Showing 9001 words to 12000 words out of 338813 words
duri ruwa, shima kanshi jamid din hankalinsa ba karamin tashi yayi ba, bazia iya motsawa ba gashi babu baki balle ya fada mata ta boye.
Sabeeha data tabbat
ar da muryar hidayar ce dai kunnenta ya jiyo mata hankalinta bai gama tashi ba saidata ji takun tafiya wajen kofar shugowa bedroom din, tabbas idan hidaya ta ganta anan alwai matsala, gashi bata samu ta tambayi jamid maganar file din da tareeq yace mata ta
tambayeshi ba, rarraba idanu ta dunga yi Har idanunta ya sauka wajen curtains cikin hanzari ta saki hannun jamid ta karasa wajen ta shige cikin curtains din tana shigewa jamid ya sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya dukda gabansa na faduwa, shi kanshi bazaiso
hidaya ta ganta anan ba, daidai nan hidaya ta shiga part din rai a bace,gaba daya kana ganinta zakasan bata cikin natsuwa, tana karasowa tsakiyar dakin ta kalli bangaren jamid dayayi saurin rufe idanunshi, kallon dakin ta somayi ganin nurse din dake kula
dashi bata nan, saukan ruwan dataji daga bathroom yasa ta cewe “ke!!! Step out this instant”
Tuni cikin sabeeha ya duri ruwa, babu abunda kirjinta keyi sai bugu, harta daga kafarta dake rawa zata futo tayi saurin dakatawa jin abunda hidayar ta fada, “akwa
i wanda ya shugo nan dakin ne?”
“No madam” nurse din data futo daga bathroom ta amsa hidayar,
“Ya akayi kofar entrance din shugowa ya kasance a bude?baki iya aikinki bane yanda ya kamata?”
“I’m sorry ma’am, na manta ne ban rufe ba”
“Are you insance?th
is will be my first and last warning,idan bana gidan nan karki sake kibar kofar nan a bude sannan karki sake kibar kowa ya shugo part din nan har sai na dawo understood?!!!” Hidaya ta daka mata tsawa.
Jiki na bari nurse din ta amsa ta “yes ma’am kafin tay
i gaggawar fucewa daga dakin.
sabeeha dake tsaye duk ta tsure,, duk a tunaninta ta dauka ta hangota ne cikin curtain din saidata ji maganar da sukayi da nurse yasa ta sauke ajiyar zuciya.
Nurse na futa hidaya ta karaso inda jamid ke kwance,kamar kullum
yauma rufe idanunshi yayi, ta lura da hakan da yakeyi, ko zata kwana tana magana bazai bide ido ba balle ya kalleta koya bude ma tsantsar kiyayyar da yake mata take hango wa cikin idanunshi, ita wannan bama damuwarta bane don qiyayyarsa bazata hanata yin
abunda ta kudirci yi ba,duk threat din datake mashi yaqi bayyana mata inda file din yake,tasan shi da taurin
kai sosai, kuma tasan bazai fada mata cikin sauqi ba shiyasa ta dage da manipulating dinshi da maganin da take bama taj, tana nan tsaye akanshi ta
soma magana “nasan idanunka biyu jamid, kuma nasan kana saurarona,”
Tsagaitawa tayi ta ajiye jakarta wajen gefen kafarsa tare da zagayowa saitin fuskarsa tace “let me remind you,yau kwana sha biyar kwayar fentaly na dawainiya a sassan jikinsa, karkayi tun
anin guda daya nake bashi, nop guda hudu yanda zata nakasashi, idan kace zakayi taurin kai jamid kai kasan na fika taurin kai,kasan illarta idan akayi abusing dinta, kashe garkuwar jiki take, kaf duniya babu kwayar dake illata gangar jiki da kwakwalwa kama
r ta, kanada damar protecting dinshi yanda ka saba kafin lokaci ya kure, ahankali ahanakli zai fara loosing kanshi, the next thing shine za ayi tunanin ko yayi hauka ne, in few days kuma labari zai sauya you just have to tell me inda file din nan yake, kan
a fadamin zan dakata daga bashi kwayar nan, in ka cigaba da acting kamar bakasan abunda nake fada ba i have no choice but to let him suffer miserably more
Yana jin abunda ta furta yayi saurin bude idanunshi, ganin haka yasa ta murmusa tare da shafa gefe
n fuskanshi tace “now tell me, ina file dinnan? Ina kakai file din?Meysa babu komai a cikin wanda agent dinnan ya baka? And whos that agent? How can i get him”
Yanda ta kura mashi idanu haka shima ya kura mata, ganin yana motsa bakinsa yasa ta matso da ku
nenta saitin fuskarsa, sabeeha dake labe sai faman zufa take baiwar Allah, fitsari ne kawai batayi ba a wajen tsabar rudanin data shiga, sai hawaye dake zarya a fuskarta badan ta toshe bakinta ba da tuni ta fallasa kanta, ta tsakankanin labulen take peepin
g tana hango su, jamid dayake ankare da ita yaji dadi, koba komai yanxu ya danji sanyi aranshi maganar dayake yayi ma sabeehar akan maganin da hidaya ke bama taj yanxu taji da kunenta kuma yana fatan zata kare taj din daga sharrin hidayar, dan yatsar ya ju
ya tare da mata nuni da kofa, da kyar ta gane abunda yake nufi don haka tayi saurin futowa ahankali har zuwa lokacin hannunshi na toshe wajen bakinta, yana ganin ta futo ya maida subansa ga hidaya dake kokarin kallon inda yake kallo, yayi saurin shammatart
a ya soma magana da kyar yanda dagashi sai ita ne zasushi, wannan ya bama sabeeha damar bude kofar ahankali ta fuce daga cikin dakin da hanzari,
Hidaya data gama sauraron abunda ya fada yanayin fuskarta ya tabbatar min da ba abunda taso taji kenan ba,g
anin hes trying her patience yasa tace
“You are making things tough for all of us,ka zabi kaga karshena ko? mu zuba mu gani.”
Sabeeha sai ikon allah ne kawai ya kawota part dinsu, tana shugowa ta tsugunna bakin kofar kirjinta na dukan uku, ta dad
e sosai tana kuka sosai, dagowar da zatayi idanunta ya sauka ga activity room dining dake gefen dakin su, kofar data gani a bude ya tabbatar mata yana cikin don haka tayi saurin miqewa ta shuge ciki, a zaune ta taddashi ya nade kafafunshi ya kankame jikins
hi, cikin saurin ta karaso inda yake batayi wata wata ba ta rungumeshi a jikinta tana ambatin allah, sun dade sosai a haka kafin ta danji sauqin abunda take ji ta dago tana mai fuskantarshi, sai yanxu komai yake dawo mata rai, ta fara tunanin komai, tabbas
shugowar hidaya part dinsu bada alkagiri bane don sai da daddare take
zuwa kuma da zarar tazo tana tafiya sai yanayinsa ya sauya, kwata kwata bata kawo cewa magani take bashi ba, sai taji ta tsani kanta for not protecting dinshi yanda ya kamata kuka ta ka
sa gane cewa cutar dashi hidayar keyi, inta tuna da yanxu bashi da kowa face ita sai taji zuciyarta na karaya sosai, dole she needs to be strong for him, kuma ko mai zai faru bazata bari ya sake shan kwayar nan ba akan idanunta bazata taba bari a cutar da
shi ba koda zai kawo karahen nunfashinta, alkawarin datayi ma kanta kenan.
Taimaka mashi tayi ya miqe suka wuce daki, bata taaya dashi ko’ina ba aai bathroom, ta tara ruwa a bathtub, cire kunya tayi gaba daya da kanta ta taimaka mashi ta rage mashi kaya
n jikinsa ya rage dagashi sai shorts tayi mashi wanka sannan suka futo suna fitowa ta zaunar dashi anan dakin, kayansa ma ita ta taimaka mashi ya saka, yana sawa ta futa ta yanko maahi fruit ta kawo mashi, babu yanda batayi ba yaqi karba haka ta hakura ta
dauro alwala tayi sallah tana mai yi mashi addua.
Wajen karfe tara daidai hidaya ta tunkari part dinsu,kai tsaye ta shugo yanda ta saba,sabeeha na zaune da hijab dinta tana lazimi shi kuma yana kan gado ya kurama bango ido, sabeeha na ganin shugowarta t
ayi saurin rufe idanu kamar mai barci, ko kallab inda take hidaya batayi ba ta nufi inda yake ta dauko kwayar nan har hudu ta miqa mashi, jikinsa har tsuma yake wajen karba, sabeeha na kallon su ta kasan idanu, a zuciyarta babu irin tsinuwar da batayi ma h
idayar ba, harta miqe ta fuce, tana futa sabeeha tayi saurin miqewa ta zare hijab din jikinta ta wuce bathroom, wani katon bowl ta dauko ta fito dashi a hannunta ta tunkari inda yake jikinsa harya wani saki idanunshi sunyi jaa sosai, sai taji zuciyarta ta
karaya ganinshi haka abun tausayi, tattara kuzarinta tayi tana mai kallonshi tace “wallahi bazan bari a cutar dakai ba, azzalumai marasa imani kawai”
Tana karashewa ta dagoshi zaune, gaba daya yayi wani irin laushi soaai kuma effect din maganin ne da zara
r yasha yake zama weak, kusa dashi ta zauna tana fuskantarsa batayi wata wata ba ta tura dan siririn yatsanta dogo chan cikin maqogoronshi, saida ta tabbatar ta tura chan ciki wajen maqoshinsa, nan da nan ya soma kakarin amai kan kace me tass ya amayar da
magungunan gaba dayan su guda hudu, yana gama amayar dasu wani aman ya sake tunkuduwa, haka ya dunga amayar da wani koren ruwa, shafa mashi bayanshi ta dunga yi sosai harya lafa mashi, ita da kanta ta gyara wajen ta killace tass sannan ta gyara mashi kwanc
iyarsa ta luluba mashi duvet dunshi,ta kwanta gefensa yau ko kasan ma batabi takai ba.
Washe gari da safe ita ta masu breakfast, ba laifi yau ya tashi da kuzarinsa sosai, yaci kuma ya koshi ita ta taimaka mashi yayi wanka ma, hankalinta ba karamin kwnaciy
a yayi ba ganinshi yau da kuzarinshi sosai, har samu kanta tayi da browsing yanda ake kula da masu irin rashin lpy sa amnesia.
Wajen karfe sha daya ta sauko kasan a daidai lokacin ta tabbatar babu kowa a gidan don haka ta fuce ta zagaya wajen data hadu da
mutallib jiya, ta dade sosai a taaye ko zata ganshi allah bai bata ikon ganinshi ba haka ta hakura ta koma cikin gida.
Tareeq kuwa yana ankare da ita,dukda hes confuse akan maganganun datayi da mutallib amma maganar file din nan dayaji sunyi yasashi dasa
question mark,tambayar daya dunga ma kanshi shine menene a cikin file din?kuma file din na menene, bashida amsar tambayoyin nan don haka yabar zancen
aranshi saidai yayi alkawarin saiya gano komai, don yayi amfani da wannan damar wajen samu abunda yake so
a wajenta.
Jiki a mace ta hau sama tana tunanin yanda za ayi taga wannan mutalib din, yabxu shi kadaine zata iya trusting kuma zatayi kokarin wajen karbo mashi abunda ya buqata wajen jamid wanda tayi imani shi zai kawo karshen wannan azzalumar.
Haka t
a wuni sukuku tana nazari,dare nayi hidaya ta sake dawowa, da gangan sabeeha ta shige bathroom daidai lokacin, saida ta tabbatar hidaya ta futa ta fito, yauma abunda tayi mahsi jiya shi ta sakeyi, saida ya amayar tass, yau yama fi jin jiki sosai don harda
jini, abunde sai Allah.
Har yayi barci tana daga zaune tana tunanin rayuwar datayi a cikin gidannan,daga ranar data sako kafarta a gidannnan zata iya rantsuwa babu ranar da taj yayi cikin kwanciyar hankali, masifar yau daban ta gobe daban, ko amnesia da y
ake fama dashi aka barshi dashi kadai ya ishesa, amma dan rashin imani da bin rudun duniya da rufewar ido wajen neman power da zalunci yasa suke wulaqanta rayuwarshi, wata sakayyar sai a lahira har yanxu ta kasa gane dalilin da zaisa yan uwanka jininka su
taaneka haka kawai, tunawa da wannan kadai yana sata jin wani iri tare da tausaya masa, “allah ubangiji ya tsareka ya kareka daga sharrin azzaluman nan
😭
insha Allah karshensu bazaiyi kyau ba”
Ta karashe tana shafa kanshi batama san sanda barci ya dauke ta
ba kusa dashi.
The next day…
Tun da safe yau ta farka tana gyara kayanta dake cikin drawer,tana cikin gyaran nan cikin ikon allah taga wannan wayar data zo da ita gidan a matsayin yar leken asiri,tun ranar da jamid ya bata ta jefata cikin drawwr tama
manta da wayar gaba daya, cikin sauri ta kunna wayar,wajen call log ta shiga, number daya ce a wajen wadda take tunanin ta mutallb dince, tana kokarin dannawa saiga kira ya shugo, tayi mamaki sosai ganin kira kamar jira ake, cikin hanzari ta daga call din,
tare da kaiwa kunenta, muryarshi ce kuwa bayyane “fatima!!!”
Ya kira sunanta, cikin sauri ta amsa ta dora da “inason ganinka don allah,you are the only person i can trust,“
“Ina neman hadin kanki, dole mu samu kusanci da jamid don na karba file din da
na bashi, shi kadai ne zai iya kubutar da ku daga sharrin hidaya”
“Ka fada min koma menene zanyi”
“Inason ki samu jamid cikin sirri, i know its very risky but you have to, im running out if time, don nemana sukeyi, we need to get the file as soon as poss
ible ta hanyar nan ne kadai zan iya kubutar daku”
“Toh!!”
“Lets meet inda muka hadu ranar, please fatima karki bari file dinnan yabar hannunki, rayuwar taj is on it please”
Duk yanda akayi sabeeha taso ta shiga part din hidaya ya gagara saboda nurse d
innan, don tasan tabbas idan nurse dinnan ta kamata dole zata fadama hidaya, haka ta dunga kokari amma abun ya gagara.
Cikin ikon allah da yamma ta futo daidai nan nurse din itama ta futo daga part din ta sauka kasa wannan ya bama sabeeha damar shiga part
din cikin gaggawa, tana shiga cikin ikon allah ta tadda jamid din idanunshi biyu, bata taaya bata lokaci ba ta mashi bayanin da mutallib ya fada mata,
sauraronta yayi cikin natsowa sosai kafin ya mata alamu da kanshi cewa file din baya wajen, take hankali
nta ya tashi tace “uncle ina yake?”
Nan ma ya sake girgiza mata kai,jiki a mace ta futo daga part din gudun kar nurse din ta dawo ta sameta,
Rufun asirin allah ne yasa bata kamata ba don tana futowa yayi daidai da dawowar nurse din.
Kasa sabeeha ta sa
uka ta nufi inda yace mata zasu hadu, tana zuwa taga baya wajen har zata juya taji an jawo hannayenta zuwa wani sakon wajen garden din, saida ta tabbatar shine hankalinta ya dan kwanta da har taji tsoro,
“Kin sameshi?” Ita ce tambayar daya fara yi mata y
ana mai miqa mata hannunshi don ta bashi file din, jiki a mace ta sauke kanta kasa tace “babu!!”
Dam yaji gabanshi ya fadi, “babu kuma?” Ya sake tambayarta
“Baya wajen shi!”
Baya ya danyi tare da kama kanshi yace “shit, how? Kin tabbatar?”
Girgiza mash
i kai ta sakeyi, “innalillahi wa inna ialaihi rajiu’”
“Ya zamuyi kenan?” Sabeeha ta tambayeshi a rude, “banajin akwai abunda zamu iyayi, shi kadaine file din dake dauke da duk wani evidence din daya shafi accident din taj, da laifukan da hidaya tayi,guda
biyu ne kawai daman wannan ne last copy daya rage original din yana wajen khaal gashi ya rasu”
“Innalillahi wa inna ialaihi rajiun, dan allah ka taimaki wannan bawan allah, wallahi banajin zata barshi a haka, wallahi zata kasheshi, kullum wani magani take
bashi dukda ina kokari wajen ganin ya amayar dashi saidai ina taoron abunda zai buyo baya saboda wanda yasha a jikinsa yana nan kuma yabi jikinsa, haryau yaqi dawowa daidai, baya magana kwata kwata, dan allah ka taimaka”
“Magani? Wani irin magani?” Ya ta
mbayeta
“Ni bansan maganin ba amma naji a ranar
danaje ganin jamid na labe batasan ina dakin ba naji tana fada mashi cewa maganin yanada illa sosai kuma idan bai fada mata inda file…”
Dan dakatawa tayi tunawa da maganganun da hidayar tayi da jamid, c
ikin hanzari ta kalli mutalib shima kallonta yake yana neman karin bayani,
“File? Tabbas naji ranar hidaya na tambayar jamid ya fada mata inda file yake har tana cewa ina yakai file din meysa wanda agent dinnan ya bashi babu komi a ciki? idan bai fada ma
ta zata illata taj, kuma da alamun yanda take fada mashi kamar neman file din takeyi ta kasa smau shiyasa take amfani da taj ta hanyar bashi maganin da zai illatar dashi don jamid ya fada inda file din yake aaboda tasan ta hanyar nan ne kadai zai fada mata
inda yake”
“Idan na fuskanci bayaninki yanxu it means file din yana hannunta kenan amma bata samu komi a ciki ba?”
“Eh tabbas har tana tambayarsa maysa babu komi a cikin file din? Ina tunanin tana zargin ko ya sauya ma file din waje ne “
Shuru muta
bvlib yayi yana nazarin kalamanta, “tabbas akwai evidence a cikin drive din daya bama jamid kuma shi kadai ne copy din da yayi saura, to amma ya akayi ya bace?Duk yanda akayi akwai wanda ya sauya drive din kenan? Ko aka goge evidence din dake ciki, hidaya
ce kawai zatayi haka amma idan har ta samu file din kuma idan itace ta goge bazata tambayi jamid inda yake ba, duk yanda akayi akwai wata a kasa, there’s always a
third party indai goge wa akayi to akwai wanda ke kokarin taimakawa hidayar wajen rufe duk mu
gayen ayyukanta, indai kuma wani ne ya dauke to basu kadaine against her ba, theres someone seeking for her downfall as well kenan”
Yana cikin nazarin nan sabeeha ta katseshi, “toh yanxu ya zamuyi kenan? Kace guda biyu ne kawai, na wajen khaal bakasan ind
a yakeba?tunda tare kuke aiki, bazaka iya tunawa ba maybe ya fada maka inda ya ajiye na wajenshi?”
“Banajin…”
Inuwar daya gani ne yasa ya dakata, kallon inda yake kallo tayi,har zatayi magana ya katseta “shii, theres someone”
Take taji wani damm a kir
jinta, nuni yayi mata da dayar hanyar dazai sadata da bari wajen shi kuka ya nufi wajen dayaga inuwar, yana zuwa yaga wayam babu kowa, instinct dinshi ya bashi cewa da akwai mutun a wajen kuma yaga inuwa a wajen,
Tareeq dake rakube daga chan dayan sa
kon, hannunshi na rike da wayarsa ya dauki hoton sabeehar da mutalib din, this time around for the second time kuma yaji gaba daya discussion dinsu, sai ayanxu komai ya warware masa ya gano inda zancen su ya dosa harda maganar file da suka dunga yi, shi a
wajenshi wannan babban makami ne,zaiyi amfani da wannan donya samu abunda yakeso don yasan hidaya will be