Showing 1 words to 3000 words out of 150519 words
*MANNUBIYA*
*01*
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM.
Kano, Shekarar alif dubu
ɗ
aya da
ɗ
ari tara da casa’in….(1990)
A gefen titi sannan a hankali ya ke tuƙin motar tasa k’irar ‘Daewo Nubira’ tamkar ba ya son ƙarasawa inda ya tasarma zuwa ne.
‘Sannu-sannu bata hana zuwa’
In ji Mallan Bahaushe dan a hakan ya samu ya ƙarasa gidansa wanda ya ke a Unguwar shara
ɗ
a. Ko da ya ƙarasa bakin gate na gidan bai yi horn ba. Alamun tsayuwar Mota da mai gadin gidan ya ji a ƙofar gidan ne ya sanya ya leƙo wa
nda ganin Mai gidan nashi ya na jira ya sanya ya koma da sauri ya wangale gate na Madaidaicin flat house
ɗ
in.
Ko da ya shiga ya ƙarasa ya yi parking, kashe Motar kawai ya yi ya
ɗ
aura kanshi a jikin sitiyarin Motar ba tare da ya fito daga cikinta ba.
Ya
fi mintuna talatin a haka ya na tunani shi ka
ɗ
ai kafin tashi
ɗ
aya gabanshi ya yanke ya fa
ɗ
i! Ranshi ya sake
ɓ
aci!
Sakamokon jin fitowar ta da ya yi dan ko ba’a gaya masa ba ya riga da ya san ‘Khadijah’ ce, kasancewar
ba su da mai aiki, a gidan daga shi sa
i ita sai mai gadi wanda shi ke yi musu har wankin kayansu da guga.
Shiruu, kawai ya yi ya na jin ta ta rufo ƙofar parlourn tukunna ta tunkaro Motar da ya ke ciki a zaune.
Kamar yadda ya zata, ta na zuwa da rashin mutunci ta soma ta inda ta bu
ɗ
e ƙofar M
otar da ƙarfi kamar ta iso filin daga, sannan ko sannu da zuwa ba ta yi masa ba, cikin fushi ta soma da cewa “shine sai da ka kira Abba ko?” Ba ta jira ya bata amsa ba ta
ɗ
aura da “ashe cin fuska da
rashin adalcin da ka kusan aikatawa bai isheka ba kenan?
tunda gashi har an kashe magana an gyara komai amma ka
ɗ
auki waya ka kira Abba, me kenan kake so
yanzu? So ka ke ya goya maka baya ko me?”
Bata jira jan numfashi ba a hassale ta
ɗ
aura da cewa
“Tou bari ka ji, ko da ace Abba ya goya maka baya akan abind
a kake so ni ba zan bari hakan ta ta
ɓ
a faruwa ba wallahi…
Zan baka mamaki dan in ka na tutiyar ka na da Abba (zai tsaya maka) to nima ina Daddy (yana bayana)”
Ta ƙarashe maganar tata cikin tsananin bacin rai da takaici.
Tun lokacin da ta iso ta fara magan
a shima ya ha
ɗ
e rai,
Fuskar nan tamau kamar bai ta
ɓ
a dariya ba.
Ba tare da ya kalle ta ba
ya zare key
ɗ
in Motar ya
ɗ
auki abubuwan buƙatar shi tukunna ya fito daga cikin Motar.
Ko kallon inda ta ke bai yi ba
ya fara ƙoƙarin wuceta.
Da
ɗ
an ƙarfi sannan da
sauri
ta riƙo Hannunsa!
Cikin tsananin bacin rai ta ce
“IMAM ,Wallahi na fi ƙarfin ka wulaƙanta ni, ai so ba hauka bane ba, bar ganin wai Ina sonka
wallahi idan har ba ka janye maganar nan ba to zan yi maka abinda sai ka yi da ka sanin ha
ɗ
uwa ma da it
a kanta ‘Khadijar’, zan baka mamaki, zan sanyaka ……..”
“Sannu Uwarsa”
Su ka ji Muryar Abba daga sama
dan sam ba su san lokacin da ya shigo ba ma.
Tabbas, ta sha jinin Jikinta amman dukda hakan
kishi da baƙin cikin da ya ke kwance a kan kyakkyawar fara
r Fuskarta bai kau ba sannan Zuciyarta in banda turniƙi da tafarfasa ba abunda ta ke yi.
Ganin yadda har zuwa wannan lokacin Abban ya kafeta da Idanuwa yana mai ƙarasawa zuwa inda suke ne ya sanya ta
ɗ
an sunkuyar da kanta ƙasa da sauri, kafin kuma ta cik
awa
Imam
ɗ
in Hannu.
Abban yana ƙarasawa
Imam ya durƙusa har ƙasa ya gaida shi, bayan sun gaisa ya
ɗ
aura da cewa
“Abba ai da ka bari mun ƙaraso,
dan yanzu dama na ke shirin in yi wanka mu karaso wajen naka.”
“kada ka damu, ai
babu nisa, kuma Ina buƙata
r yin tattakin nima”
Haka kawai Abban ya ce ya na kallon Khadijah wadda ta ke gaishe shi da “ina wuni”
Cikin
ɗ
an russunawa.
Bai amsata ba, ya juya ya bi bayan Imam wanda ya juya ya nufi ƙofar parlourn nasu da
ɗ
an sauri yana ce wa “Bismillah Abba.”
Bayan
sun shiga ciki, Abban ya zauna, Imam
ɗ
in ne da kansa ya shiga kitchen ya kawo masa lemo mai sanyi da ruwa sai snacks a gefe, dan Khadija ba ta riga ta shiga parlourn ba ta na waje ta na ta faman lissafe-lissafe, hankalinta chaa ya tashi dan tabbas
a yadd
a ta ga Abba a wannan lokacin ta san ba zai bi bayan ta ba!
Sannan ba
ɗ
aga mata ƙafa
zai yi ba, gashi ta san Abban nasu in ya ƙule sam ba ya tolerating nonsense da tirjiya…
‘Za ta iya cewa ba ta ta
ɓ
a ganin soyayyar ƴa da uba mai zafi kala ta Abban da sis
ter
ɗ
inta ba amman tunda sistern nata ta yi masa laifi ya fita harkarta shikenan ya yafe ta
har gobe ita kanta ba ma ta san inda ƴaruwar tata take ba.’
Shiyasa hankalinta ya ke a tashi maƙura, har ba ta san lokacin da ta soma kuka ba. Tsoronta
ɗ
aya kar y
a goyawa Imam baya kuma ya kafe akan itama sai ta bi ta yarda da abunda Imam
ɗ
in ya ke so
dan in dai hakan ta faru
tou wallahi ta shiga ukun ta.
Ita kanta ta san ta na da tsananin kishin da ko da ace ba Imam ta aura ba to fa ba ta jin za ta iya zama da
kishiya, ballantana
kuma Imam
ɗ
in ne, Mutumin da ta ke da tabbacin a yadda ta ke masifar sonshi tabbas ba za ta ta
ɓ
a
iya jurar ganin wata ƴa Mace a matsayin Matarsa ba, bayan ita babu kowa kawai, sannan da
ɗ
in
ɗ
a
ɗ
awa kishiyar ma ace wai ‘Khadija’
Yarinyar
da ta san ya ba tsananin so da ƙauna!
Ko satin da ya wuce haka nan ya fito ƙiri-ƙiri
ya ce mata ‘albarkacin sunan su ya zo
ɗ
aya ita da Khadijarsa ne ya sanya ya ke yi mata raha sannan
ya ke
ɗ
an kulata.’
…….
Ta san rashin shigarta a kan lokaci
zai iya sa
ke hasssala Abba, dan haka ta yi ƙoƙari da kyar ta iya tsayar da kukan nata, ta
goge hawayenta, tukunnan
ta nufi parlour itama.
Abba ya na zaune a kan kujera
Imam a gefen shi, zaune a ƙasa
A haka ta shiga ta samesu,
dan haka itama ta ƙarasa ta zauna
a ƙasa ta
ɗ
ayan gefen ƙafar Abban.
Ba tare da ya kalleta ba, Abban ya ce
‘’Sai yanzu ki ka ga daman shigowa kenan “
Bai bata damar cewa komai ba
ya
ɗ
aura da cewa
‘’Inaso ki nutsu ki ji abunda zan fada miki yanzu….
Na farko shawarace!
Na biyu ma kama
r shawarar ta ke!
Sai na uku kuma umarnine daga gareni wanda ya zame miki
dole ki ji, sannan ki yi.”
Still bai
ɗ
au lokaci ba ya
ɗ
aura da cewa
‘’Idan Mata uku Imam ya ce zai ƙaro to baki da hurumin shiga cikin lamarin da zummar hanawa”
‘’Ki zauna a matsa
yin ki
sannan ki yi wa Mijinki biyayya, ki kuma bashi goyon baya.
Ni ma a matsayina na Mahaifinki
ki yi mini biyyayya ki yi abunda na ce.
Sai da ya jaa numfashi ya sauƙe tukunna ya ce
‘’Khadijah”
Wanda hakan ya sanya ta ji gabanta ya yanke ya sake fa
ɗ
uwa
, ba ta kai ga dawowa dai-dai ba Abban ya
ɗ
aura da cewa
“Imam zai ƙara aure!
Ba na son in ji wata matsala ta kuma kunno kai daga gareki daga yau har a yi auren nan a gama
Idan ba haka ba kuma wallahi …..’’
Kukan da ta rushe musu da shi tamkar ana yankat
a ne ya sanya duk su ka zuba mata ido kawai, su na kallon ikon Allah.
Cikin kukan ta ce “Haba Abba,
ko fa wata na biyu ban gama rufawa a cikin gidan nan ba amma
ace za a yi mini kishiya!
Kuma ku ce in yi haƙuri in yi shiru?.
Shi mai ya sa ba zai yi haƙur
in ba, mai ya sa ba zai haƙura ba?.
Daddy fa ya ce bai yarda ba, ya ce ba ya ma son ya sake jin maganar. “
Cikin katse ta Abban ya ce
‘’A lokacin da Daddyn bai san cewa ita wachchar Khadijar Imam ya fara so ba kenan…a lokacin da bai san itace budurwarsa
tun asalin farko ba…
Bari ki ji abunda ba ki sani ba, tun kafin shi Daddyn ya fara maganarku Ke da Imam, tun a lokacin shi Imam ya yi mini maganar Khadija!.
Maganar aurenku ke da shi ce ta sanya ya
ɗ
aga ƙafa dan haka yanzu banga dalilin da zai sanya ya fas
a aurenta saboda ke a karo na biyu ba wallahi”
Cikin kuka ta ce
‘’Abba har fa ciki ta zubar, kuma
tsabar cin fuska har gidan nan ya kawo mini ita, lokacin ko sati biyu ban yi ba, a chan boys quarters
ɗ
in aka yi jinyar ta!
Saboda bata da kowa.
Fisabilil
lahi ta ya za a ha
ɗ
a ni kishi da wadda ta gama shigo mini gida ta san sirrina, wadda batta da iyaye,
mai yawo a titi suna tallan Nono
…..’’
‘’Ya Isa haka, Khadijah”!.
Abban ya daka mata tsawa cikin tarar numfashinta.
Kafin ya ce
‘’Tashi ki tafi ki ban
i guri‘’
Za ta yi magana ya kuma daka mata wata uwar tsawar dan haka ta miƙe ta wuce zuwa
ɗ
aki tana wani irin kuka.
Ko da ta shiga
ɗ
akin ma
ta jima ta na kukan, kafin daga karshe ta yanke shawarar neman
‘Larai’.
Saboda ta lura hatta Mahaifiyarta ita m
a bayan Abban ta ke bi….
Iyayenta su na da matukar kawaici da kara, duk an san Imam ba ya son ta!
Biyayya ce ta sanya ya aureta,
shiyasa su kuma iyayen nata ba za su ta
ɓ
a goyon bayan ta ba
saboda gudun kar su shiga hakƙinsa..kuma sosai su ke gudun dasa ma
tsala tsakaninsu da ‘Family friends’
ɗ
in nasu, shiyasa duk wani abun da zai bu
ɗ
e wannan ƙofar ba sa ƙaunarsa sam.
Dan haka ta ga gwara ta nemawa kanta mafita!
Tun kafin kawaicin Fulanin Iyayenta ya cutar da ita.
A nata lissafin….
kamata ya yi a ce an bar
ta da Imam ta juyo da hankalinshi zuwa gareta, tunda an san bai son ta, ba wai
a ha
ɗ
ata kishi da wata chan daban wadda za ta zo ta lalata komai ta kuma janye mata hankalin masoyi ba….
A chan parlour kuwa, Khadijah ta na shigewa ciki,
Abba ya
ɗ
an gyara z
ama ya kalli Imam kafin ya ce
‘’Na ji Khadijah ta fa
ɗ
i wani abu akan Khadijar da kake son ka auro wanda ni ban san da shi ba!
Ina fatan za ka ce mini ba dai-dai bane ba.”
Lumshe idanu Imam ya yi,
kafin ya yi amfani da tafin Hannunsa wajen shafa farar F
uskarshi wadda ta yi jaa zuwa wannan lokacin tsabar tashin hankali….
Abba ne ka
ɗ
ai hope
ɗ
insa..ya san kuma shi ka
ɗ
ai zai iya juyo da hankalin su Daddy a samu su barshi ya auri Khadija.
Abunda ya ke ta tsoro dama shine
kar su san ƙaddarar da ta afka wa Kha
dijan dan ya san muddin su ka sani to da wuya Abban shima ya yarda….
‘’Imam, ka yi shiru”
Muryar Abba ta katse masa lissafi.
A hankali ya sauƙe numfashi tukunna cikin sanyin jiki ya soma magana
‘’am Abba…
Kamar yadda na gaya maka
Khadija ba ta da kowa, i
ta da ƴar uwarta marayu za a ce musu kai tsaye, na santa ne a silar kawo mana Nono office da su ke yi talla daga ita sai ƴar uwarta na sani danginta sai kuma wani Kawunta
da ta ta
ɓ
a ha
ɗ
ani da shi, wabda su ke zaune a gidansa.
A halin yanzu shima ya rasu
kuma dama
Matar tashi azabtar da su ta ke yi,
tun a lokacin da ya ke a raye ma.
Shiyasa ya na rasuwa ta tattara ta barsu ta yi gaba, su sun ce mini Uncle
ɗ
in nasu da Mahaifinsu kawai su ka sani…
Ba su ta
ɓ
a zuwa garinsu ba, bama su san garin ba har Mahai
fin nasu ya rasu. To kuma su na saka ran zuwa da shi kawun nashi shima sai Allah ya yi masa rasuwa.
Shiyasa tun a lokacin na so in auri Khadijar saboda itama ƴaruwarta Miji ya fito mata ta auri wani mai mata uku da ƴaƴa ashirin a layin nasu amman ya ce ba
zai riƙe Khadijah ba.
Na san zaman ta ita ka
ɗ
ai akwai ha
ɗ
ari!
Shi kuma Daddy ya dage akan duk uzuri na ya jira, ko ma menene ya jira har a yi auren mu da Khadija tunda an riga an gama magana.
Ko uzurin nawa bai tsaya ya ji ba, gani kawai ya ke kamar tur
jiya na ke shirin yi masa, shiyasa na haƙura
a wannan lokacin kamar yadda ka buƙaci in yi haƙurin.
Itama ba yadda ban yi da ita akan ta biyo ni ba amman ta ce za ta iya zama ita ka
ɗ
ai!
Ni kuma abubuwa sun sha mini Kai
a wannan lokacin
ga hidimar biki!
G
a aiki!
To a wannan tsa-kan-ka-nin ne aka samu wani Marar Imani ya je ya yi mata fya
ɗ
e!”
Sai da ya
ɗ
an yi shiruu, zafin abun ya na ratsashi tukunna ya
ɗ
aura da cewa
“Sam ba laifinta bane ba Abba.
Dan sai da ma ta yi kwanaki biyu a asibiti ba tare da ta sa
n inda kanta yake ba ma.
Tun daga lokacin ni kuma sai na ƙi amincewa ta ci gaba da zama a gidan ita ka
ɗ
ai….
Laifina
ɗ
aya shine da na kawota nan
ɗ
in!
Na san bai kamata in kawota nan ba tunda gidan aure na ne!
Amman kuma banida wata mafitar,
tunda su Dad
dy ba za su bari in kai musu ita chan ba tare da sun san wacece ita ba!
Gashi cikin da ta samu ata dalilin ƙaddarar da ta afka mata
ya zo da matsala!
Ana yin sati biyu ta fara bleeding muna zuwa asibiti kuma ya zube.
Ga rashin lafiya ga rashin tsaro da w
ajen zama mai kyau
shiyasa na kawota nan ita da nurse, sai dai kuma tunda Khadija ta yi bincike ta gano asalin gaskiya shikenan ta fatattakesu…
Sai da na yi kwana uku tukunna na nemota da kyar.”
Shiruu ya
ɗ
an yi kafin ya
ɗ
aura da cewa
‘’Dan Allah Abba ka
duba lamarin nan..
Mu taru ni da Kai mu ceto rayuwar baiwar Allah.”
Ya ƙarashe maganar cikin ha
ɗ
e Hannuwanshi biyu waje guda kamar zai fashe da kuka.
Numfashi Abban ya fesar
bayan dogon nazari…..
Kafin ya kalli Imam
ɗ
in ya ce
‘’Zan ha
ɗ
a ka da driver
gobe
ku je a yi duk wasu gwaje-gwaje da suka kamata!
Allah ya sanya alkhairi
Allah ya yi maka albarka.
Zan yi wa Daddyn naku magana!
Kar ka damu zai fahimta shima, in sha Allahu.’’
Wani tsananin sanyi ne ya lullu
ɓ
e Imam ,har sai da wasu hawayen farin
ciki suka wanke mishi fuska.
Murmushi kawai Abban ya yi, daga haka ya miƙe da shirin tafiya….
Tsakanin uba da ƴa sai Allah!
Ya san abunda ya yi, ya ke kuma shirin yi
tabbas shine dai-dai amma
kuma a take tausayin ƴar tashi sai ya lullu
ɓ
eshi ya hanashi j
in walwala…
Saboda ya fahimci tunda har Imam ya rufe ido ya sake yi mishi zancen wata bayan ya aura masa ƴarshi ko watanni biyu ba a rufa da yin aurensu ba, to fa hakan ya na nufin ba ƙaramin so ya ke yi wa ita wachchar bafulatana mai tallan Nono ba.
Har g
a Allah, da ya ji maganar ta yi shiru bayan wata
ɗ
aya da yin auren nasa ya
ɗ
auka Imam
ɗ
in ya haƙura ne, ashe abun ya na nan!
Tabbas rayuwar ƴarsa Khadijah
ta na cikin garari…saboda tun shekara
ɗ
aya da ta gabata (a lokacinda aka fara maganar aurensu) har k
awo yanzu,
bai ta
ɓ
a ganin
ɗ
igon son ƴar tashi a cikin idanun Imam ba.
Daddy, babban Abokinsa ne tun yarinta, wanda ba dan albarkacin hakan ba da kuma yadda ya ga Daddyn ya nace da son ya ga ya ƙulla auratayya a tsakanin su tabbas da babu