Showing 258001 words to 261000 words out of 338813 words

Chapter 87 - MATAR TAJ COMPLETE

yana sonta ko?“

Shuru bahijja tayi feeling so disappoi

nted, meysa when it comes to iyalan ta kwata kwata anne bata kaunar su, in badan haka ba taga dalilin da zaisa ta nuna kin yarjewarta akan wannan zancen ba, i fact zumuncin su ne ma zai kara karfi,musamman yanda take da nanna.

Hawaye ta somayi don abun ya

tabata tace “yaushe shekaru wajen ashirin da biyar kenan, har yau ina ganin banbancin da kike nunawa a cikin mu anne,bkya kaunar majeed haka zalika maya dukdan saboda nabi abunda allah ya kaddara”

Rai a bace anne ta maido da dubanta gareta, “bahijjaaaaa,

ni mahaifiyarki kike fada wa magana?”

“Kiyi hkuri idan ranki ya baci, bazan iya yin shuru ba, wannan ne dalilin dayasa nake qin zuwa, na zabi na zauna achan, aurena da majeed mukaddarine daga allah, bashida laifin komai anne, kuma babu wanda ya kaishi tu

rasasa ni kan qin juyama asalina baya, gashi yanxu abun ya shafi yata,dama zai tsaya akanmu da da sauqi, yanxu da ace fadila ce tazo ta nemi alfarmar nan da tuni kin yarda kuma kin amince dake ni tawa yar…”

Tass anne ta wanketa da mari, wanda yasa ta yin

shuru, fadila da shugowarta kenan taji kalamanta na karshe sai zuciyarta ta karaya sosai.

“Idan kin gama fada min maganganun da kikaga dama zaki iya tafiya, ban amince ba kuma bazan taba amincewa ba da abunda kikazo dashi, ta dalilinki ko yarki bazan lala

ta zumuncin dake tsakanina da yar uwata ba, idan aure kikason yi mata nayi mata miji tun tuni, wanda nake tunanin zai iya zama da ita kuma ya gyara halayyenta, ya jure duk wani shirmenta”

Anne na fadi haka tayi mata nuni da kofa, sunkuyar dakai bahijja ta

yi ta share hawayenta ta dauki jakarta tace “allah ya tashe mu lafiya ya kara sauqi”

Tana fadin haka ta fuce fadila tabi bayanta har zuwa mota.

“Bahijja bahijja meya faru?”

“Ba komai fadila ki koma magariba ta kusa”

“Dan allah ki fada min”

“Babu komai

zan koma gida sai gobe in allah ya kaimu”

Tana fadin haka ta shige motarta da daddy ya saya mata jiya tajata.

Komawa ciki fadila tayi har inda anne ke zaune ta dafe kanta.

“Anne, dan allah kiyi hkuri, bacin ranki zai iya zamo mata masifa koma me tayi m

aki nasan baikai zuciyanta ba”

“Kiramin hajara a waya fadila” anne tayi magana…..

Hadiza na dawowa gida ko hutawa batayi ba ta dingi neman diyarta, rabi ta shaida mata tana bangaren su, koda wasa batayi gigin zuwa bangaren ba tanadai fatan zuwan mayan.

Wuraren 4 sai gasu laila sun dawo, yauma itace a gidan gaba laila kuma na daga baya, ay daga safiyar allah daya saukesu zuwa yanxu ta gama tabbatar da akwai wani abu tsakaninsu, yanda yake mata magana, da yanda take responding kosu da suke yayan cousins di

nshi baya masu haka, kuma magana fa da lallami yake mata bawai yanda yake masu ba harshly, so sweet of him gashi wani irin kallo da yake mata hmm…

Tsabar gulma direct part din su maya laila ta nufa, tana zuwa kuwa ta taddata zaune a sitting room, ta dau

ra kafa daya kan daya ta sakala airpod a kunnenta tana jin kida.

Ta bayanta laila ta karaso ta sanya hannunta waje idanunta ta rufe mata su, airpod din kunenta ta cire kafin tace “mey haka? Saikace wasu yara”

Cire hannunta tayi ta zauna kan kujerar tana

fuskantar mayar kafin ta soma magana, “yi hkuri sarkin fada ke ba’a iya maki wasa ba”

Tsaki maya tayi tana jin kanta wani himm, itafa yanxu jinta yake matar taj kawai, zatayi rashin mutunci kuwa.

“Na shigo dazu mummy tace bakiji dadi ba, how are you feel

ing now?”

Yatsune baki tayi tace “I’m okay” tana fadin haka ta maida airpod dinta ga kunnenta tare da daukan bowl din popcorn dake kan center table ta cigaba da cin abunta, laila data lura wani shasha mata kamshi take tayi saita Tashi kawai tayi fucewarta

.

Bangaren hadiza tana zaune, zaman jiran call din jamila kawai take, aiko sai gashi ta kira, cikin gaggawa ta daga wayar takai kunnenta.

“Ya ake ciki jamila”

Sauke ajiyar zuciya jamila tayi kamar wadda tayi doguwar tafiya tace “wallahi kinga faduwa

nayi a bandaki, na gurde saida akayi min gyaran hannu”

“Subhanallahi, garin yaya”

“Tsautsayi fa…allah ya rufa asiri ma ba gocewar kashi bane”

“Toh allah ya sawaqe, yanxu sai yaushe kenan zaki je wajen bokan?”

Ahanakli jamila ta furta shegiya, kanki ka

wai kika sani, hadiza bataji ba wannan yasa tace “hello”

“Ina jinki, hannun ne ya danyi min tsami, jibi idan na danji dama dama insha allah zanje”

“toh shiknan allah ya kaimu,”

Sallama sukayi jamila ta janyo kazar data sayo kashashiya ta yagi abarta ta

kora da lemo,”

Cije yatsa hadiza tayi, taso ace yau jamila taje wajen bokan nan anyi abunda akayi kawai wannan shegiyar yarinya ta karasa kowa ya huta, cikin yan kwanakin nan fargaba takeyi sosai.

The next day…

Yau ta kasance friday, Da asuba sabe

eha ta tashi, bayan tayi sallah tayi wanka tasa atamfa riga da skirt cikin kayan da aka bata, kayan sun dan kamata kadan ammafa sun mata kyau sosai ba kadan ba Masha Allah, hijab din sallarta ta dora akai sannan ta futo.

Backyard tabi zuwa ga part dinsh

i iska na kadata ta ko’ina saboda sanyin safiya, taba karasowa part din nashi ta danna pins din kofar sannan ta bude ta shiga.

Hasken fitilun kasan a kashe suke wanda yasa ta kukkunnasu don ta samu hasken yin gyara yanda ya kamata.

As usual vacuum ta k

unna ta soma vacuuming floor din parlor, saida ta gama tass ta dauko mop ta zuba mopping mist sannan ta fara mopping parlorn tana gamawa ta danyi yan goge goge, tana cikin goge gogen ta dago sama gave stairs take idanunta ya shiga cikin nashi dukda akwai t

azara tsakaninsu.

Yana sanye da pjs farare tass riga da wando,

Saurin warware hijab dinta tayi data nannade shi a kirjinta ta gyara tsayuwarta, tundata kunna vacuum dinan ya tashi.

Hannunshi yay mata nuni dashi alamun ta hauro sama, sannan ya juya ya k

oma ciki.

Saman ta soma hawa a natse tana isowa bakin dakin nasa ta dan dakata, knocking ta danyi daga ciki yace “come in”

Ta shugo a natse bakinta dauke da sallama, daga bakin kofar ta tsaya taki takowa zuwa ciki, saida ya juyo yana kallonta kafin yace

“ni zan fara gaisheki ne?”

“Good morning”

Bai amsa ta ba yace “fix the mess” ya karashe yana nuna mata beddings din dake a yamutse kamar anayi aiki akai.

Yana fadin haka ya wuce bathroom domin yayi wanka, ya dade sosai a bathroom din harta gama gyaran y

a futo daidai nan tana shirin futa ya dakatar da ita.

“Dauka min kayan da zansa” ya karashe yana zama gefen dresser, coily gashinsa yake kokarin drying don su bushe.

Badan ta soba haka ta shiga closet din tana kunkuni, yanxu ta ina zata fara nemo mashi w

ani kaya? Saita tuna da hakan da take mashi a saudi.

Bata tsaya wani zabe zabe ba ta zato wash kaftan riga da wando baqaqe ta fiddo su sannan ta futo daga closet din ta jera mashi kan gado, ta mirror yake hangota, har zuwa yanxu mamaki yake yanda ta dain

a mashi gardama duk abunda yace tayi yi takeyi shi kuma haya son haka, so yake ta dunga mashi stubborness dinann, abun yana sashi shiga shauqi.

“Zan sauka kasa”

Ta furta ahankali, juyowa yayi yana duban kayan dat aje mashi ganin babu innera yasashi cewa

“where are the inner?”

Ya kafeta da ido yau ko dan smirking dinnan bayayi, ya wani hade rai, kokarin pissing dinta off kawai yake.

Kamar tasan abunda yake shirin yi wanda batada energy din jayayya dashu as far as bazai fadama kowa abunda ke tsakaninsu ba

zata hkura tayi komai ta bishi yanda yake so.

Komawa tayi closet din ta fara budewa daya bayan dayan, yanda kaya suke a shaqe a cikin kowanne drawers da wardrop mamaki abun ke bata, dududu gaba daya ko shekara baiyi ba anan kasar.

Kuma ta lura kaftans s

unfi yawa da alamu ya fara sabawa dasu kodan suna mashi kyau sosai.

Tana cikin dube dube ta bude drawer inners dinshi, a jere farare kal, bata tsaya wani dogon tunani ba kawai ta zaro guda daya da vest sannan ta futo.

Tana futowa yanda ta barshi haka ta

taddashi zaune, ajiyewa tayi sannan tace “zan iya tafiya?”

“Zoki shafa min” da sauri ta dago ta kalleshi, ya basar kamar baiyi magana ba, “lallai ma, abun nashi ya fara yawa fa” ta fada aranta.

Dagowa yayi ya mata kallo daya wanda yake tafe da sakon ni d

aban daban.

Cije lebe kawai tayi ta nufi inda yake, yana kallonta cikin mirror yanayinta gaba daya ya sauya zuwa ga bcin rai amma bata da bakin magana.

Man ta dauka ta matsa a hannunta sannan ta mulka shi kafin ta dubeshi itama ta jikin mirror din tace “

ina za a shafa?”

“Ina ake shafa mai?” Ya maida mata martani kai tsaye, tayi saurin runtse idanunta hannunta na rawa ta dora shi kan farar fatar gadon bayansa sannan ta fara shafawa ahankali ahankali,kamar bata sonyi, tunda ya ji saukan hannunta akan skin

dinshi ya sauke ajiyar zuciya, ga sulbin man gana fatarshi abun saiya hadu biyu, tun tanayi ahanakli harta fara da sauri sauri don allah allah take ta koma cikin gida kar anty rabi ta tambayi dalilin dadewarta, yaci ace ta gama aiki ta koma.

Baimasan ta

cire hannunta ba ya shagala sai ji yayi tace na gama.

Juyowa yayi yana fuskantarta sannan ya mata nuni da kirjinshi da gashi ke kwance lub lub kamar na jariri, at that moment pashewa ne kawai batayi ba don takaici, so take kawai tace mashi bazata yi ba am

ma tana jin tsoron abunda zai biyo baya.

Wani irin malalcin signal ya mata da ido alamun other part din da bata shafa ba, ta hade rai sosai ta dan duka ta deba man ta shafa a hannunta sannan ta matso inda yake tsakankanin kafafunshi ta durkusa don yayi ka

sa da yawa sannan ta soma shafa mashi,wani irin jan nunfashi yayi har saida taji ya saukeshi akan fuskanta, itako ta cigaba da shafeshi yana sauke ajiyar zuciya, take idanunshi yayi jaa sosai kamar gauta, kujerar ma ji yay kamar bazata daukeshi ba kamar za

i fadi, ganin tana kasa kasa don batama san tanayi ba don cikin takaici takeyi badan batada farce bama data karkarceshi, yayi saurin kamo hannayenta biyu, ta kalleshi shima ya bude idanunshi da suke fire, muryanshi ta dishe yace “thats enough”

Yar kwafa t

ayi ta miqe tsaye ya zare hannunshi daya ya dauka oil ya miqa mata a hannunta, tana ganin oil din tasan na gashi ne, ta karba ta deba cikin sauri ta mulka sannan ta saka yatsunta cikin gashinsa, ta soma yamutsa kan nashi kamar tana mashi massage, baisan sa

nda ya sanya hannayenshi biyu ba a waist dinta ya janyota sosai, tuni ta dakata da abunda take jin fuskanshi wajen shafaffen cikinta, gaba dayansu sukayi shuru dagashi har ita, ya fara tunanin sanda ta mashi karyan tana da ciki, wallahi ya kaunaci cikin na

n dukda babu shi, kuma ya kwallafa rai akanshi, sai yaji dama da gaske akwai cikin, dama zai iya mata cikin ta haifa mashi babies.

“You’re warm” ya furta ahankali, “ waya baki idea din karyan ciki da kikace kina dashi kuma kikace ni na maki”

Dan baya ta

soma yi ya sake matsoda ita sannan yace “ya akayi ciki? Tell me how did we do it? Even though kinyi karyansa how did you predict anyi cikin? Did you come up with the idea?”

Tasan inda zancen sa ya dosa ita kuma bata son yi wannan maganar dashi, “please ka

sakeni time din school ya kusa”

Yi yayi kamar bai jita ba ya sake cewa, “should we give it a try for real?I mean the baby?”

Dam dam dam gabanta ya bada, itafa bata san irin wannan maganar tana shiga tsakaninsu, gaba daya saitaga taj dinma ya lalalce ya

zama wani dan iska iska

😂

Cikin sauri ta fuzge kanta tayi baya ko tsayawa kallonsa batayi ba ta fuce daga dakin da sauri.

Tana futa ya bita da kallo harta fuce kafin ya maida dubanshi ga kasanshi, “he can’t believe he’s arouse by her touching, which resu

lt him to feel erected lokaci guda, ba tun yanxu ba yasan cewa yarinyar ita kanta weakness point dinshi ce gaba daya.

Misalin wajen karfe 9 da yan mintuna ya futo cikin kayan data dauka mashi, maya ta bishi da mayen kallo, yana karasowa duk suka gaishes

a banda sabeeha datayi gumm, maya ta bita da harara, kuma ta lura da hakan arabta tace, “ai gaki gashi nan, ke kika damu da wani zaman gaba mteww”

bude masu mota yayi, sabeeha ta matsa daga wajen seat din baya, yana unlocking ta bude kofar sannan ta shige

, su laila suka bita da kallo.

Lallai ma nuna isar yarinyar nan yayi yawa, atunaninsu ko zaiyi magana don da kanshi yace ta dunga zama a gaba sai sukaga akasin haka, baima ce mata komai ba ya kyale, maya tace “chapdijan”

Laila ta dubeta tace “ki zauna ka

wai a gaban tunda daman nan kikafi so ya hanaki”

Haka dai suka shiga suka zauna kowa yayi shuru babu wanda yayi magana.

Saida sukayi nisa sosai kafin ya soma magana, “whats your course of your” yayi magana yana kallon maya, cikin rawar kai ta fada mashi

ya tambayeta cgp dinta tace mashi 2:1

Haka ya tambayi laila itama ta bashi amsa itama ya tambayeta nata cgp din tace mashi 2:2

Ya dubi fatima dake zaune, sai avoiding kallo shi take, “and you??”

Yayi magana a kausashe, tayi kamar batasan da ita yake ba,

saida laila tace “fatima dake ake fa”

Sai a lokacin ta dago tace 3:5, gaba dayansu juyowa sukayi suna kallonta banda maya laila tafi kowa mamaki, gaba dayansu duk tafisu kwakwalwa barema maya

😂

Maya dai abun ya mata yawa,ay saifa bakin cikinta yafi na

da, ta kara kullatar sabeeha.

Shiko taj saida ya bata words of encouragement, don she’s smart.

Maya akayi gumm, taj ko ya dubi inda take zaune yace “you need to work hard on your grades 2:1 is not a good one”

Wani irin embarrassment ne ya lulubeta, tayi

yaqe kawai har suka iso bata iya cewa komai ba duk rawar kan nan.

Suna sauka kowacce ta kama hanyarta bare sabeeha datayi gaba don sunada test.

Daga school dinsu bai tsaya ko’ina ba sai wajen da zasu hadu da wanda yasa ya mashi bincike akanta, gaban w

ajen yayi parking yana kallon gate din mataccen prison din,wayarshi ya daga ya kira mai yin binciken ya shaida mashi ya iso, sai gashi kuwa ya futo daga cikin wannan prison din ya shiga dashi, tunda ya shiga yake yatsinw fuskanshi, wari, bola, datti, ga gi

nin ya banbaro, kai komai ma akwai a wajen, prisoners din ma kamar mahaukata, gaba daya wajen dai sa a hankali.

Wani dan office mai kyan gani suka shiga inda ogan dake kula da wajen yasa aka kira wanda suke nema.

Wani dan sanda ne ya taho dashi wanda suk

e nema din gaba dayanshi ka ganshi kamar kwarangwal, ya bushe ya jeme.

Idanunshi daya ma kamar ya lalace don har wani fidda ruwan wari yakeyi.

Kallonshi investigotor din yayi bayan a zaunar dashi sannan yace “ya sunanka”

Ya fada masu, “sunana iliya”

H

oton sabeeha suka nuna mashi ya kalla ya sake kalla sukace “ka santa”

Yayi dariyar yan wii yace “tsakani da allah oga ina zanga wannan a rayiwar nan?”

Tsohon hotonta investigator din ya fidda sannan yace “wannan fa?”

Tuni kawu ya gano wa suke nufi ya ja

rbi hoton yace “kai wannan yar yayata ce ay, fati”

“Munsan dalilin kawoka da akayi nan saboda satar dakayi kuma baka biya kudin belli ba aka kawo ka nan ko?”

Girgiza kai yayi investigator din ya cigaba, “munyi maka alkawarin fitar dakai dagana indai zaka

bamu hadin kai”

Cikin sauri ya girgiza kai yace toh yallabai.

“Mecece alakarka da ita da mahaifiyarta? Sannan ina ne aka haifeta? Waye asalin mahaifinta.

Shuru ya danyi kafin yace “mahaifiyar babarta da babata uwarsu daya ubansu daya, ni kuma kawunta n

e, kuma a gaskia lokacin da inna ta dauko ni ta kawo ni nan habuja tun tana karama ne, nadai san babarta tayi aure anan habuja kuma anan aka haifeta, mahaifinta kuma dan taxi ne,shima garinmu daya dashi,”

“Ya alakar ta da mahaifiyarta take”

Rarraba ida

nu ya somayi yana taoron yin magana amma ganin yan sandan nan akanshi yasa shi cewa “ban gane ba yallabai?”

“Kasan me nake nufi karka bata min lokaci mana, ya alakarsu take?

“A gaskia nidai na taso naga yanda take tsangwamarta, kuma bata barinta tana fu

ta ko’ina, dan ko makaranta dakyar ta bari ta karasa primary,”

“A ganinka me zaisa tayi haka?ko ba yarta bace?”

Shuru kawu yayi yana nazarin yanda yarinyar ke shan wahala wajen hadiza, a gaskia kowa yaga haka zai rantse ba yarta bace.

“ nidai ban taba j

in wannan zancen ba, nadai san gaskia yanda ta taso ba haka kowa ya taso ba, don gaskia bata da gata”

Dan nunfasawa investigator yayi, duk wani bayanai da suke san sani sun kasa gano komai, daga kan inda aka haifeta ma.

“Kasan inda aka haifeta?”

“Eh ana

n habuja ne”

“Zaka iya fada mana wani asibiti ne?”

“Gaskia ban sani ba, kamar yanda na fada maku, tana da shekara biyar inna ta kawoni habuja, don lokacin danazo ma sun tashi daga tsohuwar anguwarsu inda aka haifeta,”

“Zaka iya fada mana inane taohuwar

anguwar?”

“Eyy a gwagwalada ne, cikin anguwar rodi”

Da dan wannan bayanan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login