Showing 204001 words to 207000 words out of 338813 words

Chapter 69 - MATAR TAJ COMPLETE

a wani sak

aki aikin banza saikace ance ni bazan iyaba,”

“Yi hakuri basira”

“Ki daina ban hakuri dan allah, kizo mu cigaba na gaji zan kwanta,”

Hannu sabeeha ta sa mata hankalinta baya jikinta kwata kwata.

Basira dake kallonta ta gefen ido ce tace “kinga balarabe

n nan? Dan nanna yanada kyau ko?”

Balarabe? Sabeeha ta nanata aranta, “kai wallahi allah yayi mashi kyau, inama ace zai aureni wayyo, hmm bari na daina haukan nan nasan achan kasarsu saudiyya akwai zillaziyas hadaddu ba kamar ni ba gaja” harda yar dariyar

ta

Chak sabeeha ta tsaya da scrubbing din da take jikinta har tsuma yake ta juya ta nufi wajen futa daga kitcehn din, daidai wajen walkway din barrier din dayayi iyaka da kitchen din ta tsaya don tana iya hango duk wanda ke dining din, adaidai lokacin ya

moqe tsaye bayan yayi ma nanna sallama zai koma part dinshi.

Wani irin jiri ta soma ji kamar zata fadi tsabar shock, babu abunda take sai “innalilahi wa inna ialaihi rajiun, “ har muryanta na dan futowa, she’s shock and confuse at the same time, juyowa ya

yi da hanzari don yaji tayi saurin shigewa saqon wajen ta boye fuskanta…



💋

BOSS LADIES WRITERS

💋



MATAR TAJ (destined with you

🩵



🤍

)

Written by

Queenmarh





Book2

PAID

Chapter 99/100

Cikin sauri ta fuce daga wajen ko ganin ga

banta batayi kirjinta na bugawa tayi saurin saka hannunta dake rawa akan kirjin nata, ji take kamar zuciyarta zata fado, marin fuskanta ko tayi yayi wajen sau biyu ko zata tashi daga mafarkin da take tunanin shi takeyi.

Samun waje tayi a backyard din ta z

auna yar a kasa, hawayen dake sauka kan fuskanta ko batama san tanayinsu ba.

“Tajudeen ta gani yanxun nan? A cikin gidan nan ? Kuka shine dan nanna?”

All this while tana tare dashi cikin gidan nan batasan shine ba?duk zamanta a saudi bata taba sanin cewa

mahaifiyarsa yar nigeria bace, tadai tuna lolacin da ammu ke bata labarin yanda yazo gidan, an rabashi da mahaifiyarsa tun yana kankani, shiyasa ya taso bashida mahaifiya a tare dashi sai hidaya daya yarda da ita sosai.

Harta fara jin emotional feelings

na ganinsa datayi, tunawa da abubuwan da suka faru achan saudiyya yasa lokaci guda ta daqo sense dinta.

Take duk abun da ya faru ya soma dawowa akanta, rayuwar da sukayi shida ita achan da abubuwan da suka faru tsakaninsu da yanda tabar gidan, duk Kokarin

datayi na ganin ta danne zafi da dacin abun kasa wa tayi kawai ta fashe da kuka, harga Allah ta cireshi daga rayuwarta ta, kuma bata fatan ta sake hada hanya dashi har abada, ta binne rayuwar datayi a saudi gaba daya kuma bata fatan wata rana ta tono shi,

amma yanxu da suke inuwa daya ta ina zata fara?? Kai wannnan wace iriyar kaddarar rayuwa ce? Rayuwarta juyawa kawai takeyi yanda bata so kuma bata tsammani, ba haka takeso ba.

Ta dade zaune bata ma san da mutun a gabanta ba saida taga inuwarshi a gabanta

yasa tayi saurin yin baya gabanta na faduwa.

Handkerchief din dake hannunshi mai kamshin gaske ya miqa mata yana kallin cikin idanunta, yanayin yanda wajen keda haske kamar hasken rana saboda wutar lantarki yasa ta gane yanad ne a gabanta,

“Please wipe

your tears”

Samun kanta tayi da sauke kanta kasa ta kasa karban hanky din sai jinshi tayi kan fuskanta kamar ana sharewa, da sauri ta dago fuskanta ta kalleshi “meysa kike kuka fatima? Meke damunki?”

Kasa magana tayi saboda yanda takeji aranta kamar tay

i pouring out komai ko zataji sauqi.

“Fatima!!!” Ya sake kiran sunanta a natse, “meysa kike kuka?An maki wani abu ne? Bakida lafiya ne?”

Girgiza kanta ta soma yi ahankali taqi yarda su hada ido dashi.

Shuru shima yayi gaba daya yayi sanyi sosai ganinta

tana hawaye haka.

“Ko baki fada min fatima i see loneliness in you, i see pain in your eyes, please share your pains and burdens with me, I’m willing to listen to you”

Sama sama ta soma sauke ajiyar zuciya, hawayen fuskanta kuwa sunqi tsayawa tana saurar

onsa, “dan allah ki fada min damuwarki, bana son ganinki cikin damuna kinji..”

Nanma shuru tayi ta kasa cewa komai tana kokarin daidata kanta.

“Fatima i…i…”

Saurin karban hanky din hannunsa dake dab da fuskarta tayi ta share hawayen dake fuskan nata ida

nunta har sunyi jaa sosai kafin ta miqe tsaye shima ya miqe yana kallonta.

Murmushi ta kakalo da kyar tace “ya hamad babu abunda ke damuna kaina ke ciwo ne shiyasa”

“Baki iya karya ba,”

Surprisingly ta kalleshi ya kureta da ido tayi saurin dauke nata ta

ce “ba karya nake ba ya hamad”

Dan murmushin da bai shirya yi ba yayi yace “shikenan, but please inason ki sani, im here for you okay? Idan abu na damunki don’t hesitate to tell me”

“Meysa ya hamad? Niba kowa bace a wajenka, ni yar aiki ce kawai, babu da

lilin da zaisa ka damu dani”

“Waya fadi maki haka? I care for you, i can see alot thru you, don’t keep it to your self okay?”

Yaqe kawai tayi tace “nagode ya hamad” tana fadin haka tabar wajen da sauri.

Maganr haya ce ta fadi mata akanshi, haya keeps te

lling her that yanasonta ita kuwa bata fatan karama ka ta wani bala’i,she wants to stay on her limit don yafi karfintaa and she has had enough.

Wanke wanken da bata karasa ba kenan ta wuce dakin rabi, ta roketa ko zata iya kwana dakinsu basira tunda bilki

ta tafi kuma akwai extra gado tace mata eh.

Koda ta fada ma hadiza bata wani damu ba tace mata taje.

Aiko kwana tayi kan sallaya tana kai kukanta ga Allah, akan ya nema mata mafuta.

Jamila na komawa gida dahiru yayita faman kiranta, karshe ma dai kas

he wayar tayi ta aje.

Washe gari, tun wajen karfe shida da rabi duk suka fito domin daura sanwar breakfast, gaba daya kana ganinta zakace bata da lafiya she looks so pale and sick, rabi ta tambayeta meke damunta tace ciwon kaine kawai.

Haka suka gama k

omai rabi tace suje su jera komai kan dining, tsoro da fargaba ne ya durar mata, yanxu the least abunda zata bari ya faru shine yasan tana nan, wanda bazata taba barin haka ta kasance ba, gashi batada dalilin da zatace bazata kai ba.

Wata dabara ce tazo m

ata ta kunce dan kwalin dake kanta dake yanada girma sosai wannan yasa ta yafashi suka soma futarda warmers din, woof datakai zata dawo, lokacin har sun fara saukowa, dake yau weekends kowa na gida.

Laila da maya ne suka fara saukowa kasan don a dakin may

a laila ta kwana jiya, hayaniyarsu ce kawai ke tashi, shugowarshi ce tasa sukayi tsit gaba dayansu, maya da kaudi tace “good morning uncle taj”

Laila ta gaishesa ya amsa su a taqaice kafin ya wuce sama, sabeeha dake labe wajen shugiwa dining din tana jin

muryarshi ta dakata gabanta na faduwa, saida taji laila na cewa “da alamu dai yau nanna a sama zatayi breakfast”

Daga mata gira daya maya tayi kafin tace “gashi nan ya wuce sama, anya maya zaki iya…?”

Hade rai maya tayi sosai tace “kisa ido mana kigani i

dan ban sa hankalinshi ya dawo gareni ba”

Dakatawa tayi da maganar tare da yima sabeeha wani mugun kallo, laila ko tsoron yima sabeeha magana take kar mayan taji haushi.

Abunda ta kawo ta aje zata juya maya tace “kinga zobenki kuwa? Naji dazu kina nema,

kinsan gidan ne yanxu a cike yake da masu hannun bera”

Bude baki laila tayi da mamaki jin karyar da maya ta zugo dukdan ta kunsa ma sabeeha itako tayi wucewarta ko takanta batabi ba.

Dawowa kitchen rabi tayi tana kallon su suna wanke abubuwan da aka ga

na amfani dashi, yau gaba daya qnai zazzabi zazzabi takeji sosai wannan yasa ta barsu da sauran gyaran.

“Sabeeha..dan allah ga warmers din bangaren nanna nan kije kikai sama, ta buqaci yin break a sama yau”

Dam gaban sabeeha ya vada, tabbas dazu taji mur

yanshi kuma taji sanda laila ke cewa da alamu a sama zaiyi breakfast, yanxu ya zatayi kenan? What if ya ganta kai bazata bat hakan ta kasance ba.

“Anty rabi bari na karasa wanke wanken basira takai saman”

“Ah ah ke zaki kai, ita ta cigaba da aikin”

Basi

ra kamar ta hadiye zuciya dan bakin ciki, ta wullo ma rabi wata iriyar harara kamar idanunta zasu futo.

Hankali a tashe sabeeha tace “toh”

Rabi na komawa daki gabanta ya tsananta, ya zatayi yanxu?.

Juyawa tayi ta koma daki ta dauko hijab dinta ta futo t

a dauka tray din ta nufi hanyar futa, har zuwa lokacin gabanta faduwa yake, su maya na breakfast basuma lura da wucewarta ba kwata kwata.

Haka ta bi stairs dinnan kamar karta kai karshe tsabar fargaba ta nufi part din nanna.

Kafun ta shiga tayi saurin ja

wo bakin hijab din nata wajen bakinta ya zamana iyakacin idnaunta kawai ake gani ta gyara tsayuwarta kafin tayi knocking.

“Yes come in”

Akayi maganada daga ciki,runtse idanunta tayi ta bude kofar tare da sallama ciki ciki,

yana zaune kan kujera idanuns

hi na kan wayanshi kamar yana karanta abu, kwata kwata bai dago ba, itako tana arba dashi taji kamar tray din zai kubce mata, ya sauya gaba daya kamar bashi ba, tana hango kwanciyar hankali a tattare dashi gashi ya wani irin kara kyau sosai, kamar ba taj b

a wallahi.

Ajiyar zuciya ta suke abubuwa da dama na yawo akanta ta nufi dining ta aje ta soma jera komai.

Gaba daya attention dinsa baya ga wanda ya shugo, yana replying messages din dake wayarsa, harta gama jerawa ta juya zata futa daidai nan nanna ta f

uto.

“Har an kawo breakfast din” nanna tayi magana don batasan wacce daga cikin yaran ta kawo ba.

Gyaran muryanta tayi kamar wadda ke mura yanda baza a ganeta ba tace “ eh ina kwana nanna”

“Ah ah yarinyar kirki yau kece kika kawo min breakfast din,”

“E

h,”

“Toh sannu”

“Ya Naji muryarki haka, ko mura kikeyi?”

Kamar mai tsoron magana dukdan karya gane tace “eh”

“Toh kunsha magani kuwa ko a kaiki asibiti?”

“Eh nasha” ta fada muryanta na breaking ganin ya dago ya mata kallo daya tayi saurin sauke kanta

kasa ta kawar dashi gefe.

“Toh allah ya sawaqa”

Ko ameen din bata iya fada ba ta juya kafarta na harde ta futa daga part din.

Kallonshi tayi ganin ya yi saurin aje wayar tunda ta futo, ba tun yanxu ba tayi sensing kamar akwai abunda ke disturbing din

shi kuma bata takura don ya fada mata ba amma tanason sanin koma menene.

“Ga breakfast ko? An kawo”

“Okay oummi”

Suka zauna suka fara cin abunci bayan nanna tayi serving dunshi, janshi take yi sama sama da hira musamman hiran business haka.

Suna gana k

aryawa zai wuce nanna ta dakatar dashi.

“Zauna tajudeen”

Ya zauna sitting room itama ta zauna tana fuskantarshi.

Shuru ne ya biyo baya kafin ta tattara courage dinta tace “ina kawunka? Banji kana maganarshi ba?”

Khaal take nufi kenan, shuru yayi yama r

asa me zaice mata, bayason tasan komai ayanxu tukunna sai yayi resolving komai.

“Yana nan lpy,”

“Are you sure babu abunda ke faruwa tajudeen? Is there something that i need to know? Meysa kazo nigeria”

“Saboda ke oummi”

“Nasani amma…”

“Oummi please…za

n fada maki komai amma ba yanxu ba,”

Sauke ajiyar zuciya tayi ganin haka yasa tace “toh shikenan, inason ka hadani dashi, its been ages rabona dashi”

“Insha Allah” ya amsa ta kafin ya mata sallama.

Bayan fitar sabeeha cikin gaggawa ta wuce part din sh

i wai don tayi using wannan opportunity din tayi gyaran part din kafin ya dawo.

Allah yaso babu wani datti a part din da zaisa ta wani dade, gyaran gado ne kawai da wankin bathroom sai kuma vacuuming da zatayi.

Da dakin ta fara cikin gaggawa ta wanke toi

let din kamar tayi tsuntsuwa ta gama haka takeji tana gamawa ta futo zuwa sitting room, goge gogen ko’ina ta fara ta saka humidifier saannan ta kunna ac parlor din, tana tsaka da kashe electric vacuum din taji karar kofa, ta zaro ido waje, abunka da batada

wani yawa tayi saurin juya baya ta duqa a gaban vacuum cleaner din kamar zata dauka abu.

Shidai yaga mutun a tsugunne ga karar vacuum cleaner sai yayi tunanin ko wadda ke zuwa gyaran part din ne.

Bai bama wadda ke wajen attention ba don bashi time din

wannan ya tunkari stairs tanajin tafiyarshi har zai hau sama ya dakata, tare da juyowa yace “are you done???”

Tasna da ita yake and bata son raising anything da zaiyi suspecting itace ko ya gane ita ce wannan yasa tayi saurin girgiza kai.

Shi ganin abun

yayi ma kamar rainin wayo sai yayi tunanin ko kurma ce, ya wani juya bai sake kalon inda take ba ya wuce sama.

Cikin sauri ta dafe kirjinta tare da janye hijab din data rufe kusan duka fuskanta dashi saboda nunfashinta dataji yana neman dauke.

Ay ko seco

nd daya bata sakeyi ba ta arce hartana tuntube.

Yana gama abunda yake ya futa daga gidan shima.

Yauma neman jamilu suka koma yi, gidan ma a rufe yau suka taddashi an saka kwado.

Sabeeha ko tana komawa daki ta samu waje ta zauna ta doka uban tagumi.



Anya bazata hakura da karatun nan ba? Saitaji dama maman nata ta maida lafiyan kawai,“



Misalin wajen karfe hudu na yamma jamila ta dawo, mai shagon saka chargy dake gefen gidan na ganinta ya shiada mata motar datazo jiya sun sake dawowa.

Tana shiga

cikin gida ta kira hadiza, ta dunga Zazzaga masifa itafa wallahi idan aka kama jamilu bazata yarda ba gwara hadiza tasan yanda zatayi tun wuri, hadiza ta shiada mata wallahi babu irin tsoratar da sabeehar da batayi ba akan ta fada mata ko wani abun tayi ak

a korota ta shaida mata ita wallahi aiki kawai taje tayi suka gaji suka sallameta, jamila tace ay wallahi duk wadda kikaga an sallamota haka toh duk yanda akayi wani abu tayi.

“Amma jamila in wani abu tayi suke nemanta mutanen nan ba hukuma zasu saka a ci

ki ba?,kuma kince masu kudi ne”

“Eh kuma haka ne fa, ke harda wani balarabe fa toh kodai….kodai santa yake ne ya biyota har Nigeria?? Dan jamilu yace daga agencies suke wai, kuma wallahi wanda ke nemanta shi balaraben ne kuma dan sauudiyya”

Shuru hadiza

tayi tana nazari tace, “kuma kince masu kudi ne?”

“Eh mana jiya kinga jibegegiyar motar da sukazo da ita”

“Ina zuwa jamila”

Kit ta kashe wayar ta futo zuwa kitchen bataga sabeehan ba ta zagaya backyard saiko ta ganta tan shanyan kaya.

“Ke zonan”

Aje b

okitin sabeeha tayi tabi bayanta suka shiga daki hadiza ta dubeta tace “akwai wani wanda yace yana sanki ne achan saudiyyar kafin ki dawo?”

Cikin sauri sabeeha ta dago gabanta na faduwa, “ah ah” ta amsa ta a natse,

“Dan uwarki me zaisa wasu suzo nemanki

anguwarmu? Eh??“

Sauke kanta kasa tayi tana nazari, badai taj ke nemanta ba? Ina babu abunda zai shashi nemanta.

“Ba magana nake maki ba kike sassauke kai kamar munafuka? Babu yanda za ayi wani balarabe yazo yana nemanki indai bakiyi wani abun ba, karuw

anci kikayi achan??”

Cikin jin zafin maganr maman nata ta dago ta kalleta “wallahi mama ban taba yin abunda allah ya haramta ba ni bansan su waye ba”

“Na rantse da allah kika jawo min bala’i ina tsaka da jin dadin rayiwata tun ban tsufa ba allah ya dauke

min talauci a wannan shekrar wallahi wallahi sai kin gwanmaci bin ubanki lahira,”

Tana gama fadin haka ta korata, sabeeha ta fita jiki a mace.

Yanxu idan mamanta ta gano cewa tayi aure a saudiyya fa? Idan ta gano abubuwan data boye mata ya zatayi? Innali

llahi wa inna ilaihi rajiun, take gabanta ya soma faduwa tunawa da maganganun da mamanta tayi, ko ba a fada mata ba tasan taj ke nemanta, amma meysa zai nemeta? Batada wani alaqa dashi kuma, alqarsu ya gama yanketa tun kafin ta Sanyo kafarta a kasarnan ya

mata kora ta wulaqanci duk halarci datayi masa.

Tana fita hadiza ta kira jamila, tana dagawa tace “jamila munafukar yarinyar nan taki fada min komai wallahi, …”

“Haba hadiza yarinyar nan tafi karfunki ne? Eyy?”

“Bari nasan dabarar da zanyi, baki cemin

komai ba gameda shi wanchan”

“Shege yanata faman kirana jiya naqi dagawa dana gaji blocking din shege nayi”

“Amma bkya tunani zai iya jawo mana matsala jamila? Kinga yanxu…”

“Kinga dan allah kibar maganar wannan dan wiwi din, babu abunda zai iya, kuma

ay baisan cewa…”

“Jamilaaa jamilaaa….” Jamilu daya bankadi dakin ya soma kiranta.

Saurin kashe wayar tayi tana kallonshi gaba daya sai warin rana yake tsabar an bugu.

“Da wa kike waya?”

“Hadiza ce”

“Mutanen nan bin yan unguwa suke suna bincike akaina

, wallahi zan fada masu gaskiar al’amari ni banida wani hadi da ita”

“Haba mai gida, so kake ka tona mana asiri, ka manta kudaden da muka karba? Da albashinta da muka dunga karban kusan rabin kason kudin?”

“Toh hadizar fa? Kin fada mata me tace?”

“Ka za

una mana” ta fada tana kallonshi yanda yaketa faman gumi.

“Me gida banajin mutanen nan wani abu tayi masu suke neman, ni nafi zargin ko daya daga cikinsu ne tayi aiki a gidansu yake sonta shine ya biyota”

Dam gaban jamilu ya bada, idan bai manta ba da k

anshi ya bada aurenta ba tare da tunani ko na sakan daya ba, kuma jamila bata sani ba kwata kwata, maquden kudade aka basu shida ogan agencies dinsu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login