Showing 39001 words to 42000 words out of 150519 words
waya ya danna kiran Najeeb….
Sai da ta katse ya sake kira nan ma ta kusan katsewa tukunna ya d’auka da sallama…
A hank
ali Yashjub ya amsa,
tun kafin ya yi k’orafi Najeeb ya ce
‘’Sorry, ina wanka ne, yanzun nan fitowa ta na ga wayar tana haske’’
Ya k’arashe maganar yana mai shirin ajjiye wayar dan ya san tunda Yashjub d’in ya ji haka zai ce ‘ok,
Idan ya shirya ya kira sa
kawai.’
Har ya maida wayar kan side drawer sai kuma ya ga still ba’a kashe ba, shiruuu ya d’an yi kafin ya sunkuya ya d’auki wayar ya mayar ya kara a kunnensa, a ransa
yana tunanin ‘shin me yake damun Yashjub haka, ko dai family matter ne? tunda dama ya
ga Daddy ya kira shi d’azun, kuma tunda ya fita ko sallama bai dawo yayi masa ba kiran sa kawai yayi ya ce masa ya wuce!.
It’s very unlike him….’.
Yana cikin wannan lissafin a hankali ya ji Yashjub d’in ya ce
‘’Am..Najeeb, Yaran d’azu ya sunansu?
I mean
, ya sunanta?’’
Shiruuuu Najeeb d’in ya yi ya zaro wayar daga kunnensa ya kalli sunan da kyau ya tabbatar Yashjub d’in ne tukunna ya mayar ya d’an tab’e Baki ya d’aga gira yana murmushi kad’an -kad’an yana jinjina Kai alamun ‘yes’ tukunna ya ce
‘’Okay!!…
’’
sai kuma ya kwashe da dariya.
Da sauri Yashjub wanda dama
tunda ya yi masa tambayar a take ya fara jin inama he can take it back(inama bai yi ba), ya ce
‘’ka ji matsalar ka, ko?
Ba abun da kake tunani bane ba tou, she just looks like someone (ta yi m
in kama da wata) shiyasa nake so in yi confirming (in tabbatar)
Ita d’in ce ko ba ita bace ba, that’s all.”
Cikin son k’ok’arin danne dariyar tasa dan ya lura mutumin nasa har ya dan k’ule, Sir Najeeb
ɗ
in ya ce
‘’Maybe ita ce, a ina ka san wacchar d’in?’
’
Cikin rashin gaskiya Yash ya ce ‘’A uk, neighbor d’in mu ce, amma gidan nasu gaba d’aya sun dawo Nigeria, har ita.
Last year’’
‘’Girlfriend??’’
Najeeb ya sake jeho masa tambayar yana mamakin yadda Yash d’in ya k’irk’iro k’arya haka tashi guda ya zabg
a masa.
Cikin d’an d’aga murya
Yashjub ya ce
“I said neighbor!!(maƙociya fa na ce maka)
Ko ife-ifen d’alibai ya kurmantar da kai ne ban sani ba?.
Maƙociya ce kawai.
ka fad’a min sunan ta kawai mu wuce gurin’’
Ya k’arashe maganar tasa a k’age, dan ji y
ake yi kamar ya shiga ta waya ya zak’ulo sunan nata daga cikin bakin Najeeb d’in.
A hankali Najeeb ya ce
‘’Gaskiya ba ita bace ba!..
Yarinyar da ka gani
ɗ
azu I don’t think ta san ko hanyar airport ma.
ko last time da kyar ta yi registration fa, har aka f
ara exams tana cike crf, da farko ma k’in yi mata signing mukayi
sai da hod ya ce ‘mu yi mata tana da d’an issue’
tukunna’’
Zuwa wannan lokacin Yashjub ya fara ji kamar ya shiga ta waya ya shak’o Najeeb!
Dukda tashi d’aya ya ji damuwa daga jin labarin
nata
amman kuma jan ran da Najeeb yake ta yi masa ya gama k’ular da shi dan haka ya kira sunansa da dakakkiyar murya, ya ce
‘’Najeeb!’’
‘’Na’am,Yash.’’
Najeeb d’in ya amsa
Ya sunan Yarinyar da na gani
ɗ
azu a office d’inka?’’
Sarai dama Najeeb ya ga
no shi, ya fahimci inda ya nufa..
Kwana-kwanar da ya tsaya yi masa ce ta sanya shima ya so ya ja masa rai amma jin yanayisa ya sanya kawai ya hak’ura!
Ya san zai dawo gareshi, soon.
Dan haka kawai sai ya ce masa
‘’Manubiya Musa’’
Ajiyar zuciyar da Yash
ya sauk’e saida Najeeb d’in ya ji,
dan haka kawai ya yi murmushi a ransa
Ya na adduar ‘Allah ya sa su daidaita’
dan ya san idan
Yashjub ya samu ya auri wadda yake so to zai fita daga wannan k’uncin da ya d’aurawa kansa k’arfi da yaji ta dalilin miskilanci
…
Yo miskilanci mana, saboda in ba
hakan ba
Mutum successful kamar Yashjub ace wai ba shi da aiki sai yamutse fuska da fushi da rashin hira da dariya da walwala, kullum…………
Yashjub yana gama jin sunan Manubiya ya yi sallama da Najeeb. ko komawa bai yi y
a kwanta ba
Ya hau instagram ya shiga searching ‘Manubiya Musa’
dan ya san idan ya samu ya ga pictures
ɗ
inta complete maybe zai samu ya
ɗ
’an rage damuwa
ya samu ta daina yi masa yawo a ido da kunne….
Sai dai kuma sam bai samu ba!
Shine twitter!!
Shine F
acebook!!!
Ko ina sai da ya duba amman sam bai samu ba
Dan ko da ace bai santa ba idanuwan waenda ya ke gani masu irin sunan ta sam ba irin nata bane ba…
Dan haka tashi d’aya yake fahimtar ba ita d’in bace ba.
Tunani yayi ‘ko dai ya sake kiran Najeeb ya
tambaye sa ko tana da wani nick name’ sai kuma ya ga in ya yi hakan Najeeb
ɗ
in zai ga zak’ewar sa,
kuma ya san yana tambayar sa ma shikenan
zai fara judging d’in sa, dan haka sai kawai ya hak’ura ya koma ya shiga searching ‘Manubiya eyes’
A tunaninsa m
aybe friends d’inta da hakan suke kiran ta!
Tunda shakka babu Idanuwanta are one in a million.
Ya jima yana Abu d’aya kafin chaaan kuma ya yi shiruuuuu!
Ya fara tunani da auna wawtar sa.
Shiruu yayi shi ka
ɗ
ai!
Yana mamakin yadda ya haukace tashi d’aya, da
n shakka babu wannan d’an k’aramin haukane yake yi…
A hankali ya ajjiye wayar ya dafe goshin sa, sai da ya d’an nutsu tukunna ya ja ya kwanta ya shiga sauk’e ajiyar zuciya a jejjere.
Yana kwanciya tashi d’aya
tunaninta ya dawo masa…
Me yake damun ta?!
M
e ya ke saka ta saurin kuka?!
Me yake saurin breaking d’inta!!!
Ya akayi bata samun kud’in registration da wuri??!….
Runtse idanunsa ya yi da k’arfi
cikin b’acin rai ya yi tsaki!!!
kafin a fili ya ce
‘’Yau ni kam na had’u da aljana’’.
‘’Wacece aljanar??
’’
Muryar Mommy wadda ta shigo yanzu ta daki dodon kunnuwansa.
Sarai, ya ji ta.
Sai dai bai bud’e idanunsa ba ma
ballantana ta yi tunanin samun amsa daga gare shi.
Wani ma
ɗ
aukakin tashin hankali ta danne da kyar, kafin ta k’araso ta tsaya a kansa tukun
na ta sake cewa
‘‘Wacece aljanah??’’
Sai da ya d’an d’auki lokaci
tukunna ya bud’e Idanuwansa ya kalle ta sannan ya ce
‘’Daddy ya ce gobe zai zo, da daddare. Yana buk’atar ganin kowa.
Sannan kin gayawa Yasir da Bakinki yadda kukayi da shi?”.
Cikin in
da inda ta ce
‘’Shi Daddyn me ya ce maka mun yi da shi??
Me yace maka na ce?’’.
Ta yi maganar ta na mai zama a Bakin gadon wajen ƙafafunsa.
Sai da ya d’an yi murmushi kafin ya ce
‘’Nothing.
Ya ce dai kawai ki san yadda za ki yi da Yasir kafin ya zo, dan
idan ya zo a goben baya son jin wata magana game da komai kuma,
akwai important abun da zai kawo shi!
So kar a zo ku bashi kunya’’.
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya ce ‘’sai anjima’’
daga haka ya nufi k’ofa.
Da sauri ta mik’e ta ce
‘’Yash.
Wacece alja
nah?’’
Juyowa kawai ya yi ya kalleta,
kamar zai ce wani abun!
Sai kuma kawai ya sauk’e wata nannuyar ajiyar Zuciya
daga nan ya sa Kai ya fice ya barta nan a tsaye……
Gaba d’aya Kan Mommy d’aurewa ya yi, ta rasa mafita game da lamarin Daddy da kuma Yas
hjub, da su da maganganun su duk sun taru
sun d’aure mata Kai kwarai.
…….
Kamar yanda Daddy ya fad’a, washegari da daddare
bayan sallar isha’a,ya zo.
Tare suka shigo da Yashjub wanda dawowar sa daga masallaci kenan ya had’u da su suna parking dan haka
ya jira suka shigo tare.
Suma gama zama ya haura sama domin yana son magana da Mommy kafin ta sauk’o saboda kar ta ga bambarakwai.
BULAMA ✍
️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*13*
Waya ya same ta tana yi, da alama da Unc
le d’intane
(yayan Abban ta….)
Yanayin maganan nata ya sa ya yi tunanin maybe ko k’ara ta kai.
A hankali ya nemi guri ya zauna yana mai lumshe idanuwansa a ransa ya ce
‘’In ban da abun Mommy, ta bar Abb’oi ya huta mana, Mutum ko gani bayayi sosai shekar
u sun ja amman tana d’aga masa hankali, tabbas shiyasa bata shiri da ya’yan da jikokinsa
dan sun lura kashe musu shi take k’ok’arin yi da tension d’in matsalolin ta……”
‘’Yash!’’
Muryarta ta katse masa tunani.
A hankali ya bud’e idanuwansa
kafin ya mik’e
ya k’arasa bakin gadon ya zauna ya ruk’o Hannayenta.
Tunda ta ga yayi mata haka
ta fahimci abu mai matuk’ar mahimmanci zai fad’a mata,
dan haka ta tarkata ilahirin hankalinta zuwa gare sa,
kirjinta yana mai dukan uku-uku.
Gaba d’aya tashi d’aya sai tau
sayin ta ya lullub’e sa, dan haka ya sake runtse Hannuwanta a nasa tukunna ya fara magana
‘’Mommy dan Allah ki yi hak’uri,
duk abun da zan fad’a miki yanzu inaso ki danne Zuciyarki, ki yi
hak’uri, ki fahimce ni’’.
Zuwa wannan lokacin gaba
ɗ
aya hankalin
Mommy ya gama tashi, da kyar ta samu ta iya ce masa
‘’in shaa Allah, Yash’’.
A hankali ya ce ‘’Su Daddy sun zo, suna k’asa shi da bak’uwa,
mun samu k’arin member a family d’in nan, jiya…….
Inaso ki fahimci ba wai saboda kun samu matsala ne shiyasa ya yi
miki kishiya ba, dama chan akwai plan d’in b’oyewa yayi.
Nima ban sani ba sai last week
But I think an d’an matso da d’aurin auren kusa saboda a yadda na sani kamata yayi ace yanzu saura two weeks.
Mommy dan Allah ki yi hak’uri
na san dole za ki ji babu
dad’i, ni kaina ina jiye miki, kinga dai bani da ko budurwa
amman ko tunani na yi
‘For instance (misali)ace
Inada budurwa, ta je tana kula wani’ to bansan ya zanyi ba!!!
Ballantana kuma ku da ku ke ma’aurata.
Ki yi hak’uri, na san babu dad’i
amman a ya
dda Daddy yake a yanzu
Idan kika b’ata masa rai tabbas ban san kuma mai zai yi ba!.
Ki yi hak’uri Mommy na san kina hak’uri da Daddy amma dan Allah ki ƙara ki sake hak’uri!!!
For us ….’’
Tunda ya fara magana ta kafe shi da idanuwa ta kasa motsi, sai da y
a sake runtse Hannunta dake cikin nasa
tukunna ta yi fir-gi-git!!!
Tabbas they saw it coming(dama sun gani), amman ba su yi tunanin kwana kusa ba!
“Innalillahiwainnailaihirrajiun”
Ta shiga ambatowa a k’asan ranta..
Ta manta rabon da ta shiga tashin hankali
Irin wannan a rayuwarta, sam ta manta!!
Ta ma kasa kuka…..ji take yi kamar an tsunduma Zuciyarta a cikin talge! Saboda tsabar azabar da tsananin tashin hanakalin
ya tsunduma Zuciyar tata a ciki.
‘’Mommy!’’
Yashjub ya sake kiran sunanta.
A hankali sannan
da kyar ta k’ak’alo wani murmushi wanda ya fi kuka da ife-ife ciwo!
Tabbas wannan babban tashin hankali ne da aiki ya same ta, amma
ta wata fuskar kuma dama ce ta samu na gyara tsakaninta da Yash, dan yadda ta hango tsantsar tausayinta da kulawa a gareta
A idanuwan Yashjub yau
wataki’ila wannan auren da Daddy yayi ya janyo mata kulawa da shaƙuwa a wajen d’annata. Ta lura kamar yadda kishi yake weakness d’in Daddy haka Yashjub shima…
A hankali ta ce
‘’Zan sak’k’o Yashjub, ka je k’asa kawai, zan taho.
I ne
ed some time alone(ina buƙatar kasancewa ni ka
ɗ
ai, yanzun.”
Har zai mik’e sai kuma ya janyota zuwa jikinsa ya yi hugging nata ya shiga bubbuga mata baya alamun rarrashi…
kafin ahankali ya ce
‘’Ki yi hak’uri Mommy, Allah zai baki lada’’
Daganan ya cikat
a ya mik’e ya fita.
A bakin k’ofar d’akin suka yi kici
ɓ
is shi da Baaba Larai alamun shiga take shirin yi shi kuma ya fito.
Murmushi kawai ta yi masa daga nan ya nufi k’asa inda su Daddy suka jiran su, ita kuma ta shige.
*Baaba Larai* cousin d’in Mommy ce
, kamar yadda Mahaifiyar Mommy ta haifesu su biyu kawai (ita da Ammin kausar)
Haka itama kakarta ta haifi maman ta da maman Baaba Larai kawai, sai dai ita Baaba Larai ita kad’ai aka haifa sannan har gobe Allah bai bata Mijin aure ba!!
Tun tana budurwa dam
a bata da samari….
Idan k’awayenta suka yi aure
sai ta koma wajen k’annen su da k’awance!!
Hatta da niece d’in k’awarta Baaba Larai ta tab’a yin k’awance.
A lokacin da ta kai shekaru talatin a duniya sai y’an k’auyansu suka fara d’aura mata sharrin *Maita
!* wataƙila ko dan sun ganta fara sol ga gashi sannan kyakkyawa amman babu Miji ne, oho.
A lokacin Mahaifiyarta ta jima da rasuwa,
shiyasa Mahaifiyar Mommy ta d’aukota daga gaban Mahaifinta da Matarsa ta ce za ta ci gaba da rik’eta, dan sharrin dama ya sa
mo asali ne daga bakin Matar uban.
A yanzu kuwa iyayennasu duk sun rasu shiyasa suka rungumi juna su uku
Ita(Mommy), Baaba Larai da kuma y’arsu Kausar.
Badaban shi Kansa Yashjub ya san Yahanasu y’ar kishiyar Mommy ce ba to da sai ya ce
‘Maybe a wajen B
aaba Larai ta gado rashin auren’
amma dukda haka a kullum adduarsa itace “Allah ya sa kar y’ar uwar tasa ta k’are kamar Baaba Larai’’
Dukda kuwa cewa
‘ita Yahanasu tanada samarin
kawai idan an zo maganar aure ne ganga-ganga da ikon Allah sai wani abun ya
zo ya tarwatsa…….’
Amma still yana yi mata adduar kar ta ƙare kamar Baaba Larai, a kullum da ko da yaushe….
‘’Tana Ina?’’
Muryar Daddy ta katsewa Yashjub tunani.
‘’Tana sauk’owa’’ ya basa amsa yana me k’arasawa cikin parlourn sannan ya nemi waje ya zau
na suka sake gaisawa da Anty Amarya. Dama shi ya riga ya santa dan employee d’insu ce, kawai dai bai san akwai abu tsakaninta da Mahaifin nasa ba sai yau da ya ganta a matsayin Matar ubansa.
Kafin su Mommy su sauk’o, Daddy ya kira Yadira ya ce mata ta kir
awo mada kowa hatta drivers da masu gadi da Kausar….
Yassir ne kawai bai hallara a wajen ba saboda har zuwa wannan lokacin bayan sati biyun da ya shafe baya gidan bai kai ga kenan dawowa ba, ya ma kashe wayar da ya tafi da ita gaba d’aya.
Mommy bata wani
b’ata lokaci ba suka sauk’o itama tare da Baaba Larai!
She looks calm amman fa ana ganin fuskarta za a fahimci ta yi kuka.
Tana zama Daddy ya umarci
Yashjub da ‘ya bud’e musu taron da addua’
Ana shafawa ba tare da b’ata lokaci ba
Ya gabatar musu da Haj
iya Saddik’a a matsayin Amaryarsa, kafin ya d’aura da cewa
‘’Na san ta, wajen aikinmu
ɗ
aya!
Shekaru sha biyar kenan muna tare da ita…
Mijinta ya rasu, shekaru ashirin da suka wuce. Tanada Ƴaƴa Mata, guda biyu.’’
Daga haka ya ce
‘Ya na so tun daga kan Ya
hanasu har izuwa kan Yadira
kowa ya bata girma da respect,
har masu aiki yana so duk kalar respect d’in da za su bashi to itama su bata, baya so ya ji wani case ko ya ga ana gwada mata rashin d’a’a , in kuwa hakan ta faru to zai sab’awa ko ma waye’.
Masu
aiki, Yahanasu sai Yashjub ne kawai suka ce
‘’InshaaAllah Daddy’’.
Daganan masu aikin suka yi introducing kansu sannan suka sake gaisheta.
Sab’anin su Yasmeen waenda suka d’auke Kai ba tare da sun ce mishi uffan ba.
Baya son creating scene shiyasa kawa
i ya rabu da su!
Da niyyar cin k’aniyar su idan ya samu lokacin su.
Cikin kulawa ya juya ga Hajiya Saddiqa
Itama ya ce ‘’ta d’auki Ƴaƴan nashi kamar nata,
In sha Allah ba zata samu matsala da su ba ‘’.
A hankali ta na murmushi ta ce. ‘’InshaaAllah’’.
Sai a sannan Yasira ta daure, da mugun kyar ta ce
‘’Daddy tou me zamu dinga ce mata’’
Cikin jin dadi da sauri ya ce
‘‘Ummi.
Ƴ
aƴanta da Ummi suke kiranta’’
Murmushi Yasmeen ta yi,
ta ce
‘’sannu da zuwa Ummi,
We are glad to have u (Mun ji da
ɗ
in zuwa
nki cikinmu)‘’.
Cikin tsananin jin dad’i Hajiya Saddik’a ta ce
‘’Nagode y’ar albarka’’.
Saboda da farko gabanta har ya d’an fara fad’uwa, dan ta yi tunanin Yasira za ta amsheta fiye da yadda ta ga ta yi mata duba da yadda suka riga suka san juna tun a of
fice, shiyasa ta yi mamakin yadda suka yi mata ita da y’an uwanta!
Gasu duk mata.
Bayan an sallami masu aikin,
hira ce sosai ta biyo baya
tsakanin Yasira,Yasmeen da Ummi!
Mommy ma tana d’an sako musu Baki sama-sama…
Kafin daga bisani Daddy ya ce “za su
wuce.”
Sun yi mamaki sosai da sukaji Daddy ya ce “ba a nan za ta zauna ba!
Already an