futa hadiza ta kwashe kudin ta saka a jakarta sannan ta saka hijab dinta ta fu
to.
Anan parlor taga sabeehar na ninke kayan ta data wanke, mamakin girman yarinyar take sosai ba kadanba, ta ciciko babu alamun rama a tattare da ita, saita fara wondering wani irin gida aka kaita ne haka? Kodai iskanci tace tanayi achan, yanxu dai ba wa
nnan ne gabanta ba wannan yasa tace “tashi muje”
Miqewa sabeeha tayi ta nada mayafin abayar kanta sannan tabi bayan hadiza suka kama hanyar bakin titi a kafa, kwatwa batayi gigin matsowa kusa da maman tata ba don tana gaba ita kuwa tana bayanta har suka
samu masu okada hadiza ta biya suka hau.
Basu tsaya ko’ina ba sai Gargajiya food service, babban wajene sosai gaskia sai faman gyare gyaren wajen akeyi ana modernizing din wajen, chan wajen parking lots ko shaqe yake da motoci masu nunfashi.
Lokacin wa
jen karfe sha biyu na rana mutane dayawa sun fito yin lunch.
Cikin wajen suka shiga ta baya inda ma’aikata suke, kowa da uniform dinshi, masu serving masu dafawa, masu sarrafawa kowa da nashi shashen harda masu wanke wanke da gyare gyare.
Madam din na da
ga tsaye tana inspection hadiza na hangota tayi saurin karasowa inda take sabeeha na biye da ita a baya tana ta sissinne kai, matar irin yarbawan nan ne.
Gaisheta hadiza tayi sabeeha ta dan duqa itama ta gaisheta daman madam tee suke ce mata.
Kallon sabe
eha matar tayi sannan tace “wannan fa”
“Daman yata ce, naga yau aikin da yawa shine nace ta biyo ko zata taimaka da wani abu, madam ta iya komai wallahi babu abunda bazatayi ba”
Kallon sabeeha matar ta sakeyi tace “yanxu wannan yarki ce? Ahh she no dey r
esemble you o, ke kin taba aiki ne?”
Nan ta girgiza mata kai, wallahi sa’a kawai sukayi don hadiza batayi tsammanin madam din zata bar sabeehar ba.
Aiko barinta datayi dinnan yasa hadiza jawa sabeeha kunne sosai, haka ta shiga cikin ma’aikata, ta soma wa
nke wanken manya manyan tukwane, don ranar akwai abuncin sadaka da za ayi.
Ay kuwa ta durzu, ga uwar rana baiwar allah ko ruwa bata sa a makoshinta ba, madam ko ta yaba da aykinta sosai don data ganta bata yarda yar hadiza bace don yarinyar tayi kalar hut
u sosai.
Sai wajen yamma suka dawo gida da takeaways, harda dubu biyu da madam ta bama sabeeha don yarinyar ta burgeta ga ladabi ga biyayya.
Washe gari haka suka sake komawa, wannan karan ba wanke wanke madam ta sakata ba, turata ta dungayi wajen deliv
ery idan anzo pickup, tama dawowa kuwa zata dawo da kudi an bata tips, aranar saida aka bata wajen dubu biyar, madam bata karba sisi ba ta basu, hadiza ko bakinta kasa rufuwa yayi, ay batansan shawarar jamila zata zame mata alkhairi ba sai yanxu don ranar
har tsire ta siya taci ta rage mata.
A kwana a tashi kusan kullum haka suke, yanxu ya zamana kullum tare suke zuwa, wani sa’in ma idan babu aiki haka hadiza ke turata itako ta zauna a gida, sai ya zamana kamar hanyar allahiri ce tazo mata, ta saya sabbin
kananun atamfofi guda biyu da atamfar leda guda biyu da hijabi biyu ta dinka, ta bama sabeehar daya saba nanata kaya da takeyi kusan kullum, sannan ta hanata saka wani mayafi, tsoffin hijabanta ta hadata dasu.
Ranar friday da sassafe suka shirya domin ran
ar akwai abuncin sadaka da wani dan majalissa ya bayar, za a rabawa mutane dari biyu, bayan sunkai wajen suka fara aiki, sabeeha na yanke yanken su albasa da sauransu.
Sunkai har yamma suna aiki sai wajen karfe biyar suka gama, suna cikin shirye shiryen t
ashi madam ta zagayo baya, daga yanda take magana a waya zakasan anyi babban order ne ko an bata kwangila mai girma sosai,
Baki a washe ta dubesu ma’aikatan nata gaba daya ta masu alamun dasu tattaso, suka zagayeta, “mun samu kwagilar abunci da zamuyi na
kwana biyar, saidai kuma wannan karan ba anan zamuyi ba hiring dinmu za ayi, so inason mutane biyar suyi volunteering”
Gaba daya shuru sukayi,aka rasa waenda zasuyi volunteering saboda cikin matan akwai waenda ke da aure, wasu kuma zawarawa ne, hadiza c
e kawai da wasu zawarawa biyu suka daga hannu, cikin yan matan kuwa mutun daya ce ta daga