Showing 135001 words to 138000 words out of 150519 words
gero tukunna suka fito.
Inna ma tun
ɗ
azu an bata nata abun karin, an shirya ta.
Ganin sun kusan kammalawa ne ya sanya Ya Musbah mik’ewa ya fita domin ya dubo ko Nafi’u ya zo, in kuma bai ƙaraso ba sai ya kira sa.
Sai da Muhsin ya mik’e ya fita tukunna Jidda ta kalli Manu ta ce “na d’auka Muhsin zai yi fushi ko kuka da aka ce an fa
sa kaishi makaranta, ashe ya girma yayi hankali yanzu’’
Murmushi Manu ta yi kafin ta ce
‘’Ya ban tausayi, Allah ubangiji ya bamu ikon sanya shi a makarantar’’
‘’Ameen’’ jidda ta ce, daganan ta zare hannunta a abincin ta d’an matsa kusa da Manubiya sos
ai sannan ta ce ’’yanzu ya za’ayi? Za ki siya masa ne a hanya tukunna ku wuce office d’in nasa?
Dan gaskiya bai kamata ku had’u ba tare da kin bashi
ɗ
an gift ba’’
‘’Babu gift d’in da zan bashi’’
Manu ta fad’a hakan ba tare da ta kalleta ba.
Da sauri Jid
dah ta d’an zabura sai kuma ta ce ’’amma wasa kikeyi ko?’’
Sai a sannan Manu ta d’ago kyawawan idanuwanta ta kalleta tukunna ta ce
‘’Da gaske nakeyi, ya riga ya fara rok’on tukuici da kanshi, kinga kuwa ai ya yi wa kansa’’
Dariya Jidda ta yi kafin ta c
e ‘’kamar yaya?’’
……yadda su ka yi da shi jiya akan batun tukuici Manu ta kwashe tsaf ta gayawa jidda…
Kafin ta d’aura da cewa ’’tun d’azu nake ta faman fargaba,
ban san me zai ce yana so ba, na riga na yarda da shi akan
ba zai cutar da ni ba,
amma d
ukda kawai ni I’m so nervous( ina cike da fargaba)”
Ta k’arashe maganar tata tana mai mayar da idanunta kan jellof d’in taliyar da ke a gaban su.
Shiruuu Jidda ta yi, ta zuba mata idanu, har sai da Manubiyan ta gaji dan kanta ta d’ago ta kalleta
Tukunna
Jidda ta yi murmushi kanta tsaye
ta ce ’’kema kina son shi ko??’’
Wata mahaukaciyar zabura Manu ta yi a lokaci guda ta yi amfani da d’ayan Hannunta na hagu ta toshema Jidda Baki, ta fara rarraba ido a cikin d’akin.
Dai-dai nan Baba ya fito daga toilet d’
in sanye da kayan da ya chanja a ciki wanda ya cire kuma riƙe a hannunshi tare da brush da vaseline d’in shi.
Kallonsu ya yi kafin ya ce ’’d’azu Kaka Mallan ya kira akan yana buk’atar ganin mu ni da su Uncle da gaggawa. idan Likitar ta zo
ku yi komai i
n kunga ban dawo ba sai ku wuce kawai ba sai kun jira ni ba’’
Daga haka ya ajjiye kayan wankin a wajen da suke tarawa ya ajjiye brush da Vaseline d’in suma a wajensu sannan ya wuce yana mai cewa “idan na dawo na ci nawa abincin’’..
Yana fita Jidda ta ce
’’Adda Manu yanzu y….’’
Cikin katseta Manubiya ta ce ’’Jidda dan Allah kar ki yi min haka, kar ki ƙarasa rikitani’’
Dariya Jidda ta yi kafin ta ce ‘’ki tsaya tou mana ki ji abunda zan fad’a ma’’
Kamar Manubiya za ta fashe da kuka ta ce ’’Plss Jidda….’
’
Daganan ta mik’e ta fad’a toilet ta wanke Hannu tare da kuskure Bakinta sannan ta d’auro alwallah ta fito.
Fitowarta ke da wuya, wayarta ta d’auki k’ara…
Tana dubawa ta ga Yash ne me kiran.
Batayi mamaki ba, dan itama tunanin sa take yi dan haka ta d’
auka a hankali ta kara a kunnenta….
…bayan kashe mata jiki da doguwar gaisuwa, ya ce
mata ’’Dr Sofia fa tana waje, ta zo tun
ɗ
azu’’
Da “to” ta amsa masa, tukunna suka yi sllama daga haka ta nufi k’ofa da niyyar fita ta je ta shigo da ita amman sai suka
yi karo da ya Musbah da ya Nafi’u dan haka ta gaya musu ita kuma ta koma ciki.
Su ne suka je suka shigo da baturiyar likitar mai suna Sofia
matar mai kirki sosai da bagwariyar Hausar ta…
Sama da awa d’aya ta d’auka tana examining (gwadawa da bincika )
innar kafin ta ce ’’su wuce asibitin ta’’
A inda ta gaya musu asibitin nata yake ya baud’e sosai da office d’in Yashjub!
Gashi sun riga sun ce masa za su zo, kuma shi kansa Ya Nafi’u ya kamata ace yana wajen interview
ɗ
insa ma yanzu haka…shiyasa suka yank
e akan
‘Ya Nafi’u ya tafi interview d’inshi,
Manubiya ta je ta yi wa Yashjub godiya a madadin dukkansu sannan ta gaya masa dalilin da ya sanya ba su zo su duka ba.
Ya Musbah shi kuma ya tafi asibiti tare da Inna.
*MANNUBIYA*
*45*
A inda
ta gaya musu asibitin nata yake ya baud’e sosai da office d’in Yashjub!
Gashi sun riga sun ce masa za su zo, kuma shi kansa Ya Nafi’u ya kamata ace yana wajen interview
ɗ
insa ma yanzu haka…shiyasa suka yanke akan
‘Ya Nafi’u ya tafi interview d’inshi,
Manub
iya ta je ta yi wa Yashjub godiya a madadin dukkansu sannan ta gaya masa dalilin da ya sanya ba su zo su duka ba.
Ya Musbah shi kuma ya tafi asibiti tare da Inna.
Babu kalar lallamin da Manubiya ba ta yi wa Jidda akan ‘ta zo su je tare’ ba, amma k’iri-k’i
ri Jidda ta ce mata ‘’A’a!, idan na bi ki wa zai kula da su mai sunan baba da Muhsin?’’
Da sauri Manubiya ta ce
‘’To duk ku zo mu tafi tare’’
Cikin tarar numfashinta Jidda ta ce ‘’kuma in Baba ya dawo sai ya ga ba kowa?’’
Haka suka yi ta fama, dan d
uk ta inda ta b’ullo sai Jidda ta toshe.
Ya Musbah ma bayan Jidda ya bi ya ce ’’ko baya ga hakama ta ya an cewa Yashjub d’in za su zo su uku yanzu kuma kawai yaga Yara.
Kawai ta je d’in in yaso ta ce masa inshaaAllah shima shi da Ya Nafi’u suna nan zuwa’’
.
Hakanan Manubiya ta fita ko sallama bata yi wa Jidda ba,
Jiddan tanata tsokanarta
k’asa-k’asa
da
‘‘Oga wife’’
Ita dai Manubiya bata kulata ba, ta barta kawai akan sai ta dawo sai su yi ta.
Har ta Isa company d’in kuwa tana fargaba! bata san
tuku
icin da zai ce yana so ba
sannan ga matsayar da Jidda ta riga ta gama cimmawa,
da kuma abunda ita kanta zuciyarta take raya mata
shiyasa gaba d’ayanta ta bi ta sake diriricewa.
Yau tana zuwa receptionist d’in ya ce mata ‘’an ce in ta zo kawai ta wuce o
ffice d’in ceo, ba sai an rakata ba’’
‘’Okay’’ kawai ta ce,
daga nan ta nufi office d’in nashi dake a chan sama kai tsaye.
A bakin glass door d’in
ta tsaya ta d’an yi knocking glass d’inc tukunna ta tura ta shiga da sallama.
A zaune ta sameshi ya k’
urawa k’ofar ido…fuskarsa tamau kamar bai tab’a dariya ba, dan har sai da ya d’an bata tsoro amman kawai sai ta dake ta k’arasa ta nemi waje ta zauna, a hankali ta ce ’’ina kwana’’.
Tunda yake a rayuwar sa bai tab’a ganinta da mayafi ba sai yau, mayafin m
a kuma mai shara shara….sanye take da doguwar riga d’inkin Ashape, atamfar army green da d’an kwalliyar milk da black, rigar bata wani kamata ba
amma yanayin jikinta da kuma mayafin da ta rufa (black clour)wanda bata saba sakawa ba ne
ya taimaka wajen fi
to da surar Jikin nata, mayafin nata babba ne sai dai ya d’an yi shara-shara.Ta yi normal d’aurin d’ankwalinta ta gaba ta baya kuma ta nannad’e sa akan ribbon d’inta wanda ta tufke uban tulin gashinta da shi, sannan ta d’aura mayafin nata akai.
Kwalli, pow
der sai man leb’e ne kawai a fuskarta
amman ba k’aramin kyau ta yi ba,
dan har wani fisfisga Yash ya ji numfashinsa yanayi….
‘‘Yanzu duk inda ta bi ta wuce tun daga gidansu har nan haka Maza suka ganta kuma suma haka suka dinga ji kenan?
bata tab’a saka m
ayafi ba sai yanzu da ya ke jin masifaffen kishin ta’’
Yashjub ya aiyyana hakan a cikin ransa.
A b’angaren Manubiya kuwa ita kanta tun d’azu a takure take dan ba wani sabawa ta yi da mayafin ba, ta yi kuskure ta bar hijabanta duk sun yi datti, kuma bata s
amu sun yi wanki da wuri wannan satin ita da Jidda ba, sannan ga abunda ya zo ya faru gaba d’aya ya d’auke musu hankali shiyasa basu nutsu ba ma ballantana ayi maganar yin wanki.
A hankali ta d’an kalleshi ta ga still ita yake kallo, dan haka ta sake yin
k’asa da kanta ta ce ’’ina kwana’’
Kamar wani mai jin bacci haka ya lumshe lumsassun idanuwansa ya had’iye wani k’ululun abunda ya tokare masa mak’oshinsa yake shirin hanasa numfashi
tukunna ya ce
‘’Me ya faru da hijaban ki yau?’’
Yayi mata tambayar yan
a mai matsar da computer dake a gabanshi gefe wanda hakan
ya bashi damar sakata a gaba ya tsura mata ido sosai.
Gaba d’aya diriricewa Manubiya ta yi, sam ta kasa magana
dan haka kawai sai ta sake yin k’asa da kanta…
Zuwa yanzu ta fahimci wataƙila mayaf
in da ta rufo ne ya b’ata masa rai shiyasa duk sai ta ji ba dad’i, dan sam bataso ta zamto silar b’acin ransa ta ko wacce siga. Ga kuma tunanin ta na ‘maybe kishina yakeyi’
gaba d’aya sai ya sake kashe mata jiki.
Yanayin yadda ta yi ‘k’asa da kai ta yi s
hiru’ ne ya sanya yayi tunanin ‘maybe ranta ya d’an
b’aci’ne, ga kuma yadda ya tamke fuska ko maraba bai yi mata ba wanda shi kanshi sai yanzun ya lura da hakan, shiyasa tashi d’aya shima duk sai ya ji ba dad’i dan haka ya sauk’e wata y’ar siririyar ajiy
ar zuciya kafin ahankali ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna yace’’Sorry!(yi haƙuri)”
kawai.
Duk shiruu sukayi kafin ya sake cewa
‘’Ya jikin Baba??’’
Ba tare da ta d’ago fuskarta ba sannan a hankali ta ce “Alhamdulillah’’
Murmushi ya yi kafin ya ce
‘
’Fushi kikayi?’’
Girgiza kai ta yi da farko sai kuma bata san ya akayi ba amman kawai sai ta tsinci kanta da ce masa
‘’’(yi haƙuri)!’’
itama.
Murmushi mai sauti ya yi kafin yad’an had’e rai tukunna ya ce
‘’Kar ki damu next time idan kika sake saka wan
nan abun, ni kad’ai na san me zan yi miki’’
Ya k’arashe maganar yana dariya ahankali ahankali.
Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba itama kafin a hankali ta fara magana
“Sofia ta zo, tun a yau kawai har ta k’ara mana haske akan yadda za mu ding
a yi wa Inna, na ji tace kullum itama za ta dinga zuwa ko?’’
‘’Um’’
kawai yace
Idanunsa akanta.
A hankali ta ci gaba da cewa “ban samu na yi maka godiya yadda ya kamata ba,
da tare za mu taho da su Ya Musbah tou kuma dole sai da shi tukunna za’a kai In
na asibiti, shiyasa ya ce in baka hak’uri in ce suma suna nan zuwa kuma mun gode sosai
Baba!Jidda!da Muhsin suma duk sun ce ayi maka godiya…
Allah ya saka maka da alkhairi’’.
Murmushi ya yi kafin ya ce ’’Allah ya k’arawa su Inna lafiya, bana buk’atar god
iya daga gareki ko Ahalinki..
Dan Allah ki cewa su Musbah suma ba sai sun zo ba…’’
A hankali ta ce ’’a ganina ya zama dole mu yi maka godiya’’
Jin ya yi shiru yanata kallonta ne kawai ya sanya ta ce ’’once again mun gode, Allah ya biyaka.”
Kamar wadda b
a zata yi magana ba sai kuma ta ce ’’zan tafi’’
ta fad’i hakan tana mai sunkuyar da kanta k’asa sosai.
So takeyi kawai ta tafi tunda ta gama abunda ya kawota, maganar aikin da ya ce akwai yau dama ta san kawai jan magana ne.
A hankali ya sauk’e nannauyar
ajiyar zuciya sai kuma ya sunkuyar da kanshi yana murmushi
kafin ya d’ago ya ce ’’nima, a ganina ya zame min dole in bawa abunda nake tsananin k’auna kariya.’’
‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’
Haka Manubiya wadda ta runtse idanuwanta tashi d’aya t
a shiga nanatawa a cikin zuciyarta, tana mai jin wani kalar fad’uwar gaban da bata tab’a ji ba tunda take a rayuwarta.
A take gaba d’aya ilahirin Jikinta yayi wani irin sanyi, kamar babu jini ko
rai a k’afafuwanta haka ta ji..
dan tabbas inda ace za a tsi
kara mata allura a wajen tou da ba lalle ta ji ba!…
A haƙiƙanin gaskiya ba ma ta jin dukkannin ilahirin Jikinta saboda tsabar yadda ta
ɗ
auke lokaci guda koina ya yi mata sanyi.
Dakyar ta samu ta fara dawowa dai-dai ta d’an fara jin jinin jikinta yana kai m
ata a jikin nata, sai kuma ta d’an fara kyarma
ahankali ahankali.
Ganin yadda ta runtse idanunta ta k’ame a waje d’aya ne
ya sanya Yashjub ya furzar da wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya tashi ya koma inda take ya zauna a kujerar da ke a gefenta.
Ka
mar jiya yau ma yadda ya ga ta zabura sai da ta kusan bashi dariya…Kamar zata fashe da kuka haka ta juyo ba tare da ta yarda sun had’a ido ba ta ce ’’Dan Allah ka daina, banaso.’’
‘’Bakya so in ce miki Ina sonki?
K’arya kike so in yi miki?
Ko so kikeyi in
ci gaba da azabtar da zuciyata ta hanyar hanata muradin ta??’’
Ya ce da ita yana kallonta.
Mik’ewa Manubiya ta yi da wani kalar sauri, ta juya za ta fita amma kafin ma ta yi taku d’aya kawai sai ta ji ya damk’o Hannunta!.
Da sauri ta juyo sai dai kafin
ma ta ce wani abun tuni ta ji hawaye sun b’alle mata.
A hankali Yashjub ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya lumshe idanuwansa ya bud’e tukunna a hankali ya mik’e tsayen shima still yana rik’e da Hannun nata wanda
ya ke jinsa kamar kar ya cik
a kamar ya rik’e har abada kar ya barta ta je ko ina, ga wani musulmin taushi da d’umi da Hannun nata ya ke ƙunshe da! Wanda atake suka taru suka d’imauta sa.
Da kyar ya iya cewa “ki yi
hak’uri Mannubiya in abunda na gaya miki ya b’ata miki rai ne ki yi
hak’uri,
Dan Allah.
Ba na son ganin hawayenki, ba ki san yadda nake ji a cikin raina ba, pls ki daina kukan nan….burina in sanya ki farin ciki in kula dake a ko da yaushe,
ba zan so in zamto silar zubar hawayenki ba, kar ki sa in kasa yafewa kaina pls.
A
ganina ba laifi bane idan na gaya miki sirrin zuciyata shiyasa tun jiya nace miki alfarma da kuma tukuici, saboda na san dama ba lalle kema kina jin abunda nake ji ba, amma in har kikayi min wannan alfarmar kika bani wannan damar kika amince da ni kika ba
ni damar kasancewa tare da ke har abada
Mannubiya
kin gama min komai.
Tun ba yau ba a matse nake, inaso in faiyyace miki sirrin raina, inaso kuma in ji naki,
Inaso in ji abunda yake cikin zuciyarki kema gameda ni, amman tabbas a yanzu ina jin tsoro sani s
aboda hawayen nan naki da na gani ba alama ne mai kyau ba!..
Dan haka in har kin san amsar da za ki bani ‘No’ zata kasance, to na rok’e ki da girman Allah kar ma ki ce min komai, ki je ki sake tunani kawai
dan tabbas na san zan iya rasa raina idan kika ce
mini
A’A …..’’.
Bata ce dashi komai ba, bata ma da niyyar cewa komai, kukanta kawai take yi tana d’an k’ok’arin kwace Hannunta daga cikin nasa.
A hankali ya lumshe idanunsa yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya bud’e ya d’an sunkuyar d
a kanshi k’asa..ba abunda ya tsana a ynzu irin kukan nan da takeyi, sam ko da wasa baya son ganin hawayenta…Shiyasa ya bud’e idanunsa ya d’an runtse hannunta da ke a cikin nashi sannan a hankali ya sake matsowa kusa da ita, ya d’aga d’ayan Hannunsa wanda b
a ya riƙe da komai, ya kai dai-dai setin fuskarta.
Tabbas ta fahimci so yake ya goge mata hawaye, dan haka cikin kuka wanda yake d’auke da b’acin rai ta ce “iyakar Hannuna da ka rik’e bai ishe ka ba??’’
‘’Oh no
(Wayyo)”
Yashjub ya fad’i hakan a fili, d
an shi wallahi sai yanzu ya fahimta ya kuma fara ganewa…
Shi fa Indai yana gabanta to mantawa yake yi da kowa da kuma komai.
Har ga Allah bai san lokacin da ya damk’i Hannun nata ba da farkon da kuma ya rik’e d’in sam sai ya gagara saki.
“Damn it!”
Ya fa
d’a a chan kasan ranshi yana jin takaicin kanshi,
dan tabbas ya san ya kwasa.
Da ikon Allah kuma gashi har zuwa wannan lokacin ya gagara sakar mata Hannun nata yana nan riƙe da shi gam.
Da k’arfi Yassira ta daki glass d’in k’ofar wanda hakan yake nuni d
a alamun knocking…
A tare gaba d’ayan su suka d’aga Kai suna kallon k’ofar shigowar.
Sun yi mamakin ganin Kausar da Yassira a tsaye a cikin office d’in, dan basu san lokacin da suka k’araso ba ballantana su san lokacin da har suka shigo.
Da sauri Manu
biya ta juya, ta goge hawayenta, daganana bata sake yarda ta juyo ba.
Cika mata Hannu