Showing 282001 words to 285000 words out of 338813 words
dakatar da su, fadila ma na taaye don majeed ya shiga da bahijja, daman ba a yarda a shiga gaba daya saidai mutun daya, nan suma suka buqaci mutun daya da zata shiga da mai naqudar, inna na kokarin shiga hadiza tace da jamila take son shi
ga, basu kawo komai aransu ba aka shiga da hadiza labour room jamila na rike da hannunta.
Suna shiga second ward kafin labour room a gaggauce nurse ta soma shirya hadiza cikin kayan delivery, tana gamawa ta dan fita wannan ya bama hadizar damar magana, ja
mila ta matso da kunenta yanda daga ita sai hadizar ne zasuji abunda zata fada nata. “inason ki sauya duk abunda na haifa da abunda bahijja ta haifa”…..
Take gaban jamila ya fadi ta dubi hadiza
Cikin sauri tace “ta ina kike tunanin hakan zai yuwu ha
diza? Ina zan iya yin haka? Asibiti ne nan fa? Kuma goge goge kawai nakeyi anan”
“Jamila ki taimaka min ta hanyar nan ne kawai zansan cewa nayi masu abunda bazasu taba mancewa ba, kuma koba komai abunda na haifa bazaizo duniya ba ya taso cikin rayuwar d
ana taso na girma a ciki ba”
Jamila hankali a tashe tace “idan aka gano fa”
“Jamila ke kadai zaki iya kin haka” hadiza ta fada tana cije lebe, jamia tayi shuru tana nazari kafin ta dubi hadizar tace “shikenan, daman ban fada maki ba anan nake aiki, zansa
n duk yanda zanyi na sauya su”
Tana fadin haka daidai nan nurse ta shigo, ta shiga da hadiza labour room ita kuma jamila tayi gaggawar zuwa dakin su na cleaners ta sauya kaya zuwa na masu goge goge ta futo.
Tana futowa daidai nan tayi kicibus da dahiru d
a shine ya mata hanyar aikin don tare aka kawosu shida ita ma, su kadaine hausawan da aka dauka anan.
Yana ganinta kuwa ya tambayi zuwanta don yau ba shift dinta bane, ba tare da wani tunani ba ta shiada mashi wani abun ya kawota daban, harzai sake mata w
ata tambayar ta dakatar don daman shishige mata yakeyi, ganin yar hannu ce .
Tana futa ta nufi emergency ward, harta wuce su fadila da inna babu wanda ya lura da ita saboda mask data saka sannan ta shige ciki, tana shiga second ward daidai wajen room din
da aka saka hadizar da bahijjar ta tsaya kamar wadda ke aikinta na goge goge saiga nurses sun fito da jarirai, lokaci guda coincidentally, akan idanunta aka wuce dasu dakin da za gyara su sannan a bunciki lafiyarsu, suna shigewa dasu ta nufi wajen ta saka
dan card din dake bude kofar duk wani authorize ward da ake basu idan zasuyi gyara, tana sakawa yaqi buduwa, duk yanda taso ya bude yaqi budewa, take hankalin ta ya tashi ta koma da sauri ta tsaya bakin kofar tana gogewa daidai nan daya daga cikin nurse di
n data shiga ta futo da sauri, sukayi kicibus da dayar nurse din ta taho hannunta rike da baby bag dake dauke da abubuwan da za a gyara jarirai dashi, dayar na ganinta tayi gaggawar cewa “we need pediatric immediately” tana fadin haka dayar tayi saurin kar
bar abubuwan ta wuce ciki tana shiga bata jima ba tayi saurin futowa itama cikin gaggawa ba tare da ta rufo kofar ba daman kofofin irin automatic door ne tana rufewa ne da kanta, hadiza tayi gaggawar shigewa kafin ta rufo da sauri, tana shiga ta tadda jari
ran a cikin gadajen jarirai, su kusan biyar, a gaggauce ta fara duban yanda zatayi identifying dinsu, dake kowanne jariri ana haifarsa ake saka masa tag wannan yasa ta fara binsu daya bayan daya tana duban tag din, har idanunta ya sauka kan yar bahijja da
aka rubuta “baby majeed” tana ganin sunan majeed ta gane yar bahijja ce a jikin tag din, daga ganin jaririyar ma tun kafin taga tag din tasan yar bahijja ce, don ta fita daban, jajawurr ce gaba dayanta, gefwnta kuwa sai taga an saka “baby hadiza” dake a ji
kin file din da aka bude mata daga zuwan nasu ba a saka hadizar nada spouse shiyasa aka saka sunan ta,sai a lokacin jamila ta lura da yaran ma kebance suke don ba a incubator suke ba suna daga gefe sauran biyun kuma suna cikin incubator, da oxygens kamar b
asuda lafiya, ba tare da wani bata lokaci ba ta yaye abun da aka nannadesu dashi ta fidda tag din dake maqale a kafar yar bahijjar ta saka a kafar yar hadiza sanann ta juya, jin kamar ana magana daga wajen, harta juya jikinta na rawa ta dawo ganin jikin ga
don nasu ma an rubuta sunaye akai, cikin sauri tayi switching dinsu ta sauya su sannan tayi gaggawar neman wajen boyewa don har an bude kofar za a shugo kar a kamata, daidai nan doctor ya shigo da nurse din data fara futa dazu wadda taje kiransa, ita kuma
dayar data ce mata taje ta kira doctor din bata sake shigowa doctor ya fara duba babyn da akace nunfashinta baya regulating soaai, bayan ya gama binciken ya tabbatar masu baby is perfectly fine kafin ya futa, yana futa nurse din ta bude jakar babyn da aka
kawo aka ta shirya bothe babies din sannan dayar ta shugo suka fito da jariran.
Suna fita jamila ta soma zuru zuru da idanu, asirinta zai tonu, don idan aka kamata a cikin nan tata ta kare, tunda har card dinnan yaki bude mata toh ba a yarda ma’aikata kam
arta su shigo wajen ba, tuni cikinta ya duri ruwa, ta biyaka hadiza buqatarta gashi uta kuma ta shiga wani bala’in, tana cikin tunanin yanda zatayi kawai taji an bude kofar, dahiru ya soma kiranta, “jamilaa jamilaa” cikin sauri ta futo ya mata nuni da tayi
sauri ta futo, aiko cikin sauri ta futo sukayi gaggawar barin wajen a daidai lokacin allah ya nunama anne futowar jamilar, kamar yanda ya nuna mata shigewarta cikin wajen, tabbas data ganta da farko cikin kayan ma’aikata da mask a fuskanta bata gane ko wa
cece ba saida ta futo daga wajen nan ta cire mask din fuskanta sai kuma wucewarsu ta gabanta da sukayi ita da dahiru,su kuma basu lura da ita ba.
jamila na nishi ta soma magana in a whispering way tace “ya akayi kasan ina ciki?”
Dahiru yace “naga abund
a kikayi a ciki, kuma na ganki da idona kina sauya…”
Cikin sauri taja hannunshi suka bar wajen suna barin wajenko nurse dinnan ta dawo.
Tabbas anne taji wannan saidai kuma bata kawo komai aranta ba sai kuma batayi wani tunani akai ba.
Jamila na nish
i gaba daya duk ta furgice jikinta sai faman rawa yake kamar mazari ta dubi dahiru da shima kallonta yake yanda take kallonshi, duk abunda taje tayi akan idanunshi kuma da idanunshi yaga sanda tayi switching yaran.
Koda ya fada mata ya ganta sanda take
switching yaran tambayarshi tayi me zatayi mashi da zaisa ya rufe bakinshi kamar bai taba ganin hakan ta faru ba ya rufa mata asiri, dake dan iska ne sai kawai yace mata kawai so yake suyi lalata, aiko ba tare da wani dogon tunani ba ta bashi hadin kai yay
i abunda zaiyi.
Suna gamawa ta sauya kayanta zuwa wanda tazo dashi sannan fuce zuwa dakin hadiza tana zuwa ward din da aka kwantar da hadiza ta shiga da sallama, hadizar na zaune ta juyama kofar baya inna kuma na daga gefe tana zaune da jaririya a hannu
nta duk sunyi jungum jungum.
Sallamar jamila yasa inna dagowa ta kalli jamilar, gaba daya itama yanayinta sai a ahankali don bason haihuwar shegwn take ba, daga ita sai jamilar ne sukasan wannan yar bata sunna bace, a titi aka sameta, karasowa jamila tayi
ta kalli inna sannan tace “me aka samu inna?”
Inna tayi shuru kafin ta dubi yar hadizar fara tass kamar ba ita ta haifeta ba tace “gata nan, mace aka samu, ita kuma ki mata magana tunda aka shigo da yarinyar nan taqi juyowa balle ta dauketa”
karasowa
jamila tayi ta dubi inna sannan ta karbi yarinyar tana murmushi kafin tace “allah ya raya” tana fadin haka ta nufi wajen hadiza data juya masu baya, babu abunda take sai hawayen baqin ciki, jamila ta duka agabanta daidai wajen kunenta ta soma magana yanda
daga ita sai hadizar ne zasuji tace “ai saiki huce takaici ki juyo kiga yar da suka haifa ko”
Jamila na fadin haka hadiza ta juyo ta dubi jariraiyar dake hannun jamilar, kana ganinta kaga replica of majeed da bahijja saidai wanda bai gani ba.
Take wani
karfi yazoma hadiza itada ta haihu ko hour daya batayi da haihuwa ba ta tashi zaune taja mayafinta sannan ta dubi jamila tace “mu tafi”
Inna na kallon ikon allah tace “ina zakuje hadiza baki gama warkewa ba?”
Hadiza ta dubi inna tace “idan har kinason k
i sake ganina a duniyar nan inna to ki bar aikin nan mu koma inda muka futo”
“Wannan wani irin magana ne hadiza??”
Hadiza bata saurareta ba ta futa jamila ta biyo bayanta ganin da gaske suke, ta soma kiran hadizar amma taqi amsa ta.
Haka suka futa daga
harabar asibitin cikin gaggawa harda innar.
Basu dade da futa ba anne ta ahigo ward din da aka kwantar da hadiza tana shiga taga wayam, babu inna babu hadiza, daidai nan wata nurse ta futo, ta shiada ma anne ay sun fita, sunyi sunyi ta tsaya a sallameta t
aqi.
Anne dai tayi shuru, ta kasa komawa dakinsu bahijja.
Tunda aka kawo yar bahijjar kallo daya kawai ta mata ta mata addua sannan ta futa.
Daidai nan futowar anne idanunta ya sauka kan dahiru, sai kawai ta tuna da ganinshi datayi da jamila dazu suna k
okarin futowa daga dakin nan tana da damar tambayarshi ina yasan jamilar don ta gane kawar hadiza ce da suka shigo asibitin tare sai kuma kawai tabar zancen.
Hadiza tunda sukabar asibitin nan ko tunanin komawa gidan nan batayi ba, tasa inna ta kwaso k
ayansu ta fito, duk yanda inna tayi ta bari suyi sallama da hajiya qi tayi, a ganin inna idan sukayi haka butulci ne gashi haduzar taqi fada mata dalili haka suka tarkata sukabar gidan, tundaga lokacin basu karajin motsin hadiza da inna.
Bayan wata uku ba
hijja da majeed sukabar nigeria, bangarensu hadiza kuwa lafia suka koma shekaran su uku acahn saida rayuwa tayi tsanani sannan suka dawo abuja amma fa da shirinta ta dawo don bata samu zama ba saida suka tafi chan sukayi tsubbace taubbacen su suka rufe ba
kin kowa akan yarinyar, suka rufe rayuwarta gaba daya, ta yanda bazata taba hada hanya da duk wanda ya danganci asalinta ba, koda kuwa sun hada hanya toh fa babu wanda zai iya shedarta ko ya ganeta.
Bayan wannan kuma ta kara da nata, kiyayya babu irin wan
da bata nuna ma yarinyar ba ta rufe kaf rayuwarta ta maida ta kamar doluwa mara wayau ta rabata da duniya gaba daya da mutanen dake cikinta ta kulleta gudun kar asirinta ya tonu, hatta halitattarta bata bari ba wannan gatson dake kan fuskar sabeehar ma tun
kafin yakai ga haka yake fuskar yarinyar har ya zame mata matsala a fuska da zarar an ganta saina tsoron halitattar ta, ahiyasa koda yaushe take rufe da fuskarta da hijabi.
Yarinya ta taso da tsoron mutane, har gwanda wata akuyar kulle akanta, hadiza ta
davaibaye rayiwarta ta hanata jin dadin rayuwa, makaranta ma saida inna ta dage kafin ta barta tayi.
Inna har ta koma ga Allah batasan da cewa hadiza chanzo yar bahijja tayi ba, dataga yanda hadiza take tsangwamar yarinyar saitayi tuninin ko dan saboda ba
ta sameta ta hanya mai kyau bane shiyasa take kyamatarta da hanta rarta.
MATAR TAJ (destined with you)
Written by
Queenmarh
Book2
PAID
Chapter 109
Cigaban labari….
Deeda hospital abuja.
Ahankali ta soma bude idanunta da
suka mata nauyi soaai harta sauke akan doctor dake kokarin dubata, “if you can hear me bling your eyes”
Doctor ya fada wanda hakan yasa ta kifta idanunta, sannan ya dubi hamad dake tsaye yace “shes stable now..shock ne ya sa ta shiga stage din semi coma,“
“Thank you doc”
Doctor na fita komai ya soma dawoqa maya, kamar sabon faife.
Tuni wani hawaye ya soma sauko mata mai dumi tayi kokarin miqewa zaune hamad ya fara kokarin dakatar dashi ta fara dube dube kamar mahaukaciya “mummy daddy ina mummy na da dad
dy”
Shuru hamad yayi yana kallonta cikin tausayi , “wheres mummy??????”
“Calm down, you’re not okay yet”
“Ka fadamin ina mummy na?? Daddy fa? Please mafarki nayi ko? Wani mummunan mafarki nayi ya hamad wai mummy da daddy ba parents dina bane, god forbi
d Wai parents din wannan yar iskan yarinyar yar mai aikin nan mteww, please ina mummy na?”
Tana fadin haka ta fara kokarin sauka kamar mahaukaci ya dakatar da ita ta hanyar kama hannunta, “ba mafarki bane maya…”
Take gabanta ya bada wabi daammmm, idanunt
a ya nemi kankancewa ta dubeshi tace “ina mummy????????”
“Calm down maya…”
“Don’t tell me to calm down ya hamad…why im i here kuma mummy bata tare dani?, da gaske ne kenan? Niba yar mummy bace,?? Ni yar mai aiki ce??? Wannan yarinyar itace yar su mummy e
hhh??” Ta fashe da kuka sosai ta fara fusge fusge kamar mahaukaciya hamad na kokarin kamata tana tureshi ta cizge drip din hannunta ta futa a guje yabi bayanta.
Tabbas wannan ba mafarki bane, gaskia ne, tunda har za a iya kwantar da ita a asibiti bataga
mummy a gefwnta ba bata ga daddy a gefenta ba.
Innalililkahi wa inna ialihi rajiun ta dora hannu a ka lokacin dataji wani irin jiri na dibanta yuu tayo baya hamad ya tarota ta zube a kasa, ta fashe da wani matsanancin kuka mai fitar rai, “na shiga uku…mek
e shirin faruwa da ni?“
“Maya…mayaaaa listen to me, dan allah ki natsu, ki natsu pls”
Tana shesheqa tace “dan allah ya hamad ka kaini wajen mummy, wallahi babu wanda ya isa ya rabani da ita ina rokonka da Allah”
Dakyar hamad ya lallabata suka koma cik
i doctor ya hata magunguna sannan suka fito, suna fitowa ya bude mata seat din gaba ta shiga ta zauna, gaba daya saita zama kamar batada sauran kuzari, sai hawaye kawai takeyi kamar ranta zaj futa.
Suna isowa gida hamad ko gama parking baiba ta wuce part
dinsu cikin gaggawa, tana shiga kai tsaye ta nufi part din mummy, tana shiga dakin ko sallama batayi ba ta hango bahijja zaune nanna a gefenta, a abunci a gefwnta amma ta kasa cin komai, yau kwana biyu kenan da tashin hankali daya faru a gidan, ta kasa tat
tara gaba daya natauwarta, an kara mata ruwa yafi guda shida, ta kasa ci ta kasa sha, ta kasa magana da kowa, sai kuka, nanna ce kawai ke forcing dinta tanashan koda dan tea ne, shima tanasha yake futowa, gaba daya lokaci guda ta fita hayyacinta ta rame so
sai kamar ba bahijja ba, as expected blaming kanta take tare da tsanar kanta na abubuwan datayi ma diyarta ta asali a baya, tayi kukan tayi kukan harta godema allah, nanna saidai tazo tayi ta mata nasiha, tana nuna mata ba laifinta bane, saidai tace da wan
i ido zata kalli yarta? Da wace fuska zata kalli yarta ta asali? Dubaga duk abubuwan data mata, ta wulaqanta yarta, ta mata korar wulaqanci, saboda idanunta ya rufe akan yarda ba yarta ba, tabbas bata illatata amma ta illata alakarta da yarta ta asali, she
can never forget wannan tabon da hadiza ta mata ta cuceta ta cuceta ta cuceta.
Tana cikin wannan tunanin tana hawaye saijin maya tayi a jikinta, “mummy…mummy kece mummy na ko? Karya suke ko? Nice yarki ta asali ko?”
Maya na magana amma bahijja ji take k
amar ana watsa mata gauta a jikinta, tayi saurin rintse idanunta jininta na boiling, muryar maya takeji amma kamar maganar hadiza ce ke echoing a kunenta, yar hadiza ce data rike a matsayin nata, ta bata so da kauna ta fifitata da komai kuma sanadiyarta ta
kusa illatata yarta ta asali, innalillahi wa inna ialaihi rajiun, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, abubuwa da dama na yawo a kwakwalarta, wanda bataji ya kamata maya ta bayyana a gabanta adaidai wannan lokacin dukda tana kaunar mayar har cikin zuciyarta
, ayau sai taji ko ganinta bata kaunar yi, bata son ganinta kwata kwata, “mummy pls talk to me…mummy kimin magana” maya ta fada tana shesheka, nannan batasan sanda hawaye ya soma saukar mata ba, maya na jijiga bahijja tana rokonta amma ina, itama bahijjar
hawaye take sosai, kamar wadda ake tunzirawa ta miqe da gaggawa ta janye hannun mayar daga jikinta idanunta yayi jaa sosai ta wuce bathroom maya tabita a guje ta kamo hannunta, bahijja ta fusge hannun ba tare da ta kalleta ba ta wuce bathroom nanna tayi sa
urin kiran maya “maya…kyaleta.. tana cikin wani yanayi yanxu, she needs time alone kinji”
Bahijja na shiga bathroom sai hawaye, tanajin maya na bugun kofar bathroom din tana ihu tana kuka,
Ko gajiya batayi don ta dade sosai, har saida ta jigata nanna
n ta kamata ta tashi tsaye suka fuce daga dakin zuwa bedroom din mayar, nanna ta sata tayi wanka dakyar sannan ta sauka kasa tasa basira ta kawo mata abunci taci.
Yau kwana biyu kenan, gidan gaba daya ya zama wani iri babu walwala babu farin ciki, tabbas
hadiza ta masu abunda bazasu taba manta ba, cuta kam ta cucesi saidai kuka allah baya barci don shine majigon bayinsa, aun karbi kaddarar da allah ya kaddaro masu, ka bazasu taba maida hannun agogo baya ba, tunda ya rugada ya faru kuma haka allah ya kaddar
a kuma ya rubuta zai faru, farin cikinsu daya da allah ya kawo